5
💕NUFIN ALLAH 💕
BY
Anisa Muhammad yahaya
Page5️⃣
tana ɗagowa taga umma riƙe da ƙugu,
"Munafukar Allah, To aniyar ki yabiki, kece ke kokarin hure wa ƴata kunne ko?? har take kokarin bujire ma uwarta, To wallahi baki isa ba, ƴar yarinya dake Amman sai shegen makirci da munafurci a zuciyar ki irin ta uwar ki, ta mutu tabar irin tsiya, shegiyar yarinya mai fuskan munafukai, micijin sari Kanoƙe".
Juyawa tayi kan zuhura
"Ke kuma tashi mu tafi, wawuya wadda bata kishin uwarta da ƴan'uwanta, sokuwa, wuce kafin ina ɓalla ki, banza kawai, ace kanwar bayan ki ke hure miki kunne".
Saida taji masifar umma ne ta ɗago, ta kalli wa ake ma, dan tayi tunanin ita aka mara, shiyasa ta kasa bude ido sai yanzu.
Haka tatisata a gaba suka tafi.
binsu tai da ido, hawaye na zubo mata, umma bata taɓa ɓata mata rai kamar yau ba, bata taba faɗin abinda ya sosa mata zuciya ya tsaya mata kamar na yau ba, duk ciki ba wanda ya mata zafi kamar zagin mahaifiyarta datai,
Haka ranar ta yini tana kuka, sai lokacin da juwaira ta dawo ne ta kwanta, ta kanannaɗe a bargo dan kar ta ganta tana kuka, koda ta tambaye ta, sai tace mata bata da lafiya,
Ko abinci kasa ci tai, har dare, bacci ma sai barawo ne ya sace ta wuraren 2, bayan tayi sallah, tayi addu'a, ta gayawa Allah.
Koda papi ya dawo ya nemi ya ganta, dayake bata da kuzari saboda abinda yafaru , gaba ɗaya ta zama kamar mara lafiya dan kalaman har yanzu suna mata yawo a rai, tunda bata taɓa mata irin wannan cin mutuncin ba sai jiyan, daman gashi kwanakin duk ta bi ta rame.
"Ƴar babanta ya jikin kalli yanda kika ra..............."
"Papiiiiiiiii" munif ne dasu munifa suka shigo da gudu juwaira beye da su, suna murna ya dawo.
Suna zuwa suka fada jikin shi,ya tambaye su ya suke,ya school,ya ƴan gidan, munif ne yace "papi addah bata da lafiya"
"jiyama ko abinci bata ci ba" fadin juwaira, ta na kwaɓe fuska zatayi kuka, "nima kuma banci ba, saboda batada lafiya".
Murmushi yayi kawai, dan gani yake kamar bayan rashin lafiya bane, akwai damuwa tare da ita, Amman zai zaunar da ita yaji, yana ƙoƙarin ƙara magana ne wayan shi ya fara ringing, ya tashi ya fita.
umma ce ta shigo tana yaƙe, dan fargaba take kar rukayya ta dauki shawarar zuhurah.
Har wunin ranar dai basu zauna ita da papi ba, hakan yama umma daɗi, dan kafin ya fita taji sanda yace mata in yadawo zasuyi magana, kumar har lokacin be dawo ba.
wuraren karfe 8, harta kwanta, munifa tazo tace papi na kiran ta.
Tana zuwa taje har kujerar da yake ta zauna a kusada kafafun shi, tace "papi ina wuni, ya gajiya hanya, ya aiki".
Murmushi yayi,jin yanda ta jero mai tambayar
"Lafiya klau yar babanta, yakike? ya jikin naki?, kinji sauƙi?"
Jinjina mai kai tayi alamun eh
"Ɗiyar babanta meke damun ki??".
Tambayar yazo mata a bazata, kawai sai ta dago ta kalle shi, Sai ta girgiza kai tace "ba komai papi, Banda lafiya ne kawai".
"Wannan ba iya rashin lafiya bane Mama na, ramar tayi yawa ji beki fa kamar a hure ki fadi, kuma duk wanda yaganki yasan kina cikin damuwa, in baki fada ma papi ba wa zaki fadama eh rukayya ?".
Yanda ya mata maganan da sanyayyar murya yasa ta fashe da kuka
Ta kwantar da kanta akan cinyarsa, a zuciyar ta tana tunanin ta faɗi ko karta fadi, se kawai tace
"Daman, daman fa, ina yawan tunanin Mama ne shiyasa, inna tunata sai inta kuka daddare, abinda ya sani rashin lafiya kenan"
jiyayi ta famo mai wani miki a zuciyar sa yace,
"Ai ba kuka ake ba Mama na, addu'a ake, in kina so hankalinta ya kwanta, in kin tunata addu'a zakina yi kinji"
"To in sha Allah zan na yi mata"
"Yauwa haka ake so to tashi kije ki kwanta kinji"
"Toh papi, Allah tashe mu lafiya, ya jikan Mama"
Da Ameen ya amsa mata dashi yana Bin bayan ta da murmushi, a ranshi Yana musu fatan alheri da yiwa harira addu'a.
A bakin kofa suka ci karo da umma, da ta dage ta kafe kunnuwa tanajin me suke cewa, so take taji idan za tace itace take hanata, ko inta dauki shawarar zuhrah.
Zabura tai taja da baya kadan, ganin rukayya ce yasa ta dan dakata tana wani haɗe rai, ita kam batai mamakin ganin ta ba, dan tama yi mamakin da bata ganta aciki ba yau, dan indai zasu yi mgn ita da papi sai ta shigo ta kasa ta tsare, tana mata kallon banza, Amman sai taga bata ganta ba yau.
"Shegiya, munafukar banza, ashe dai ba iya munafurci da makirci kwai kika iya ba, kin shahara a ƙarya" tana maganar tana hararar ta, kuma duk tabarmar kunya ne kawai take son nade shi da hauka.
Ita dai bata ce mata uppan ba, ta bi ta gefenta ta wuce, tana ce mata saida safe.
Haka suka cigaba da rayuwa, Amman yanzu umma ta daina gangancin hanata zuwa school, se dai tace in ta dawo ta mata aikin, dan tana tsoron abinda zai haɗa ta da papi, Amman yanzu mugunta take mata sosai,
Akwai ranar da ta bata tulin wanki tana cikin wankin taji wani abu mai zafi ya ziyar ci kwakwalwar ta, tana duba wa taga reza cikin aljihun kayan, sai ta ijje kayan hannunta datake wanke wa, ta fara laluban kayan ɗaya bayan ɗaya, saida ta fiddo reza uku acikin wasu kayan, kawai sai taji wani abu ya tsaya mata, Yanzu Banda tulin wankin da tabata, ga kwanakin nan da take mata horon yunwa, shine harda sa reza saboda ta illata,gaba ɗaya abin duniya ya ishe ta,wani lokacin sai taji daman itace keda kwarin gwiwa da rashin tsaro irin na juwaira, dan ita basa mata kuma saboda yanda da amma ta zata ta rama ko da sunfi karfin ta, ko kuma tai attempting fada ma papi, shiyasa suke kyale ta, dan banda tana hana juwaira faɗa mai,datuni wani zancen ake, kuma ita gani take kar a fara mai umma ta san yanda tai ta ƙaryata su, kokuma yaƙi yarda,abun da take tsoro kenan.
Tashi tayi takai wa umma reza tace "umma kin manta da wannan acikin Kayan har ciwo suka jimmin".
"Ka ji makira" har zata kara magana sai tai kwafa ta na kallon ta tana girgiza ƙafa,sai kuma tace "riƙe na barmiki".
Galala ta tsaya kallon ta abin ma dariya ya bata, wani zubin idan umma tai abu tana bata mamaki, dan gani take wani abun ko juwaira baza tayi ba.
Fitowar ta parlour kenan daga ɗaki zata je kitchen duba abincin da ta daura,
Taga shigowar wata mata parlourn da sallama, ganin ta yasa matar ke tambayar ta mamanta na nan, gaishe ta tai tace "tana ciki ɗaki Bara a kira ta"
"No bashshi, Bara na hau saman" bata hana ta ba, tunda bata san alaƙarta da umman ba,kar ta hana ta, ya zama wani abun da zai bata headache, Dan Allah yasan bata son tashin hankali,
saman ta nufa, ita kuma ta tsaya kallon ikon Allah,
inka ganta sai kace ba dattijuwa ba, dan ko bata da aure se dai ace bazawara, dan aƙalla zata kai 40 wani abu, Amman shigar jikinta kamar wata matashiyar budurwan da basu jin nauyin fita a haka, tasha fitted gown, ga tsaga ta gefe da gefe har ƙauri, ga mayafin a saƙale a kafada wanda dashi gwara Babu, tana tafe tana chewing gum tana yin bubbles dashi, tana wani rangwaɗa.
Tana hawa sama ta kwada sallama, jin sallama kamar ta aminiyar ta yasa ta fitowa, aikam suna ganin juna suka hau guɗa, aka rungume juna.
'Kaiiii Hajiya kursum, daman ana ganin ki a duniya, yaushe rabon da ki zo gidan nan, saidai inje miki kokuma waya, Kai Amman naji dadin zuwan nan, kinga yanda kika koma kamar ba matar aure ba, kamar bake ba,kin yi kyau fah ƙawata"
"Hmm kedai bari kawaii ai yanzu fantamawa nake yanda nake so wallahi, kawata naga abida a waje Amman sai naga ta sauya mun,tunda nasan zuhura ta girma wannan, kuma dai muneefa ai bata kai haka ba Yanzu,duk da na dade ban ganta ba"
Kodai rukayya kika gani, tunda abida ai tana school taje amsan exam card"
"Okay Amma dai ba ƴar ki bace,dan bansanta ba"
"Hmm kedai ki bari kawai, ai yaran kishiya ta data rasu shekarun baya ce"
Zaro ido tai tace "yara, Bama ɗaya ba"
"Su biyu ne ƙanin su na hannun dangin mahaifiyar su"
"To su maisa biki kaɗa su can din ba kike riƙe su dan inni ce Wallahi bazai saɓu ba wai anyi wa mai dami ɗaya sata, riƙe yaran kishiya, badani ba wallahi, naga ƙoƙarin ki tabb"
"To ai nayi niyyar hakan, har fa dangin mahaifiyar ta su sun ɗauke su, papi yace yafi sonsu wai a gidan shi, yasa aka dawo dasu"
"Dan yasa an dawo dasu,ai kamata yayi ki tada borin baza ki riƙe su ba, sai ya maida su"
"Hmm ai nayi Amman Bai haifar da ɗa ne ido ba, dan har iƙrarin sai ya sake Ni ya auri wadda zata riƙe har nawa, kuma Allah yasan ban fatan barin gidan nan, akan yaran da basu kai ba, gwara dai inta azabtar dasu su gane Allah ɗaya ne, shima ɗin yanzu jina ke kawai zan kyale su, in San hanyar da zan bi su bar gidan, sbd ita karamar rashin kunyar tsiya ne da ita, har ita naso in haɗa in hora su ,Amman ita ba muje ko ina ba tai ƙoƙarin fada ma papi, shiyasa nike kaffa kaffa da ita dan duk makirai ne, kuma ban shirya amsar red card wallahi"
''Ashe baki da wayo,Ai wlh inni ce Allah kasheni bazan riƙe ba, tabb, ai yanzu an dai na Wannan, waya gaya miki borno gabas yake, ai riƙe mijin ki zaki yi a hannu yanda duk abinda kikai zai ji shakkun tankawa, kuma duk abinda kika sa shi shi kawai zaiyi, koda ace dukan su zaki a gaban shi ko uppan ba zai ce ba bare ma ya kalli inda suke, in ba haka ba ai ke zaki wahala"
"Kamar yaya kenan"
Ijje cogalallen mayafin tai gefe tace "wai ke baki yi mamakin yanda nike fantamawa ta ba, ada na isa na fito ko inyi wadaƙa da kuɗi irin haka, Ai tunda aka nuna min wani malami in gaya miki shikenan fa, ga aikin shi kamar yanka wuka wallahi"
"Kee boka fa kenan" ta fadi tana zare ido,
"Koma menene dai badai buƙata ta tabiya ba, gashi yanxu ina cin kare na ba babbaka"
Tunani ta shiga yi kodai zata gwada sa'ar ta
"Kin tabbatar ya iya aiki, kar ayi inyi biyu babu"
"Hmm ai bama zaki yi dana sani ba ƙawata,ina da tabbacin akan malamin nan"
"To shikenan, idan nayi tunani sai in sanarda ke"
"duk sanda kika shirya danni koda yaushe a shirye nake, sai muje in raka ki idan kinyi tunanin dan yanzu ba'a zama haka ai kan mage ya waye"
"Tom inna shirya zan faɗa miki"
Suka shiga wata hirar daban har tai mata sallama ta tafi dan ko abinci cewa tai bazata ci ba.
Bayan kusan 1 month da maganar, A cikin satin kuma juwaira ta saci wayar shahida da ta yi mata laɓe taga password ɗin, ta kira papi Dan ta kasa jure ƙin faɗa mai dan sun kaita bango wannan karon, yanda suka ma rukayya duka akan kawai ta yi ƙarfin halin cewar bazata basu kudin sana'ar ta ba tunda ba biyanta zasuyi ba, shine suka mata duka, sukace wai rashin kunya ta musu,
"Abinda ma kuɗin umma kike sata tunda dai beci ace kin samu wannan kuɗin a popcorn da aya ba"fadin shahida
"Ke se yau kika San barauniya ce ai in kika ga bakiga abu ba a gidan nan ki tabbatar ita ta dauka"
"Yanzu shahida meye haka, ba dole abida ta raina ki ba, kina biye mata kuna wannan jahilcin"
Zuhura da ta shigo yanzu ta faɗi
"Oh nice jahilar"
"Idan baki kama girman ki ba"
Ta nufo gurin ta tada rukayya sukai daki,suko suka bi su da kallo, dan daman ita abida tsoron zuhura take,dan ba face take bata ba dan tasanta da raini.
Juwaira da suka dawo daga makaranta dan lokacin suna school basu dawo ba, taga yanda fuskarta ta kumbura ne, yasa take tambayar
Nan ta faɗa mata abinda ya faru da basa nan Amman ta hanata zuwa gurin su
Ita ko wannan karan bazata yarda ba, da farko zuwa tai ayi duk wadda za'ayi, sai tai sa'an gani password ɗin shahida, nan kawai ta yanke kiran papi,Dan gaskiya ta gaji,su da gidan ubansu Amman suna rayuwa kamar en aikin gidan, barin ma adda rukayya,
Tana ganin ta tashi tabar wayan ta faki idon munif dake zaune a parlourn yana buga video game,ta dau wayan tai garden da gudu.
Tana shiga ta nemi numbern papi tai dailing.
Yana ɗaga wa ta fara kuka, tana faɗa mai abinda su abida suka ma rukayya,harda irin zaman da suke a gidan rukayya nace mata karta faɗa mai tsoro take ji
Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba dajin abinda tace
Sai yace "Ita sabuwar"
"Eh papi"
"kwantar da hankalin ki kinji Mama na, in Sha Allah next week zan dawo, wannan maganar bana waya bane, dan sai an zauna kinji, duk wani plans dina zan yi cancelling Bazan ma kai next week ba, kaɗai ki bari tasan kin faɗa mun"
Kai kawai ta daga kamar wani wadda yake ganinta, ta kashe wayar.
Tana dawowa sukai ido hudu da umma da tai mutuwar tsaye tana kallon ta ta kasa motsa koda yatsa
____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺