DUHU BAYAN MURMUSHI

13

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 13.

Sarac Stars R Pen...✍️


Daura.

A lokacin da suka isa har ƙofar gida driver ya kaisu nan yaran unguwa suka zagayesu suna farincikin ganin inna ta dawo, saboda ita ta jama'a ce tana da kyauta da son mutane, shiyasa duk wasu yara da matasa nata ne, dan in yaro ya rasa abinci a gidansu to zai samu a gidan inna ko babu sai ta samarwa mutum abunda zai sa a bakin salati. Yaran ne suka shigar musu da kaya Inna ta bisu, Mujaheed ma yana biye da ita, ya jima rabonsa da garin shiyasa yake jinsa wani iri ya kasa sake jikinsa. Ba jimawa inna ta dawo da ruwa a kofi ta bawa driver ya amsa yana godiya sai ta koma ciki ta sallami Mujaheed da ruwan ya zauna yana sha, ita kuma ta kabbarta sallar azahar da ya cim musu a hanya basu tsaya sunyi ba, bayan ta idar wani yaro ya dawo da kofin da driver yasha ruwa tare da saƙon shi zai kama hanya dan yace ba zai kwana ba sai a Kaduna, inna ta miƙe cikin sauri ta shiga ɗaki, ba jimawa ta fito da leda mai zane da tarkacen tsaraba ta fice ƙofar gida, ta bawa driver suka yi sallama yana zuba mata godiya kafin ta koma gida, shi kuma yaja mota ya tafi yana yaba kirkin inna duk in ya dawo da ita Daura to tabbas sai ya tafi da ledar tsaraba wa iyalinsa.

Bayan sallar isha'i suna zaune a falonta ga tuwo nan har kwano huɗu a jere wanda maƙota da 'yan uwanta suka kawo musu, wannan zumunci ne da suka saba yinsa muddun idan inna ta dawo daga tafiya to a ranar ba zata ɗaura sanwa ba baƙota sune zasu ciyar da ita dan sun san bata huce gajiya ba, haka itama da zarar gari ya waye zata kwance tsaraba ta aika gida-gida, shiyasa baba yake siya mata taliya da dama dan ya san duk rabarwa take yi.

Ɓangaren Mujaheed kuwa yana cikin rigar sanyi sai rawar ɗari yake yi, inna ta damu sosai da halin da yake ciki.

Ai dana san wankan dana tilasta maka zai haifar maka da haka da ban ce kayi ba, wai ni na yi maka gata ne yadda zaka samu bacci mai kyau saboda gajiyar hanya.

Mujaheed dai baice mata komai ba dan bayi da amsa, kawai dai rashin sabo ne da yin wankan ya illatashi, saboda jiya yayi da daddare ɗazun yayi da safe gashi ansaka yayi yanzu, abunda bai saba bane dan sai yafi ƙarfin wata ruwa bai taɓa jikinsa da sunan wanka ba, shiyasa dole ma yayi zazzaɓi. Haka ta ɗauko paracetamol wanda ta saba aje wa matasan da suke shigo mata, ta ɓallo biyu ta bashi da ruwa ya amsa ba musu yasha sai ya kwanta a carpet ɗin ɗakin, ganin haka sai Inna ta miƙe ta shiga ciki ta ɗauko masa pillow ta ɗaga kansa ta saka masa sai ya gyara kwanciya, ba jimawa bacci ya ɗaukeshi, ta sauke numfashi ta tattara kayan abincin da suke falon ta matsar gefe sai ta fito ta rufe ƙofar gida, ta dawo ta rufe ƙofar ɗaki ta wuce ciki ta kwanta a gadonta mai rumfa.

Da asuba ta tashi tayi sallah sai kuma ta koma bacci, sai Safiya ta farka saboda sallamar da ake ta yi a ƙofar gida, tasan 'yan uwanta ne maza suke ta zuwa yi mata sannu da zuwa kafin su tafi gona da kiwo, dan sun saba yi mata wannan karamcin, haka ta fito ta shimfiɗa babbar tabarma abarandar tsakar gida taje ta buɗe ƙofa, sai ta ga ɗan ƙaninta Adam Marigayi ne, shi ne babba ɗansa mai suna Sayyadi tare da ɗansa Ahmad wanda yake kusan sa'an Mujaheed, inna ta saki yalwar murmushi tana yi musu maraba suka amsa suma da murmushi a fuskarsu, sai ta juya zuwa ciki suna biye da ita a baya har suka yada zango anan kan tabarma suka shiga gaisa wa, inna ta tambayi iyalin Sayyadi ya tabbatar mata da suna lafiya suma sunanan zuwa su gaisheta, a lokacin Mujaheed ya fito daga falon ya farka daga bacci, saboda matsawar da Inna tayi masa da asubahi dole ya tashi yayi sallah kuma ikon Allah baiyi fisharin kwance ba, ya dai tashi a matse yaje yayi shi cikin sauri, tabbas lalaurar Mujaheed da akwai sakacin kulawar iyayensa a ciki dan da sun saka ido ƙila cutar ba zata yi tsamari akansa ba.

Sayyadi yace cikin kulawa.

Wannan kamar ɗan yaya Musa ko.?

Shi ne ai tare muka dawo, kasan yana fama da wannan lalura ta kwakwalwa shi ne na zo dashi dan mu gwada maganin malam babba anan.

Allah sarki, to Allah yasa a dace ya ƙara lafiya.

Ameen ya rabbi, malam Amadu ga aboki na yi maka sai ka zame masa idon gari, ka kuma jashi a jiki dan Allah, wataƙila zai riƙa buɗe baki yayi magana.

To Inna In Sha Allah na karɓi wannan abotar.

Cewar Ahmad yana murmushi, Inna ta juya ga Mujaheed.

To kai ga Amadu abokinka sai ka je ka ɗauraye baki kazo ka karya.

Ƙala bai ce ba sai dai ya miƙe ya nufi bakin rijiya ya ɗauki buta, Baba Sayyadi ya bishi da kallon tausayi.

Ohhh Allah mai iko mutum har mutum amma babu lafiya, to amma can ɗin suna ƙoƙarin nima masa magani ko.?

Sunyi iya ƙoƙarinsu, nan ma zanyi iya nawa ƙoƙarin.

To hakan yayi Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ce, Inna bari mu shiga gona sai Allah yayi mana dawowa.

To Allah ya tsare ya bada sa'a, ku dawo lafiya.

Allah yasa.

Baba Sayyadi ya faɗa kafin suka fice daga gidan. Haka inna ta cigaba da karɓan baƙuncin 'yan uwa har zuwa wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi kafin ta samu sukunin kiran Babangida, ko da ya ɗauka suka gaisa ya shiga bata haƙuri akan bai samu kira jiya ba, tace babu komai ai itama bata samu kanta ba sai yanzu, sai baba ya shiga sanar mata da abunda ya wakana jiya dama shirin ɗaurin aure da suke ta yi tun safe, Inna ta riƙe haɓa cike da tsantsar mamaki.

Wannan abu bai yi gaggawa ba kuwa Babangida, daga magana jiya sai zancen ɗaura aure yau anya kuwa.?

To Inna baba Sanusi shi ne ya yanke wannan shawarar duba da duk abun na gida ne, sannan ya sauƙaƙa musu zarya ne saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a can Zamfara, kin ga bai dace nace a'a ba in dai ina da kara.

Eh wannan gaskiya ne, to Allah yasa hakan ya zama alkhairi. Yanzu tariya sai wata biyu mai zuwa kenan.?

In Sha Allah haka muka yanke, amma Inna ku zaku iya zuwa tun kan lokacin dan ayi komai akan idonku.

To Allah ya nuna mana yasa muna da rabon gani, idan an ɗaura ka sanar da ni sai na faɗawa 'yan uwa a nan su taya mu murna.

In Sha Allah za ayi hakan Inna, nagode. Ina mutuminki babu dai wata damuwa ko.?

A'a babu komai dan gaskiya ko fita bai yi ba yana ɗaki yana kallon tv, kuma duk yasha maganinsa nayi masa hayaƙi, In Sha Allah in an kwana biyu zan kai shi wajen malam babba ya duba shi.

To Allah ya bashi lafiya yasa ƙarshen wahalarmu ne.

Inna ta amsa da amin kafin suka yi sallama suka kashe wayar.

****

Kaduna.

A lokacin da aka idar da sallar azahar ne aka gabatar da ɗaurin auren Aina'u wanda mutanen unguwa sun sha mamaki duba da babu wanda ya samu labarin haka, sannan ba wanda ya kawo zasu aurar da ita da ƙanƙanin shekaru. Haka aka yi komai cikin farinciki aka gama Aina'u ta zama mallakin Idris, farincikin a gurin wannan ahali ba cewa komai, mama duk da bata sanar ba kuma bata yi gayya ba sai da tayi girkin loka biyar na shinkafa, ta kira ƙawayenta a waya ta sanar da su, zuwa ƙarfe biyu tuni gida ya cika da abokan arziki ana tayasu murna, Aina'u kuwa leshin da baba ya ɗinka musu da babbar Sallah shi mama ta ce ta saka tunda ba tada sabon kaya sama da shi, haka ta ƙule a ɗakinsu taƙi fitowa abinci ma kasa ci tayi saboda jikinsa yayi sanyi da fargaban sabon rayuwar da zata shiga, ga kuma damuwar barin gida daya dirar mata, tasan tana son Idi bata damu da kauye zata yi aure ba amma kuma bata son barin gidansu, sai dai ƙaddara ta riga fata kuma dole sai ta tafi ko da kuwa babu shiri.

Zuwa ƙarfe uku mutanen Magami suka kama hanyar Zamfara, a lokacin baba ya samu kansa wanda abokan kasuwancinsa suna tare da shi a ƙofar gida suna taya shinmurna, bashi ya samu kansa ba sai bayan magrib daya sallami kowa ya shigo gida da sallama, gidan ma shuru dan duk matan da suka zo suma sun tafi. A falo baba ya same su har da ita Aina'un, ya zauna, yaran suka yi masa sannu da zuwa ya amsa fuska sake, mama tayi masa sannu sannan suka shiga yiwa juna barka da arzikin wannan aure da ya zo musu bagatatan, baba ya cire hula ya shafo seƙonsa yana cewa.

Ai Salamatu naji daɗin wannan Al'amari, muma mun samu sauƙi sosai, yanzu sai dai mu ji da ranar tariyarta. Aina'u to girma ya kama ki dan haka banda fita sai da Izinin mijinki, duk da Yaya Tijjani ta tabbatar min babu matsala duk abunda ya taso naki sun bar min wuƙa da nama, dan sai da na sanar dasu kina zuwa koyon ɗinki.

Ai malam karka damu domin Aina'u ba mai son fita bane, sannan abu na gida ne babu takura a ciki, yanzu batun kayan ɗakinta shi ne abu na farko da zamu yi, gobe In Sha Allah zan amso kuɗin adashena a cikin satin zan shiga kasuwa na haɗo mata kayan kitchen, wannan shi ne gudunmawa ta.

To Allah ya saka da alkhairi nima zanyi ƙoƙari na baki wasu kuɗi masu kauri a samo mata labulayya da zanin gado da sauran abubuwan buƙata.

Cewar baba, mama tace Allah ya kaimu haka suka cigaba da hirar har aka kira sallar Isha'i baba ya tasa kan yara maza suka wuce masallaci. 

******

Jabir. 

Bayan ɗaurin aure yayi busy sosai bai samu kansa ba sai da suka dawo daga wajen dinner, suka sauke Zaliha a gidansu sannan shi ya dawo gida, har ya nufi ɗakinsa sai ya juya zuwa ɓangaren Ummi ya shiga, yayi sa'a ba mutane sosai a falon wasu ma sunyi bacci, ya gaida tsirarun mutanen ya wuce ɗakin Ummi ya buga, daga ciki tace ya shigo, sai ya murɗa handle ya shiga da sallama, Ummi ta yalwata murmushin fuskarta. 

Ango ne ashe. Da fatan an watse taron lafiya.? 

Lafiya lau Alhamdulillahi, Zaliha tana gidansu mun sauketa tare da Ikilima, tace zata kwana a can. 

Masha Allah, kuma Ikilima da take ƙawar amarya ai kwanan shi ne yafi, gobe dai In Sha Allah amarya zata tare Allah ya sanya alkhairi ya kawo zuri'a nagari. Yauwa kamar kasan ina son ganinka.

Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta isa wajen wardrobe ɗin kayanta ta buɗe ta ciro wani jaka ta dawo ta zauna gefen gado, ta ciro abu a ciki ta miƙa masa, Jabir ya amsa cike da mamakin abunda ya gani ko kafin yayi tambaya ta riga shi da cewa. 

Na shirya muku tafiya zuwa Dubai kuje ku ci amarcinku, wannan ita ce kyauta mafi tsada dana yi muku, na tabbatar kuma zaku ji daɗinsa.

Wow, Ummi wannan bazata haka, wlh kin shammace ni, mun gode sosai, bari yanzu zan je na fara shirya kayana, amma batun tariyar Zaliha a Abuja fa.?

Yana nan yadda muka tsara gobe In Sha Allah, za a wuce da ita kaima sai ka shirya ka bisu, dan jirgin dare zaku bi a nan Abuja. 

To Allah ya kaimu, nagode Ummi Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da shekaru masu albarka. 

Cewar Jabir cikin tsantsar farinciki bakinsa kamar gonar auduga, haka suka ɗan taɓa hira daga bisani yayi mata saida safe ya wuce daɗinsa. Ko da ya shiga kwanciya yayi rigingine a gado yana ayyana irin amarcin da zai kwasa a Dubai, dama ɗazun irin ƙamshin daya ji a jikin Zaliha ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba duba da ya jima baya tare da mace, sai ya ƙosa a kai masa ita yadda zai kwashi romon amarci, sai gashi cikin sauƙi Ummi ta yalwata masa shan romon wanda yake cike da nishaɗi babu hayaniya ko wani tsaiko, haka ya cigaba da hasashen yadda komai zai kasance, sai zaƙuwa da ɗoki ya gama cikashi wanda a haka bacci ya ɗaukeshi tare da mafarki kala-kala na Zaliha. 

Zuwa asubahi sai da yayi wanka kafin ya samu gabatar da sallar asubahi a ɗaki saboda ya rasa jam'i, ko da ya idar kayansa ya shirya a jaka sai dai kaɗan ya ɗauka saboda a can zai siya wasu. Ya zauna a gefen gado ya kira Zaliha sai dai bata ɗauka ba saboda tana can sashim Babanta yana ƙara yi mata faɗa. 

Wajen ƙarfe sha ɗaya motar kai amarya ya ɗaga daga gidansu zuwa gidansu Jabir, anan aka sake wani zaman wanda 'yan uwa Hajiya Maryam suka danƙa amanar Zaliha a gurin Ummi, ta saki murmushi mai ƙayatarwa. 

Ai Zaliha koda ba Jabir ta aura ba 'yata ce domin nima ina ɗaya daga cikin wanda zasu kaita ɗakin miji, kawai dai abun yazo ne a tuwona maina ne shiyasa, dan haka karku ji komai gida ta zo, Allah ya yiwa auren albarka ya kawo zuri'a ɗayyiba. 

Duk matan dake falon suka amsa da amin kafin suka cigaba da magana ana yiwa amarya nasiha, har sai da suka ɓata kusan awa guda sannan suka fito tare da 'yan rakiyar amarya zuwa motocinsu, duk suka shiga suka kama hanyar Abuja a wannan lokacin. Jabir kuwa tun wajen ƙarfe goma shi da Yaƙub suka wuce a motarsa. 

Bayan sallar Isha'i 'yan kawo amarya ne zube a carpet ɗin falon gidan Jabir cike da gajiyar zaman mota, ɓangaren Zaliha kuwa tana ɗakinta da suka sauketa, ta kuma yin wanka ta sauya kaya, ta gama shirin tafiya dan tun da rana Jabir ya sanar da ita, wanda suna isowa Ikilima ta tayata haɗa jakar kayanta, yanzu Jabir kawai suke kira ya ƙaraso. Wajen tara na dare suka kama hanya bayan sunyi sallama da 'yan kawo amarya akan sai washegari zasu tafi bayan sun ƙarasa kimtsa mata gidan saboda saura kwana biyu biki aka kawo kaya aka rufe gidan. Zuwa goma da rabi jirgin su Jabir ya lula sararin samaniya zuwa Ƙasar Dubai dan cin amarci wanda ɗokin hakan yasa shi mantawa da Safiyya saboda Zaliha ta maye gurbinta, gata a kusa da shi, hankalinsa yana wayarsa akan kallon status ɗin hotonsu da ya ɗaura wanda suka ɗauka a filin jirgi dama cikin jirgin kifin su ɗaga zuwa sama, daga bisani ya kife wayar ya jingina bayansa da kujerar da yake kai ya lumshe ido. 

Bayan sun isa Dubai, masauki ya fara samar musu mai kyau suka sauka, daga nan suka fara shimfiɗa sabon rayuwa mai cike da kulawa, dan Zaliha gogaggiya ce da iliminta bata bari kanta yayi murfi ba wajen kula da mijinta ba, ta saki jiki suka fara gudanar da amarci, kuma ƙarin armashi abun Jabir ya sameta a cikakkiyar budurwa, shiyasa ta riƙa narke masa, shi kuma yana aikin rarrashi tare da nuna mata tsantsar kulawa, a haka suka shafe sati biyu wanda Zaliha ta mantar da shi wata Safiyya dan ko ya tuna ta sai yayi saurin kawar da tunaninta dan kar ta shiga cikin lokacin Zaliha, ya bari sai ya dawo kafin zai waiwaye ta da kuma hanyar da zai bi wajen dawo da ita cikin rayuwarsa. 

Safiyya...

Rahma ce.