MEERAH

09

by @oumfatima33

*MEERAH*
 
    *OUM FATIMA*
    
     *09*


      Yau shopping muka tsara fita na kayan da zamu saka, sai dai tunanin yanda za'a bar ni fita ni kaɗai nake yi. Sauƙi ɗaya da na samu shine azababben nan baya gidan bare ya saka min ido.

   Don haka naje na lallaɓa Momy, cewa tayi sai dai driver ya kai ni mu sayo duk abinda nake so ya dawo dani gida. Ƙara shigewa jikinta nayi nace.

   "Momy ba fa ni kaɗai zan je ba, ni da Zeezee ne kuma Yaya Abdul ɗin su ne zai kai mu." Na ƙare maganar cikin ƙaramar murya. Ajiyar zuciya Momy ta sauke sannan tace.

  "Shike nan to Allah ya kiyaye, amma kar ku daɗe kin san Yayanku ya hana ki fita ke kaɗai." Rungumeta nayi cike da farin ciki nace.

    "Thank you Momy." Murmushi ta yi ta shafa kaina taci gaba da abinda ta ke yi, bedroom ɗina na nufa na hau shiri. Tsaf na fito cikin riga da wando sai kimono da na ɗora a sama na yi rolling mayafinta.

   Kayan sun min kyau sosai dai-dai jikina, shigar dana fi so kenan English wears idan zan fita kuma in ɗaura after dress. Kafin kaga na saka atamfa, lace, ko shadda sai dai ranar juma'a, ko sallah, ko kuma idan zamu fita da Momy tace dole sai na saka.

   Ɗakin Momy naje nayi mata sallama sannan na fita, a hankali nake taka wa har ƙofar gidansu Zeezee. Nocking nayi mai gadi ya leƙo, buɗe min ƙofar yayi yana washe min baki yace.

   "Sannu da zuwa Hajiya." 

       "Yauwa Baba." Na faɗa sannan na ɗora da gaishe sa, amsa wa yayi da kulawa yace min.

   "Ai Hajiya ƙaramar tana ciki." Kai kawai na gyaɗa masa na shige ciki. A Palo na samu Zeezee zaune cikin shiri tana jira na.

    "Kullum idan zamu fita sai na jira ki Bestie." Zeezee ta faɗa tana miƙewa tsaye. 

   "Ke kuma kullum sai kin yi ƙorafi ba, yanzu dai ina Mom in gaishe ta mu wuce." Na faɗa ina zagaya idona a Palon.

   "Tana shashen Dady, kizo mu wuce idan mun dawo kya gaishe ta." Zeezee ta faɗa tana jan hannuna muka yi gaba. Sai da muka fita Compound sannan ta nufi ɓangaren Yaya Abdul ɗin ta masa magana.

   Bata jima da shiga ba suka fito tare da Yaya Abdul ɗin.

    "Good evening Yaya Abdul." Na gaishe sa da girmamawa kamar yanda na saba. Amsa min yayi da kulawa sannan yace.

   "Bismillah muje ko." Yayi maganar idanunsa a kaina yana sakin murmushi. Duk baya muke ƙoƙarin shiga ya harare mu yace.

   "Waye zaku mayar driver ɗinku." All ready Zeezee ta riga ta shiga, don haka na fasa shiga bayan na shiga gaban da ya buɗe minda kansa. 

   "I'm sorry Yaya Abdul." Na faɗa ina duƙar da kaina ƙasa.

       "No kar ki damu, ai ba laifinki bane, laifin ƙawarki ne." Ya faɗa yana min murmushi, murmushin nima na mayar masa ban ce komai ba ya tashi motar muka wuce, Zeezee dake baya tace.i

   "Kai Brother akwai abinda zamu tattauna da ita fa." Juyawa yayi ya maka mata harara yace.

   "Ai kuwa zan sauke ki a nan idan baki min shiru ba." Shirun kuwa tayi tana tura baki gaba, murmushi na saki ina tuna namu rikicin ni da Ya Aryan.

***** Babban shopping mall Yaya Abdul ya kai mu muka sayi duk abinda muke buƙata, hatta kayan da Birthday girl zata saka mun saya wata haɗaɗɗiyar Birthday gown ce muka zaɓo. Nima na ɗauko wacce zan saka da sauran abinda nake buƙata, sai gab da magrib muka koma gida da kaya niƙi-niƙi.

   Muna zuwa nace zan wuce gida saboda magrib data kawo kai, kuma bana kai wa magrib a waje.

   "Ni zan wuce gida Bestie, gobe in sha Allah zan dawo mu ƙarasa abinda ya rage." Na faɗa ina miƙewa tsaye.

   "Ki bari mana ayi magriba mu duba kayayyakin sai mu kai ki gida ni da Yaya Abdul. Zeezee ta faɗa tana buɗe laidar dake gabata.

   "A'a Bestie Momy tace kar na kai magrib, in Allah ya kai mu goben ma duba." Na faɗa ina duba agogon dake manne jikin bangon Palon, saukowar Mom ɗin Zeezee daga sama yasa na mayar da hankalina kanta na gashe ta da girmamawa.

   Da kulawa ta amsa min da tambaya ta Momy, nace mata tana lafiya, tana gaishe ta.

   "Masha Allah, ki gaishe min da ita." 

    "In sha Allah zan sanar mata." Na bata amsa sannan na juya da niyyar tafiya.

   "Muje na sauke ki." Ya Abdul ya faɗa yana bin baya na, miƙewa Zeezee tayi ita ma ta biyo baya na. Har bakin mota ta raka ni ta buɗe min gaba na shiga ta rufe sannan ta ja baya tana ɗaga min hannu.

*****  Hira Yaya Abdul ya riƙa min a hanya ina amsa masa da "eh" da "a'a" har muka ƙarasa gida. Cewa na yi ya sauke ni a ƙofa amma yaƙi amincewa, horn yayi security ɗin dake bakin ƙofar ya leƙo don ganin waye.

   Sauke glass yayi na leƙa na masa magana sannan ya koma ya buɗe ƙofar, har ciki Yaya Abdul ya shiga sannan ya tsaya, buɗe wa na yi na fita sannan na tsaya zan duƙa in masa godiya. Gani na yi ya buɗe ƙofar ya fita ya zagayo inda nake tsayen yana min wani irin kallo.

   "Thank you Yaya Abdul." Na faɗa ina ƙoƙarin juyawa zan tafi ya dakatar dani, komawa yayi cikin motar ya ɗauko wata ƴar ƙaramar bag ya miƙo min yana cewa. 

   "Ga wannan." Bag ɗin na kalla na kalle sa ina neman ƙarin bayani.

   "Take it." Ya faɗa yana ƙara miƙo min. Hannu na saka na amsa nayi masa godiya sannan na juya na shige ciki. Ina shiga cikin Palo ana ƙwala kiran sallar magrib.

   Kitchen na nufa don can na jiyo Muryar Momy tana yi wa Bintu magana.

  "Sannu da aiki Momy, na dawo." Na faɗa lokacin dana shiga Kitchen ɗin ina rungumeta ta baya.

   "Yauwa Meerah, sai yanzu kuka dawo?."

   "Eh Momy, mun yi sayayya da yawa ne. Ko kayan bamu duba ba ma na taho gida." Na bata amsa ina lumshe ido cike da gajiya.

   "Okay Maza aje ayi haramar sallah to." Momy ta faɗa sannan ta ɗora da bawa Bintu umarnin kwashe abinci ta kai dining.

   "Okay Momy." Muka faɗa nida Bintu sannan muka kwashi food flask ɗin muka fita, ina ajiye na hannuna na haye sama. Bintu ce ta koma Kitchen don ta ƙarasa abinda ya rage.

   Kai tsaye bathroom na shiga nayi alwala na fito na tayar da sallah, koda na kammala Alqur'ani na ɗauko na shiga biya haddata kamar yanda na saba. Sai da aka kira isha'i na ajiye na gabatar sannan na fita neman abinci.

   Bayan mun kammala cin abinci yau ban zauna zaman hira ba, kasancewar duk babu ƴan hirar. Ya Aryan da Ya Jawad sun fita, Momy ce kawai don haka nayi shigewa ta.

   Wanka na shiga na yi, na yi brush na fito. Shirya wa na yi cikin rigar bacci pink color kasancewar ita best color ɗina, shi yasa mafi yawan kayana pink color ne. Gado na hau na ɗauki IPad ɗina zan buga game idona ya sauka saman bag ɗin da Yaya Abdul ya bani.

   Tunda na shigo ɗakin na ajiye ta saman bed side drawer na manta da al'amarinta, sai yanzu da na ganta na tuna. Hannu na miƙa na ɗauko ta na leƙa abinda ke ciki, haɗaɗɗun chocolates ne masu tsada a ciki.

   Kasancewata shazumama sarkin shan zaƙi yasa murmushi suɓuce min, hannu na saka na shiga ciro su ɗaya bayan ɗaya ina dubawa.

   "Thank you Yaya Abdul." Na faɗa ina kwashe su na mayar, bayan na cire wanda zan sha. Game ɗin da nake matuƙar so n shiga bugawa ina shan chocolates ɗin da suka min daɗi sosai.

   Ƙarfe 10:00pm na fara jin bacci, ɗin haka na ajiye Tab ɗin na shiga bayi na sake yin wani brush ɗin na ɗauro alwala sannan nazo nayi addu'a na kwanta. Ina kwanciya Momy ta shigo duba ni ta ƙara yi min addu'a ta gyara min abin rufa.

   "Good night Momy." Na faɗa ina sumbatar hannunta.

   "Good night Meerah." Ta faɗa itama tana sumbatar goshina sannan ta fice bayan ta dai-daita min Ac ta kashe min hasken ɗaki.


★★★

   Washe gari Zeezee ce tazo ta tashe ni a bacci, don bacci nayi sosai har ƙarfe 10 ban tashi ba.

   "Wai Bestie har damar bacci kika samu bayan kin san abinda ke gabanmu?." Muryar Zeezee ta ratsa kunnuwana a cikin barcin dake matuƙar yi min daɗi.

    Slowly na buɗe idona na kalleta a fizge na mayar na kulle, Cike da masifa ta janye abin rufar tawa tana cewa.

   "Allah baki isa ba tashi zaka yi!."

   "Please Bestie ki bari ba yanzu ba."  Na faɗa cikin muryar bacci ina ƙara janyo abin rufar.

    "Labari mai daɗi fa nazo maki da shi, ki tashi Malama." Ta faɗa tana ƙara janye min abin rufar, na san idan ban tashi ba masifar Zeezee ba zata bar ni ba. Tashi na yi ina miƙa haɗi da addu'a sannan na zuba mata idanuna ina mata kallon, bani labarin.

   Ai kuwa gyara zama tayi cike da farin ciki tace.

   "Kin san waye ya min waƙar birthday ɗina kuwa?." 

   "Sai kin faɗa." Na bata amsa cikin muryar baccin da bai ƙarasa saki na ba.

   "Mawaƙina Nawaz Baffa!." Ta faɗa cike da farin ciki tana ɗaukar wayar da tazo da ita ta shiga nemo waƙar. Na daɗe ina jin sunan Nawaz Baffa da waƙoƙinsa a wurin Zeezee, tana matuƙar son waƙoƙinsa sosai don tana dasu da yawa a Tab ɗinta.

    Ita ce ta koya min sauraron waƙoƙin nasa, kuma sai suke yi min daɗi sosai, kasancewarsa mawaƙin soyayya da yake yin waƙoƙin masu matuƙar daɗi da sanyaya zuciya. 

    Duk da cewar har yanzu bai samu wata babbar ɗaukaka ba, don babu wanda ya san sa a fuska. Tunda bai taɓa hawa waƙarsa yayi video kamar yanda mawaƙa ke yi ba.

   Sauka nayi a saman gadon na shiga bayi na wanko bakina sannan na fito na fuskanci Zeezee nace.

   "Amma a ina kika samo shi Bestie, keda baki san shi ba. Sannan har yanzu ba wani sanuwa yayi ba, bare a ce ƴan gidanku za su neme sa?." Nayi mata tambayar.

   "Ai saboda ƙaunar da nake yiwa waƙoƙinsa yasa na roƙi Yaya Abdul na ce masa ya nemo sa ya yi min waƙar birthday ɗina, a matsayin birthday gift ɗin da zai bani. Shine ya nemo sa ta hannun wani ɗan gidan ƙanwar Mom da yace ya san shi tare suka yi Secondary School." Bata jira na yi magana ba taci gaba da cewa.

   "Wai kin san ma wani abin farin cikin?!.".......

   Barka da dare.