MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 48

by @maimunabala209

MATAR GIDA 048



SHUUKRAN/022



YOTA ASSOCAITION





P48



Bayan komawar Ɗalha gida ɗakinsa ya wuce bayan shigarsa ɗaki ne ya yi tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo inda ya bar ɗakin haka ya tarar da shi a tunanin sa Unaisa ta gyara masa, numfasawa ya yi tare da ajiye jakar laptop ɗinsa kan bed side drower daga haka ya rage kayan jikinasa ya wuce bathroom ya yi wanka,bayan fitarsa daga bathroom shirya kansa ya yi cikin wasu sabbin singlet da boxers kafin ya zura jallabiya kalar toka mai matukar laushi,ba tare da ɓata lokaci ba ya wuce kitchen hannunsa riƙe da wayarsa,bayan shigarsa kitchen nan ma ya tarar da tukwane biyu da plate wanda Unaisa ta yi amfani da su,ko kaɗan bai son yin wani surutu saboda haka ya wanke tukwane da plate kafin ya daura shinkafa dafa duka ya cire kaɗan daga cikin kazar da ya siyo ya tafasa kafin ya soya, sauran namar kajen ya zuba su a firij tare da namar rago da ya siya ɗazu,kiran sallar magrib da aka far yi cikin masallatan unguwa yasa ya ya wuce bathroom ya dauro alwala daga haka ya wuce masallaci,bayan an idar da sallah zama ya yi cikin masallaci yana addu'a ya dauki a ƙalla mintina goma yana azkar kafin daga bisani ya shafe addu'a tare da fidda wayarsa ya kira layin Unaisa har wayar ta ƙatse bata ɗaga ba,ya so ya zauna a masallaci sai bayan sallar isha'i ya koma gida amma hakan ba zai yiwu masa ba saboda abinci da ya bari kan wuta,sai da ya yiwa Unaisa kira kusan huɗu amma bata ɗaga ba hakan yasa ya hakura,jiki babu kwari ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da fita daga masallaci a hanyarsa ta komawa gida ne ya tsaya wani shagon unguwa ya siya biredi kafin ya wuce gida,bayan komawarsa gida kitchen ya wuce da sauri Allah ya taimaka ya rage wutan abinci kafin ya tafe sallah hakan yasa abincin bai ƙone ba,nan cikin kitchen Ɗalha ya dire ledar biredi sosai yake jin yunwa rabonsa da abinci tun safe,plate ya dauka ya zuba shinkafar dai dai yadda zai ishesa daga haka ya koma parlour ya samu waje ya zauna ya fara ci,bayan ya gama ci ne ya kai plate kitchen,sai da sake gyara kitchen kafin ya fita ya wuce ɗakinsa hannusa riƙe da gorar ruwa mai sanyi,a gajiye Ɗalha ya shigo ɗaki sosai yake jin bacci amma ba zai iya kwanciya a ɗakin haka ba tare da an gyara ba,tsayawa ya yi yana ƙarewa ɗakin kallo yana tunani,can dai ya samu waje ya ajiye gorar ruwa da yake riƙe da shi daga haka ya shiga gyaran ɗaki,har cikin zuciyarsa a dole yake gyaran ba dan ransa ya so ba rabon da ya gyarawa kansa ɗaki tun kafin ya aure Amirah,haka dai ya daure ya gyara ɗakin har sharar ɗakin ya yi,bayan ya gama share ɗakin ne ya koma kitchen tare da ɗaukar morper da niyyar morping ɗakinsa abinda ya basa mamaki shine Unaisa ba ta wanke morper ba bayan ta gama amfani da shi barinsa ta yi da ƙaurin omo jikinsa duk ƙasa,zuciya babu ɗadi Ɗalha ya dauki morper ya fita da shi fanfo dake compound,sai da wanke shi tsaf kafin ya  wuce ɗakinsa ya fara morping,yana cikin morping ya ji ana kiran sallar isha'i,bayan ya gama morping an idar da sallah a masallatai hakan yasa ya yi sallar sa a gida,kwanciya ya yi shiru yana tunanin zamantakewar sa da Unaisa kwanan sa biyu baya gari ranar da ya dawo ta cusa masa bakin ciki ya je aiki ya dawo a ajiye amma haka ya shiga kitchen ya dafawa kansa abinci, abinda ya fi ƙona masa rai shine yana da tabbacin tana jinsa tun sanda ya dawo amma ta ƙasa fita ta yi masa sannu da dawowa, runtsa idanunsa ya yi murya can ƙasa yana ambaton sunan Ubangiji,ya dauki a ƙallah mintina biyar a haka kafin daga bisani ya tashi ya dauki ledar magani tare da ruwar gora,bayan ya gama shan maganin ne ya cire jallabiyar jikinsa ya rage iya singlet da boxers jikinsa,fita daga ɗakin ya yi ya nufi ɗakin Unaisa,hannu ya kai jikin kofar da niyyar buɗe kofar sai kuma ya tsaya yana nazari can dai ya buɗe kofar,ganin ta ya yi kwance tana bacci hankalinta  kwance kanta babu hula ko dan kwali,sanye take cikin wata rigar bacci da ta wuce mata gwiwa da ƙadan tun daren jiya tasa rigar ko ɗazu da safe Ɗalha ya dawo daga legos rigar ne jikinta,doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke hakan yana nufin yau bata yi wanka ba gaba ɗaya a hankali ya ja mata kofa daga haka ya koma ɗakinsa,bayan komawarsa ɗaki wayarsa ya dauko tare da kiran layin Amirah wayar ta yi ringing har ta ƙatse ba ta ɗaga ba sake kira ya yi nan ma bata ɗaga ba,a hankali Ɗalha ya ajiye wayar tare da gyara kwanciya yana karanto addu'a bacci



















Washe gari karfe takwas da rabi Ɗalha ne zaune parlour yana shan tea sanye yake cikin riga da wando na suit ɓaki sosai ya yi kyau,a gaggauce yake breakfast ganin lokaci yana tafiya hakan yasa ya bar sauran tea da biredi ba tare da ya gama ci ba,cikin sauri ya dauki jakar laptop ɗinsa,har da hutun kwanaki biyu da aka basa ofis jiya bayan ya je ofis ogansa kamar jira yake ya dauki wani babban aiki ya basa,ɗakin Unaisa ya nufa bakinsa dauki da sallama ya shigo ɗakin Unaisa na kwance tana bacci da alama ko sallar asuba bata yi ba,shiga ɗakin Ɗalha ya yi yana kiran sunanta a hankali sai da ya kira sunan ta kusan sau huɗu kafin ta amsa idanunta cike da bacci kallo ɗaya Ɗalha ya yi mata ya ce ''ni zan wuce ofis,zuwa anjima yaran almajirai za su zo suyi sharar compund'' ya faɗa yana cire ƙudi naira ɗari biyar ya miƙo mata tare da faɗin ''in sun gama sharar ki basu wannan'' ya faɗa tare da daura mata kuɗi kan gado har sannan bacci cike a idanunta da ƙyar ta iya furta ''to zan basu'' gyara tsayuwa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''yau zan kasance very busy a ofis dan Allah ki dafa min wani abu kafin na dawo na sani da yunwa zan dawo,sannan duk wani kwano ko tukunya da za ki ka yi amfani da shi ki wanke su pls bayan kin gama'' cikin yanayi na bacci Unaisa ta ce ''to zan dafa'' fita Ɗalha ya yi daga ɗakin ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga mota zuwa ofis,bayan fitar Ɗalha Unaisa ta cigaba da baccin ta ba ita ta farka ba sai karfe tara nan ma yunwa ce ta farkar da ita,sallah asuba ta fara yi kafin ta fita daga ɗaki da niyar zuwa kitchen,nan daining ta ga kofin da Ɗalha ya sha tea daukar kofin ta yi ta wuce kitchen dan samarwa kanta abinda za ta ci bayan shigar kitchen kofin da Ɗalha ya sha tea ta dire cikin sink kafin ta dauki wani kofin ta haɗawa kanta tea nan cikin kitchen ta sha tea kafin ta ajiye kofin cikin sink tare da wanda Ɗalha ya yi amfani da shi tana shirin barin kitchen ɗin ne ta ji ana sallama a can wajen gate,sai da ta koma ɗaki ta zura hijab kafin ta fita ta buɗe gate,wasu yaran almajirai ta gani tsaye jikin gate duk ba za su wuce shekaru sha biyar ba,cike da girmamawa suka gaishi ta kafin ɗaya ya ce ''mai gidan ne ya turo mu ya ce za mu yi shara'' a daƙile Unaisa ta ce ''to ku shigo'' bayan shigarsu tsintsiya guda ta dauka daga ciki ta kawo masu suka fara shara cikin ɗan kankanin lokaci sun share harabar gidan,gidan ya yi tsaf ɗari biyar da Ɗalha ya bata ta dauka ta basu, karɓar kudin sukayi suna yi mata godiya ko kallo ba su isheta ba, babban robar zuba shara dake gefin gate suka dauko sun je sun zubar da sharar dake ciki kafin sun dawo da robar 
















Unaisa na nan kwance cikin ɗaki riƙe da waya tana chating kamar yadda ta saba har karfe biyu saura tana nan kwance da rigar bacci da ta sa tun shekaran jiya,wani saƙo aka tura a group ɗin matan gida wanda ya dauki hankalin Unaisa ganin an yi taging ɗinta fita ta yi daga instagaram ta shiga whatsApp bayan ta buɗe saƙon ne ta ga ba ita kaɗai aka yi taging ba kusan duka mutanen group aka yi taging ɗinsu saƙo aka tura kan taron karshen wata da suka saba gudanar duk karshen wata an rubuta sunan wacce za a yi taron a gidanta tare da address ɗin gidanta,nan aka shiga tattauna batun taron kowacce tana faɗin kalar shigar da za ta yi,nan Unaisa ta saki jiki a ka cigaba da hira da ita,nan ta ɓata lokaci ita ce har karfe huɗu da wasu ƴan mintina,ganin lokaci ya tafe yasa ta ajiye waya tare ta wuce kitchen ndomie ɗaya da kwai ta dafa nan cikin kitchen ta zauna ta ci indomie kafin ta wuce ɗaki,bayan shigarta ɗaki bathroom ta wuce ta dauro alwala,fita ta yi daga bathroom ta dauki darduma ta shimfiɗa hijab ɗinta dake daure kan bed ta dauko ta zura daga haka ta tayar da sallah,gaba ɗaya Unaisa ta manta maganar girki da Ɗalha ya ce ta dafa masa wani abu,duba lokaci ta yi cikin wayarta taga karfe huɗu harda mintina hamsin wata doguwar ajiyar zuciya ta sauki tana tunanin abinda zata dafa masa bayan wasu ƴan sakanni ta dauki wayarta ta yi masa order chicken suya pizza tare coke,tana nan zaune cikin ɗaki har aka kawo mata oder pizza da ta yi,kitchen ta wuce hannuta riƙe da pizza da coke bayan shigarta kitchen plate ta dauko ta cire slice biyu na pizza ta sa a plate tare da rufa plate ɗin, kofi ta dauko ta daura kan tray tare da plate ɗin pizza sai coke ta kai daining ta ajiye daga haka ta wuce ɗaki,bayan shigarta ɗaki bathroom ta shiga ta yi wanka bayan fitarta ta shirya kanta cikin wani doguwar riga materail,karfe biyar da mintina arba'in Ɗalha ya shigo gida ba ƙaramin gajiya ya yi ba ji ya yi kamar an yi masa duka bakinsa dauki da sallama ya shigo parlour hannusa riƙe da jakar laptop ɗinsa babu kowa cikin parlourn a hankali yake tafiya har ya shiga cikin parlour, yana daf da shiga ɗakinsa ne idanunsa ya sauka kan plate dake daure kan daining wani yawu ya haɗe yana sauki ajiyar zuciya,sosai yake jin yunwa rabon sa da abinci tun tea da biredi da ya sha da safe har yanzu babu komai cikinsa,aiki suke kan wata kwangila da aka bawa kamfanin su,sosai kwangilar ke da muhimmaci a wajensa,shugabar Kamfanin daracta ya damƙa kwangilar a hannusa wannan dalilin yasa Ɗalha ya mayar da hankalinsa sosai kan kwangila ko kaɗan bayan son a samu kuskure in har sun yi nasara ba ƙananan kuɗaɗe kamfanin za ta samu ba,bayan Ɗalha ya shiga ɗaki wanka ya yi ya shirya kansa cikin ƙananan kaya farin riga armless da wani wando three qauter wayarsa ya dauko tare da barin ɗakin,bayan fitarsa daga ɗaki daining ya wuce ya zauna kan ɗaya daga kujerun daining wayar hannusa ya ajiye can nisa da plate yana mai buɗe plate ɗin cikin sauri fuskarsa dauke da murmushi,lokaci guda murmushi dake kwance fuskarsa ya ɓace wani irin ɓacin rai ya ziyarce sa lokaci guda,me Unaisa take nufi da shi wannan shi ne abinci da ya ce ta dafa masa? pizza? bayan ya gama kwaso yunwa ya dawo gida ya tadda pizza matsayin abinci dafe kai ya yi yana furta kalmar inna lillahi wa'ina ilahi raji'un sai da ya faɗa sau uku kafin ya kira Unaisa cikin ɗaga murya,Unaisa dake zaune kan darduma ba ta dade da idar da sallah ba ta ji yadda Ɗalha ke kiran ta cikin ɗaga murya tun da take da shi bai taɓa kiran sunanta cikin wannan yanayi ba,tashi ta yi tare ta fita daga ɗakin tana amsa kiran tun fitar ta daga ɗaki yake ƙare mata kallo itama shi take kallo a sanyaye ta ce ''gani'' idon Ɗalha kanta yana nuna plate ɗin pizza dake gabansa ya ce ''me wannan'' fari da ido Unaisa ta yi kafin ta ce ''pizza'' fuskar Ɗalha cike da mamaki ya ce ''pizza?" gyaɗa kai Unaisa ta yi tare da faɗin ''pizza da coke'' gyara zama Ɗalha ya yi kafin ta ce ''oky ina abinci da nace ki dafa min'' fuskar Unaisa cike da mamaki take kallon sa baki buɗe kafin ta ce ''ga abinci nan gaban ka''  ''wanna ɗin ne abinci'' cewar Ɗalha ''kwarai kuwa abinci ne nima shi zan ci na kwanta ba abinci bane daman?" shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya tashi ya bar daining ba tare da ya sake cewa komai ba,da ido Unaisa ta bisa har ya shiga ɗaki bayan shigarsa ɗaki ta dauki plate ɗin pizza ta shiga duba slice ɗin pizza ko wani abu ya sami pizza ne bata sani ba ta ƙarewa pizza kallo amma ba ta ga komai taɓe baki ta yi tare da zama kan kujerar da Ɗalha ya tashi ya fara cin pizza  hankalinta kwance










SHUUKRAN