MEERAH

010

by @oumfatima33

*MEERAH*
   *OUM FATIMA*
      

            *010*

      "Wai kin san ma wani abin farin cikin Bestie?!." Ta yi min tambayar muryarta cike da wani irin emotion na farin ciki. Tagumi na yi na zuba mata ido ina kallonta kawai.

    "Menene?." Na tambaye ta ina ci gaba da kallonta.

      "An gayyato shi zai zo ya gabatar da waƙar da kansa." 

   "Congratulations Bestie, finally dai za mu ga Nawaz Baffa." Na faɗa ina bata hannu irin na taya murna.

   "Sosai ma kuwa Bestie ina cikin farin ciki sosai zan ga mawaƙina." Cewar Zeezee.

   "yanzu miye next?." Na faɗa ina shafa cikina don yunwa nake ji.

   "Tashi za ki yi ki shirya wu wuce mu ƙarasa abinda ya rage."

   "Okay bari na samawa cikina wani abin kafin na shirya." Na faɗa ina sauka daga saman gadon. Sauka tayi itama muka fita tare zuwa dining.

   Zama nayi ina ƙwala kiran.

   "Aunty Bintu?." Fitowa Bintu tayi daga Kitchen tana cewa.

    "Na'am Hajiya ƙarama, akwai abinda kike buƙata ne?."

   "Eh a bani breakfast." Na bata amsa. Kitchen ta koma ta haɗo mana breakfast ɗin ta kawo. Ni kaɗai na ci don Zeezee tace already ta yi nata a gida.

   Ban wani tsaya ɓata lokaci ba na kammala na miƙe muka koma ɗaki, wanka nayi na fito na shirya muka je mu ka yi wa Momy sallama a kan zamu ke gyaran gashi da lalle. Addu'a ta yi mana ta saka driver ya kai mu.

   "Ki dawo gida da wuri Auta, kin san dai Yayanku ya hana ki fita ke kaɗai." Momy ta faɗa lokacin da take bani Atm Card ɗinta.

   "In sha Allah Momy." Na faɗa daga haka muka wuce. Wani babban wurin gyaran gashi aka kai mu, aka yi mana wankin kai tare da baƙin lalle a hannu.

   Sosai lallen ya yi kyau kasancewar mu farare ni da Zeezee, don na ma fita haske sosai. Bayan an kammala Zeezee tayi booking make up sannan muka wuce.

   Gidan su Zeezee na saka driver ya kai mu, nace yaje da yanma ya dawo ya ɗauke ni. Shopping ɗin jiya muka ɗauko muka ware komai, nima nawa kayan na fitar zan wuce da su gida.

   Labarin chocolates ɗin da Yaya Abdul ya bani jiya na bata, dariya ta saka tana cewa.

   "An ya kuwa Bestie Yaya Abdul ba kamu yake yi ba kuwa?." Harararta na yi nace.

   "Amma dai baki da man kai Bestie, Yaya Abdul fa nace."

   "Eh Yaya Abdul ɗin nake nufi." Ta bani amsa.

   "Allah ya taro ki to,yanzu dai mu ajiye wannan maganar a gefe. Meye ya rage bamu tsara ba?." Na kawar da zancen da wani don har ga Allah ta saka min kokonto a zuciyata, don sai yanzu nake tuna wasu abubuwan da Yaya Abdul ɗin ke yi min. 

  Wan da a da na ɗauke su a matsayin normal ne, don ina ƙawar ƙanwarsa ne kawai. Maganar Zeezee ce ta dawo da Ni daga tunanin dana tafi.

   "Babu abinda ya rage, gobe kawai muke jira mu baza capacity."

   "An gama gayyatar duka Friends ɗin mu kuwa?." Nayi mata tambayar ina ƙara duba rigar da zan saka.
   
   "Duk wanda ya kamata na tura musu invitation, da yake  ba wasu yawa ne da friends ɗin namu ba, ƴan'uwa duk sun fi yawa." Ta bani amsa. Hira muka ci gaba da yi har aka yi sallar la'asar sannan Momy ta turo driver yazo ya ɗauke ni.


★★★

   Washe gari ta kama ranar Birthday ɗin, ƙarfe 4 na yanma aka shirya yin taron a cikin gidan su Zeezee. Tun da safe Zeezee ta kira wayar Momy ta ce in shirya in taho.

   Ce mata na yi sai zuwa jimawa tunda babu abinda ya rage da za mu yi, don yau tashi na yi ina jin ciwon mara kaɗan kaɗan, wan da ban taɓa jin irinsa ba.

   Duk yanda Zeezee ke kira ban samu fita ba sai 4:30pm gab da za'a fara taron, a hakan ma daurewa na yi na ƙarfafa kaina don da Momy cewa tayi in haƙura da fitar. Haka dai na shirya cikin kayan da muka sayi tare da Zeezee, tawa rigar pink color ce. In da ta Zeezee ta kasance purple.

   Sallama na yi wa Momy tace.

   "Kije driver ya kai ki, sannan idan kin ji ciwon bai daina ba ki kira waya azo a ɗuko ki. Naso na leƙa musu nima sai dai babu dama Saboda yau Dad ɗinku zai dawo nan, ci ke ma Hajiya Bilkisu ina taya ƴata murna in sha Allah zan zo daga baya."

    "Okay Momy." Na faɗa ina wucewa, compound naje na yiwa Baba driver magana ya fito da mota muka ta fi. Lokacin da na isa tuni an fara taron, kai tsaye inda ake gudanar da taron na nufa cikin sanyin jikin da nake ji.

    Zeezee na hango ni ta miƙe ta nufo inda nake, tana zuwa ta riƙe hannuna cike da damuwa take faɗin.

   "Wai Bestie sai yanzu zaki zo, kin san dai shagalin nan ba zai yi daɗi ba idan babu ke ko, sannan ina ta kiran wayar Mom bata shiga." Runtse ido nayi saboda mintsinin da marata ta yi min.

   "Lafiya kuwa Bestie, ko dai ciwon cikin ne har yanzu?." Zeezee ta faɗa tana riƙo hannuna cike da damuwa. Murmushi na ƙaƙalo nace mata.

   "Kar ki damu ba wani takura ni yayi ba, yanzu dai muje aci gaba daga inda aka tsaya, su Zuleey sun zo kuwa." Na faɗa ina riƙe hannunta. 

  "Eh tuni sun ƙara so." Ta bani amsa. Wurin su Mom ɗinta muka je muka gaisar dasu, har da Dad ɗinta a wurin da sauran Yayunta Mata da Maza. Sai baƙin da aka gayyato.

    Muna tare da Aunty Raulat Yayar Zeezee wacce ke aure a Abuja, ita ma tazo wurin birthday ɗin ne. Mc muka ji yana sanar da zuwan Nawaz  Baffa wanda zai zo ya waƙe birthday girl da daddaɗar waƙar daya rera mata.

   Cike da farin ciki Zeezee ta ja hannuna muka nufi hanyar da zai bi ya shigo, ai kuwa muna zuwa dai-dai suna shigowa tare da Yaya Abdul da abokinsa JB da ya yi masa rakiya. 

  Kyakkyawan matashi ne mai cike da natsuwa da kamala, sanye yake cikin sassauƙar shiga black trouser da blue shirt, yayi stocking da black belt, haka ma takalmin ƙafarsa black cover shoes ne. Ya yi kyau sosai abinsa, sai abokinsa JB dake riƙe da jita shima cikin shigarsa mai kyau.

    "Wayyo Allah Bestie yau gani ga Nawaz Baffa wanda ya rera waƙar Ƙauna, waƙar da nake matuƙar so!." Zeezee ta faɗa tana doka tsallen murna. Murmushin yaƙe nayi mata nace.

   "Congratulations Bestie." Na faɗa ina riƙe hannunta, jan hannuna tayi muka ƙarasa har inda suka tsaya. Raba idanu ta fara yi tsakaninsa da abokinsa JB don tan-tance waye Nawaz ɗin.

   Fuskantar hakan ya saka Yaya Abdul nuna mata Nawaz dake tsaye idanunsa a kan Meerah da kanta ke ƙasa tana ɗan yatsuna fuska alamar akwai abinda ke damunta.

   "Na cika alƙawari, ga Nawaz Baffa a matsayin 16th birthday ɗin kin." Yaya Abdul ya faɗa yana kallon Zeezee da farin ciki yasa ta kasa rufe baki. A hankali Nawaz ya ɗauke kallonsa daga saman fuskar yarinyar da ta fisgi hankalinsa tun shigowar sa wurin.

   Zeezee ya kalla yana ɗan sake mata murmushi yace.

   "Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki ƙanwata." Wani irin daɗi ya ratsa zuciyarta fuskarta cike da murmushi tace.

   "Thank you, I'm so happy to see you. Ina matuƙar son waƙoƙinka, musanma waƙar ƙauna." 

    "Thanks you." Ya bata amsa a taƙaice yana mayar da kallonsa ga yarinya da ya kasa daina kallonta.

   "Ga Bestie na sunanta MEERAH ita ma tana son waƙoƙinka sosai." Zeezee ta faɗa tana ƙara riƙo hannun Meerah.

   "Naji daɗin hakan, na gode sosai." Ya bata amsa still idanunsa a kanta. JB da ya lura da hankalin abokin nasa na a kan yarinyar da aka kira da Meerah ne yayi gyaran murya yace.

   "Ya kamata muje muyi abinda ya kawo mu." Kafin ya bashi amsa Yaya Abdul da hankalinsa shima ke kan Meerah yana tambayar ta ko lafiya take ne ya juyo yace.

   "Haka ne, bismillah mu ƙarasa wurin." Ƙarasawa suka yi inda aka shirya kayan kiɗa, birthday girl kuma ta ƙarasa ta zauna a inda aka tanada domin ta. Bestie ɗinta ta zauna a gefenta. Haneef da sai a lokacin ya hango Meerah ya nufi inda suke zaune.

   "Sannu da zuwa Queen, kin yi late kina babbar aminiya." Ya faɗa yana kallon yanda fuskarta take a kame, kamar dai bata jin daɗi."

   "Queen what's wrong?." Ya kuma tambaya cikin sanyin murya ganin taƙi kula sa." Ɗagowa na yi na masa kallo ɗaya na mayar da kaina ina cewa.

   "Bana jin daɗi ne Haneef." Tashi hankalinsa yayi ya shiga jera min sannu da tambaya ta abinda nake so ya kawo min.

   "No thanks." Kawai na amsa amsa muka miƙe ni da Zeezee muka hau saman stape inda Mc ke neman birthday girl, don tuni Nawaz ya fara rera daddaɗar waƙar birthday da yayi.

    Rawa Zeezee keyi cike da farin ciki mawaƙinta na waƙe ta, yayinda ƴan'uwa da dangi ke zuba mata ruwan kuɗi.

   Nima ba'a bar ni a baya ba don na kira Dady ya saka Ya Jawad ya bani sababbin kuɗin da zan mata liƙi, don haka kuɗin na shiga zuba mata ina jin daɗin ganin farin cikin da take ciki. Yaya Abdul da Haneef kuwa duk mu biyun suka haɗe suna zuba ma kuɗi.

   Sosai MC ya ruɗe yana ci gaba da koɗa birthday girl tare da Bestie ɗinta da suke ta wal-wali a cikin filin.

   Nawaz kuwa waƙar yake yi cike da nutsuwa yayin da idanunsa ke kallon yarinyar da ake kira da Bestie ɗin Birthday girl, yana kuma nazarin Maza biyu da suma hankalinsu yake kanta, wato Yaya Abdul da Haneef.

   Sosai waƙar tayi matuƙar daɗi duk da cewa wannan ita ce waƙar birthday ta farko da ya taɓa yi, sannan kuma wannan shine karo na farko da ya taɓa yin performance a wurin wani shagali.

   Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa ya kasa sake wa sosai a wurin, yake jinsa uncomfortable. Sai dai kuma abu ɗaya da ya ɗauki hankalinsa a wurin, ita ce wannan kyakkyawar yarinyar ma abociyar nutsuwa da kamewa.

  (Wai nutsuwa, Nawaz baka ga mata bane a lokacin da suke ƙalau ne shi yasa 😆)

    Tsaf ya kammala waƙarsa cike da natsuwa inda ya nuna ƙwarewarsa da baiwar da Ubangiji ya ba shi, an yi masa liƙi kamar ba gobe. Bayan ya kammala wasu daga cikin ƴan'mata da samarin da ke wurin suka riƙa zuwa ɗaukar hoto da shi. Yayin da shi kuma hankalinsa ke kan yarinyar nan dai da ta ɗauki hankalinsa tun kallon farko.

**** Zuwa wannan lokacin ciwon da marata keyi ya yi  tsananin da ba zan iya ci gaba da zama a wurin ba, gashi kuma ba'a kammala taron ba don yanzu ake bayar da kyautuka ga birthday girl. Wan da kamata yayi ace nice tsaye a kusa da ita ina taya ta karɓar gift.

   Fahimtar halin da nake ciki ya saka Zeezee taso wa tazo inda na koma na zauna na kwantar da kaina saman table ina dafe marata tace.

   "Bestie ki shiga ciki ki kwanta, ina gama sallamar mutane zan shigo sai mu mayar dake gida." Tayi maganar cike da kulawa. Kai kawai na gyaɗa mata don na kasa magana, tashi tayi zata koma na riƙo hannunta.

   Hand bag ɗina na buɗe na ciro wani ƙaramin box na saka mata a hannunta, da ƙyar na iya buɗe baki na furta.

  "Happy birthday Bestie, I wish you long life and prosperity."

   "Wow!." Ta furta tana rungumeni lokacin da ta buɗe box ɗin cike da ɗokin ganin kyautar da Bestie ɗinta ta kawo mata, taci karo da kyakkyawar sarƙar zinari da Momy ta bani na bata a matsayin birthday gift.

   "Thank you so much Bestie, your very, very specific to me!." Ta faɗa cike da murna tana ƙara rungume ni. Sakina ta yi ta ruga da gudu don zuwa ta nuna wa Mom ɗinta da ƴan'uwanta. 

   Lokacin data tafi ni kuma ciwon ya ƙara min tsanani, don wata irin ƙullewa mara ta tayi. Zuwa can kuma naji kamar danshi a jikin pant ɗina, ba shiri na miƙe ina gyara mayafina na ɗauki hand bag ɗina na silale na fice a wurin ba tare da ko sallama nayi wa Bestie ba.

   A hankali nake taka wa a gefen shimfiɗaɗɗiyar kwaltar dake malale a street ɗin namu, shiru babu motsin kowa bare in saka ran za'a taimake ni, don zuwa yanzu na fara kasa tafiya yanda ya kamata.

  Riƙe wa ƙafata tayi gam na kasa ci gaba da tafiya ina jin azaba na ratsani, tamkar ana saka wuƙa ana yankar naman mararta, babu shiri na durƙushe a inda nake ina fashe wa da matsanancin kuka. 

  Ina cikin wannan halin ne naji tsayuwar mota a kusa da ni, da ƙyar na iya buɗe idona don ganin ko wanda zai kawo min ɗauki ne na samu.

  Wasu matasa ne su biyu suka fito daga motar, irin yaran nan ne mara sa jin magana. Don yanayin shigar dake jikinsu, da irin kiɗan dake tashi a cikin motar kaɗai zai shaida cewa basa jin magana.

   "Nazzy ina ga mun yi tsintuwa fa." Ɗaya daga cikin yaran ya faɗa da wata murya irin ta shaƙiyanci.

    "Da alama kam, shike nan kaga sai ka huce haushin da shegiyar can ta cusa maka." Wanda ya kira da Nazzy ya bashi amsa, dariya suka sheƙe da ita suna cafkewa cike da ita shege, kai tsaye inda nake kwance ina murƙashin azaba suka nufo.......

Barka da dare.

  Oum Fatima
   ***