Chapter 19
Gida nafada kamar antulloni tare da yin sallama .inna kande na iske tafito daga toilet hafsat da zainab kuma suna akan tabarma atsakar gida kasan icce hafsat na azaune tana cin tuwo zainab kuma tana akwance tana yin baccin maraicen da tasaba yinshi kullum .
inda nake zama na nufa nasamu guri nazauna inata maida numfashin wahalar saurin da naci dan insamu inyima saurayin da ya tsayar dani nisa kada yagane gidanmu .araina nace "babu yanda za'ayi yagane gidanmu tunda nayimashi nisa bakuma biyoni abaya yayi ba" .
inna kande ta kalleni ta harareni tawuce tashiga dakinta . kaina nayi sauri na kauda nacigaba da nishin da nakeyi ina sauke ajiyar zuciya .
Sallama naji anyi hafsat ce ta amsa sallamar najuya inaso inga wake kokarin shigowa cikin gidan? sai ganin saurayin dazu nayi tsaye daga bakin kofa gabana yawani fadi sosai ganinshin da nayi ban kawoma raina ba.
"kanwata ya sunanki ?" ya tambayi hafsat tabashi amsa da cewa "sunana hafsat jamilu" tambayarta ya karayi cikin karfin hali "baba nanan kuwa ?"
hafsat ta girgiza mashi kai alamar "Aah" kara tambayarta yayi " mama fa?" tabashi amsa da cewa "inna tana daki" tahau kawalama inna kande kira " inna! inna! gawani yazo yana nemanki"
"good girl " yafada tare da yin smiling yana satar kallona . mutuwar tsaye nayi nakasa ko motsi tsabar mamaki da tsoron da yabani .
inna kande tafito jin maganar da hafsat tayimata . durkusawa yayi ya gaisheda da ita ta amsa gaisuwar tare da yimashi kallon bata ganeshi ba da takeyi.
"inna sunana Usman , ina zaune a GRA ne inayin business inada shaguna akasuwa da wasu unguwannin "
Kallonshi inna kande ta cigaba dayi tana sauraron shi tanason taji dalilin zuwanshi gurinta .
usman yakara da cema inna kande "inna izini nake nema gurinki inruka zuwa wajen Amatullah mu dai daita da ita"
juyawa inna kande tayi da saurin ta ta kalleni sannan tacema shi "bari babanta yadawo in sha Allah zani sanar dashi"
godiya usman ya yimata ya juya yafice daga gidan .nidai ina zaune cike da mamakin tayanda yagano gidanmu har da confidence dinshi yashigo cikin gidan da neman izinin zuwa gurina .
araina na tambayi kaina "kodai zatona ne ya tabbata aljanin ne shi!?"
Kuttu inna kande tayi wadda nasan ko ba'a fadamani dani take ba nasan danni tayita .
araina nace "nashiga ukku ni yau tawa ta sameni!"
inna kande bata kara cemani komai ba bayan kuttar da tayi , sai da aka kai yan mintina sannan "wato samari kike turomani har gida ko ? aiko zakiyi bayani" tafada tare da cije bakinta da tayi cike da mugunta.
rasa amsar da zani bata nayi nayi zaune ni ban motsaba daga inda nake ba ni bance komai ba kamar wata gunki .
Ranar naga tsangwama , dandanan inna kande takara yimani wata irin tsana tayita kara sakani ayyukan da take sani kullum ta linkasu yafi na kullum dan ko sallolina bata barni nayiba haka nayita cin aiki kamar baiwa. dukan da nasha kuwa yanda kikasan jaka .
tsayawa tayi atsakar gida ranar har dare tanata jiran baba yadawo ta kullaman sharri ta kuma bashi umarnin hana usman zuwa gidanmu .ni duk bama wannan ya dameni ba ma , tashin hankalin da zani shiga acikin gidan , dan inna kande ta nuna rashin san cigabana karara saboda tunda usman yazo ya tafi ta cigaba da kara gana mani azabar da takeyi kullum .
Zaune nake nayi tagumi ina tunanin ta yanda rayuwata zata kasance adai dai lokacin ne baba yadawo yashigo tareda yin sallama.
Ko amsa sallamar baba inna kande batayi ba taruka fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba" wai ai ina turomata samari har gida hakama ranarnan na turomata wani marar tarbiyya da taaba abakinshi yashigo abige da kyar tasamu takira samarin unguwa aka fiddashi daga gidan" nidai nasan ba'ayi haka ba . Ko kunya bataji ba da maganar da tayi ta cigaba da fadanta har tagaji .
shidai baba banda hakuri babu abunda yake bata .komawa dakinta tayi afusace ta maida kofa ta rufe . baba shima yashiga dakinshi bai kara fitowa ba har sai da gari yawaye sannan.
Safiyar sunday ne ranar gashi babu inda nake zuwa . haka nayita cin aikin da na sha da muguwar wahalar da na sha aranar .
ganin ban hadu da baba bane yasa naleka window n dakinshi ko yananan naga baya ciki na cigaba da sharar da nakeyi .
inna kande ce najiyo tana yin waya daga dakinta " barira kiyi sauri kizo dan Allah inason ganinki yanzu dan Allah"
gabana yafadi sosai inayin aikin jikina na rawa ahaka nasamu na karasashi da kyar .
shigata toilet kenan najiyo muryar inna barira tayi sallama , amsamata sallamar inna kande tayi da take atsakar gida tun tuni da tagama wayar da ita takasa zaune takasa tsaye .
gabana yakara faduwa "yauwa aminiya kamar kinsan kece araina" inna kande tafada kyalkyacewa da dariya inna barira tayi adai dai lokacin da nafito daga toilet . butar da nafito da ita ahannuna na ajiye na maida inda take nakoma na zauna gefen dakin kajin inna kande
"shiga daki kidauko dari biyar din dake kan gadona kije shagon ma'awuya ki sawomani sabulu da omo " inna kande tacemani cikin gaugawa tare da hararar da ta watsamani .
"toh"kawai nace nashiga dakin na dauki kudin na sanya hijabi nafita daga gidan .
akan hanyar zuwa shagon ne na hadu da Nura janwuya yana tahowa . dauke kaina nayi na nuna ma kamar banganshi ba inata addu'a araina nace "Allah yasa kada ya lura dani " amman addu'a ta bata amsu ba sai da ya ganni .
da karfin shi ya kwalamani kira yana dagomani hannu tareda cemani "tauraruwata ta kaina kihuta kawai ki sarara" ga mutane ta ko ina kowa yajuyo yana kallanmu nida nura janwuya"munafukai kuji da kyau budurwata ce" yafada afusace . dandanan kowa yakama kanshi mutanen suka juya suka cigaba da harkokinsu suka dena kallonmu .
dasauri ya karaso inda nake yace mani "dazu bakije dibar ruwa ba nayita jiranki haka na hakura nabar gurin gashi banida number wayarki bare inkiraki inji...." nikuwa da ba surutun shi nashirya jiba da saurina na katse shi da cewa"ai banida waya" kallona yayi cike da mamaki "haba big girl dake kicemani bakida waya? kawai dai kice baki gayyar numberta awayarki shiyasa" banida waya amman idan ka yarda" nacema mashi na cigaba da tafiya ina kokarin barinshi agurin.
" ki sarara kawai kihuta abunki wasa nake yimaki nima" nura janwuya yafada tare da juyawa da yayi yatafi yana cemani "sai munhadu anjima nasan idan ban gankiba da safe zani ganki da yamma"
"Allah yakaimu"nabashi amsa inata cigaba da tafiyata ya kara mai yatafi.
Karasawa shagon nayi tare da yin sallama , ma'awuya da yake zaune bakin shagon akan plastic chair ne ya amsa mani sallamar nafada mashi abunda zani saya ya mikoman sabulun da omon nabashi kudin najuya natafi nakoma gidan .
Shigar danayice na iske babu kowa atsakar gida nayi sallama ba'a amsa mani ba . sai dai naga takalmin inna kande da na inna barira abakin kofar dakin inna kande da alamun dai suna cikine suna magana dukansu .inaso inshiga cikin dakin inba inna kande sabulun sai naji tsaron kada inshiga suna magana injama kaina nafasa shiga na daura sabulu da omon akan window n dakin kajin inna kande .nikuma nasamu guri gefen dakin inna kande n nazauna ahankali gudun tagane hutawa nazauna inayi ta hantareni ta hanani .
Inna kande ce naji ahankali tana yima inna barira magana "wlh kuwa barira daga ganinshi mai kudine yaronnan har gida fa yazo ya sameni yayi mani wannan maganar , yanzu miye abunyi ya kike ganin za'ayi ? ni so nakeyi ma yau ki rakani gurin malam na tsanni ayi faka faka ayimana aiki "
inna barira tace "kinsan aikin malam na tsanni kamar yankar wuka yake kada kizo kizabi aikin da baiyimaki ba nan gaba kuma kiyi nadama gwara kizauna kiyi tunanin mi za'a yimata tun kafin muje gurinshi ,ko itama irin aikin da akaiyima uwarta za'a yimata ne ?"
Inna kande tace "Aah ai kuma idan aka yimata aikin da aka yima lubabatu abun ni zaya komama wa rasa mai yimani aiki da hidima zanyi kinga gwara anyimata wani abun na daban "
inna barira tace "Eh hakane kuma gwarama abunda zaifi yimaki sauki a aikin yanda baza'a samu matsala ba "
" ai har yanzu inanan inata kara kiyayewa kada wancen aikin ya rushe, wlh barira duk sanda naji ankira lubabatu sai naji gabana yafadi ko tafiya nakeyi naji ankira sunanta sai naji tsoro inkarama tafiyata sauri, ke hadama gudu duk ina hadawa dan kada inganta barema inhada ido da ita" inna kande tace .
dariya inna barira ta wani irin kyalkyalewa da ita . inna kande takara da cewa "ai gaskiya ce ,gwara ma asamata kowa yaji ya tsaneta kowa yaji baya sonta tazama kamar mujiya kinga tananne hanyar da babu wani namijin da zaya sota , ke harma matan suji sun tsaneta kowa yaji bayason ganinta"
Inna barira tayi karab tace" haka za'ayi aminiya sai ki shirya anjima in anyi la'asar muje gurin malam na tsanni nasan dai bai wuce gashin kanta ba da zayace adatsa ko kuma atsinta kinsan shi daman bayada wani abu da yake cewa akai mashi inba gashi ba tunda yake yimana aiki "nakuma jiyo karar kashewarsu .
nayi sando nasamu nafita daga gidan inakokarin boye emotion dina a time din ,nadan dauka lokaci sosai saboda inaso inyi pretending kamar ban koma gidanba banshiga ba barema inji abunda suka fada .
shiga nakarayi gidan ahankali na nufi dakin inna kande nayi sallama suka amsa dukansu nakarasa shiga , na ajiye sabulu da omon har najuya zan fita inna kande tace "ai wanki zaki yimani yanzunnan" kullin kayan dake adaure ahijabinta ta nunamani tace in daukeshi inje waje in wanke mata su .sannan ta hada da cewa " kayan makarantar hafsat nanan su zaki fara wankewa saboda baniso su dawo daga hutu ta rasa kayan sawa "kai na kadamata cike da bakin cikin da nakeji araina da nayi kokarin boyemata shi .
Kayan na dauka nayi waje dasu na nufi gurin toilet inda nasaba yin wankin na cigaba da wanke kayan har nagama inna barira bata tafiba suna cikin dakin suna kus kus . ganin na dawo ne yasa suka dena magana da karfi azatonsu banji duk abunda suke cewa ba .sai chan kuma suka fito daga dakin lokacin har namanta ma da nagama wankin har nayi sallar la'asar . inna kande ta kalleni tareda cemani "toh mu dai mun fita sai da daddare zani dawo ,shinkafa nanan na kifeta da roba gefen murhu ki dafata zani dawo da man gyada da maggi da yaji "
na amsa mata da "toh" inna barira nata washe mani baki tana shimani albarka inna kande tasa makulli ta kulle dakinta suka tafi da kyar nasamu nabude baki na cemasu "sai kundawo"
inna kande ko kallon arziki ban isheta ba ,inna barira ce kawai ta bani amsa da cewa "sai mundawo Allah yayi albarka" suka fice daga gidan araina nace "inda za'a yimani asirin kenan zasu je?"