Chapter 13
Har nashiga aji ko teacher da na iske cikin class din yana lesson ban gaidashi ba haka na nufi seat dinmu na zauna fatima sagir nata yimani magana ban kulata ba dan ko kallonta banyi ba . ashe teacher nata yimani magana banji ba chan sai fatima sagir ta taboni da har zanyi banza in kyaleta sai kuma na kalleta raina abace, uncle Emeka ta nunamani da yaketa faman zazzagaman masifa sai alokacin ma ni naji mi yake fada "see this girl , she arrived late and now she...."bai karasa maganar da yakeyi ba na katseshi da cewa " am sorry sir" let me finish what am saying first!" uncle Emeka yafada afusace.
"ok" na cemashi ba tareda na cigaba da saurarenshi ba dan ko kallon inda yake ma ban karayi ba .haka yagama masifarshi yakuma cigaba da koya lesson din sai lokacin yama yagane ba fahimtar lesson din nakeyi ba, maidani seat din gaba yayi yace intashi daga na tsakiyan da nake .alokacinne ni nama lura da mi yake koya mana ma a period din, saboda subjects biyu ne yake daukarmu yana daukarmu basic technology yana kuma daukarmu further mathematics .
haka uncle Emeka ya cigaba da dagewa akan ingane abunda yake koyamana lokacin amman babu abunda nagane sai ma wahalar da energy n shi da yayi . gamawa yayi ya yimani tambaya kallonshi kawai nayi ba tare da na cemashi komai ba har yagaji da maganarshi period din koyawarshi yakare yatafi yanata babatunshi shi kadai yana cewa wai dazu nayi disappointing dinshi .
ni kaina nasan daa wani ne cikin classmates dina yayima uncle Emeka haka da ya shiga ukku ranar .nima din kokarina ne ya ceceni nasan . sukuma classmates dina banda dadi babu abunda sukeji sunata yimani dariyar da ban damu da ita ba ma dan ni ba tasu nake ba .
tashi nayi natafi nakoma seat dina na zauna itama wadda yayi replacing dinta a seat din ta tashi takoma seat dinta da nabaro tanata faman kakkabe kakkabe tana yatsina fuskarta. Ko kallo bata isheni ba .
fatima sagir da take zaune agefena a seat din taketa kareman kallon da bai wani dameni ba "Amatullah lafiyarki kalau kuwa ?" tambayar da tayimani kenan, raina abace na amsa mata da " lafiya lau mi kika gani ?" "tunda nake bantaba ganin ranki yabaci ba sai yau " fatima sagir tacemani cike da damuwar yanayina da taga ya chanza takara da cewa " kinga idanunki kuwa ? gaskiya ba lafiya ba kigayaman abunda yake damunki kinga ni kawarki ce dan Allah mi yasameki Amatullah?"
ban cemata komai ba hawaye kawai suka ruka zubowa afuskata na ruka yin kuka marar sound .rarrashina ta cigaba dayi saida nayi kukana mai isata nagama na danji sauki araina amman ba wai bakin cikin da nakeji yatafi gabaki daya bane .
classmates dina kuwa banda dariya da murna babu abunda sukeyi . wata daga cikinsu har cewa tarukayi wai "inji yanda sukeji idan anyimasu questions basu bada answer ba kawai daga yau dai rana daya nakasa bada answer sai inzauna inta yima mutane kuka toh infadi inmutu mana"
mikewa fatima sagir tayi da niyyar zata rama mani fadan na ruko hannunta na nunamata alamun ta kyaleta kada ta biyemata da dan yatsana . takoma ta zauna tana huci dan ita gaskiya ta iya masifa kullum cikin fada akeyi da ita a class saboda ni . hannunta nakama muka fita waje dari biyun da baba yabani ce na fiddo na nufi shop din makaranta nabada kudin nace abani sweet ta dari aka bani tare da chanjina sannan naje gurin mai wainar fulawa na mikamata darin nace tabani taduka tabani muka koma class.fiddo sweet din nayi na rabata biyu naba fatima sagir kashi daya sauran kuma nasaka cikin schoolbag dita. Nakuma bude wainar fulawar nacema fatima sagir muci ita kuma tace mani takoshi nacigaba da cinta, nacita ne kawai dan kada inmutu saboda jiya abincin da inna kande tabani kamar na mage dankadan dan har gwarama na kullum akanshi .
haka ranar ta zamar mani bakar rana sai da na kwammace daman ban tambayi baba labarin mamata da na tambayeshi ba .
Kowane teacher zaya shigo bani gane komai a lesson dinshi har period din takare babu abunda nake tsinta cikin koyarwarsu .
haka nayi asarar zuwa school aranar . lokacin tashinmu yayi aka tashemu nayi bankwana da fatima sagir "Amatullah nasan fa bakida lafiya yau hakanan dai kika cemani babu komai ai nasani wlh , anjima kadan in sha Allah zanije gidanku ganinki" fatima sagir tacemani .
da saurina nacemata " Aah dan Allah ba sai kinje bama ba lallaine ki sameni bama in kinje " hmm rowar gida bakiso inje gidanku koh ?" fatima sagir tafada tana dan turo bakinta . yaken dole nayi tare da cemata "Aah wlh ba haka bane ba inna ce, tace anjiman zata aikeni shiyasa "
tambayata fatima sagir tayi cike da mamaki " aike kuma keda baki da lafiya !?" amsa mata nayi da "ai naji sauki "toh shikenan babu damuwa Allah yakara sauki "Ameen na amsa mata . tana kokarin son taga damuwata tadan ragu tace "yar rainin hankali shine bazaki iya cemani baki da lafiya ba zaki wani zauna ki cigaba da kuka kamar wata baby ?" cike da tsokana takara da cemani " Amatullah babyn roba" tana mani gwalo tana tafiya tana dariya .
murmushin dole nayimata dan kada takara ganin alamun akwai damuwa atattare dani takara dawowa ta tambayeni mi yafaru. tafiya na cigaba dayi ahanya tunanin duk abubuwan da inna kande ke yimani ne sukayita dawoman da yanda take maltreating dina da duk muguntar da take yimani . natuna da sanda inna barira ke tambayarta Ko nima yanda aka yima uwata za'a yimani ?" araina nace " kenan da sa hannun inna kande cikin bacewar mamata kenan ba hakanan ta bace ba kenan ?"
Ji nayi duk duniyarnan babu wanda na tsana kamar inna kande . haka na cigaba da tafiya ga gajiyar da jikina yayi ta ko ina na gaji gashi babu ta yanda zani ruka hawa express dole akafa zani cigaba da zuwa dan tuntuni inna kande tagane baba yana bada ajiyar kudi abani a school da na break da na hawa express taje ta samu matar da baba keba kudin tayimata rashin mutunci sukayi kacha kacha tadena amsar ajiyar kudin . sannan tayima baba gargadin kada yasake yakara bada kudi ko dawasa idan kuma yabari takara bincike tagano gaskiya zaya sha mamakinta duk matakin da ta dauka akanshi shi yaja .ji nayi kamar insamu wuka in chakama inna kande kowama yahuta tsabar tsanarta da naji takaru araina .haka na isa gidan agajiye ,
sallama nayi tare da tura kofar shiga gidanmu ba'a amsa sallamar ba , inna kande ce na iske rungume da hafsat atsakar gida tanata kuka ita kuma tana rarrashinta taki tayi shiru cike da damuwa na tambayeta "mi yasamu hafsat ?" tabani amsa da cewa" bansani ba uwarta sai kace wani abu zaki iyayi ? dallachan wuce kitafi kiciro kayannan kije inda zaki kidawo kiyi abunda ke gabanki shashasha kawai bazaki daddara da tabaman yarinya ba koh ? toh inma kasheta kikeso kiyi sai dai ke kimutu, ganinan bari dumamen mayya" sannan takara da kwaikwayata "mi yasamu hafsat" tare da wani dogon tsaki da taja .wani abu ya tsayamani a makogorona , takaicin da nakeji aranar duk sai naji yakaru jin maganar da inna kande tayiman akan hafsat raina yakara baci naji nakara tsanar inna kande har cikin raina .
Daki nashiga na durkusa nahada kaina da guyiuwa ina kuka dan maganar da inna kande tayimani ba karamin hurting dina tayiba . araina nace akanmi zan kashe hafsat ita da take yaruwata ? akanmi zata jefaman wadannan maganganun mararsa dadin ji ? Ina cikin tunanin ne bacci ya kwasheni ba tare da nasani ba saboda bansamu nayi bacci ba daren jiya ga wahalar da nasha da gajiyar da nayi .
Ban ankaraba cikin baccin da nakeyi naji saukar abu abayana tareda jin wani mugun zafi abayan nawa wanda yasa na rude nakasa yin kuka . aranar ne nagane wata azabar ma kuka baya zuwar mata . banyi kuka ba ko kadan tsabar tashin hankalin da nashiga . ni dai nasan nadago kaina da sauri na hada ido da inna kande da take tsaye akaina tana cije baki da tabarya ahannunta , daganan kuma ban kara sanin mi yafaruba alokacin.