BIYU A ƊAYA

Chapter 24

by @barista

BIYU A ƊAYA 
     (Don't judge a book by its cover)


Page 24
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends



Kurawa siririyar sarƙa dake ɗaure a ƙafarta, me ɗauke da tambarin heart idanu ya yi, yana kare mata kallo, a lokacin guda kuma gabansa ya faɗi, yana tuna a ina ya taɓa ganin irin sarƙan? Ganin jini kwance a ƙafarta ta yasa gabansa ya bada ras! Yana tsoro kada dai ya yi wa yarinyar nan aika akai, a hankali ya lumahe idanunsa ya buɗi yana jin zuciyarsa na yi masa zafi, ya ɗan yaye mata skirt nata zuwa sama yaga ciwo ta ci a gwiwarta shi yasa yake jini.

Ya yi saurin maida skirt nata ya rufe ƙafar ya yi baya, ya dage kansa yana sauke ajiyar zuciya, thank God ba abin da yake tunani ne ya faru ba, ya kurawa fuskar idanu yana kallon yadda ta jike da gumi kamar an watsa mata ruwa, har gashin da ya baje a fuskarta ya manne, a hankali ya sanya hannu ya dawo da gashin baya, ya gyara mata. Ya sanya hannu a wuyarta yaji har yanzu bata motsi ya mik'e ya ɗauko first Aid kit da cool bottle water ya kawo ya zauna tare da yayyafa mata ruwan, nan take ta sauke ajiyar zuciya tana numfashi on²...

"Bilqees"

Ya furta a hankali, idanunta a rufe ta soma magana 

"Don Allah kada ka cutar dani, na shiga uku kashe ni zai yi..

"Ke!"

Ya faɗa cikin ɗaga murya, a tsorace ta buɗe idanunta zuciyar na ci gaba da bugawa, cikin tashin hankali da kaɗuwa na abin da ya sameta sai dai a lokacin da ta sauke idanunta akan Yallaɓai likita ta tsaya chak da tsoron tana kallon sa, ta soma kalle kalle mamaki ya lulluɓe ta, yaushe tazo ɗakin Yallaɓai likita? Ta yaya ta tsira daga hannun azzalumin nan...

"Sannu me kike ji a jikinki?"

Ta kalle shi hawaye suka gangaro mata, ya matsa jikin bed ta takure jikinta, a hankali ta ce

"Mayafina"

"Ban san inda yake ba"

Ya bata amsa tare da kawar da kansa, ya miƙa mata ruwa ya ce

"Ki sha"

Hannunta na rawa ta karɓa ta ɗan sha ta ajiye tana sauke numfashi, ya kalli ƙafarta tare da cewa 

"Bani ƙafar"

A tsora ce ta kalle shi kuma ta kalli ƙafarta da ta kudunduneta waje guda sai a lokacin taji wani azaba ya ratsata ta furta

"Aush!"

Ya kai hannu zai riƙe ƙafar ta sake yin baya ta buge da jikin bed ta saka ƙara, ya ce

"Ki nutsu na duba ƙafar, ni likita ne"

Sai a lokacin ta fara dawowa daidai, a hankali ta miƙar da ƙafar ya ce

"Ki ɗaga skirt naki"

"Uhm"

Ta ce, ya sauke numfashi ya ɗago suka haɗa ido fuskar sa a ɗaure timau babu wasa a tattare da shi, ta soma jan skirt ɗin ganin jini ya ɓata ƙafarta yasa ta ce

"Na shiga uku! Me ya same ni?"

Bai bi ta kanta ba ya ɗauko hydrogen da Auduga ya zuba a ɗan ƙaramin kwantaina yana dangwala yana goge jinin, har zuwa inda taji ciwo, aiko yana taɓa ciwon ta saki kara sai hawaye.

"Sannu"

Ya faɗa ya ci gaba da gogewa, sai da yayi dressing wajen sannan ya kalleta yaga duk hawaye ya ɓata mata farar fuskar ta, gashi tayi ja don azaba, ya ce

"Sannu"

"Yallaɓai likita hannuna yana min ciwo"

"Wanne?"

Ta nuna masa, ya duba yaga ta ji ciwo a gwiwar hannunta ya gyara tare da dressing wajen, ta kura masa idanu tana kallon yadda yake aikinsa cikin kwarewa, a nutse yake yin komai, sai dai yadda ya haɗa rai yasa ta sudda kai ƙasa har ya gama, taji sauƙar muryar kusa da ita ya yi magana cikin cool voice 

"Me ya kai ki ɗakin shi?"

Gabanta ya bada ras! Idanunta suka ciko da ƙwalla...

"Ba kuka za ki yi min ba, amsa za ki bani"

"Uhm daman uhm abinci na kawo masa"

"Abinci?"

Suka haɗa ido ta ɗaga masa kanta alamun eh, ya sauke numfashi ya kawar da kansa tare da cewa 

"Bai je restaurant bane?"

"Eh bai je ba order ya yi"

Ransa ya matuƙar ɓaci, ya san da gangan Dr Isma'il ya yi order abinci amma ba komai ya yi na farko kuma ya yi na ƙarahe..

"Ban san shi zan kawo wa ba, sai da na kawo naga shine"

"C'est pas grave"

It's okay, shikenan ya faɗa a hankali yana tattare first Aid kit ɗin shi yana ƙoƙarin tashi, ta ce

"Marci"

Thank you ta faɗa, na gode kenan, bai ce komai ba, ya wuce palour shiru bai fito ba, a hankali ta mik'e ganin dare yana yi, tana ɗingishi ta iso bakin kofar palour tana yana saƙe waya, da alamu magana yake yi a wayar. Ya ɗago ya kalleta ta sudda kai tare da cewa 

"Zan tafi"

Ya mik'e ya iso gare ta ya ce

"A haka zaki tafi babu mayafi"

Ta girgiza kanta ta ce

"Na yada a ɗakin mutumin"

Ya rasa ya zai yi, ya wuce ta ya ɗauko rigar  jacket nasa me haɗe da hula, ya iso ya miƙa mata tare da cewa 

"Ki saka"

Ta yi saurin ɗagowa ta kalle shi, rigarsa ce kuma ya ce ta saka...

"Shi ne kawai mafita"

Ya faɗa yana kallon gefe, ta sanya hannu ta karɓa a hankali ya shige toilet, ta saka, ƙamshi ya mamaye ta baƙi ɗaya tana mamakin ƙamahin masu kuɗi na musamman ne, ya fito ta tadda ta saka, rigar ta sauƙo mata har ƙasan gwiwar ta, ta sanya hular ya rufe mata gashin kanta. Ya yi taku zuwa bakin ƙofa tabi bayansa suka fito ya rufe ƙofar a hankali suke tafiya har suka baro cikin hotel ɗin zuwa bakin titi...

"Ina za ki je?"

"Restaurant"

"Ki wuce gida"

"Jakata tana cen"

"ALAJA ce ta turoki ki kawo masa abinci"

"Eh"

Ta faɗa jiki a sanyaye, ya sauke numfashi, ya tari mashin guda biyu ta hau ɗaya, ya hau ɗaya suka iso Alaja restaurant duk da ba wani dogon tafiya bane. Tare suka shigo tana gaba yana biye da ita, ya dakata ganin tana ƙoƙarin shigewa wani bangare da yake da tabbacin nan ne side nata. Yana tsaye yaga Alaja ta gifta zuwa Corido ya yi saurin isowa tare da cewa 

"Madam"

Ta tsaya da mamaki take kare masa kallo, mutumin da Bilqees take yiwa aiki ne, ta ce

"Ya dai ince ba laifi tayi ba"

Kai tsaye ya ce

"Ba ita ce tayi laifi ba, ke ki kayi laifi"

ALAJA ta bushe a tsaye, yau take ganin ta kanta, wai ita ce tayi laifi, ta ɗan yi murmushin ƴan duniya ta ce

"Have a seat"

Ya zauna yana kallon ta zauna, ta ce

"Me yake faruwa?"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Ke ce ki ka tura Bilqees hotel a wannan lokaci?"

"Ni na aike ta, menene?"

"Amma ya mu ka yi dake?"

"Heee! little Man, what are you talking about? Who are you da za ka shiga tsabgar business nawa?"

Yana jinjina Kai tare da ciji lips nasa, yana jin ransa yana ɓacewa yana ganin son kai tattare da Alaja, cikin ɓacin rai ya ce

"I'm not apart from you, but we have an agreement"

"Agreement for what?"

Ya dubeta sosai ya ce

"Ni ban damu da shiga abin da bai shafe ni ba, kuma ba yunƙurin ɓata miki kasuwanci nake ba, ina yin abin da ya shafe ni ne"

"Menene ya shafe ka?"

"Mun yi yarjejeniya akan zan biyaki Bilqees za ta yi min aiki na wata uku, kuma ba za ki sanyata ta yi wa kowa aiki ba"

Ta jinjina kai ta ce

"Eh mun yi, to ai ba abin da ya sauya, ko yau sai da na tambaye ta ya aikin da take maka ta ce komai normal"

"Tabbas komai normal amma ke kin karya yarjejeniyar dake sakanin, kin tura ta hotel kai abinci"

"Ah wannan ai ba sabon abu bane kai abinci wa baƙi a hotel, kuma ba mu yi da kai akan ba zata kai abinci hotel ba, aiki ne ba za ta yi wa kowa ba sai kai"

"A'a ba haka bane, ba zayyu ki tura ta ga kowa ba, iya ni kaɗai za ta yi wa aiki, zan biya ki duk abin da ki ke so ko nawa ne, abin da zan amince da shi shi ne ta yi aiki wa kowa cikin restaurant amma banda waje ko hotel"

ALAJA ta kura masa idanu, tana karantar yanayinsa, me yake nufi da haka? Me yasa zai yi wa Bilqees iyaka da kowa? Ko dai Bilqees ta sanar da shi wani abin ne? Ta sauke numfashi tare da cewa 

"To na ji sharuɗanka, ai muna dab da ƙarewar wata, na gani a ƙasa, in dai bai yi min ba dole ta yi wa kowa aiki"

Ya ɗan yi murmushi yana mamakin matar tana son kanta da yawa, ya ciro wayar sa, ya ce

"Bani account details naki"

Ta washe baki ta ba shi, a take taji Alert na 100k ta waro idanuwa waje tana kallon sa, aiko shi wanda ya nema takai masa abinci bai bada haka ba, ta ce

"Na menene wannan?"

Ya mik'e tare da cewa 

"Na yarjejeniya ne, sai kuma ƙarahen wata sai na tura miki kuɗin aikin ta"

"Ah madallah Yallaɓai aiko ba za ta yi wa kowa aiki ba"

Bai tsaya ya sake bin ta kanta ba ya wuce ya fice, kai tsaye sai hotel. Bilqees tana zaune a side na Server's, tana gyara jakarta, ta giya jakar a bayanta, tana ƙoƙarin fitowa ALAJA ta shigo, Bilqees ta ɗauke kanta bata ce komai ba, ALAJA ta tsaya kare mata kallo ganin rigar namiji ne a jikinta ta ce

"Ina kayanki? Wannan kuma a ina kika samo shi?"

Bilqees ta kalleta da jajayen idanunta, tana jin kamar ta sanya ihu sabar haushin Alaja da take ji, cikin ɓacin rai ta ce

"Maa me na yi miki kike yunƙurin cutar dani? Me yasa kina so ki ɓata min rayuwa? Kuɗi za ki yi dani? Wane kuɗi ne ba ki tara ba? Me kika nema kika rasa a duniyar nan sai ta sila ta za ki samu?....

Sauƙar mari taji a ƙuncinta, ta yi saurin dafe wajen, ta ɗago tana kallon Alaja, jikinta har rawa yake yi sabar kaɗuwa da abinta Bilqees ta faɗa mata, tana ganin chanji tare da Bilqees, yarinyar da ko idanunta bata iya gani yanzu take mata magana kai tsaye, ta nuna ta da yatsa ta ce

"Ke! Ki iya bakin ki, wallahi zan yi miki abin da har ki mutu ba za ki manta ba, ni kike faɗawa haka? To ko uwar ki bata isa ta kalli sabar idanuna ta gaya min magana ba, balantana ke, ƴar cikina"

Kuka sosai Bilqees ke yi, tana jin zafin marin, ta kalli ALAJA ta ce

"Ki kashe ni na huta, na gaji, na yi miki biyayya iya ƙarfina, bana ketare duk wani abin da kika gindaya min, ina yi, me yasa za ki tura ni wajen mutumin da zai cutar dani, ƙoƙarin fyaɗe yake min"

Ta fashe da kuka, jikin ALAJA ya yi sanyi, wai daman har yanzu Bilqees bata san namiji ba? Tana nan a budurcinta, gashi tsoron namiji take, to ai ta yi tunanin wannan mutumin da yanzu take yi wa aiki a hotel ya wayar mata da kai, to in kuma babu abin da yake shiga saianinsu shi wannan kuɗin da ya tura mata na menene?...

"Maa ba zan iya ba, na hakura da aikin"

"Bilqees"

Cewar ALAJA ta matso kusa da ita ta riƙe hannunta tare da sassauta murya ta ce

"Waye yake so ya yi miki fyaɗe, mutumin da kike yi wa aiki?"

Ta share hawayenta ta ce

"A'a ba shi ba, wanda yau ki ka ce na kai masa abinci"

Ta sauke numfashi, tana jinjina kanta, cikin kulawa ta ce

"Ya aka yi kika taho nan?"

"Na samu na fito, Yallaɓai likita ya cece ni daga sumar da nani, shine ya rako ni"

Sai yanzu Alaja ta fahimci kan zancen, kenan shiyasa wannan mutumin ya ce kada ta yi wa kowa aiki, ta riƙe hannun Bilqees zuwa bangaren ta suna shigowa ta zaunar da ita tare da cewa 

"Rigar waye a jikin ki?"

"Na Yallaɓai likita ne"

"Menene alaƙar ku?"

"Babu komai aiki nake yi masa"

"To shi kenan, daga yau ba zan sake tura ki hotel yin aiki ba, sai na Yallaɓai likita, ba zan bari kowa ya cutar dake ba"

"Zan zauna a gida"

"A'a za ki dinga zuwa kamar yadda ki ke yi, zan biya ki albashi har da ƙari, kuma in ya biya mu aikin da ki ke yi masa shi ma zan ba ki"

"Na ji ciwo a ƙafata"

ALAJA ta yi sauri ta duba, ta ce

"Amma an yi ɗan iska wannan ai rashin tausayi ne"

"Har marina ya yi"

"Ba damuwa gobe zai same ni sai na yi masa rashin mutunci"

Bilqees ta share hawayenta, Alaja ta fahimci Bilqees bata waye ba, bata san rayuwa ba, ita dai tana nan a liƙe da Mamanta kamar chewing gum, a hankali ALAJA ta ce

"Yawwa ina ma kan shirye shiryen birthday party nki, wani cake na zaɓa miki sai ma kin gani"

Tana rarrashinta ganin ta saki ranta ta tura mata 10k ta ce ta saya abu, sannan ta ce

"Gashi ƙafarki tana ciwo, na san in Maman ki ta gani ba za ta yi bacci ba"

"Zan ce ai mutumin bai yi galaba a kaina ba"

"A'a ki ce ciwo kika ji, na aike ki ne mashin ya buge ki"

Bilqees ta waro idanuwa waje tana kallon Alaja, ta ci gaba da cewa 

"Bana so Mamanki ta kasa bacci"

"To ai ba zayyu na ɓoye mata ba"

"Zayyu, yanzu ki cire wannan kayan na Yallaɓai likita, zan baki hular aiki ki saka, sai mu tafi, gobe sai ki mayar masa da rigar sa"

Ta ce 

"To"

Haka tayi, ta bata hula ta saka, sannan ta ajiye rigar Yallaɓai likita a ɗakin ALAJA suka fito, suka tadda duk sun shirya tafiya gida. Tare suka fito kamar yadda suka saba, suka dawo gida...

Bilqees ta shigo dakinsu ta tadda Mamanta tana zaune tana ƙimtsa kaya ta zauna tare da cewa 

"Mama waye ya yi min wanki?"

"Ni ce"

"Kai Mama da kin bari ai zan wanke"

"To ina kike da lokaci, yanzu har weekend kina fita restaurant ba kamar lokacin baya da a ranakun kina gida ba"

"Ai Mama duk da haka da kin bari nayi, ai sai ki gaji"

"Ba komai ƴar albarka, ki sauya kaya ki huta"

"To Mama"

Ta mik'e ta shige ɗaki ta rage kayan jikinta, ta fito ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta dawo ta yi shirin kwanciya...

"Bilqees"

Cewar Mama, ta ɗan tashi ta zauna ta ce

"Bandeji a ƙafarki da kuma hannu me ya faru?"

Bilqees ta yi raurau da idanu tana kallon Mamanta, shikenan yau babu me raba Mama da Alaja, ta shiga uku kuma bata so ta yiwa Mama ƙarya, ta sudda kai ƙasa, Mama ta sake cewa 

"Tambayar ki nake yi, garin yaya hakan ta faru?"

"Uhm.... Daman... Yau...




Ayi hakuri da typing errors



A karanta ayi comments sannan ayi sharing fisabilillah