NUFIN ALLAH

3

by @anisamuhammadyah897

💕NUFIN ALLAH 💕
By 
Anisa Muhammad yahaya 

Page 3️⃣


Asalin su ammi.......

Alhaji Adam baffayo wani attajiri ne dayazo daga nijar yayi gida a nigeria, da farko aikin kasuwanci ke shigo da shi nigeria, ahankali ahankali mutanen da Kuma yanda kasar ta fara shiga ranshi yasa ya taso daga nijar shida iyalinsa yagina babban gida a Kaduna, saboda yawancin kasuwancin shi Kaduna ne da katsina da Kuma kano, Amman yafi yawa a Kaduna shiyasa ya tare acan.
 yanada mata biyu ta farkon itace 
ya kaka sai Kuma hajja ganah, suna zaune zaman Lafiya tsakanin su.

Ita ya kaka yaranta biyu da ahmad da Kuma abdullahi.
Ita Kuma hajja gana yaranta uku maimuna da safiya da munir.
Duk cikin su ahmad ne babba sai maimuna, safiyya, munir,abdallah ne karami acikin su. kuma duk tazaran shekara 3 ko 2 ne tsakanin su, tsakanin munir da abdallah ne dai wata biyu

Rayuwa suke cike da so da kulawa abun bugewa har izuwa lokacin da yaran suka girma suka fara neman nakan su.
Ahmad ya karanci business admin yayi aure shima a Kaduna, matan sa biyu 
 ta farko itace sahura ana cemata sabuwa Kuma allah yayi mata shegen masifa Dan bata ragama Wanda yamata.
Sai amaryar shi itace harira itakuma saliha baiwar Allah, baruwan ta da duk wani hayaniya da tashin hankali, tana zaune da kowa lapiya shiyasa familyn suke sonta.

Lokacin yaran Ahmad biyu Kuma duk yaran sabuwa ne, duk mata ne da shahida da zuhrah,
Suma maimuna da safiyya sunyi aure.

maimuna ta haifi twins din ta maza hakeem da haleem, ita tana gama secondary school bata cigaba ba. Amman safiya ta cigaba a gidan mijin ta tana karanta nursing yaronta ɗaya alamin.

sukuma munir da abdallah suna University, course daya suke computer engineering, Dan akwai shakuwar me karfi a tsakaninsu, komai tare suke kamar en biyu, in ba fada Maka akai ba ƴan biyu bane bazaka sani ba, saboda komai tare suke, Kuma kamannin mahaifin su suka dauko dukansu, harma gwara abdallah hancin shi irin na ya kaka ne.

Se Bayan shekara hudu ne Allah ya azurta harira Matar Ahmad da ƴan biyu mata kyawawa, Amman ɗayar batafi mintuna goma ba ta koma ga mahalcinta.

 sunyi kuka Kuma sun godewa Allah da ya bar musu dayar bai amshesu duka ba.
Ranar suna yarinya taci sunanta rukayya.

ta taso cikin gata da kulawa gurin mahaifiyar ta.
Lokacin Kuma yaran sahura uku, ta Kara haihuwar mace aka sa mata abida.

Saida rukayya tayi 4yrs tukuna takara haifan juwaira, sai Kuma bayan 2yrs ta haifi Adam, Wanda yaci sunan kakanshi.
Itama lokacin sabuwa nada shahida, zuhura, abida, muneefa da muneef, ƴan biyun data haifa last bata kara haihuwar ba.
Bayan haihuwar Adam ne harira ta fara ciwon a tsatstsaye, takusan 8 months tana ciwo, duk tabi ta rame ga rashin kuzari, Kuma a asibiti in anyi test sai ace ba wani ciwo bane zazzaɓi ne Dan an kasa gane meke damunta, kuskuran daakai shine rashin scanning da ba ai ba se daga baya, Saida aka je akai scanning dinne aka gane tumur ne a brain dinta, daman sign dinshi ba wani yawa ne dashi ba, 
hankalin Ahmad ne yayi mugun tashi yana tausayin makomar yaran shi, ga rukayya yanzu bata fi 8yrs ba, juwaira 4, Adam kuma 2 ,
 gashi ance sai amma ta surgery Kuma it's very risky, za'a iya yi ba'a samu problem ba, kuma za'a iya yi tasamu memory Lost, ko kuma a iya rasa ta,

 preparing na fita da ita waje aka fara amata surgery saboda nigeria basuda kwararan kayan aiki, suna kuma fatan in Sha Allah komai zai tafi daidai

 an gama preparation har an shiya tafiya, ana washe gari zasuyi tafiya, waanda zasu tafi tare duk sun shirya sun zo gidan papi wato Ahmad, da anty safiya da uncle abdallah ne sai shi papi zaayi tafiyan.

A daren ranar Allah yayi mata rasuwa, da safe papi yashiga yaga Allah ya amshi bar shi.
ko sahura da ba shiri suke ba taji mutuwar 

"Lahaula wala quwata illa billah, innalilahi wainnailaihir raju'un, allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha"

 Shi take ta faɗa,tasan harira ba tasan tashin hankali shiyasa koda yaushe take neman ta da tsokana, Amman bata biye mata, ita duk da ake ta rashin lafiyanan bata taba kawo yayi worse ba sai da taji ana kiran za'ayi surgery, gashi Allah bai nufa amma yin ba ya amshi kayar sa.

Kafin 12 zancen mutuwanta ya zagaye ko ina a dangi, yayyinta hafiza da hadiza ne suka fara zuwa gidan.
Akamata wanka aka kai ta makwancinta.

 Allah kasa muyi kyakkyawar karshe.......
 
Da ana zaman makoki ne anty hadiza ta dauki Adam, sai ta hadashi shida hafiz danta dabaifi Adam din ba,  

Itakuma anty hafiza ta dauki rukayya da juwaira.

Amman papi yace iya zuwa agama zaman makoki ne 

Bayan an gama zaman makoki ne
 Papi yace a dawo mishi da yaran sa,

Da farko anty hafiza ƙi tayi, a cewar ta sukadai ne yaran ƴaruwar ta, kuma in tana ganin su sai taji sanyi, nan fa papi yace bai yarda ba.
Da gidan ubansu da komai ba zasu je su zauna gidan mutane ba kamar marayu ba, bayan Yana raye,

Haka juwaira da rukayya suka dawo,
Amman anty hadiza tamai kwarjinin yace ta dawo da adam.

tunda itace tace anty hafiza ta dawo da su juwaira 
Kuma ma itace babba, sai anty hafiza, saikuma Mama harira.

 su uku ne kawai agurin iyayen su, Allah yayiwa iyayensu rasuwa dadewa, bayan anty Hadiza tayi aurene ta dauko mama, harira kenan bayan hazifa tayi Aure ta dawo ƙarƙashin kulawanta,

Kuma ta bashi point masu ƙarfi dayasa dole yabar Adam agurin ta. cemai tayi "ba'a tara ma sahura nauyin yara ba ita kadai ga nata ga na yaran kishiya Kuma harda karamin yaro" 
Shiyasa taga tunda ita tanada sa'an shi sai yafi ta riƙe shi gurinta.

Haka ya yarda badan yaso ba sai Dan ta fishi gaskiya.

Amman wani mamakin da sahura ta bashi shine da ta nuna papur bazata riƙe yaran da ba nata ba, itama taji da nata, maisa bai bari ƴanuwan mahaifiyar su sun ɗauke su ba,zai haɗa ta da aiki to wallahi bazata iya ba.

Haka taita masifa kamar ta ari baki Amman ko uppan be kara cewa ba tunda ya fada mata.
Daga karshe ne da yaga bata da niyan denawa ya daka mata tsawa yace Kar ta riƙe su din sai ya sake ta ya auri Wanda zata hada har nata ta riƙe.

A kiɗime ta kalle shi jin zancen da yake yi da bazata iya daukar shi ba, dududu yaushe harirar ta mutu da zai sake mata wata kishiyar, Bama zai yiwu ba


___________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺