WA ZAI FUSKANCE NI??

Chapter 8

by @umsar

‎WA ZAI FUSKANCE NI??

‎BOOK 1

‎Umma Mustapha

‎@umsar Arewapen

‎Wattpad: Umma Mustapha

‎PAGE 8

‎Kwanaki suka sake ja.

‎Bayan an tabbatar da admission ɗin Nihla, gidan ya fara ɗaukar wani sabon salo.

‎Maganar makaranta ba ta ƙarewa a gidan.

‎"Yaushe za ta tafi?"

‎"Me za ta tafi da shi?"

‎"Me ya rage a saya?"

‎Waɗannan su ne tambayoyin da suke ta yi wa junansu.

‎Kowa yana cikin shirye-shirye.

‎Kowa yana ƙoƙarin ganin Nihla ta tafi da duk abin da za ta buƙata.

‎Amma ita kanta Nihla...

‎Duk lokacin da ta tuna cewa ranar tafiyarta tana ƙara kusantowa, sai jikinta ya yi sanyi.

‎Wani lokaci har ta kan zauna ita kaɗai, tana kallon kayanta da aka fara tattarawa, zuciyarta cike da tunani.

‎"Da gaske zan bar gida?"

‎"Da gaske zan kwana a wani wuri dabam?"

‎"Yaya zan yi ba tare da Hajiya Mama ba?"

‎Waɗannan tambayoyin suka dinga yawo a zuciyarta.

‎Nihla ba ta taɓa zuwa wani gari ta kwana ba.

‎Tun tana ƙarama, gidansu ne duniyarta.

‎A nan ta tashi.

‎A nan ta yi karatu.

‎A nan ta saba da muryoyin 'yan uwanta, da zolayar Hafiz da Fa'iz, da hayaniyar 'yan gidan da ta saba ji kullum.

‎Amma yanzu...

‎Za ta bar komai.

‎Ba don wasa ba.

‎Ba don yawon buɗe ido ba.

‎Saboda ilimi.

‎Burin da ta daɗe tana mafarkin cikawa.

‎Wani lokaci idan fargabar ta yi mata yawa, sai ta lumshe idanuwanta ta yi dogon numfashi.

‎"Jami'a fa..."

‎Sai ta yi murmushi a hankali.

‎A nan ne burinta yake.

‎A nan ne za ta fara wani sabon babi na rayuwarta.

‎Tana son ta ganta a makaranta.

‎Tana son ta shiga aji da, ta zauna cikin sauran ɗalibai, ta ji ana kiran ta da 'yar jami'a.

‎Har ma wani lokaci idan ta tuna Hafiz da Fa'iz, sai ta yi murmushi.

‎"Yanzu kam ba za ku ƙara samun damar tsokanarta ko su dameta da labarin makaranta ba."

‎Sai ta ɗan yi dariya ita kaɗai.

‎Sai dai abin da Nihla ba ta sani ba shi ne, jami'a ba karatu kaɗai za ta koya mata ba.

‎Za ta koya mata rayuwa.

‎Za ta koya mata yadda ake mu'amala da mutane daban-daban.

‎Za ta koya mata cewa ba kowane murmushi ne yake nufin ƙauna ba.

‎Ba kowane mutum da ya kira kansa aboki ne yake zama alheri ba.

‎Kuma za ta koya mata wasu darussan da ba za ta taɓa mantawa da su ba.

‎Shirye-shiryen tafiya kuwa suka ƙara kankama.

‎Babu abin da aka bari.

‎An saya mata sutura masu yawa, kayan abinci, kayan kwalliya, takalma, hijabai, jakunkuna da sauran abubuwan da za ta buƙata.

‎An shirya komai.

‎Kayanta suna killace a dakinta, ranar tafiya kawai ake jira.

‎Anty Asiya ma ba a bar ta a baya ba.

‎Tun daga Gombe, ta bayar da saƙo a kawowa Nihla.

‎Pant da bra, hijabai, takalma, da sauran abubuwan amfani.

‎Lokacin da Nihla ta buɗe kayan, sai ta yi murmushi.

‎"Anty Asiya tawa... ina matuƙar ƙaunarki."

‎Ta buɗe kayan tana dubawa, murmushin na ƙara bayyana a fuskarta.

‎Hajiya Mama kuwa, tun ranar da aka ce Nihla ta samu admission, bakinta bai huta da nasiha da faɗa ba.

‎Kullum sai ta tunatar da Nihla.

‎"Ki kula da kanki, Nihla."

‎"Ki riƙe mutuncinki. Kada ki bi ƙawayen banza. Ki san irin mutanen da za ki yi mu'amala da su. Duk inda kika je, ki tuna mutuncin gidanku da kuma martabar gidanku."

‎A duk lokacin da Hajiya Mama take mata irin wannan tunatarwar, sai Nihla ta ce:

‎"In sha Allah, Hajjajuna."

‎Kullum maganar kenan.

‎Idan karatu ne, yaci ace Nihla ta haddace.

‎A ɗaya ɓangaren kuma, 'yan uwan Nihla sun yi rawar gani, kowa da irin gudunmawar da ya bayar.

‎Yaya Umar ya aiko mata da sabuwar waya kirar Apple tare da power bank.

‎Lokacin da Nihla ta ga wayar, sai ta yi ihu da farin ciki.

‎"Wayyo! Yaya Umar!"

‎Ta ɗaga wayar sama tana murmushi.

‎"Allah Ya saka masa da alheri."

‎Kowa ya yi dariya.

‎"Yanzu kam 'yar jami'a ta samu waya."

‎"Ki kula, kar ki je kina danna waya ki manta da karatu!"

‎"Wallahi, za mu dinga kawo miki ziyara mu ga kina karatu!"

‎Nihla ta yi dariya.

‎Ba ta ba su amsa ba saboda hankalinta yana kan sabuwar wayarta.

‎Irin waɗannan hirarrakin da suke yi da kuma dramarsu sun sa ta ji kamar ba ta son tafiya.

‎Tabbas ta san za ta yi kewarsu sosai.

‎Za ta yi kewar hayaniyar falon.

‎Za ta yi kewar Hajiya Mama.

‎Za ta yi kewar gidansu.

‎Uwa uba kuma, za ta yi kewar rayuwar gidansu mai cike da farin ciki.

‎An gama komai.

‎Ranar tafiya kawai ake jira.

‎Ana gobe Nihla za ta tafi, Yaya Babba ya zo gidan da daddare.

‎Ya ce wa Hajiya Mama:

‎"Nihla ba za ta samu ta fiya gobe ba. Maybe sai zuwa wani satin, saboda har yanzu ba ta samu accommodation ba."

‎Hajiya Mama ta ce:

‎"Ba damuwa. Da gobe da wani satin, duk ɗaya ne ai. Allah Ya sa hakan ne mafi alheri."

‎Shiru ne ya biyo bayan maganar tasu.

‎Kowa da abin da yake cikin zuciyarsa.

‎Shi Yaya Babba yana tunawa da wayar da suka yi da abokinsa dazu, da kuma irin shawarar da ya ba shi a kan Nihla ta zauna a off-campus, tunda ba ta samu accommodation ba.

‎Sam, shawarar ba ta kwanta masa a rai ba.

‎"Yaran da suke zaune a cikin hostel ma ya aka kare su, bare kuma waɗanda suke off-campus? Sai wanda Allah Ya tsare."

‎Yana ganin idan Nihla ba ta samu ɗaki a cikin hostel ba, to sai dai ta hakura da karatun.

‎A jira wata shekarar.

‎Ko kuma ta hakura da karatun gaba ɗaya.

‎Domin bai san da wane irin mutane za ta haɗu ba.

‎Zai ba shi sati ɗaya kamar yadda ya ce masa.

‎Nan da sati ɗaya zai ƙara bincikawa.

‎Idan an samu, zai sanar da Abubakar.

‎Da wannan tunanin, ya musu sallama ya tafi nasa gidansa.

Umsar ✍️ 

***