AMATULLAH

Chapter 10

by @ameerahfarouk

Chan sai idea n zuwa gidansu fatima sagir tazomani duk da nasan gidansu zuwa gidanmu da dan nisa . babu yanda na iya ahaka naci tafiyata na koshi har na isa gidan . nayi knocking sai kuma nayi sa'ar fatima sagir ce tazo tana tambayar"waye?" 


amsa mata nayi da cewa "Amatullah ce budeman" budemani kofar tayi tareda cewa " oyoyo su Amatullah yau wace rana banzaci zaki kara zuwa gidannan ba wlh !" cike da murnar ganina da tayi .


nace mata " hmm nidai yanzu dan Allah kunada ruwa atankin ku? fatima sagir tace " munada ruwa yanzunnan ma ba dadewa yacika "


bucket din hannuna ta amsa tare da nufar gurin famfon gidansu da tayi ta bude famfon ta taraman ruwan yacika ta kulle famfon ta cemani "gashi mamarmu batanan da sai inrakaki" 


"babu komai wlh ba sai kinraka ni ba inda nake debo ruwanne famfon yaballe shiyasa, zani dawo fa inkara dibar wani ruwan " 


fatima sagir tace "ayyah toh shikenan sai kindawo" bucket din na dauka najuya nafita gidan . ina tafe inata tunanin irin wahalar da zani sha ayau . 


isa nayi gida na iske inna kande zaune akan tabarma tana jin radio ganin shigowata ne yasa ta rage volume din radio n ta kalleni tareda tambayata da tayi "kin samo ruwan koko ? " Eh" na amsa mata dashi . kara tambayata tayi cike da tsangwama " ina kika samo shi ?" nabata amsa da cewa " wani gidane chan gangare.



"kin kyautama kanki " tafada tare da kara volume din radio n tacigaba daji . nufar robar da nake sama ruwan kullum nayi na daga bucket din na juye ruwan cikin robar na kuma juya nakara fita daga gidan ,haka nayita dibo ruwannan har saida na cika komai sannan . 


Har mamarsu fatima tadawo daga inda taje tacema fatima taruka rakani muna  kai ruwan tare tana kama mani bucket din. Fatima sagir taruka Kama mani bucket din muna tafe muna labari ni da ita . amman sai nace mata bazamu ruka idawa gida da ita zata  tsaya abakin corner idan najuyo ruwan sai in sameta achan . guduna kada inna kande tagane tayani dibar ruwan akeyi taji haushi ta hukuntani tananne ma Allah ya taimakeni naji saukin dibar ruwan . 


gama dibar ruwan mukayi nacema fatima sagir, bucket din karshe ne muka dauko  mukayi bankwana da ita tajuya ta tafi nikuma na karasa isa gida da ruwan .sallama nayi inna kande ta amsamani tareda cemani "ni kiyi sauri ki karasa dibar ruwannan dan nafara jin yunwa gaskiya" cike da tausayin kaina na cemata "Ai nagama ma diba wannan ne na karshe " 


amsa tabani da cewa " ai ko baki gama ba ma daman aje shi zakiyi ki dauramani abinci inyaso idan kin gama dafa abincin kin karasa dibo ruwan" juye ruwan bucket din nayi aroba sannan na fita waje na tsinto ledoji na hura wuta amurhu , na daura abincin .  

har abincin yayi na sauke shi nakuma kira inna kande tazo taraba . miko mani kaso tayi wanda baya isata kamar na kullum da take bani . na amsa nakoma gefe naci abincin nayi yan lomomin da nake yimashi na cinyeshi dandanan . tadauki wanda tajuye tashiga daki dashi. 


Haka nayita wahala ahutunnan har hutun yakare . inda nasamu Allah ya taimakeni babu dadewa aka gyara famfunan gurin da muke dibar ruwan hakan ne yasa nakoma dibar ruwana gurin duk da shima gurin akwai yar tafiya daga gidanmu amman bai kai zuwa gidansu fatima sagir nisa ba . 


Aka koma school muka cigaba da inda muka tsaya nakuma cigaba da zuwa 1st position a class dinmu aka cigaba da bani kyauta . amman wannan karan sai naruka ba fatima sagir kyaututtukan tana ba mamarsu ta ajiye mani su . 


Lokacin da nake da shekara sha hudu ne inna kande ta haifi hafsat Sai kuma aikina yakaru ga kuma rainon hafsat da nakeyi wanka kawai inna kande ke yima hafsat ta shiryata . haka zata tulomani kayan wankinta ga nata ga na hafsat ahaka kuma zani amsa in wanke babu yanda na iya . idan kuma inna kande taga alamun nagaji sai taruka duraman ashar tana dukana tace sai na karasashi  takuma yi creating wani aikin ta bani inyi .

 
Tun hafsat na ganin inna kande tana dukana bata fahimtar mi akeyi har tazo tafara fahimta idan inna ta dukeni sai tayita yin kuka ina kuka itama tana kuka . 


Lokacin da hafsat tana da shekara biyu ne wata ranar asabar inna kande ta aikeni kasuwa inyimata siyayya tabar hafsat adaki ita kuma ta shiga toilet . ni kuma ganin anbar hafsat ita kadai ne yasa na sabeta na goyata na kama hanya muka tafi kasuwa ba tareda inna kande ta sakani yin hakan ba . 


Komawata gida kenan na tarar da inna kande nata uban kuka ga baba da yake agefenta ga kuma matan unguwa da suketa rurruketa suna ta faman rarrashinta. 


Karasa shiga gidan nayi jikina asanyayaye da hafsat dake goye abayana . shigarmu gidan ne yasa hankalin kowa ya koma akaina   tashi inna kande tayi da saurin ta karasa inda nake tareda yayeman hijabin da take jikina . hafsat tagani goye abayana ta shafa fuskarta sannan ta kwance zanin ta ansheta . 


tsallake kowa tayi daga baba har sauran matan unguwarmu da suke bata hakuri ta nufi daki tashige ta barmu ni dasu atsakar gida ba tareda tabude baki tayi magana ba. 


Hankalin baba ya tashi sosai ganin shirun da inna kande tayi batace komai ba . nima hankalina duk sai ya tashi nayi tsaye chak ni ban zauna ba ni ban karasa shigar da nakeyi cikin gidan ba.