MATAR GIDA PAGE 49
MATAR GIDA 049
SHUUKRAN/22
YOTA ASSOCAITION
P49
Bayan shigar Ɗalha ɗaki sauya kayan jikinsa ya yi zuwa farar jallabiya mai taushi sosai,makullen motarsa dake daure kan bed site drower ya dauko daga haka ya fita daga ɗakin,nan parlour ya tadda Unaisa zaune tana cin pizza da ta ajiye masa bai ce ba,girgiza kai kawai ya yi ya wuce ta ya fita ita dai ta bisa da kallo tare da taɓe baki,mamakin Unaisa cike fal cikin zuciyarsa ya fita ya shiga mota ya bar gidan, ya yi fushi bai ce pizza ba maimakon ta fahimci fushi ya yi amma sai ta zauna ta sa pizza a gaba tana ci, lallai bata da hankali,kofar wani eatry ya yi parking mota kafin ya fita ya shiga,bayan shigarsa waje ya samu ya zaune tare da yin order tuwon masara da miyar danyen kuɓewa, ya riga ya saba cin tuwo duk dare,bayan ya gama cin abinci biyan kuɗi ya yi kafin ya bar eatry ɗin,daga haka ya nufi gida,ba ƙaramin gajiya ne a jikinsa ba,bayan shigar sa ya tarar Unaisa bata parlour daga haka ya wuce ɗakinsa,ya rage kayan jikinsa kwanciya ya yi tare da lumshi ido,sosai yake jin bacci amma bazai iya yin bacci ba tare da jin muryar Amirah da yara ba, rabon da ya yi waya da ita yau kwana uku hakan ya sa ya dauki waya ya kira layinta,yau ya take sa'a saboda bugu ɗaya ta ɗaga kiran tashi zaune Ɗalha ya yi yana faɗin ''an gama jan ajin kenan'' murmushi mai sauti Amirah ta yi kafin cikin kwantar da murya ta ce ''assalamu alaikum barka da dare Abban Sudais'' shima murmushi ya yi kafin ya ce ''yauwa barkan ki dai ya ki ke ya yaran?" Amirah ta langwaɓar da kai cike da shagwaɓa ta tura baki gaba tare da ajiye apple da take riƙe da shi kamar yana ganinta ta ce ''duk muna lafiya'' numfawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''masha Allah'' daga haka shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni kafin Amirah ta ce ''mun yi waya da Kabir ɗazu'' sai kuma ta yi shiru a hankali Ɗalha ya koma ya kwanta ya rufa idanunsa ya kai hannu kan pillow daje gefensa yana shafa pillow a hankali,murya can ƙasa ya ce ''uhmm ina jin ki'' saida ta saita nitsuwarta kafin ta ce ''na gode Allah ya ƙara buɗe'' kamar bazai amsata ba sai kuma ya ce ''na me'' a shagwaɓe Amirah ta ce ''ya ce ka tura masa kuɗi tun ranar da muka yi magana amma ka ce kar ya faɗa min'' sai kuma ta sake yin shiru can ta ce ''ya turo min ribar da aka samu ne'' Ɗalha na shafa pillow ya ce ''uhmm'' Amirah ta daura da ''suun yi yawah'' cikin wani irin salo tare da karyar da murya ta yi maganar da ita kanta bata san kanta da wannan muryar ba lokaci guda Ɗalha ya ji ya shiga yanayi cike ba juriya da son ɓoye yanayin da yake ciki ya ce "har nawa?" ''950k'' ta faɗa kamar me koyun magana gyara kwanciya Ɗalha ya yi kafin ya ce ''kin gode'' dariya ya bata wai ta gode, murmushi mai sauti ta yi kawai bata ce komai can ta ce ''tnxs again Allah ya ƙara buɗe ya bar min kai'' ita kanta bata san sanda ta furta hakan ba kawai ta tsinci kanta da faɗin hakan sai da ta faɗa ta ji kunya harda rufe fuska kamar yana ganinta tana sakin murmushi mai sauti a hankali shima murmushin ya yi kafin ya ce ''na ki ɗin ne ma'' daga haka ya faɗa mata wani magana da sai da ta zaro idanu waje kamar wacce ta yi mugun gani ''me? kunya ki ke? ki bani amsa'' gaba ɗaya Amirah ta rasa yadda zata yi da Ɗalha kwana biyun nan ya canza mata kamar ba shi ba sai yiy ta sakin magana kamar bai wani yaro,tana tunanin abinda zata faɗa masa ya sake jefo mata wani zencen Amirah bata san sanda ta kashe wayar ba har da wurgi da wayar gefe tana murmushi ita kaɗai,apple ɗin da take ci ɗazu ta dauka da niyya cigaba da ci ta shiga jujjuya shi tana tunani kan abinda Ɗalha ya faɗa mata fuskarta dauke da murmushi can dai ta dauki waya ta yi rubutu layi biyu ta tura masa daga haka ta tashi a hankali hannunta riƙe da blow ɗin fruit da take sha,a hankali take tafiya har ta kai side ɗin Ammi inda ta tarar Ammi da yara zaune suna kallo, cike da hikima ta zauna kan kujera Ammi na yi mata sannu har sannan ɗinki da aka mata bai gama warkewa ba,bayan ta zauna ne Ammi ta miƙo mata wata damammiyar madarar shanu ta ce ''karɓi'' babu musu Amirah ta sa hannu ta karɓa saida ta karɓa ta mayar da dubanta ga Ammi taga ita Ammi take kallo sunkuyar da kai ƙasa ta yi kafin ta ce ''Ammi ban gama shan fruit ɗin ba'' Ammi ta mayar da dubanta ga TV ta ce ''ki fara shan wannan in kin gama sai ki karasa fruit ɗin'' shiru Amirah ta yi ta fara shan madarar kwana huɗu ras da fara shan magunguna amma gaba ɗaya jikinta ya fara canza mata wannan dalilin yasa bata son cigaba da shan magunguna,Ammi ta mayar da dubanta ga Salame ta ce ''je ki yiwa yaran nan shimfida dare ya yi'' ta kare magana tana kallon Salame, yunƙurawa Salame ta yi tana miƙewa tsaye Ammi ta mayar da dubanta ga Sudais da Afef dake buga game cikin wayarta ta ce ''kai Sudais miƙo min wayata ku je ku kwanta dare ya yi''
Fuskar Ɗalha dauki da murmushi yake karanta abinda Amirah ta tura masa ya karanta ya fi a ƙirga sake kiranta ya yi amma bata ɗaga ba sanin kansa ne ba lallai ta ɗaga kiran ba,gyara kwanciya yana rufa jiki da bargo bayan ya rage wutan ɗakin ya rage iya dim ligth kaɗai,a hankali ya rintsa idanunsa yana karanto addu'a bacci,a can wajen Unaisa kuwa bayan fitar Ɗalha zama ta yi ta ci pizza ɗinta da coke ta share baki daga haka ta tashi ta kai plate kitchen daga haka ta wuce ɗakinta ta dauki waya ta cigaba da chat,saƙo aka tura daga group ɗin matan gida inda aka ce kowacce zata iya fara tura dubu talatin ɗinta ga wacce za'a yi taro a gidanta sati biyu masu zuwa, sai a sannan Unaisa ta tuna da zance dubu talatin ɗin taro nan hankalinta ya tashi gaba ɗaya abinda ya rage mata a account dubu saba'in ne da wasu ƴan ɗore,rabka tagumi ta yi tana tunanin inda za ta samu dubu talatin,bayan dogon nazari ta yanke hukuncin siyar da ɗaya daga cikin dogayen riguna disigner's da Ɗalha ya zuba mata cikin lefe cike da kwarin gwiwa ta tashi ta buɗe ɗaya daga cikin akwatunan lefenta wanda take da tabbacin dogayen riguna ne ciki ta ciro wani mai mutuƙar kyau ta ajiye gefe tana sakin murmushi,gyarawa sauran akwatunan zama ta yi kafin ta dauki waya ta kira wata number bugu biyu aka ɗaga kiran,bayan sun gaisa da matar ne Unaisa ta ce mata tana da wata riga tana son siyar, asalin kuɗin rigar dubu tamanin ake siyar da ita amma matar ta cewa Unaisa zata bata dubu hamsin Unaisa bata yi wani ciniki ba ta cewa matar ta yarda daga haka sun tsayar da magana gobe zata tura yaro ya karɓi rigar bayan ta turawa Unaisa kuɗi,cike da farin ciki Unaisa ta kwanta bata sake bi ta kan Ɗalha ba,washe gari da wuri Ɗalha ya tashi ya haɗawa kansa abin kare tea da biredi a gaggauce ya sha ya fita,ko bi ta kan Unaisa bai yi ba karfe bakwai da rabi ya gama komai, fita ya yi zuwa inda ya yi parking motarsa,shiga mota ya yi tare ta ciro wayarsa daga aljihu yana kiran layin Ammi,Ammi dake zaune tana azkar ta ga kiran Ɗalha sosai ta yi mamaki saboda bai saba kiranta a irin wannan lokacin ba amsar kiran ta yi bayan ta shafe addu'a cike da girmamawa Ɗalha ya gaida Ammi,Ammi ta amsa masa cike da kulawa nan Ɗalha ya kwantar da murya ya ce ''Ammi daman na kira ne saboda ban san yaushi su Sudais a za su dawo ba'' Ammi ta ji zancen nasa ya mata wani irin bata tsammaci wannan maganar daga garesa ba kawai ta ce ''ban gane me ka ke nufi ba?" gyara zama Ɗalha ya yi kafin ya ce ''daman ina tunanin ko za su dawo gobe'' cike da mamaki Ammi ta ce ''ina za su dawo'' babu kunya Ɗalha ya ce ''Kaduna'' ita dai Ammi mamaki bai barta ba har sannan kawai ta ce ''ni na ce su zo?" sai a sannan hankali ya fara dawo jikin Ɗalha ya ƙasa bawa Ammi amsar tambayar da ta yi masa ya yi shiru jin ya yi shiru ya sa Ammi faɗin ''wani abun ne ya faru ka ke son su dawo?" ba zai iya faɗawa Ammi abinda Unaisa ke yi masa ba kawai ya ce ''a'a babu komai'' numfasawa Ammi ta yi kafin ta ce ''sai sun gama hutu za su dawo kamar yadda suka saba duk sanda suka zo sai hutu ya ƙare suke komawa'' shiru Ɗalha bai ce komai ba can dai ya ce ''to Ammi Allah ya kaimu'' Ammi ta amsa da ''ameen'' daga haka suka yi sallama shiru Ammi ta yi tana tunani ya za'a yi mutumin da ya yi sabuwar amarya ko wata ɗaya bata yi ba ya fara niman uwar gidansa anya kowa babu wani abu can Ammi ta sauki ajiyar zuciya tana faɗin ''Allah shi kyauta'' a can wajen Ɗalha kuwa ya kira Ammi ne saboda gani yake kafin Amirah ta dawo zai sha wahala a hannu Unaisa tun ba yau ya fahimci Unaisa bata da hankali bata san abinda take ba ya za a yi ya uni da yunwa a ofis ya dawo gida ta bashi pizza da coke ba zai yiwu ba gwara ya kira Ammi ta tura masa Amirah gida a raba girki kafin cutar yunwa ta kamashi, sanin kansa ne ko ya kira Amirah ya ce su dawo cewa za ta yi ya ma Ammi magana yanzu ya kira Ammi ta ce sai sun gama hutu dafe kai Ɗalha ya yi yana tunani,Ɗalha ya riga ya saba duk daren duniya tuwo yake ci mai dumi ya kuma sha shayi kafin ya kwanta,amma tunda ya auro Unaisa babu abinci safe mai kyau babu na rana babu na dare jiki babu kwari yaja motarsa ya tafi ofis
SHUUKRAN