MUMMY'S CLIPS

1-2

by @oumhairan1

Katafaren parlour ne na Alfarma, cikin parlourn Wasu mata ne guda shida zaune kowacce tana danna waya da alama abinda suke yi a wayar yafi abinda ya zaunar dasu muhimmanci, a hankali cikin salon taku me ɗaukar hankali wata kyakkyawar mace ta fara saukowa daga Step na benen dake can gefe wanda in baka San dashi ba Bama zaka taɓa kawowa wani guri na daban zai kaika ba sanye take da wani baƙin less na alfarma tana taku cikin isa waya a kunnenta tana cewa “Ok hubby bakada matsala cikin satin nan zan shigo" tana maganar tana zama saman wata kujerar da take nuna ita ta musamman ce ta sauke wayar a kunnenta tayi gyaran murya tace “Kowa yayi aikinsa na wancan satin? ɗagowa kowa yayi ya kalleta suka gaisheta cikin girmamawa kowacce ta jinjina kai, tayi dariya tace “Akwai wata shawara da nake da ita sabuwa, maganar gaskiya sabbin abubuwa sunyi ƙaranci a wannan ƙungiya tamu Ina ganin ya kamata muyi tunanin hanyar da zamu bi domin samarwar da kungiya ci gaba musamman Malama Hamidah da Malama Zahrah wanda kuke da tarin mabiya kuma ake muku kallon wasu waliyyai a cikin al'umma" murmushi Malama Hamidah tayi tace “Ranki ya daɗe nayiwa kaina alƙawarin bazamuci wuta mu kaɗai ba dole ne kamar yanda aka hallakar damu sai mun hallakar da wasu wannan dalilin yasa yau ɗinnan na buɗe makarantar matan aure babba a cikin wannan sabuwar makarantar da Ambersedor ya bani  filin na gina"
Zuba mata ido kowa yayi a tare suka haɗa baki sukace “Meye hikimar ki ta yin hakan?" miƙewa tayi ta zare Hijjab na jikinta dogo har ƙasa ta juya ta kuma juyawa cikin wata matsiyaciyar shiga da tayi wacce babu abinda ta rufe daga irin albarkatun da Allah ya tanada a jikinta tace “Ranki ya daɗe Kamar Ni yanzu me na nema na rasa meye matsalata kuma meye aibina shin ilimin addini na rasa ko na zamani? kyau na rasa ko diri?" ta tambaya tana bin kowa da ido suka haɗa murya suka "babu ko ɗaya"  ta share Hawayen da suka zubo mata tace “Amma gani kicin kicin a cikin wannan CLIPS harda rank me girma a  cikinta kuma ba komai ne sila ba face abu ɗaya da kowa a nan ya sani" jinjina kai sukayi taci gaba da cewa “to Gara Ni babu talauci a cikin rayuwata akwai wata tananan ga talauci ga rashin lokacin miji ga kuma jahilci duk sun mata katutu so ta ya zamu gano irin waɗannan matan mu janyo su a jiki mu jiƙasu da dukiya mu maidasu yan gata sannan mu nuna musu zaman aure anayinsa ne yanzu don kare kai daga zargi ba domin samun lada ba, taya zamu fahimtar dasu cewa shi auren na yanzu riga ce kawai ta kariya ba mafita ce a cikinsa ba?" da sauri kowa yace “Kamar ya kenan?" ɗaukar Hijjab nata tayi ta saka tace “Babu mafita a mafi yawan auren wannan zamanin kamar yanda muka sani Muna zaune ne don rainon ya'yan da tsautsayi yasa muka haifa sannan muna rayuwa da mazanjenmu ne don su zame mana riga ba wai soyayya ba, akwai irinmu da yawa a cikin matan da muke gani a gari amma basu san hanyar da zasubi su nemowa kansu mafita ba saboda haka buɗe makarantar zai bamu kusanci dasu mu samu damar nemo mafitarsu da tamu baki daya ko ya kuka gani?"