14
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 14.
Sarac Stars R Pen...✍️
Safiya.
Bata taɓa zaton cewar akwai lokacin da zai zo tayi rayuwa na tsawon lokaci ba tare da Jabir ba, domin ta yi tunanin mutuwa ce kaɗai zata raba su wanda tsabar so har fata take yi Allah yasa lokaci ɗaya zasu bar duniya, sai gashi cikin ƙiftawar ido komai ya faru kuma Allah ya ganar da ita zahirin Jabir, a nata lissafin na irin son da Jabir da yake yi mata, to ba zai taɓa zaɓar wata mace ta maye masa gurbinta ba, sai gashi ya bata mamaki irin mamaki daya kaɗa dukkan tunaninta, ta yarda cewar mata zunfi zurfafa soyayya, sun fi zurmawa a kwazazzabonsa wanda so tari yake sauke su a tashar danasani, domin shi namiji yana da iyaka a so, basa zurfafa zuciyarsu a ciki ta yadda ko da an samu wani akasi zasu zame jikinsu cikin salama, ko da yake mace tana da rauni shi ko namiji da jarumta a kasanshi, sun iya danne damuwa matsawar zai kawo musu mafita. Itama irin wannan jarumar ta gwada yi tare da ƙoƙarin yakice shi a zuciyarta dan ta samu sukuni tunda ya barta cikin fige kazar wahala bai san ma tana yi ba, shiyasa tunda suka dawo daga asibiti ta shiga cikin hankalinta ta seta tunaninta cikin ambaton Sunan Allah, Salati Annabi s.a.w, Sallar dare tare da tsananta Addu'a a cikin sujud, sallar Walha bata wuce ta, sannan tofin da Baffa yake yi mata a ruwan zam-zam ita ta koma tana yiwa kanta a lokacin kwanan ta biyu da sallamarsu daga asibiti, ta je har ɗakin Baffa ta tambaye shi addu'ar da yake yi mata a ruwan zam-zam, Baffa sai da yayi murmushi farinciki domin ya fahimci ta dawo da akalarta zuwa ga Allah, sai yace cikin kulawa.
Alhamdulillahi jiki yayi kyau Safiyya, ko zamzam ko ruwa mai kyau kika samu sai ki karanta suratun Fatiha kina tofawa a cikin ruwan ƙafa bakwai, sai kiyi addu'a akan duk abunda kike buƙata na samun lafiya a gurin Allah sannan ki sha, idan kuma kin samu kanki cikin fargaba da wasi-wasi ko ki riƙa tunanin wanin abu a zuciyarki da bayi da amfani to sai ki kasance kina karanta wannan Ayar, Huwal Awwalu Wal Akiru Zazzahuri Wal Baɗin Wahuwa Bi Kulli Shai'in Alim, ki riƙa maimaitawa In Sha Allah zaki samu natsuwa, ki kuma tuna dukkan tsanani yana tare da sauƙi, Allah ya shiga lamarin ki ya kawo miki mafita.
Amin Baffanmu nagode.
Safiyya ta faɗa cikin farinciki kafin ta miƙe ta fita tana maimaita wannan ayar a zuciyarta. Haƙiƙa tunda ta bar komai ga Allah ta dage da addu'a da kuma ibada sai ta samu sauƙi da salama a zuciyarta, babu wasi-wasi ko tunani mara amfani, sai ta yini tunanin Jabir bai faɗo mata ba saboda ta saka kanta cikin hidimar aikin gidansu bata zama ita kaɗai. A hankali walwalarta ta fara dawowa wanda hakan ba ƙaramin faranta ran mutanen gidan yayi ba, saboda ita Baffa ya dawo da yiwa su Kausar karatun dare na littafan Musulunci, itama ta fara zuwa tana kwasar karatu, sai wajen goma suke komawa ɗakinsu saboda ta koma ɗakin su Kausar da kwana, idan suka ɗan taɓa hira sai kowanne ya kwanta bayan sunyi addu'a babu jimawa bacci zai ɗauketa ba tare da ta ɓata daren da tunani mara amfani ba. A sati uku da auren Jabir wanda ya kasance saura kwanaki ne ta fita Idda, Safiyya ta tabbatar tunda aka kawo wannan lokacin tabbas Jabir ya maye Zaliha a matsayinta, kuma itama tayi alƙawarin ta barshi kenan, sannan ba zata ƙara bari damuwarsa ta illata lafiyarta ba, shiyasa ta yanke wa kanta hukuncin yin aure da zarar ta kammala Idda, sai dai bata san wa zata aura ba, amma ta ƙudura zata saki zuciyarta tayi rayuwa kamar yadda kowa yake yi, sannan tayi alƙawarin ba zata sake zurfafa soyayya irin na Jabir ba da ya nima halaka zuciyarta.
Yau Litinin kuma ya yi daidai da fitar iddar Safiyya da kwana ɗaya, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ta saka gyalen da ya shiga da kayan, ta fito riƙe da jaka iri guda da kalar takalminta, babu kwalliya a fuskarta amma ta shafa power da man baki sai kwalli data zizara a idaunuta wanda suka ƙara fito da kyawunta, duk da ta rame amma bai rage komai daga kyawunta ba, sannan ma ta fara kumari saboda samun nutsuwa data fara yi. Mama babba tana ɗakin Baffa sai mama ƙarama ce a tsakar gida tana aikin ƙirga kuɗi da zata aika Salim ya siyo mata kajin da zata yi dambun nama domin sana'arta kenan, Safiyya ta tsaya daga ƙofar ɗakinsu kamar tana nauyin ɗaga ƙafa ta wuce, mama ƙarama ta san ta fito amma sai bata kulata ba har sai da ta kammala haɗa kan kuɗinta ta waigo ta kalleta cikin murmushi.
Alhamdulillahi Safiyya ta fara dawowa mutum, kin yi kyau Tubarakallah, ni rabon dana ganki cikin kyawun shiga tun kafin wannan yaro ya rikita miki kwakwalwa.
Kai mama kar ki saka na kasa fita fa, wlh ni kaina wani iri nake ji.
Yo ba dole kiji wani iri ba duk kin bi kin susuta kanki akan wani wanda bai san darajarki ba, ai Alhamdulillahi kin fita idda kuma In Sha Allah kin yi masa nisa.
Shigowar yaya Ali shi ne ya katse maganar mama, ya ƙaraso ciki suka gaisa sannan ya kai dubansa ga Safiyya wacce ta sunne kai tana wasa da hannun Jakarta.
Muje ko, dan ina sauri daga can zan wuce aiki.
To tace masa kafin ta wuce ɓangaren Baffa ta shiga ta yi musu sallama, Baffa ya dinga saka mata albarka tare da addu'ar fatan nasara a interview da zata je yi yau na aikin da Ali yake ƙoƙarin samar mata, ta amsa da amin kana mama itama ta koro mata nata fatan alkhairi, haka Safiyya ta fito tana mai jin alfahari da samun iyaye nagari, tabbas sune suka tsaya mata har ta dawo hayyacinta, ta fito ta kuma yiwa Mama ƙarama sai ta dawo kafin ta nufi ƙofar gida ta jira fitowar Yaya Ali daya shiga ɓangaren Baffa shima. Ba jimawa ya fito suka kama hanyar zuwa gidan MN tv inda za a yi mata interview. Sun yi nisa a tafiyarsu motar shuru, can sai yaya Ali ya dubeta da ɗan murmushi a fuskasa.
Da fatan kin shiryawa wannan interview ɗin dan suna da tsari da doka a wannan gidan tv, dole sai kin iya turanci da Hausa mai kyau fa.
Tun shekaran jiya nake ta bincike akan yanayin aikin, kuma na shirya tare da addu'ar zaɓin Allah.
Da kyau Safiye 'yar Baffanmu, Allah ya baki sa'a, da kin fara zuwa aiki zaki nima ko wani damuwa ki rasa. Sannan dan Allah ki buɗe zuciyarki ki bawa manema dama kar ki riƙa tuna baya domin akwai mutanen kwarai, zaki dace In Sha Allah.
Hmmmm Safiyya ta faɗa da ɗan murmushi a fuskarta sai ta nisa tare da kallon gefen hanya, sai ta mayar da idonta kan titi tana kallon bayan motar dake gabansu.
Yaya a yanzu na baka wuƙa da nama ka samo min mijin aure, In Sha Allah ko waye zan yi maka biyayya.
Ta ƙare maganar tana dubansa da murmushi, shima ita yake kallo da Maɗaukakin mamaki a fuskarta tare da irin kallon nan na baki da hankali, sai ya kawar da idonta zuwa hanya ya saki ajiyar zuciya.
Safiyya a auren farko ma ke ce kika zaɓo mijinki balle a yanzu da shari'a ta baki damar zaɓa, ni ba zaki ɗaura min wannan nauyin ba, abu ɗaya zan iya yi miki shi ne addu'ar samun miji nagari.
Yayanmu wlh bana sha'awar sake yin wata soyayya zuciyata a cunkushe take, ina so ya zamana sai a cikin gidan aurena zan ƙara buɗe zuciyata, kuma a yadda nake ji bana so na wuce sati biyu banyi aure ba domin ina so na haramta kaina ga Jabir na har abada.
Wani irin birki Yaya Ali yayi kafin ya ja motar zuwa bakin titi ya ɗaure fuska tamau.
Kina nufin idan ya dawo a yanzu zaki iya ƙara bashi wata dama kenan shiyasa kike so kiyi auren gaggawa dan kar ya dawo.? ko kuma kina son yin auren huce takaicin ko, Kenan ba dan Allah za kiyi ba sai dan saboda Jabir yaji kin yi aure kin haramta a gare shi. Safiyya wai sai yaushe zaki gane cewar baki da sauran amfani a gurin Jabir, duk abunda za kiyi ba zai taɓa damunsa ba dan haka gaggawa aikin shaiɗan ne kibi komai a hankali, kiyi addu'a ki barwa Allah zaɓi.
Yana kaiwa nan a maganarsa ya kunna motar kafin ya cigaba da tafiya, Safiyya bata iya sake cewa komai ba saboda jikinta yayi sanyi, ta ɗauka in yaji maganar data faɗa masa zai mara mata baya tayi aurenta cikin ƙanƙanin lokaci, hawaye ya cika mata ido amma ta shanye basu zubo ba, tana son ta nisanta kanta ga Jabir dan bata son abunda zai ƙara haɗasu, yanzu zata fara aiki in kuma yaji ko ya ganta wataƙila zai sake dawowa rayuwarta ganin ta samu cigaba a rayuwa, ta san waye Jabir idan yaga ta dawo cikin natsuwarta zai iya sake dawowa ya dagula mata lissafi, dan ba zata ce bata son shi ba, kawai dai ta koyawa kanta juriya da haƙuri ne sannan shi so lokaci guda yake shiga wanda a hankali yake yaɗo har ya gina gamsheƙa a zuciya, mutum ba zai san yayi nutso ba sai wani abu ya faru wanda zai jijjiga wannan son, itama irin wannan halin ta samu kanta a soyayyar Jabir wanda tasan shi ne babban ƙalubalenta, ba zata iya yakice shi lokaci guda ba, Jabir zai iya dawo mata ya nima su shirya harya karya wancen ƙudurin nasa dan ya samu kanta, zuciya ba tada ƙashi zata iya amince wa dashi a karo na biyu wanda tana tsoron ta samu matsala da ahalinta, shiyasa take sauri da gaggawar yanke wa kanta hukunci. Har suka isa tafkeken gate ɗin gidan tv yayi parking, sai ya buɗe ya fito itama ta fita, yayi gaba suka shiga cikin wajen yana gaisawa da masu gadin gidan, suka tsaya a haraba inda ake aje motoci, Ali ya kira wani a waya ba jimawa ya fito suka gaisa ya kalli Safiya.
Wannan ce ƙanwar tamu.?
Eh gata nan dan Allah kayi mana ƙoƙari akan lamarin.
In Sha Allah Aliyu karka ji komai, bari mu shiga.
Nagode Allah ya saka da alkhairi.
Cewar yaya Ali, mutumin mai suna Musa yace amin kafin ya wuce gaba Safiyya ta bi shi, har sunyi nisa kafin ta juya taga yayanta ya kusa fita daga gate ta juya da sauri tabi shi, har ya fita, ta same shi yana shirin tayar da mota zai wuce, ya kalleta yana ƙara haɗe fuska.
Lafiya.?
Yaya kayi haƙuri idan na ɓata maka rai, amma wlh da gaske nake yi ka sama min miji kuma ba gaggawa zanyi ba, hakan kawai nake buƙata da wuri.
Tsaki Ali yayi ya ja motarsa ransa a dagule, tana kallo ya wuce sai ta juya jiki ba kwari ta koma ciki tana tunanin aurenta a wannan lokacin shi ne kawai mafita. Shi kuma Ali ganin rashin hankalinta yake yi na yin aure a kurkusa, yaso ta samu natsuwa ta huta sosai, musamman da likita yace ba a so ta samu ciki nan kusa sannan ga zuciyarta da ta kumbura duk bata sani ba an ɓoye mata, shi ne zata jawo wa kanta wata damuwar, tabbas yasan aure ba damuwa bace domin yinsa ya kan samar da natsuwa ga mutum sannan ga Lada da Falala mai yawa, sai dai a halin da Safiyya take ciki tana buƙatar hutu na zuciya dana gangar jiki gabaɗaya, sannan ma waye zata aura wanda zai yarda da lalurar da take fama da shi har ya amince ya aureta a haka, dole ne za a sanar da koma waye halin da take ciki idan yaso ya aureta a haka ko ya fasa, abu ne mai wuya a yanzu ace namiji ba zai tara da matarsa ba dan kar ta ɗauki ciki, kuma ba zai yuwu tayi planning ba tunda shi ne ma ya sata a wannan matsalar, aure ba nata bane a yanzu da gaggawa saboda suna burin samun lafiyarta ta dawo cikin Aminci. Kuma wani sashi na zuciyarsa yana gasgata ta akan tayi auren, yasan har yanzu tana son Jabir kar kuma ya dawo cikin rayuwarta ya dagula mata lissafi, ya santa tana da saurin yarda, idan ya marairaice mata ya kalallameta da magana zata iya sake amincewa da shi ta ƙara komawa gidan jiya, domin baya hango nadama ko danasani a cikin lamarin Jabir, tun sakinta da ya yi da kuma auren da yayi ya gane cewar son Safiyya yafi nashi kuma da shi yake amfani yake gallaza mata, haka ya isa gurin aiki zuciyarsa a cunkushe ransa babu daɗi, yayi parking a babban companynsu inda ake ajiye motoci, ya kife kansa a sitiyarin motar yana haɗa tunani akan lamarin Safiyya. Hamisu wanda yake hango masu shigowa campanyn daga saman bene ta jikin taga, yaga shigowar Ali har ma da parking ɗin da yayi, ya saki murmushi yana jiran zuwansa amma shuru bai fito daga motar ba, ya tsaya shuru yana nazarin ƙila yana ɗaukar abu ne a ciki, amma shuru baya ganin komai tunda glass ɗin mai duhu ne, ya sauke ajiyar zuciya ya koma mazauninsa ya ɗauki waya ya danna number ɗin Ali, bugu ɗaya zuwa biyu ya ɗaga.
Mutumin yaushe a gari.?
Cewar Ali cikin ƙaƙalo murmushi, Hamisu ya sauke ajiyar zuciya.
Ka shigo ciki mana sai ka tabbatar da na shigo ɗin, tun ɗazu naga kayi parking baka fito ba, Allah yasa lafiya.?
Hmmm Alhamdulillahi ƙalau, amma shi ne zaka shigo Ƙasar ba labari wlh baka da kirki.
In kai kana da shi ai babu matsala, dalla ka shigo karka ɓata mana lokaci za a fitar da kaya.
OK CEO ɗin Hazan Company.
Cewar Ali yana murmushi, Hamisu ya kashe kiran yana juyawa akan kujerar da yake zaune, A haka Ali ya shigo ya same shi, Hamisu ya miƙe ya bashi hannu suka gaisa suna dariyar farin ciki.
Kaga yadda ka koma ɗan lukuti, kusan wata goma kayi a China.
Ai naso nayi shekara cur amma Hajiyata ta saka ni a gaba dole na dawo. Sati ɗaya nayi a Abuja kafin na dawo Kano jiya. Ya iyalin.?
Lafiya lau Alhamdulillah. Yasu Hajiya da fatan kowa lafiya.
Kalau wlh, daga Ina kike ne.? Naga baka shigo company da wuri ba.
Safiyya na sauke a MN tv zata yi interview.
Ko gidan tv ɗin abokina Maina Nasara.? Amma ita Safiyya ta dawo Kano ne da mijinta.?
A'a ita ce dai ta dawo, kai dai labari ne mai tsawo, yanzu muje mu ga yadda zasu fitar da kayan mutane kar lokaci ya ƙure. Kuma dama MN Tv na Maina ne ban sani ba.?
In dai MN tv ne na Maina ne, amma zan kira shi anjima na tambaye shi. Ina Sha Allah Safiyya ta samu aiki.
Aiko ka kyauta nuna godiya.
Cewar Ali yana miƙewa dan ɗazun ya zauna ne, Hamisu ya ɓata fuska ya kafe Ali da kallo ba tare da ya ce komai, Ali ya sauke numfashi.
To me nayi kuma.?
Me kake ɓoye min, yaushe muka fara irin wannan.?
Hamisu lamarin ba mai daɗi bane wlh, amma shikenan bari na faɗa maka komai ko zaka bani shawara.
Sai ya soma bashi labarin mutuwar auren Safiyya dama abunda ya faru duka.
Rahma ce.