4
💕NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
Page 4️⃣
Ahaka dai ya kashe bakinta, Amman ta dau alwashin muddin suka dawo sai sun gwammaci kida da karatu wallahi, bayan nata yaran shine za'a kawo mata riƙon yaran kishiya, kishiyar ma wacce ta tsana, ta tsani harira saboda sanyin halin ta,
Duk wani sharri da zata kulla mata sai tasan yanda ta fita, ko faɗa ta neme ta dashi ba tanka take ba kuma hakan na mugun ƙular da ita, dan duk hanyar da zata bi ta fitar da ita ta kasa, Saida Allah ya raba ta da alaƙaƙai tukuna zai ce wai zata riƙe yaran ta, ai bama zata saku bane.
Bayan sati biyu dayin haka suka dawo gidan, da farko tamusu tarba mai kyau, saboda Kar papi ya zargi wani Abu su samu matsala.
Shikuma ya dauka ta hakurane, harda shimata albarka Yana kara lallaɓa, yana nuna mata muhimmancin zaman su a gidan ubansu,tunda yana raye bawai mutuwa yayi ba.
Tanuna mai ta fahimci abinda yake nufi, Amman a ranta mugunta kala kala kawai take shiryawa.
Sai lokacin yaji hankalin shi ya kwanta, dan ya yarda da ita, gani yake Banda masifarta ba ruwanta, Amma fa afadar shi Dan baruwa na.
Ahankali ahankali tafara Maida ayyukan gidan kan rukayya.
Da farko sai tace taimata sharan tsakar gida tunda ba abunda take, sai takoma har wanke wanke sai tace su hadu ita da juwaira su koyi aiki tunda maman su kafin ta rasu ba sasu take ba bare su iya, ita nata yaran sun riga da sun iya saura su.
koda papi ya dawo yaga suna aiki yake tambayanta maisa suke aiki ba akwai masu aiki a gidan ba.
"A gaskiya papi kasan ba son masu aiki nake ba kasan ko ada' babu masu aiki a sashi na, kaika kawo wannan na marigayiya, Kuma ni su shahida kemin aiki, and in basu koya yanzu ba sai yaushe,tunda dai ba zaiyu insa nawa suyi musu su suna zaune ba,kuma katuna yara mata ne aure zasuyi wata rana".
haka ta kashe bakin shi yasallami ƴan aikin sashin harira yabar daya kawai yace ita sai ta dunga Taya yaran abunda yafi karfin su,
Daga baya kuma tace ai gwara su dawo part din ta saboda be dace suna zama sukadai ba, gwara su dawo tunda akwai ɗakuna a part din.
Ganin ta samu dama yasa har wanki sai ta dibo ta kawo ma rukayya, hartakai tafara nuna musu kyara da hantara a fili,
Ko da' papi ne ya dawo yagansu su kadai suna aiki, saitace ai saboda basu saba ba ne yasa basa yi da jiki, su zuhura har sun gama nasu sun shiga daki, Kuma karya ne ko cokali bata sa yaranta dauka sai dai su.
Wani lokacin Kuma dasun ji horn din motarn shi, zata ce su abida su amsa aikin su tayasu, daya shigo sai ya gansu gaba ɗaya suna aikin tare,
Idan ya gansu haka suna taimakon juna cike da kulawan juna, ko suna abubuwa tare sai yaji zuciyarshi tayi haske.
Shekaru sun shige Amman ba abu daya canja na yanda umma ke muzguna musu aboye ba tare da sanin papi ba har yanzu,
Adam yakai 9yrs yanzu, yana ziyartan gida akai akai suma kuma suna zuwa.
Allah ya cigaba da daukaka kasuwancin papi har yafara fita kasashen waje saro kayaki da kai kaya, yanzu har takai ma baifi yayi sati biyu ko daya a nigeria ba.
Hakan Kuma yayi mutukar yima umma dadi saboda tana cuzguna musu yanda taga dama.
Komai nagidan hatta da girki rukayya a ƙananun shekaru take yimusu, dan lokacin batafi 10 ba ta fara girki a gidan, tun baya dadi har ta iya, Kuma in baiyi dadin ba ta kamata ta duka kamar Allah ya aiko ta, makarantar ma cemata take in bata gama aiki ba bazata je ba, har gwara islamiya bata hanata a cewar ta koda bata sonsu bazata hana su ilimin addini ba, tunda tasan mahimmanci shi, kar Allah ya kamata da hana su neman addini.
Amman dai boko in bata gama mata gyara ba Saidai ranar kawai taje islamiya.
Ita Kuma juwaira in dai yayarta bazata ba itama bazuwa zatai ba, akwai shakuwa mai ƙarfi tsakanin su Saidai ta zauna ta tayata aiki.
Duk cikin yaran
Umma, zuhura ce kawai take taimaka musu, Kuma ita ce ke tausayin su, inka cire munif da munifa da baruwan su, dan Bama sufi 9yrs ba, Dan sa'an nin Adam ne, watanni ne kawai suka bashi.
zuhura 19 take, abida 16, ita kuma shahida 21, sai rukayya 15, itakuma juwaira 11yrs.
Amman abida da shahida bakin halin maman su ne dasu.
haka suma suke tattaro kayan wankin su, su watsa mata wai tamusu, kamar wata baiwar su.
Itakuma abinda yasa takeyi saboda duk yayyinta ne, ba wanda ya bata ƙasa da one year acikin su. Kuma daman bata iya musu da nagaba da ita ba dan itama Shiru Shiru ce kamar mamanta, Amman juwaira kam shegen tsiwa gare ta, dan tana yawan yimusu rashin kunya, haka zasu gwaɓe ta, Kuma abinda ke ƙona ran rukayya shine yanda suke dukanta kamar wata sa'ar su suka samu, akwai ranar da suka fasa mata gefen baki Saida tayi sati tana jinya.
Abun takaicin da tafadawa umma sai cewa tai "Ai ita tamusu rashin kunya, gwara da suka koya mata lesson, gobe ma ta kara musu".
Kuma tace bazata bata kosisi ba bare a siya mata magani.
Daman ta iya wannan in taje ta tambaye ta kudi dan ta sayi wani abun amfanin saitace
" Ki jira idan papi yazo ya bani wanda zan baku sai in baki,yanzu tunda ba ajiya kika ban ba ko ubanki bai ban in baki ba sai ki tafi ki ban guri".
Tun Lokacin ta yanke zata fara sana'a, saboda ta samu Wanda zata dinga musu Dan abubuwan da be kai ya kawo ba.
aya da popcorn ta fara. dayake papi yana basu kudi duk sanda zai yi tafiya, to bata taɓa nata har na juwaira ma amsa take saita bata kadan daga ciki.
kudin ta dauko tafara tunanin ya zatayi, ta iya popcorn na tukunya, Amman bata san inda ake saida ingredients din ba,
sai da taraba kudin, ta ɓoye rabi tukuna ta fara tunanin in taje islamiya zata tambayi wanda yasan inda ake saida kayan yin aya da popcorn, duk da tasan na aya baza suyi wuya ba
Taje ta fada ma umma, tace "Allah bada saa umma ta gaida Aisha, ita taga zata iya tunda ai bata rasa ci da Sha ba, zatace wai sanaa zata fara Dan munafurci,
Kuma ba abun ta hanata ba tunda sunyi waya da papi tafada mai yayi encouraging nata, harda cewa "ai su mata daman da sanaa aka San su".
Ta fara sanaar ta, Kuma alhandulillah tana ciniki, barin ma in takai islamiya, amma bata bada bashi, ƴan gidan ne dai sai su dauka suce zasu biya ta, Kuma ba abun ta hanasu ba, Amman duk da haka tana cin riba.
Ahaka ahaka aka bada abu sai umma ta amshe tace "ba sana'a take ba ai tana da kudin yiwa kanta tunda sana'a take yi meye amfanin kudin nata datake samu,ko kudi ne papi yabayar ko wani abu sai tace Banda ita meye amfanin sana'an nata,
Kuma Sarai tasan ba wani kudi take samu ba, kawai baƙin cikin popcorn machine din da papi ya siyo mata ne ɗan ƙarin encouragement, and tasan kudin da take samu irin na kashe kanamin bukatun ne kawai, tunda ba bata take ba,idan ta fada mata haka, sai tace bawani sai dai cinyewa take a banza.
Dadinta daya ba ta hanata abinci da zuwa islamiya.
Amman boko kam, kusan 2 weeks kenan rabon da ta bari taje,
ta samu ta lallaɓa juwaira tana zuwa, tunda ita bata hanata ba.
Yau tana can tana ta rizgar wanki, kawai taji umma nata kwaɗa mata kira.
Ashe papi an kirashi daga makaranta, ance rukayya bata zuwa makaranta kusan 2 weeks kenan, and next week zasu fara exams din shiga SS2,so suna son suyi confirming ko lafiya??.
Shine yace baya gida, but bara ya tuntuɓa yaji, in yaji sai ya sanar dasu,
Shiyasa ya kira umma yaji ko dai bata da lafiya ne, ba'a sanar dashi ba.
sai tace
"Eh daman, amm daman ta kwana biyu tana zazzaɓi,shine shine, nace ta zauna, sai yau Monday ta koma, Amman yau din ma batada wani kuzari, shiyasa nace ta bari gobe, and ganin kawai zazzaɓi ne yasa ban fada maka ba"
"Eyya amman ai da an fada mun, banji dadi ba amma nakusa dawowa, inshallah zuwa gobe ko jibi.
Zuciyar umma ce ta doka, wani gumi na tsatsafo mata kar kwabar tai ruwa, tasan yana son yaran shi, amma duk ciki yafison waccan yarinyar, duk da bawai nunawa yake a fili ba, shiyasa tafi muzguna Mata, taƙi jinin ta rike yaran da banata ba, suna gama Wayan ta kwala mata kira, dan so take ta kafa mata warning,
"Wallahi idan har kika bari papi ya dawo yace maisa ba kya zuwa school kika ce Ni na hanaki, nida ke ne, ba iya ke ba har ita juwairan sai nayi silar dena zuwan ta school din kankat kuma saina karyaki wallahi, ta fada tana bangaje ta tayi hanyar toilet.
har ta murɗa handle,ta tsaya bata juyo ba tace, "idan ya tambaye ki kice zazzaɓi kikai, nace ki bari sai gobe kin jini".
"Tom" kawai tace da kyar dan wani abune taji ya tokare mata kirji, yaki wucewa, abin duniya ne ya mata yawa, ga mari ga tsinka jaka, tana son fada ma papi halin da suke ciki a gidan, amma Allah ya sani tana tsoron makircin umma,
yanda take muzguna musu ma a ɓoye ba tare da ta bar alaman da papi zai gane ba, na bata mamaki, koda yayi kokarin gane hakan saita san yanda ta toshe kafar, ga Kuma abinda tace na hana juwaira zuwa school, in taje ta faɗa ma papi Kuma akai rashin nasara, shikenan ta jama juwaira, gwara dai karta faɗa, wani zuciyar kuma na cewa ta faɗa.
kawai ƙasa tsuguna, ta saki kuka iya karfin ta.
zuhura ce ta shigo dan dawowarta kenan daga school, ta ganta tsugunne a parlour tana kuka, ta riga shahida dawowa tunda ba department din su ɗaya ba, level 1take biochemistry, ita kuma shahida na level 2 microbiology.
"Kee ruky meya same ki kike kuka" dagowa tai takalle ta
"Addah nikam ya zanyi, ina son fadawa papi abunda ke faruwa, amma ina tsoron matakin da umma zata dauka, tace kar in kuskura ince ita ke hanani zuwa school.
Ɗaga ta tayi suka shiga ɗakin su, ta zaunar da ita kan gado, hannun ta ta ɗaura kan cinyar ta, tasa ɗayan hannun ta tana share mata hawayen, tana bata hakuri
"Duk da nasan umma mahaifiya tace Amman ina ganin ki faɗa mai duk da nasan matakin da zai dauka be zama lallai yayi dadi ba, dan...."
Bata kara sa mgnar taba kake Jin tasss
Jitai ta dauke wuta na wucen gadi, sai wani walƙiyar da ta gani dan ya zo mata unexpected....
_____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺