MATA GIDA PAGE 50
MATAR GIDA 050
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P50
Bayan tafiyar Ɗalha ofis meeting suka shiga tun karfe takwas da rabi na safe ba su suka fita ba sai karfe sha biyu na rana,a gaggauce Ɗalha ya je kafterai ya siya snack da drinks ya ci daga haka ya koma ofis sun cigaba da aiki,yau ma kamar kullum Unaisa ta uni kwance tana aikin chating, kamar yadda suka ajiye magana da matar da ta siyar mata da riga hakan ne kuwa ya faru, matar ta tura yaro ya karɓi riga bayan ta turawa Unaisa kuɗi,karfe huɗu dai dai ta fita daga ɗaki ta daurawa kanta abinda zata ci bata bar kitchen ɗin ba saida ta gama dafa indomie bayan ta gama ci ne ta haɗa sallar azahar da la'asar kamar yadda ta saba, tana zaune cikin ɗaki tana tunani ko mai Ɗalha zai ci yau oho ta yi masa order pizza jiya ya nuna bai ji daɗi ba numfasawa ta yi tare da faɗin ''ƙila baya cin pizza ne bara na yi masa order samosa'' ta faɗa ita kaɗai tare da daukan waya ta yi order samosa tana nan zaune cikin ɗaki aka kawo mata oder fita ta yi kofar gate ta karɓi oder tare da komawa gida,bayan shigarta gida kitchen ta nufa tare da dauka wata haɗadɗiyar wormer ta zuba samosa ciki daga haka ta fita daga kitchen riƙe da wormer nan kan daining ta ajiye masa wormer tare da lemo daga haka ta koma ɗaki,ana daf da kiran sallah magrib Ɗalha ya shigo gida a gajiye kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ya gaji sosai tsabar yadda yake jin yunwa idanunsa sun koma can ciki sun yi ja sosai sama sama kansa ke masa ciwo,yana daf da shiga ɗaki ne idanunsa ya sauka kan wormer da Unaisa ta daura kan daining wata doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke ganin wormer daure kan daining ba plate ba yasa zuciyarsa ta raya masa abincin arziƙi Unaisa ta dafa masa yau murya can ƙasa ya ce ''ƙila taliya ce ko shinkafa na sani baza taɓa yin tuwo ba'' ya kare magana tare da shiga ɗaki,bayan shigarsa ɗaki rage kayan jikinsa ya yi kafin ya wuce bathroom ya yi wanka,bayan fitarsa daga wanka shirya kansa ya yi cikin wata jallabiya koriya mai tsamsi sosai yake jin yunwa amma haka ya daure ya fita masallaci dan gabatar da sallah magrib kasancewar an fara kiraye kirayen sallah cikin masallatan unguwa,bayan Ɗalha ya idar da sallah ya yi addu'a ne ya koma gida bai tsaya yin sallar isha'i ba kamar yadda ya saba,bayan komawarsa gida zama ya yi kan daining tare da jan tray ɗin da Unaisa ta daura wormer a kai buɗe wormer ya yi ganin samosa cikin wormer Ɗalha bai san sanda ya ja wata doguwar tsaki ba cike da tsantsan ɓacin rai ya mike tare da nufar ɗakin Unaisa bayan shigarsa ɗakin bai ganta ciki ba,motsin ruwa da ya ji cikin bathroom ya tabbatar masa tana cikin bathroom,karasa shiga ɗakin ya yi yana ƙarewa zanin gado dake shimfiɗe kan katifa kallo,gaba ɗaya yana hargiste babu alamar gyara kamar ta yi dambe da zanin gadon,yana nan tsaye har ta fita daga bathroom fuskarta jiƙe da ruwa da alama alwala ta yi ganin Ɗalha tsaye yasa ta yi saurin kawar da kai gefe ita a dole tana fushi da shi ko kallo bata ishi ba kawai ya ce ''me ki ka ajiye a kan daining?" ba tare da kallon inda yake tsaya ba ta dauke darduma ta shimfiɗa ta ce ''samosa'' jinjina kai Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ok na waye?" numfasawa Unaisa ta yi saboda ranta ya fara ɓaci a takaice ta basa amsa ta ce ''na ka ne'' ta kare magana tana kafesa da ido Ɗalha ya ce ''ok then bana buƙata, je ki dauki abin ki'' yana gama faɗin haka ya fita daga ɗakin da sauri Unaisa ta bi bayansa tana faɗin ''me ka ke nufi ne? jiya na yi maka order pizza ka yi ƙorafi yau na yi maka order samosa still ba ka ci ba me hakan ke nufi?" ta faɗa tana biye da shi shiru Ɗalha ya yi bai ce mata komai ba ya shiga ɗakinsa,bayan shigarsa ɗaki makullin motarsa ya dauka ya fita daga ɗakin,yau ma eatry ya ce abinci,bai yi wahalar kiran Amirah ba kawai ya yi kwanciyarsa sosai ransa ya ɓaci da abinda Unaisa ta masa ya ji gaba ɗaya aurenta ya fita kansa tabbas zai yi maganinta
A can wajen Unaisa kowa bayan shigar Ɗalha ɗaki zama ta yi tana tunani kan halaiyyar Ɗalha har ga Allah bata ga dalilin da zai sa Ɗalha ƙin cin pizza da samosa ba to wai wani irin mutum ne wannan tana zaune bakin gado ta rabka tagumi murya can ƙasa ta ce ''bai san nawa nake kashe duk sanda na yi masa order ba'' numfasawa ta yi kafin ta ce ''in Allah ya kai mu gobe da kaina zan shiga kitchen na yi masa sandwich,maybe ya ci'' washegari kamar jiya Ɗalha ya tashi da wuri ya haɗawa kansa abin kare bayan,ya gama ci ya yi tafiyarsa ofis ita kowa Unaisa na can tana barci ba ita ta farka ba sai karfe tara kamar yadda ta saba kullum,yau ma hakan ta yi,ta uni kwance riƙe da waya karfe uku dai dai ta fita daga ɗaki zuwa kitchen ta yiwa Ɗalha sandwich ta sa cikin wormer daga haka ta koma ɗaki,bayan dawowar Ɗalha kallo ɗaya ya yiwa wormer ya wuce ɗaki,daga masallaci eatry ya wuce ya ce abinci daga haka ya dawo gida,har ya kai kofar ɗaki sai kuma ya dawo ya buɗe wormer da Unaisa ta ajiye masa ganin sandwich yasa ya rufe wormer kawai ya wuce ɗaki,Unaisa ta dauki tsawon sati biyu tana yiwa Ɗalha order sanck dangin fish roll, meatpie,cake,da sauran su,ko sau ɗaya Ɗalha bai taɓa ci ba ita kuma ta ƙi daina ajiye masa a fadinta ta sauƙi hakkinsa dake kanta na kula da cikinsa,shi kuwa Ɗalha da ya buɗe wormer yaga abinda ta ajiye masa ba ya cewa komai kawai sai dai ya dauki makullin mota ya fita eatry ya ce abinci me kyau tsawon sati biyu nan wani irin soyayya suke sosai da Amirah gaba ɗaya ya fita harkar Unaisa sai su yi kwana uku zuwa huɗu basu haɗu ba ita dai bata damu ba hasalima daɗi take ji tun da baya damunta da ƙorafe ƙorafe,Ɗalha ne zaune cikin ofis ɗinsa daga gefensa kuma Muhsin ne suna tattauna batu kan kwangila da aka bawa kamfaninsu,cikin taimakon Ubangiji sun fitar da duk wani project na kwangilar wanda hakan yasa sun yi nasarar samun gaba ɗaya kashe ɗari na ƙwangilar kowanensu fuskarsa dauke da fara'a, ba ƙaramin farin ciki daracta ya yi da wannan nasarar da suka samu ba,wannan dalilin yasa ya yi masu kyautar kuɗi naira miliyan ɗadɗaya bayan wanda kamfanin zata biya su Ɗalha da Muhsin su suka jajerce wajen aiki kan kwangilar,yanzu haka fitar su kenan daga meeting,Muhsin ya ajiye wani file kan tebir ɗin Ɗalha ya ce ''ya maganar tafiya gidan ka ganin amarya yaushe za a je? sanin kanka ne duk wanda ya yi aure ana kai masa ziyara a gai da amarya a ce a sha so Mallam yashe zamu je?" shiru Ɗalha ya yi lokaci guda annurin dake fuskarsa ta ɓace shi dai Muhsin na kallonsa bai ce masa komai ba yana jiran jin abinda zai faɗa,bayan wasu ƴan sakanni Ɗalha ya sauki ajiyar zuciya kafin ya mayar da dubansa ga Muhsin ya ce ''mai zai hana ku bar zuwan kawai na yafewa kowa,ka faɗawa sauran duk na yafe zuwan ba sai sun zo ba''...shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''bafa auren farko bane ƙari na yi so na hutar da kowa'' murmushi mai sauti Muhsin ya yi kafin ya ce ''har oga na faɗa masa ka yafe? ko ka manta har da shi ake tafiya'' dafe kai Ɗalha ya yi kafin murya can ƙasa ya ce ''oh my God'' shi dai Muhsin kallon Ɗalha kawai yake tsaf ya gane dalilin Ɗalha na cewa ya yafe masu ƙila saboda Unaisa ce yasa ya faɗa hakan gyara zama Muhsin ya yi kafin ya ce ''saboda amaryarka baka son mu je gidan ka?" a hankali Ɗalha ya ɗago yana kallon Muhsin can ya ce ''gani nake kamar bata iya girki ba aurena da ita yau watan mu ɗaya amma ko ruwan zafi bata taɓa dafa min ba kullum order shawarma ko cake take yi min,dan rainin hankali sai ta sa samosa ko fish roll cikin kola zaka rantse abinci ne ciki da na buɗe sai naga snack'' tun bai kai ga idah zancen sa ba Muhsin ke dariya shi dai Ɗalha bai ce masa komai ba,sai da Muhsin ya yi dariya iya son ransa kafin ya ce '''tsoro kake kar muje gidanka ta tara mana shawarma da pizza?" shi dai Ɗalha bai ce komai ba kawai ya buɗe file dake gabansa ya fara dubawa ganin bai da niyyar magana yasa Muhsin faɗin ''bafa wani abun damuwa bane dan mun je gidanka matarka ta bamu pizza da shawarma,daman aiy gaisuwa kawai zamu je ba wani abu ba so l think is normal kawai ka faɗa mata zamu zo jibi asabar in Allah ya kaimu'' har sannan idon Ɗalha kan file kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ''oky'' shiru Muhsin ya yi yana nazari can ya ce ''in kuma ka fi son ta yi girki mai zai hana ka kira waccan matar da take yiwa Amirah aiki ta zo ta taimaka mata l think that will better'' shiru Ɗalha ya yi yana nazarin abinda Muhsin ya faɗa can ya ce ''ok shawara ce mai kyau zan kirata,kamar ina da number ta bara na duba'' Ɗalha ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa dake daure kan tebur ɗin gabansa,daukar wayar ya yi ya shiga duba number Aina'u bai dauki wani lokaci sosai ba yaga number nan take ya kira layin bugu biyu ta ɗaga kiran,nan suka gaisa Ɗalha ya yi mata bayani cike da girmamawa ta amsa ta ce babu damuwa gobe za ta zo gidan sai su fara shirya abubuwan da za a dafa,sosai Ɗalha ya ji dadin amsar da ta basa bayan ya kashe waya ne ya mayar da dubansa ga Muhsin ya ce ''gobe zata je can gidana..insha Allah baza a samu matsala ba ko ita Unaisa ba yi girkin ba na tabba Aina'u zata yi komai'' ɗaga kafaɗu Muhsin ya yi ya ce ''is oky hakan ya yi'' daga haka suka cigaba da hirar su,da dare misalin karfe goma Ɗalha ya shigo gidan dawowarsa kenan daga masallaci ɗakin Unaisa ya wuce ya tarar tana sallah, kallon agogon wayarsa ya yi ya ga karfe goma ta wuce harda mintina shidda sai yanzu take sallah isha'i,waje ya samu ya zauna bakin gado yana danna waya bayan ta idar ta mayar da dubanta ta garesa rabon ta da ganin fuskarsa yau kwanaki huɗu kenan taɓe baki ta yi tana cire hijab ɗin jikinta a hankali ta miƙe tsaye tare da ɗaukar darduma da ta yi sallah a kai ta daura kan gado ba tare da kallon fuskarsa ba ta ce ''barka da dare'' shiru Ɗalha ya yi kamar ba zai amsa ta ba sai kuma ya ce ''ya ki ke'' kamar mai ciwon baki ta ce ''lafiya''ajiye wayar hannusa ya yi kafin ya ce ''ok ya yi kyau'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni can ya ce ''in Allah ya kaimu jibi abokan aikina za su kawo min ziyara..am za su zo ganin amarya ne..so za su zo ku gaisa..haka muke a ofis ɗinmu duk wanda ya yi aure ana kai masa ziyara..abu ne wanda mun saba yin sa'' shiru Unaisa ta yi tana ƙare masa kallo gani ta yi kamar ya ɗan rame sai ta yi tunanin ƙila ba shi da lafiya ne kawai ta ce ''ciwo ka ke?" tambayar ta zo masa a ba zata mayar da dubansa ya yi gareta kamar zai bata amsa sai kawai ya share ya ce ''ina son za a dafa masu abinci kamar kala biyu haka,and akwai wacce take taimakawa matata Amirah da aiyukan gida na kirata zata zo gobe, zata taimaka maki da wasu aiyyukan'' ya kare magana tare da kafe ta da ido yana jiran jin abinda zata faɗa a tunanin sa zata yi masa rashin mutunci kamar yadda ta saba duk sanda ya ce ta yi wani abu ga mamakinsa sai ya ji ta ce ''yaushe za su zo'' cike da mamaki ya kalleta kafin ya ce ''jibi'' a takaice ta ce ''Allah ya kaimu''
SHUUKRAN