MASIFAFFAN NAMIJI

39

by @jamilaumarjanafty

MASIFAFFAN NAMIJI..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*



_Wannan Shafin naki ne *MMAN SADIQ...* Ina jin Dadin yadda kike karanta wannan Labarin da Dukkan Zuciyarki...Nagode kwarai Allahu ya bar zumunci Ameen.._


*039*



"Barkat da kafarta ta taka Har bakin Titi,Bata samu Abun hawa ba sai da tazo Wajen makarantar Albani kana ta samu mashin din Daya Dauketa Zuwa Gida Har Ya sauketa Kofar Gidansu ta sauka ta Biyashi Kudinshi Kuka take,kuka mai Cin Rai da Tsanar Hafsah acikin Ranta Domin Tagama bama kanta yakinin itace Silan Faruwar komai.

Koda ta Zo Shiga Gidansu Kofar tana Kulle alama da har sun kwanta Bugawa tahau yi ammh ba Motsin kowa ganin karta tara Mutane yasa ta Fiddo Wayarta Cikin karamar Jakarta ta Kira Bahijjat,tunda ita Tana Gida Bahijjat ta Fara Barci Wayar Barkat ta tasheta Lokacin Da Taga Kiran Ta Tsorata sai da ta Duba agogo Wajen 10pm da wani Abu na Dare Cikin Tsoro ta Daga Kiran Tunkafin ma Tayi mgana Barkat din Cikin kuka Tace tazo ta Bude mata kofar gida Lokaci Daya tana katse Kiran


Hankalin Bahijjat ya Tashi Da Farko kamar ta Fara Shiga Dakin Hajiya ta Tadota sai Taga Ba amfani Tunda batama Jira Taga mai Barkat din tazo Dashi ba ammh acikin Jikinta Tana Ji ba lafiya Sai kawai ta Zari mayafi ta Bude Kofa ta Fice Zuwa Waje ta Zare Sakatan Kofar Tana Bin Barkat da kallo Wacce ta Shigo Dauke da akwatunta Cikin mamaki da Rudani Bahijjat ta Bita da kallo Bata samu Zarafin mgana ba Barkat ta Fada Cikin Falonsu ita kuma sai tayi Saurin maida Gidan ta Kulle ta Bi Barkat din da Gudu Zuwa Falo.

Tana Shiga,sai ta iske Barkat din Jikin Hajiyarsu Tana kuka ashe Hajiya Taji Fitanta zuwa Waje sai ta Fito Taji ko lafiya kafin ma Takai ga Fitowa sai ga Barkat din ta Shigo Da Akwati Tana ja kee tana kuka ganin Hajiya yasa Rauninta ya karu ta Fada Jikinta Tana kuka Hajiyar ta Riketa tana Lallashinta Da Tambayanta Ko lafiya ammh Taki Mgana Bahijjat ta kallo Wacce ta kariso Kusa dasu Tana Fadin"Bahijjat Tare da Megidanta Take ne ko yaya..?

Bahijjat ta saki Numfashi Tana Fadin"a"a Hajiya ita kadai ce.."Cikin Tashin Hankali Hajiya Amina taja ta kan Kujera suka Zauna Lokaci Daya Tana Fadin"Bani Ruwa tasha Sai ta samu Natsuwan yima Bayanin mai ya Faru.."Da gudu Bahijjat ta Runtuma Kitchen ta Dauko Ruwa mai Sanyi ta samu Wani karamin Kofi ta Tsiyaya ta kawo ma Hajiyar ita kuma ta kafa ma Barkat din Abaki Tana Fadin"Sha Ruwa Baraka zaki samu Natsuwa.."

Batayi musu ta karba tasha Da yawa kana ta mikama Hajiya Kofin Tana Sauke wasu Tagwayen Numfashi Lokaci kuma Natsuwarta na Dawowa Jikinta Cikin Sigar Lallashi da Rudani Hajiya Amina ta kalli Barkat tana Fadin"Baraka meya Faru Dake ne..?Ina megidanki Da kika Fito Daga Dakin Mijinki da wannan Daran..? Ina Fatan Allah yasa lafiya..? 

Tafada tana kallonta Jin Haka yasa Barkat ta Barke da kuka Tana Fadin"Hajiya ta shiga Tsakanina da Abdullahi..Tun Zuwana Gidan bata barni na Huta ba komai nayi ma Mijina bana Burgeshi Aduk kalamansa Sunanta ne, akomai nashi Itace kan Gaba Hajiya Shin Nima ba matarsa bace kamar yadda take matarsa ba..? Cewa fa yake Tafini iya komai tafini Biyayyah da Ladabi Hajiya ta Rabamu.."Ta karishe Fada Tana Fadawa jikin Hajiyan Tana sakin Wani Marayan kuka Daga Hajiya Amina Har Bahijjat Dake Tsaye Abun ya Dakesu Cikin Tashin Hankali Hajiya ta Dago ta Tana Fadin"Kinga Bar wannan kukan yi min bayani..? Abdullahin Sakin ki yayi..?

Tafada Cikin Zullumi Girgiza mata kai Tayi kafin ta Dora da Basu Labarin Abunda ya Faru Ta kara Harda karya da gaskiya Ta karishe da Fadin"Wlh Hajiya ita ta Hadamu..Duk Abunda ya Faru itace sila.."Shuru Hajiya Amina Tayi tana wani Nazari Bahijjat kuwa wata Ashar ta lailayoma Hafsah Tana Fadin"Lalle ma Matar nan Shegiya ce..Ahaka kamar ta Allah ashe bata da mutumci bansani ba..! Wlh ban so ki Fito Daga Gidan nan baki Nuna mata ke Haifaffiyar Tudun wada bace ita awa..? Banza a banza da ita.."

Take Fada Cikin Masifa da Fada Dagowa Hajiya Amina Tayi Tana Fadin"Ki Rufemin baki Bahijjat...Banzance komai akan wannan mganar ba Tukunnah..Ammh Tunda har kika ji Mijinki ya Furta matarsa tamai Abunda bkya mai toh Tabbas akwai inda kika Kuskure..Bahijjat kama Hannun Barakat ku Tafi Daki ki sata tayi Wanka ku kwanta mu Jira wayewar gari in Allah yaso zan Kira yayanku muyu mgana in ta kama sai a nemi Shi Abdullahi koma menene sai mu kara ji Daga bakinsa Allah ya kyauta.."Bahijjat zata kara mgana Hajiya ta Dakatar da ita da Fadin"Kar na kara jin wata mgana..Kiyi Abunda nace kawai.."Dole tayi Shuru ta kama Barkat ta Dauki akwatunta da karamar Jakarta Zuwa Dakinsu Hajiya Amina ta bisu da kallo kafin ta kada kai ta koma Dakinta acikin Ranta bata Fatan Auran Baraka ya samu Mtsala ba Saboda komai sai saboda Aure Wani Abu ne,na Rufin asiri.

Bahijjat ita ta lallashi Barkat ta Shiga tayi wanka tazo tayi Shirin kwanciya ta kwanta koda ta kwanta ba Barci take ba,Sai faman Ajiyar zuciya take Tunda ta bar kukan Tun Bahijjat na Farke tana bata baki Har itama Barci ya kwasheta ita kuwa Barkat tayi Barci ne da Tsanar Hafsah acikin Ranta.

****

Kamar yadda Hajiya Amina tace Hakan ce ta Faru da safe ta Kira Salisu a waya tace yazo Tana son ganinshi kafin ya wuce wajen aiki ya Biyo Shima Ganin Barkat agida da Abunda ya faru sai Jikinsa yayi sanyi labarin da Hajiya ta bashi sai yasa Ransa ya baci ya Kira Barkat din yana Mata Fada Cikin kuka take Fadin"Allah ya Salisu ina mai Biyayyah Daidai iyawata.."

Dakuwa yayi mata yana Fadin"Karya kike Wlh..Ke din ne bansani ba mai Shigen Girman kai da isa..Uban waye zaki je gidansa yana auranki kice zaki mai wannan isar naki Ku zauna lafiya..? Kuma Wlh Hajiya karki Ji da waj laifin yarinyarnan ne Tunda kikaji ya Bude baki yace batamai Biyayyah hakane Domin Dama Barkat kina da Gaddama Bamai saka ki bamai Hanaki ke akomai Kina Bin Ra"ayin kanki ne,kuma na Tabbata Shi kika je kina Kokarin nunawa ya Nuna miki bazai Dauka ba Shine kika Maida laifin kan matarsa Tunda ke sakaryace mara Tunani.."


Ya karishe Fada Ransa na kuna Hajiya ta kada kai Tana Fadin"Nima nayi wannan Tunanin Sanin Halinta ba Tun yau ba..Shiyasa ma ban goyi bayanta kuma Allah na Tuba indai Namiji yasan Darajansa kansa yaushe zai zauna mace ta Dinga Iko Dashi kuna yana Auranta..? Har kuma ta Dinga aibatamai mata Duk yana kallo..? Wlh yama kyauta miki da bai miki Shegen Duka ya Hada miki da Takardan saki ba.."

Tafada Cikin Bacin Rai kukan Barkat ya karu ganin ba wanda ya Fahimceta Cikim kuka Take Fadin"Allah Yaya ni..."Katseta yayi yana Fadin"Karki ce min Tak anan wajen..Hali ai zanen Dutse mun sanki Ba tun yau ba babu kuma wanda zai gwadamana Halinki..Wlh kin bani kunya na kuma Dauka Nasihan Danayi miki ta Shigeki Ashe Duk abanza nasha gayamiki wannan Girman kan naki da isarki Ki Ijiyesu agida Domin in kika je dasu gidan wani bazai Haifa miki Da mai Ido ba Kinsa ma naji kunya yanzu da wani Ido zan kalli Abdullahi..? Ta ina ma zan Fara..?

Ya fada yana Dafe kansa Ajiyar Zuciya Hajiya ta saki Tana Fadin"Hakuri zakayi..Ka kirashi Ka Bashi Hakuri su Daidaita bayan Tayi alkawarin zata gyara Halinta.."Salisu yace"Bazan iya ba Hajiya..Zan dai Kira Amininsa Nazifi muyi mgana nace mai ya sameshi su Tattauna in ya yarda sai naje na sameshi muyi mgana.."Hajiya tace"Shikenan Allah ya kyauta na gaba.."Nan ya fice Ransa bace ya bar Barkat nata kuka Hajiya ma Dakinta ta Shige Cikin Takaichin Abunda barkat din ta aikata gashi Bahijjat bata gida Tatafi makaranta.

Salisu yana Fita ya Kira Nazifi a waya sukayi mgana Nazifi yayi mamaki sosai ya kuma Rantse ma Salisu kan Abdullahi bai gayamai Abunda ke Faruwa ba,Daga karshe yayi mai alkawarin zai kirashi yanzu in ya koma Gida Domin yazo nan Cikin kasu yana kamallah ma Jidda Registration dinta,Da haka suka Rabu Nazifi kuwa Acikin Ransa yace dama ai yasam za'a Rina Ko Mata 100 Abdullahi zai kara Aura bazai iya zama dasu ba matukar basu da Hakuri da Biyayyah irin na Hafsah kuma Dukkansu Zasu Dinga Dora laifin kan Hafsah ne Tunda basu san Dawan garin ba.

Bai samu Kiran Abdullahi ba sai Zuwa Dare Don Daga Makaranta Wajen aiki ya wuce sai Dare ya Dawo,bayan ya Dawo yayi wanka yaci Abinci kana ya Fita Haraban Gidan ya Kira Abdullahi saboda bayaso Jidda ta Fahimci Abunda ke Faruwa Sakina dai Bata nan Jiya Ya kaita kano Hajiyarta ba Lafiya sai shi ya Dawo ya barta achan.

Lokacin da Kiran Nazifi ya Shigo Abdullahi na Zaune a kasan Cafet din Dakin Hafsah yana Cin Abinci Hafsah na gefenshi Dauke da Noor tana bata Nono Amir da Amira na Daga gefe suna yi aikin da aka basu a makaranta,Falon yayi Shuru kamar ba Mutane sai Motsim Cokalin da Abdullahi ke Cin Abinci,wanda Fuskarsa take Tamke ba Annuri Tun Jiya Da har garin Allah ya waye bai ma Hafsah mgana ba Data gaisheshi Sama sama ya amsa,Breakfast kuwa Haka ya Fice bai ci ba,Tana so ta karamai Mganar Barkat bata samu Fuska ba sai Taja bakinta ta Tsuke kawai bata ma zaci zai ci Abinci ba in ya dawo sai gashi bayan yayi wanka ya Sauya kaya yace ta bashi Abinci.

Yana ganin Kiran Nazifi Ransa ya bashi wani Abu bai Daga ba sai da ya gama cin Abinci Ya Ture Farantin gabansa ya Dauki Wayarsa ya Shige Ciki Hafsah ta Bishi Da kallo yana Shiga ya Kira Nazifin Bayan ya Daga sun gaisa Da Tambayan iyalai Nazifi ya karkace Baki yana Fadin"Mutumina Dazu da safe Salisu ya Kirani yake gayamin Abunda..."Wani Salisun..? Abdullahi ya katseshi.

Nazifi yace"Salisun dai daka sani Abokinmu yayan Matarka Barkat.."Cikin Basarwa yace"Umh ina jinka sai yace maka me..? Nazifi yace"Gayamin Abunda ya Faru yayi Tsakaninka da Barkat..Abundai bai yi Dadi ba ayadda ya nuna Ranshi ya baci kuma ya bata Rashin gaskiya shida Hajiyarsu yace min kunyarka yake jin in ka bashi Dama yana so ku Hadu kuyi mgana.."Numfashi Abdullahi ya Sauke kafin yace"Dama Nima ina son mu Hadu Dashi..Zan Tambayeshi Dama kanwarsa bata da Tarbiya bansani ba..?

Baki Nazifi ya Rike yana Fadin"Assha..Yada haka Mutumina..? Don Allah karkacemai Haka Shima ai ba laifinsa bane..? cikin Fusata Abdullahi yace"Toh laifin waye Nazifi..? Ace yarinya batasan Darajan Auranta ba ka fa Duba ni kaina ta Rainani ban isa in ce ga Abunda zatayi tayishi ba sai Abunda Taga Dama wai kamar ni abokina ina Fada Barkat tana Fada,kuma wai Daga karshe ta kare  a zagin Hafsah... ? Matata Uwar ya"yana matar Data ke Rufamin asirina na Duniya Itace Abun zaginta Abokina... ? Me Hafsah ta mata..?ni kaima Danake mijinta Bana ce ga laifin Da Tataba min da gangan ba sai Cikin Rashin sani ammh wai har Yarinyar nan zata Bude baki tace ma Hafsatuna Munafuka.! Wlh Kalmar ta Dakeni Mutumina inda Ace Ina Daga Cikin maza masu Duka Da Tuni Barkat tana Chika Emergency Domim sai na sauya mata kammani da Duka kaji ma na Rantse.."


Yafada Cikin Tabbatar da Abunda ya Fada,Dariya ta kusa kama Nazifi ya kanne yana Fadin"Lalle kuwa bata kyauta ba..Ammh Kasani Abunda nake gayamaka abayane yau zan maimata maka..Wlh Tallahi mutumina Ko mata 100 zaka Aura matukar basu tafiyar da kai yadda Baiwar Allah nan Hafsah ke Tafiyar dakaiba, bazaku Taba Shiryawa ba..Fada ne kawai zaku yi Tayi Domin komai suka maka zaka ga ba Daidai bane,Saboda samun mace irin Hafsah sai An Tona Hakurinta Daga Allah ne,wanda Ba kowa Allah ke bamawa ba,Su kuma matan zasu ga suna iya bakin kokarinsu baka gani kullum sai kace Hafsah tafisu Don Allah ko kai ne ya zakaji in Kana Abu ba"a gani kuma ana cewa abokim Hamayarka yafi ka iya komai..? Ka auna Abunda da Mizanin Kishi... ? Don Allah za"a zauna lafiya..? Baza"a zauna ba lafiya ba Fada ce kullum zaku Dinga yi Daga karshe ku kasa Fahintar juna ku Rabu ina amfaninshi..? Sai da na Hanaka wannan Auran kaki jin mganata..? Yanzu ina amfaninshi Aure Wata uku bai ma kai  ba,an fara Jin kanku..? Wlh Duk Abun bai Yi Dadi ba Mutumina sam.."

Ya Karishe Fada Cikin Damuwa,Ajiyar Zuciya Abdullahi ya saki Yana zama Gefen Gado Lokaci Daya yake Fadin"Wlh Duka mganganunka gaskiya ne Abokina..Abaya ban Fahimci haka ba sai da nayi kuma na gani..Hakika Ba mace kamar Hafsah abokina..Zan Tauye mata Hakki maimakon Tayi Fushi sai ma Tamin Godiya zan Mata masifan kan laifin da bada gangan ta aikata ba ammh Ta bani Hakuri zan Kaurace mata Bisa karamin Abu ammh Tabini tabani Hakuri zan Hukunta ta kan laifin da ba nata ba ammh Tabini tabani Hakuri Akullum Hafsah bata Fushi mai Tsawo Dani koda kuwa me zan mata..? Arayuwarta na Hana ta Cikar Burikanta Dadama Abokina ammh Bata Taba Nuna mim wani Abu na Rashin Jin Dadinta ba ita dai Abu Daya ta sani Abdullahi Mijinta ne kuma Bautar Aure take zatayi Hakuri Dashi a Duk yadda yazo mata bakomai take Fata ba sai Aljannah Hakurinta ba irin na Mutanen Duniya bane Mutumina Hakurin Hafsah na Irin Matan aljannah ne Wlh Ina Ji ajikina Tabbas Banga mace wacce zata Iya yima Mijinta Biyayyah kamar yadda Hafsah kemin ba ta Jura Zama da Masifffan Namiji ta kuma koyo Zama dani ahaka Hakika ta Chanchanci kowani yabo na kuma na Fahimci Abunda ya kamata Tuntuni na Fahimta Nagode Mutumina..Insha Allahu zan kira Salisun miyi mgana.."Abdullahi ya karishe Fada Cikin Sanyi Jiki,Shi kanshi Nazifin Jikinsa yayi sanyi Cikin Wani yanayi yace"Duka kalamanka gaskiya ne..Nima sai bayan dana Auri Jidda na Fahimci bai kamata mu Rika ma Abu Dubar duka Daya bane..Wake Daya baya bata Buhu Duka koya aka Tsince za"a samu na kwarai Ina Nadamar Shawarwari  da na Rika baka kana Muzguna ma matarka ina jin kunyar kaina ayanzu na saka ka kana Hukunta matar da bai Dace ta samu komai a wajenka ba Face Soyayyah.."Mirmishi Abdullahi yayi kafin yace"Karka Damu Mutumina..Koda Shawaranka nima da nawa Halin na Saurin Fushi da Zuciya..Ammh Insha Allahi Fushina bazai kara Tashi kan Hafsatuna ba sai dai in Cikin Rashin Sani ne.."

Nazifi yace"Dakyau Mutumina naji Dadin Haka..Sai da safe sai mun kara mgana.."Daga haka suka yanke Kiran Tagumi Abdullahi ya Zabga yana Tuna Irin Abubuwan Dayasha yima Hafsah da alherinta garesa Nadama na kara Shigansa Da kuma wani Sonta da Tsausayinta,Yana nan zaune ta Shigo ta Shimfidar da Noor,bayan Ta kada su Amira sunje sun kwanta tazo Kusa Dashi ta Dafashi ya Dago Jajayen Idanuwanta yana kallonta Cikin Mamaki tace"Abban Amira lafiyanka kuwa..? Kaga yadda idanuwanka Sukayi ja kuwa..?ko Ciwo suke maka ne..?

Ta fada Cikin Tashin Hankali Girgiza mata kai yayi Lokaci Daya ya Mike tsaya ya Rike Duka Hannayenta yana Fadin"Karki Daga Hankali ba komai..Wannan Jan ido bafa komai bane acikinsu illah Tsananin Son Matata HAFSATU da Tsausayinta Uwa uba kuma Sha"awarta Nagaji da wannan Horan naki fa Rabona dake Tun Da Cikin ki ya Tsufa bayan Kin Haihu na Daga kafa kikazo kika gama wanka kikace sai kin gama wayon arba"in kin gama kuma kika Fara jamin aji da nayi mgana sai kice kin barma Amaryani Tagama Morewa kana anya kin min Adalci kuwa..? Kinbar bawan Allah Cikin wani hali.."


Yafada yana kureta da Ido Mirmishi ta saki kawai Tana kallonsa kafin tace"Eh mana...Na bar ma Amarya kai Na wani Lokaci Tunda ai ni Tsohuwar Hannuce ko..? Ya"ya na uku fa Abban Amira..?kallonta yayi ido Cikin ido kafin yace"Zaki iya yafemin Laifikan dana aikata Miki Tun Farkon Auranmu zuwa kawo yau Hafsatuna...?


Mamaki ya Cikata ta Tsuramai Ido Tana kallonsa yadda ya marairaice mata kamar zai mata kuka bata gama mamaki ba Taga yayi kasa ya Duka kan gwiwowinsa Lokaci Daya yana Rike da Hannayenta ido ta kwalalo Cikin mamaki Take Fadin"La'ila..Meye haka Abban Amira.."Ta fada tana kokarin Dagowa yaki sai ma Fadi Daya ke.."Zaki iya yafe ma Abdullahinki Duk da yasan Shi mai Tarin laifi ne gareki..?

Yafada yana sakarmata idanuwansa masu Cike da wani Sirri wanda Hafsah ne kadai ta sani,Tuni Jikinta ya Fara rawa ganin Abdullahi Durkushe agabanta kamar zai mata kuka itama Binsa tayi ta Durkushe Lokaci Daya tana Damke Hannunsa Cikin Sanyin murya tace"A"a Abban Amira bai dace ka Dukamin ba..Ni matarkace kuma ina karkashinka..Kuma aljannata tana Wajenka Abban Amira taya zan ce kamin laifi har na iya Rikeka acikin Raina..? Ko Daya Wlh bakamin komai ba koma kamin Tun Alokacin nake yafe maka Abban Amira Nine ma zan Rokeka ka yafemin Abunda na maka Abban Amira ni yafi Chanchanta na Rokeka gafara kila Ina Kuskure maka ban..."Shiiii! Bai bari ta karisa ba yasaka Dan Yatsansa ya Dakatar da ita Tsurama Juna ido Sukayi na wani Lokaci Kafin ya Bude Baki Cikin wata Murya yana Fadin"Baki Tabamin laifi ba Hafsatuna...Nine dai mai laifin a wajenki..Kuma Daga yau nayi Miki alkawarin Duk wani laifi da zakimin da gangan ko Cikin Rashin sani ni Abdullahi na yafe miki Duniya da lahira..Kuma nayi miki alkawarin Masifaffan Mijinki zai Rikide ya koma Miki Cikakken Masoyi kuma Miji na Hakika aljannah kuma Hafsah Wlh Kin Riga da kin samu Domin Tuni na Daga Miki kika Shiga ke zaki zama Jagoran Matana na gidan al"jannah Nagode Hafsatuna Nagode kwarai Allah yayi miki albarka.."Yafada yana kara Damke Hannuwanta Jikinsa kawai ta Fada tana sakin kukanta Shima ya kamata ya kamkame yana Sakin Numfashi kamar ya saki kukan Lokaci Daya yana Bubbuga bayanta alaman lallashi.

Ganin Taki Tsagaita kukan yasa ya Dagota yana Share mata Hawaye Cikin Shagwaba yake Fadin"Wannan kukan naki nasan mganinsa... " Yafada yana Lakace mata Hanci,Saurin Zillowa tayi ta koma Kirjinsa ta lafe Shi kuma ya mike ya Dagata Cak yana Fadin"Yau ko ana so ko ba"a so sai na More Abuna.."Cikin Dariyan Farinciki tace"Balle ma ana so.."

Tafada tana Zagayo da Hannayenta saman Wuyansa ta makadesa Lokaci Daya tana sakarmai Kiss Bangare mata yayi yana mata Kukan Shagwaba Ahaka suka Shiga Tiolet ya Sauketa ya samusu Ruwan sanyi Cikin Wani Babban Bawan Hafsah da takan Tara Ruwan sama,Dayake garin ana zafi ya Tube itama Hafsah ta Tube ya Dauketa ya Tura Cikin Ruwan Shima ya Shiga Dayake Babban Baho me mai Girma,Watsa watsan Ruwa suka Fara suna Dariya kafin kuma wasan ya Chanza Salo Abdullahi yakamkame Bakin Hafsah yana Tsota gefe Daya kuma yana ta Wasa da Nonuwanta da suka Cika Sakin mata Numfashi kawai yake itama Wasa take da Nipple dinsa Lokaci kuma tana wasa da reaction dinsa wanda ta saka ya Birkice mata yana neman Shigarta acikim Bahon Dakyar ta lallashe shi ya bari suka Fito Daga bayin bayan sun yi wanka Daga Tiolet din Sai kan Gado bama wanda ya nemi kaya suka kama juna Cikin Fitan Hayyaci baka jin komai sai Tashin Numfashi Kamar zasu Cinye juna bamai Saurarama Dan"uwansa kowa kokarin Nunama Dan"uwansa yake yadda yayi kewarsa.


Kusan kwana sukayi suna Abu Daya Stayels kuwa Kala kala ba Wanda basu yi ba sun Jiyar da Juna Dadi Sosai wanda baya misaltuwa sun kuma kara yardan ma juna sun Riga sun zama Hanta da Jini,Sai Wajen 3pm na Dare suka Sararama Juna Suka je sukayi wankan Tsarki Suka Dawo suka kwanta Inda Allah ya Taimakesu Noor bata tashi ba sai gabanin Asuba Ta Fara kuka Barci ya ci Idanuwan Hafsah Dole Abdullahi ya mike ya Dauketa yana Lallashi Acikin Ranshi kuma yana Gode mata Domin ta bashi Dama ya More Dakyau.


Gabadayansu sun makara Sallar Asuba,Makaranta ma su Amira Sai wajen 8am na Safe Abdullahi ya Tafi ya kaisu yabada Hakuri Daganan ya Dawo Gida yayi wanka ya karya Sukayi Sallama da Hafsah ya Fita Zuwa Cikin makaranta Domin Allah ya Taimakeshi ya kusa gama Project dinsa,Dagachan ya wuce Wajen aiki,Wajen 2pm na Rana bayan sun Fita Sallah ya Kira Salisu yace in ba Damuwa su Hadu yace Mai bakomai gashi nan zuwa ba"a Dau lokaci ba kuwa sai gashi Suka samu wani Waje sukayi mgana sosai Salisu ya bama Abdullahi Hakuri Yace mai bakomai Dayayi mai mganar Komawan Barkat Sai Abdullahi yace ta Dakata ba yanzu ba Yana son ta ZAUNA agida Tayi koda wata Biyu ko uku in ta kara Hankali sai ta koma Ammh mganar gaskiya yanzu Baya Bukatarta Duk da bazai Saketa ba Saboda baya son ya zama Namiji mai sakin Aure ammh Tabbas ta zauna agida ta kara sanin Rayuwa da kuma yadda ake ma Miji Biyayyah.

Ba yadda Salisu zai yi ya bashi Goyon Baya suka Rabu akan Haka,awaya ya Kira Hajiya ya gayamata komai da yadda suka kare mgana da Abdullahi Hajiya tace ai yayi mata Daidai gwara ta Zauna agida Sai ta kara Hankali da Barkat Taji labari bata Damu ba tana ganin Dole ya Sauko yazo ya bata Hakuri ya maidata,Ita kanta Bahiya Da tadawo Gida Taji Labari bata Ji Dadi ba kuma itama Barkat din ta Dorama laifi tare da ankaran da ita kuskuranta ammh alokacin Tayi Nisa batajin kira.


****

*Bayan Wata Biyu..*

Zuwa Lokacin Tuni Kowa yasan Labarin Barkat bata Gidan Abdullahi,Labari har gusai Umman Sadiq dataji labari tace ai Daman ta Fada Ba kowa zata iya ZAMA da Abdullahi ba sai Hafsah.

Haka kowa yake fada in yaji Labari Subai kuwa tafi kowa Murna Hafsah kuwa bata ji Dadi ba Duk da Tama Abdullahi mganar Barkat din ya Roketa da Allah da Annabi karta karamai wannan mganar,Dole ta kama bakinta Hakika Abdullahi ya Chanza kamar yadda ya Fada,Domin Yanzu Lallaba Hafsah yake kamar Tsoka daya Amiya sai Dai Abunda ba'a Rasa ba,Fushinsa kuma yanayi Lokaci Bayan Lokaci ammh yana Controlling dinshi ba kamar baya ba Bangaran Kulle kowa Babu Abunda ya Sauya in yayi Ra"ayi Taje in bai yi Ra"ayi ba yace ya Hanata Dole ta Hanu,Bata da yarda zata yi kaifi Daya ne Dama Kuma yana nan bai Sauya ba.

Bangaran Barkat kuwa Bayan Dawowarta Gida Da Sati Uku Suka koma makaranta Tattara ta Tafi Tare da Jiran Tsammanin Abdullahi zai nemeta ya bata Hakuri,Wanda bai taba Kiranta awaya ba Itama Girman kanta ya Hanata ta kirashi ta koma makaranta da kwana Goma Jiri ya Dibeta  Ranar sun Fito daga Lecture ta Fadi aka kwasheta Zuwa Clinic Din makaranta gwajin Farko sai ga Ciki ya bayyana a Gareta dan Wata uku,Yayanta Salisu tace kawayenta su kira mata ta karbi Wayar tamai Bayani Shi yazo ya Tafi da ita Tare da Takardan gwajin Cikin Barkat tafi kowa Murnan da Cikin Domim tana ganin ta samu Hanyar da Abdullahi zai zo gabanta ya bata Hakuri ta koma Dakinta Ko Domin Cikib Jikinta sai dai kuma Kash Batasan waye Abdullahi ba Koda Salisu ya Kirashi ya gayamai bai zo ba Fatan samun lafiya kadai yayi mata sai kuma 20k Daya Turama Barkat din Ta Bankinta yace na Hidimar asibiti kira ko awaya bai yi ba kuma bai je ba,Da Hajiya ma Taga Samuwar cikin Sai Take Fatan komai ya Daidaita ammh kuma Ba Tabbas Domim Tunda Barkat ta Dawo gida bai Tako Kafarsa ba sai da Hafsah ta gayama Su Mama bayan yazo ya gayamata Barkat Nada Ciki tayi kokarin Nuna mai yaje Zuwansa nada Muhimmanci ammh yayi mata Rantsuwan kafarsa bazai Taka ba Tukunnah dai Har yanzu Barkat Batayi Hankali ba in Lokacin yayi zata nemeshi da kanta Wannan Dalilin yasa ta Kira Mama ta gayamata ita kuma ta gayama Inna Abu suka Tafi Gidansu Barkat din suka Dubata,Sun iske ma Taji Sauki Hajiya Aminan tace musu ma Zata koma makaranta sati mai zuwa Karatu nata wuceta,Sauran kayan Sawanta Bahijjat tazo ta Diban mata Wajen Duka Kadan Ta Rage Hafsah na Gida sun gaisa Dai sama sama Tunda Ita Bahijjat din tana Bin Bayan yar"uwantane.

Tun Barkat na saka Ran ganin Abdullahi har ta sare Tana ji Tana gani ta Tattara ta koma makaranta Lokaci Daya tana Cigaba Da Renon cikinta,Don ma Suna Tare da Bahiya tana Taimakamata Sosai Tunda Har yanzu a wajenta Take Sukwatin.






*Janafty*