BAYA TA HAIHU

4

by @rabiattu0444

https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
BAYA TA HAIHU 

Ummu Maher(Mrs SHU'AIBU)



Page 4



  Wata ƴar matashiyar mata ta nufo wajen mu da sauri, ta tsugunna a gabanmu ta ta ce" ikon Allah ku kuma me yasa su ka dake ku haka? In waje na jiyo alamar ba lafiya a ɗakinnan shi ne na shigo me ya haɗa ku?.

Cikin kuka Badawiyya ta bata labarin duk abin da ya faru. Ta yi shiru fuskarta akwai alamar tausayinmu ta ce" uhum a lokacin da ina kamar ku Nima haka nake shan duka a cikin gidan nan, saboda idan na tuna da abin da ya faru dani kafin shigowata gidan nan sai na ji kamar ma ace su kashe ni na huta, saboda abin da ya faru dani ya sanya na fuskanci wanene ɗan adam zamanin da za kaji ana cewa kada ka yarda da kowa in ba mahaifinka ko mahaifiyarka ba, saboda kana zaton sune ba za su cutar da kai ba amma a yanzu wannan misalin ya shafe saboda na fuskanci Allah ne kaɗai ya kamata ka damƙawa yarda da kuma amana, saboda shi ne ba zai cutar da bayinsa ba saboda shi ke wanda ya ƙage mu ya halicce mu kun ga kuwa ba zai taɓa cutar damu ba".

  Su Mero sai kallon dattijuwar suke, saboda sun kasa gane wannan wani irin misali ne? Ta kawo zancen uwa da uba to ai suma a ganinsu uwa da uba ba zasu taɓa cutar da kai ba tunda babu wanda ya kai su sonka sai da suka tuna da wani abu da ya shuɗe a rayuwarsu, sai suka tuna da suma akwai gudummawar iyayensu a ciki lalacewar rayuwarsu, da yawan iyaye suna aikata kuskure a tunaninsu su kaɗai suke da hakki akan ƴaƴansu su yaran b su da hakki akan iyayensu. Allah da kan shi yace dukkanin ababan tambaya ne akan kiwon da aka ba ku.
 Ganin sun tafi tunani sai ta ce" yanzu dai kuje ku gyara jikinku tunda sun muku duka, zan baku labarin rayuwata kuma ina so ku ba ni na ku labarin".

 Suka yi yadda ta ce, har muka dawo tana zaune akan gadon mu tana jiran mu ta dinga kallon su har suka zauna sannan ta ce" Allah Sarki duniya tun ina shekara ashirin aka kawo ni gidan nan ga shi yanzu shekarata ashirin a wannan gidan".
Dukkansu kallonta suke da mamaki akan fuskokinsu tausayinta ya kama su sosai, su dai a yanzu shekarunsa bai fi 26 ba tun da tun suna ƴan 18 to 19 aka kawo su.
Za ta fara basu labarin ta Mero ta ce" zai fi kyau na ƙarasa ba da labarina Ummah, saboda na fara bawa Badawiyya kinga idan na kammala sai ki bamu na ki ko? Amma duk yadda kika ce".

"A ba da na ki tukunna Badawiyya ma ta ba da na ta, ai ba sauri na ke yi ba ni dai nasan labarina duk ya fi na ku kaico".

  Murmusawa suka yi dukkansu kowa yana tuna badaƙalar da take cikin labarinsa.



CIGABAN LABARIN MERO

   "Wasa_wasa sai abu ya zama gaske, aurena da Hammah Hamzah sai ya kusa zama gaske na ci kuka na ƙoshi babu me rarrashina, ina zaune Anty Hafsah ta shigo ta zauna kusa dani ta dafa kafaɗata sannan ta ce" yi haƙuri ƙanwata gaskiya yanzu na fara son Hammah Hamzah, kuma wallahi dama can ina sonsa saboda ni Allah ya yi ni da son auren me kuɗi, saboda haka zan je na samu Baffah na faɗa masa gaskiya ni na auri Hammah ke kuma ki auri muradin ranki Habibu".

 Wani irin tsallen murna na yi, ina kuka na fara ce wa "Da kuwa kin taimaki rayuwa ka saboda Wallahi idan aka aura min shi komi zai iya faruwa dani saboda son da nake wa Habibu bana haɗa shi da kowa". Muka rungume juna ita Anty Hafsah tana jin daɗi za ta auri me kuɗi ita kuma Mero tana murnar auren talakan saurayinta Habibu.

 Nan da nan magana sai ta canja, domin kuwa Anty Hafsah ta samu Baffanmu ya yi na'am saboda ko waye zai so ya haɗa zuri'arsa da Hamzah saboda yaron kirki ne. A waje ɗaya aka so a  samu matsala da aka kira Hammah Hamzah, domin Baffanmu ya ji ta bakinsa anan ne ya so ya kwafsa har ya buɗe bakinsa zai ce ba ya son Hafsah sai kuma ya tuna da alkhairan Baffanmu a gare shi yana ƙwallah ya karɓi auren dole na Hafsah, wanda da ansan zai zama BAYA TA HAIHU da ba a haɗa wannan mummunan auren da ya tarwatsa rayuwa da yawa ba.

 Mero ta kalli Ummah da Badawiyya tana share hawaye ta ce" wallahi da nasan wannan haɗin auren zai zama masifa da na yarda na auri Hammah Hamzah, saboda auren Hammah Hamzah da Addah Hafsah shi ne zai yi silar zuwa na gidan nan ya rabani da ƴan uwa da abokan arziƙi wallahi da kuwa ko zan mutu sai na aure shi".

  Dukkansu suka tsaya suna kallon Mero, saboda a zahiri basu hango matsalar ba.

Mero ta ce" Tabbas Ammi ta yi baƙin ciki sosai, kuka babu wanda ba ta yi irinsa ba, ga roƙon Baffanmu da take ta yi babu dare babu rana saboda a cewarta ko za ta yi yawo tsirara ba zan auri faƙiri irin Habibu ba na janyo musu tsiya yadda Addah Sailuba ba, Haka dai Ammi ta yi abunta ta gama domin ni dai na sanya dutse na sanya a ƙoƙon kunnena saboda duk abin da za a ce sai na aure shi, shi kuwa Habibu faɗar irin murnar da ya yi ma ɓata baki ne tuni ya yiwa iyayensa maganar nan da nan suka yarda suka nema masa aurena har da sadakinsu dubu ashirin suka zo. Anty Hafsah kuwa dubu ɗari biyu aka kawo sadaki akwatin lefe kuwa sai da aka kawo 12 , ni kuwa ko akwati ɗaya ba a kawo ba saboda ya faɗa min bai yi tanadin komi ba ina ji ina gani ɗan lefen da akewa ƴammata wanda suke tutiya da tunƙaho da shi ni ba a yi min ba, haka dai na haƙura saboda soyayya".

 Ina zaune a ɗaki Ammi ta shigo, da sauri na gaisheta sai na ga ta juya bayanta ma'anar ba ta son ganina sannan ta ce" kin tabbatar ba ki da wata uwar in ba ni ba, sannan har na umarce ki abu ki ƙiyi sannan kice kina son ganin farin cikina, to bari kiji wallahi tallahi in sha Allah wannan auren na ku ba zai taɓa albarka ba, in sha Allah sai wata babbar masifa ta auku a wannan auren, ba dai ni kika ce za ki bijirewa ba to idan ba kiyi wasa ba wannan auren sai ya zama silar kai ki gidan yar..."

 Saurin rufe mata baki na yi ina wani irin kuka me masifar ƙarfi, hawayena kuwa tamkar dai an kunna  famfo idan har ka sanya ƙaramin kofi domin tararsu to dole sai sun cika shi da hawaye. Na durƙushe a wajen ina wani irin kuka tamkar ƙaramar yarinya har da birgima. Ina cikin kukan Baffanmu ya shigo gidan, da sauri ya yo hanyar ɗakina saboda jiyo sautin kukana ya fara tambaya " Uwata me ya faru? Ke da waye".
Ina kukan nake shaida masa mugun fatan da Ammi ta yi min. Jikinsa ya yi sanyi fuskarsa ta canja zuwa ɓacin rai, idanuwansa suka yi jawur kamar jini sannan na ga ya ta shi ya fita daga ɗakin cikin gaggawa kuma a cikin ɓacin rai.

Na jiyo Muryar Ammi tana ce wa "Ai muddin ka ga na yafewa wannan yarinyar sannan na janye maganata akan ta to tabbas ta fasa auren wannan matsiyacin yaron ɗan gidan ɗan caca me shan giya".
 Babu yadda Baffah bai yi da ita ba, sam ta ƙi yarda ganin tana son ɓata masa rai don ta ga ana bin ta yasa Baffah ya ce "Kar Allah yasa ki janye kalamanki ki barsu ai ƴarki ce kuma sannan ke ce kika ɗauki cikinta tun yana wata ɗaya har ya yi wata tara da kwana tara, sannan idan kin so kar ki sa mata albarka in har ni na sanya mata shi kenan".

 Wannan matsalar da aka samu ya sa Baffanmu ya yi gagarumin fushi da Amminmu, sai ya zama ko maganar kayan ɗakinmu ƙanwarsa ya samu ya bata duk abin da ya dace, ita kuwa ta siyo komi yadda ya dace ta bada kwangila aka yi mana kaya iri ɗaya masu kyau, sai dai an samu matsala domin itan ma sai da ta banbanta mu a wajen siyayya Baffanmu gonarsa gari guda ya siyar ya ce ta siyo har da kayan kitchen, a siyayyar kayan kuwa sai da ta siyo na Addah Hafsah ya fi nawa yawa nesa ba kusa ba, domin a kayan ɗaki ma sai da ta sanya aka yiwa Addah furnitures guda biyu komi da set ɗinsa duka masu masifar kyau, ni kuwa guda ɗaya aka yi min, a cewarta wai tuwo girma ai miyarsa nama ce sannan ita Hafsah gidanta hamshaƙin gida ne gari guda, ni kuwa na wa Bama gida bane gidan surukai na zan zauna a ɗaki ɗaya ko kitchen ba ni da shi, shi yasa aka siyo min kayan kitchen ɗin ma kaɗan. Ban damu ba kuma ban yi ƙorafi ba saboda ni ba kayan nake so Hammah Habibu kawai nake so, duk kyara da zagi duk na jure ina ji ina gani har gyaran jiki aka yiwa Addah Hafsah amma Ni babu wanda ya kalle ni. 


 Rannan ina ɗaki na yi Baffan mu yana ta faɗa alamar an ɓata masa rai sosai, ina fitowa na hango shi a ɗakinsa ga ƙanwarsa a gefe ita ma rannan na ta a ɓace na jiyo muryarsa"wallahi sai kin mayar da kayan nan, ni komi iri ɗaya nace a yi bance a banbanta ba, kar ki raba min kan ƴaƴa saboda son zuciyarku to idan ma uwarsu ce ta sanya ki wannan aikin wallahi duk zaku gane da wa kuke". Da sauri Ammi ta fito tana wani huci tamkar dai za ta dake sa, wai don ma tana sha yinsa ne saboda Baffanmu namiji ne a cikin maza, baya ɗaukar raini ko kaɗan sannan dogo ne faffaɗa irin ƙirar ƴan dambe, ko don wannan ma kaji tsoronsa. "Lafiya kika tsaya min a gaba, ko dukana za kiyi ne"?.
Ammi ta ja Gwauron numfashi sannan ta ce" Ni fa kada a shafa min kashin gaji, a barni na ji da baƙin cikin da aka goga min na yi min ƙarfa-ƙarfa a game da auren da za a yiwa ƴata da ɗan gidan ɗan caca me shan giya, sannan ga shi zaune gari banza ba aikin fari balle baƙi, saboda haka na rantse da Allah da Manzonsa ba za a ɗora min laifi ba, cewa nake ina zaune ka ɗauki kuɗinka ka bawa ƙanwarka saboda cin mutunci, ga ni ga yayansu Hamzah baka bamu ba amma wallahi ni abin da ta yi ma burgeni ta yi, ai tuwo girma miyarsa nama idan an siya musu kayan saiti biyu an kai musu suna da wajen ajje su a gidan? To kaga kuwa babu amfanin ɓata goma ɗaya bata gyaru ba".
Bai kula ta ba na jiyo sa yana ce wa" Ta shi ki tafi amma ki sani kin ɓata min rai sosai kuma kije yanzu-yanzu ki aiko min da wancan ɗayan furnitures ɗin wanda ba a ce ki ƙara ba ke kika ƙara".
Ammi ta kasa magana saboda takaici, ko mi ta tuna kuma sai na ji ta ce" Ai wallahi bi'izinillah wannan auren da kake ta ƙoƙarin gyarawa sai ya zama sanadiyyar mutuwar..."


Tas!Tas!!Tas!!!


Ƙarar mari ce ta cika gidanmu, dukkaninmu muka firfirto Ammi ce riƙe da kuncinta wataƙila ma a gigice take saboda ta kasa ɗaga idonta duk suna a rufe, abin da ko car baki ban taɓa ganin iyayenmu suna yi ba sosai abin ya bani mamaki ƙafafuna suka kasa tsayuwa. Baffah cikin fushi ya ce" kije na sake ki saki ɗay...."
Ai ban san lokacin da na dora gaban Baffanmu ba ina kuka na riƙe ƙafafunsa ina ce wa "Don Allah Baffanmu ka yi min rai, ka rufa min asiri kabar Ammi a cikinmu mutuwa za muyi idan babu ita".
Baffanmu ya kalle ni cike da tausaya wa, sannan ya ɗago ni na tsaya a tsaye amma ƙafafuna sai rawa suke tamkar mazari ya ce "Uwata kin san jahilci ya fi hauka ciwo, gani na yi tana son sanyani a matsala ta haifar min da ɗa mara ido shi yasa na yi mata wannan sakin, kuma ba son ki take ba a haka dai tana iƙirarin ita ce mahaifiyar ki amma ina banga alamar hakan ba, da ma ba a gabana ta haife ki ba zan ce tabbas tsintarki ta yi, ai duk abin da ɗan ka yake so to kai ma ka so shi in har bai take Shari'a ba, sannan wannan mugun fatan da alkaba'in da take yi in sha Allah ba za suyi miki komi ba".
Ƙanwar Baffanmu tunda ta dafe bakinta ta kasa magana saboda mamaki, don acan baya kiranta suke da suna matar so, saboda ko cacar baki basu taɓa ganin sun yi ba balle faɗa, har ta kai ga ya mare ta duk da suna ƴar tsana sam ba ta ji daɗi ba amma bata isa ta yi magana ba domin tasan halin Hammah yanzun nan zai zage ta tsaf duk da tana da yara da jikoki.

 Ammi a fusace ta wuce ɗakinta, kukan ma ta kasa yi sai ajiyar zuciya kawai take Su Addah Hafsah suka bita ɗaki da sauri da ita da Humairah ƙanwata, ganin hakan yasa nima na biyu cike da furgicewa.

Wata irin mahaukaciyar tsawa Ammi ta buga min, wacce ta sanya na tsaya cak a wajen saboda gaba ɗaya jikina ya ɗauki ƙyamar ga wani fitsarin wahalar da yake son zubowa.



Magana ta fara yi da babbar murya "Wallahi Maryam aurenki ba zai taɓa yin albarka in sha Allah, kuma wallahi tunda kika bijire min dalilin ki igiyar aurena uku ta ɗaya ta tsinke na yi alƙawarin ko zan yi yawo tsirara wannan tsinannan auren na ki sai ya mutu ko kina so ko baki so, kuma zan faɗa miki da babban murya babu ni babu ke in sha Allah kuma wata babbar masifa sai ta faru dake da zaune gari banzan mijin na ki".

 Tana yi tana haɗa kaya tana kuka, idanuwanta sai zubar da hawaye suke tamkar an buɗe famfo, na daskare a tsaye na kasa ƙarasowa saboda zuciyata ba ki ɗaya ta gama daskarewa kwakwalwata ta tafi tunani na wuccin gadi, anya kuwa ba zan ce na fasa auren Hammah Habibu ba? In har mahaifiyata za ta samu farin ciki zan iya haƙura tuni na yi saurin fitowa daga ɗakin na yo hanyar ɗakin Baffah sai layi nake kamar ƴar wiwi, saboda rabona da abinci tun jiya da daddare shima ba wani na kirki ba, dama tunda wannan al'amarin ya faru na tsangwami kai na a gidan domin nasan a rina wai an saci zanin mahaukaciya.



Mrsßhuaibu ce.
***