AMATULLAH

Chapter 11

by @ameerahfarouk

Dakin inna kande baba ya nufa ya daga labulen dakin ya shiga cikin hanzari . matan unguwa ne da na iske suna bata hakuri ne sanda muka shigo naji sunata hamdala "Alhamdulillah Alhamdulillah" wata daga cikinsu tace " kunga ikon Allah ko ? da har an fidda rai da yarinyarnan ashema tare da yayarta suka fita kai Allah mun gode maka" 



ni dai sai zara idanu kawai nakeyi nayi tsaye kamar icce  ina tunanin halin da zani shiga . fitowa baba yayi daga dakin inna kande yashiga dakinshi.


sauran matan suka tashi suma tare da nufar dakin inna kande da sukayi .suka tsaya bakin kofar dakin suka dage labulen "Allah yakara tsarewa Allah ya kyauta"suka cema inna kande tareda juyawa su tafi


"Ameen ya Allah nagode sosai ku gaida gida" inna kande ta cemasu . cike da tsokana wata daga cikinsu tace "ku kalla mai kuka har tawashe" dariya sukayi dukansu suka fita suka bar gidan .


Kuka nacigaba dayi gabana sai faduwa yakeyi , jina ya dauke dib kwalwata ta toshe takoma kamar babu komai acikinta alokacin . jin kafafuwana sun kasa daukata ne yasa na nema guri na zauna akasa . bakin baba naga yana motsi yana kallona na bishi da ido . sai chan naga yanufi inda nake ya kamo hannuna na ya jani babu inda muka ci burki sai dakin inna kande . 


isketa mukayi kwance akan gado ga hafsat da take kwance itama agefenta tanata bacci abunta hankalinta kwance  bata san mi akeyi ba . ko kallon inda muke inna kande batayi ba  "Amatullah tazo tabaki hakuri " baba yacemata sannan yakara da cemani" Amatullah ba innarki hakuri" da sauri na cike da tsoro da fargaba muryata narawa nace " inna dan Allah kiyi hakuri!" banza inna kande tayi damu daga ni har baba . baba yayi sukuku yayi shiru nima nayi tsaye atsorace . 



gajiyar tsayuwar da mukeyi ne yasa baba yafita daga dakin ya barni da inna kande . nima kuma naci tsayuwata nagaji . juyawar da zanyi kenan da niyyar infita nima sai ji nayi inna kande tacemani "dawo " najuyo jikina na rawa atsorace"matsonan " takara cemani . kyarmar da nakeyi ne yasa nakasa karasawa inda take tawani kwatsa mani tsawa tare da tambayata da tayi " BA MAGANA NAKE YIMAKI BA!?" 

Ba arziki na zuabura na karasa isa inda take . karfen labulen dakinta tazare labulen dake jikinshi ta dagashi sama ta cigaba da dukana dashi kuka na rukayi sosai ga azabar da narukaji ajikina . baba yarugo daga dakinshi tare da cema inna kande"haba kande dan Allah kiyi hakuri mana ta baki hakuri kiyi hakuri mana" 


"malam idan baka fice kabani guriba wlh zan dawo kanka!" inna kande tacema baba afusace .Komawa baba yayi da saurin shi ya shige dakinshi bai kara fitowa ba har sai sanda inna kande tayi bacci sannan. 


Kwanciya nayi adaren ba da niyyar inyi bacci ba dan baccin ma bazai yuyuba alokacin . alamun shigowa dakin naga anayi , na zabura na tashi afirgice zatona inna kande ce takara shigowa dakin . 


sallamar baba naji da yayi ahankali na amsa mashi sallamar ina hawaye "Amatullah kiyi hakuri wlh naso inhana kande dukanki sai naga ranta yabaci sosai shiyasa nabari sai tahuce sannan sai kuma naga taki ta sauko" 


kallon baba na cigaba dayi ina kuka "baba dan Allah ka maidani gurin dangin mamata dan Allah" hannunshi baba yasa ya share hawayen dake bin fuskata tareda cemani "nafada maki iyayen mamarki sun rasu miyasa kuma kike kara yimani maganarsu Eyeh Amatullah ?" hawaye baba ya cigaba dayi shima yakara da cemani "wlh Amatullah da inada inda zani kaiki ruko da tuni na kaiki amman babu yanda zaniyi dole sai agidana zaki ruka rayuwa dole kande ce zata rukeki babu yanda zaniyi da tuni wata maganar akeyi ba wannan ba!, kiyi hakuri kinji ke dai ki cigaba da addu'a wata rana sai labari in sha Allah " baba yafada mani tare da goge hawayen fuskarshi da yakeyi . 
  


Kara tambayar baba nayi " kuma baba babu koda mutum dayane  da yarage cikin dangin mamata ?" Shiru baba yayi andan jima kadan sannan yace mani "zani fadamaki duk abunda yafaru amman sai gobe in sha Allah" ya juya ya fita daga dakin . 


daren kwata kwata ban runtsa ba inata tunanin wane irin labari ne baba zaya bani na mamata? haka nayita Allah Allah gari yawaye baba yabani labarin miyafaru.