AMATULLAH

Chapter 12

by @ameerahfarouk

Tunani nayitayi har lokacin tashina yayi inna kande tazo tayi kokarin tashina daga baccin da ni  kaina banma san nayishi ba . fita nayi nashiga toilet nayo alwallah nakoma daki nayi sallah nakuma fita tsakar gida nafara yin ayyukana kamar yanda nasabayi kullum . 



sai naga yau ban hadu da baba ba gurin fita masallacin da yake zuwa. dakinshi na nufa nashiga ciki da niyyar in tadashi yayi sallah in bai tashiba sai naga baya cikin dakin . araina nace " yau baba tun kafin asuba yafita kenan dawuri yafita ?" 


Tsintsiyar da na ajiye gefen dakin ce na dauka na cigaba da share tsakar gidan nagama yin komai . bucket din dibar ruwa na dauka nafita na debo ruwa . komawata gidan kenan ina ruke da bucket din ruwan nature kofar gidan da niyyar inshiga ciki injuye ruwan , ji nayi kamar wani abu yatokare kofar . karfina nasa sosai ina kokarin ture kofar sai kuma naji kofar tana sakewa ahankali . 


kara turata nayi naga tabude babane na iske abakin kofar , gabana yafadi saboda tsoron ganin shi da nayi agurin gashi banyi expecting ganin mutum ba alokacin, inna kande ce daman zanyi tunanin gani itama idan ta tadani dakinta take komawa ta cigaba da baccinta sai tagama shakar baccinta sannan tafito . watarana ma tana baccin zani tafi makaranta . 


dan murmushi baba yayimani na maida ajiyar zuciya nace "baba wlh kabani tsoro" murmushi baba yayi tare da cemani "ya hakuri bansan zakiji tsoro ba"na gaishe da baba  ya amsa sannan ahankali ya cemani "innarki batasan nadawo ba yau tare zamu tafi makaranta ni dake amman ba da machine ba kada inzo fiddoshi ta tashi , baniso tagane nadawo kuma baniso tagane tare zamu tafi yanzu zani jiraki achan bakin corner sai kije ki sameni achan kiyi sauri kigama abunda kikeyi ina jiranki " 

"toh " nacema baba nima ahankali nayi maganar gudun kada inna kande ta tashi ta rusamana plan . baba yajuya yafita gidan . dandanan nayi sauri na cigaba da abunda zanyi nagama .ruwa nazuba abuta na wanke fuskata sannan na shiga daki , kayana da suke kulle adankwalina ne na kwance na fiddo uniform din da basu samu wanki ba sunyi dukun dukun kamar na mai yin kuli kuli haka na daukesu na makama jikina su nayi sauri nasa safa da sandals dina na sabi schoolbag dita na nufi waje . 


jin numsharin inna kande ne da tuntuni nake jiyoshi ta cika gida dashi ne yasa banje dakinta yimata sallama ba . fita nayi daga gidan nasami baba inda yace iskeshi, na karasa daidai inda yake . baba yakara cemani "akasa zamu tafi ba kince inbaki labarin mamarki ba ?" Daga ma baba kai nayi yakara da cemani " mutafi tanan ne zamu samu damar yin magana sosai " sai natuna da ranar da nafara zuwa school sanda inna kande ta hana baba ya kaini amachine muka tafi akasa .


Yan mintina muka dauka babu wanda yace ma kowa komai munyi shiru dukanmu .sai chan kuma naji baba ya maida ajiyar zuciya tareda cewa " lubabatu" dago kaina nayi da saurina na kalli baba .baba yakara cewa "sunan mamarki kenan lubabatu , na hadu da ita agurin sana'ata ta kayan miya lokacin tun ina saida kayan miya a unguwarmu" kamar ince ina ne unguwarkun? sai kuma na tuna da warning din da yayimani akan kada inkara tambayarshi danginshi . 


araina nace "bansani ba itama tambayar unguwarsun zata sa ranshi ya baci kilama in nayimashi ita injama kaina labarin mamar tawama ya fasa bani" sai nayi shiru nafasa tambayar baba na cigaba da sauraron shi . baba yakara da cemani " kayan miya taje saye gurina naga tamun muka daidai ta da ita na samu iyayenta natura magabata na aka nema mani aurenta . ita kadaice agurin iyayenta suna zama a tudun katsira layin yan buredi tunda nake da ita bata taba yimani maganar danginta ba ko kuma yanuwan iyayenta nima kuma bantaba yimata tambayarsu ba, ko lokacin neman aure da akaje babanta malam bukar da abokanshi aka samu babu wanda ya nuna na daga danginshi ,da iyayena suka tambayi malam bukar game da danginshi sai yabasu  amsar cewa " dayake garinsu da nisa sosai a naija state suke shi da danginshi ,shima aikine ya kawoshi katsina . dan uwanshi kuma kwara daya ne saboda nisan garinsu ne yasa yace mashi yabar zuwan sai wani cikin  abokanshi malam bukar din yazo amadadin kanen nashi .iyayena suka fahimci malam bukar aka tafi ahaka .


 Bayan angama maganane har ansa ranar aurenmu da mamarki lubabatu ne nagano gaskiyar abunda yake faruwa. ranar naje zance gurinta take cemani "baba da umminta suna  nemana ni da ita saboda suyi magana damu dukanmu"tambayar lubabatu nayi lafiya?" ta bani amsar itama wlh batasan dalilinsu na yin hakan ba sai dai in munje cikin gidan munji . nikuma araina sai na dauka nasiha ce zasu yimana atare .

 
Shiga mukayi ni da lubabatu tareda yin sallama muka iske malam bukar da umminta (Hanne) tsakar gidansu. gaishesu nayi suka amsa atare suka samana albarka tareda cewa "mu samu guri mu zauna" muka zauna dukanmu malam bukar yakara da cewa "abunda yasa nace zamuyi magana da ni da ummin lubabatu daku, dukanku kunsan cewa aure shi ba abun ayimashi boye boye bane ba kai jamilu lubabatu taceman shekarunka ashirin da biyar kekuma lubabatu kin shekara sha tara kunga dukkaninku kun kai matakin da yakamata kusan abunda ya shafi rayuwarku" kwalla ummin lubabatu ta share da bakin hijabinta jin maganar malam bukar da yayi . malam bukar yakara da cewa"idan ban fadamaku  maganarnan ba dukkaninku na chucheku babu wanda baida hakkin sanin maganarnan cikin ku . toh dan haka inaso nima in sauke nauyin dake kaina infita infada maku gaskiyar magana . baba yakara da cemani " gabana yaruka faduwa tsoro ya kamani inataso malam bukar yafadi maganar shi da zaiyi .

 
Malam bukar yakara da cewa " ni da hanne ba mu muka haifi lubabatu ba , ansota mukayi agidan marayu sakamakon haihuwa da bamu samu Allah yabamu ba . yanuwana da iyayena suna naija , dukanmu ni da hanne yanuwan juna ne mu . na nunama iyayena muna tare ni da hanne nakuma nunamasu mun fahimci juna auren juna mukeso muyi . sai aka samu matsalar iyayenmu sunki yarda da maganar da naje masu dashi . saboda yawancin family n mu auren zuminci sukeyi amman matsalar da ake yawan samu auren nasu baya lasting wani ko shekara bayayi wani tun awata daya yake mutuwa wani ma ko watan basuyi auren nasu ke mutuwa. Wannan ne dalilin da yasa iyayenmu suka ki yarda da maganar da nazo masu na auren hanne da ita sukaki goyamani baya akan maganar , har family meeting akayi akan maganata da hanne akace baza'a bari muyi aure ba har aka sa dokar dena auren zumincin da akeyi akanmu , sukace sai dai mutum yaje wajen family n yayi aurenshi amman ba cikin family n mu ba tunda zuminci na neman baci .


Malam bukar yakara da cewa " wannan ne dalilin da yasa hankalinmu ni da hanne yatashi munyi magiyar munyi rokon munyi kukan amman babu wanda yajimu . shine muka yanke shawarar guduwa muyi aurenmu asirri ba tareda danginmu sun sani ba . shine mukazonan Katsina anan aka daura mana aure anan nasamu sana'ar da nakeyi yanzu. 


sanda mukayi shekara shidda ne Allah bai bamu haihuwa ba shine muka yanke hukuncin zuwa gidan marayu anan mukaje muka dauko lubabatu , sukuma gidan marayun sukace tsintar ta akayi aka kaimasu ita. cikin sanyayyar murya malam bukar yakara da cemana "amman dan Allah kuyi hakuri yazama dolene kusani hakkinku ne akaina shiyasa nafada muku, kada ku tayar da hankalinku ku zauna da junanku lafiya , kada wannan maganar tasa kuyi tunanin wani abun na daban"baba yakara da cemani " jikina duk sai yayi sanyi , ita kuma mamarki babu abunda takeyi sai kuka . nacema malam bukar "babu komai ".



Iyayena kuma ban bari nafada masu wannan maganar ba gudun kada nima su hanani auren lubabatu . 
 

Watanmu biyu da yin aure ni da lubabatu Allah yayima malam bukar rasuwa . rashin shi ne da kuma rashin yanuwa akusa yasa hanne tasamu heart attack tarasu itama bayan wata hudu da rasuwar malam bukar .


Zaman mu lafiya muke ni da lubabatu hankalinmu kwance . kwatsam sai wata rana nace mata zan karo aure, lubabatu bata wani damu ba akan maganar zan kara aure da nayi . alokacinne Allah ya kaddara na auri kande nahadu da ita akusa da wani gida a unguwar galadanchi inda nake kaima wani babban Alhaji kayan miya agidanshi mukayi aure da ni da kande .

 
Sanda muka cika shekara ukku dayin aurenmu ni da mamarki lubabatu ne aka haifeki . itakuma kande lokacin satinta ukku agidana . 


lokacin da kikeda wata sha dayane aka nemi lubabatu aka rasa . shigata dakinta kenan sai dai ke kadai na iske azaune kan gado kinata kuka .na nemeta sama da kasa babu ita babu alamunta , na gewaye duk gidajen unguwa babu inda ban shiga nemanta ba amman ban ganta ba , munyi kiran mun gaji ga kominta yana cikin dakinta babu wani shedar da zayasa ace tafiya tayi ko kuma unguwa taje nayi cigiyar har gidan tv da gidan radio nakai cigiyarta amman kullum ba labarin ta kullum gani nake kamar zani ganta tadawo gida . amman Allah kadai yasan dalilin yin hakan shi kadai yasan daidai kuma idan ya kadarta abu babu wanda ya isa ya kawar da faruwar shi ko kuma ya tuhumeshi akan miyasa yayi . 

  
Hannu baba yasa ya share hawayen dake zuba afuskarshi sannan yakara kallona tareda cewa  " kinga dalilin da yasa na cemaki babu inda zani kaiki wlh Amatullah nafiki rashin jin dadin zamanki agidannan, da inada inda zan kaiki da tuni na kaiki da inada yanda zaniyi inhana kande ganamaki azabar da takeyi da nahanata!, amman kiyi hakuri komai lokaci ne wata rana sai labari " 


Hawaye ne kawai ke sauka a idanuwana "baba dan Allah idan mun koma gida inaso inga hoton mamata nasan bakaso inna kande taga ina kallon hoton, dan Allah ko da asace ne ka gwadamani inaso inganta " nacema baba cikin takaici da kuncin da nakeji araina . cike da takaicin da yakeji baba yacemani "bani da hoton lubabatu ko daya agurina!, kande ta tattaresu duka ta konesu har wani guda daya na ajiye na boyeshi kasan kayana shima tabi har chan tadauka ta koneshi" .


Tunda baba yabani wannan amsar ban kara cemashi komai ba tsabar takaicin da nakeji shima bai kara cemani komai ba ahaka muka karasa isa makarantar raina abace ga bakincikin da nakeji da takaicin da ya isheni araina ga idanuwana da suka yimani nauyi saboda kukan da nasha. Isa mukayi kofar makarantar baba ya fiddo dari biyu a aljihunshi yabani na amsa yajuya ya tafi nikuma nashiga cikin makarantar jikina asanyaye ina tafiya kamar wadda kwai ya fashemawa acikin ta.