15
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 15.
Sarac Stars R Pen...✍️
15.
Bayan Ali ya kai aya, Hamisu ya kafe shi da ido ƙuri mamaki ya cika shi sai ya haɗe fuska ƙunshe da damuwa.
Haba Ali shi ne ba zaka faɗa min ba, Safiyya fa ƙanwata ce.
Kayi haƙuri, kasan baka Ƙasar shiyasa, amma yanzu ka bani shawara, me ya kamata muyi akan lamarin Safiyya ina tsoron yaran nan ya dawo ya dagula mata littafi kuma tana gabda kamuwa da ciwon zuciya, sannan idan tayi aure a yanzu shima matsala ce dan ba a so ta samu juna-biyu saboda ba tada lafiyar mahaifa.
Allah sarki Allah ya bata lafiya, gaskiya wannan abun babba ne Allah ya kawo mafita, ina ganin babu abunda ya wuce addu'a shi ne zamu dage da yi akan Allah ya zaɓa abunda yake alkhairi.
Hakane kuma, muje to mu yi aikin nan.
Cewar Ali yana miƙewa, ba musu Hamisu ya miƙe shima suka fita tare. Hazan company mallakin Hamisu ne wanda a shekaru biyar baya ya gina shi, ya yi amfani da farkon sunansa HA sai ya ɗauka daga harafin sunan matarsa mai suna Zainab ZAN, sai ya bada kalmar HAZAN kuma koda ya je registern company sunan ya hau HAZAN GLOBAL IMPORTS LIMITED. Yana shigo da kaya daga ƙasar waje wanda komai suna kawowa har da motoci da komai da ake amfani da shi a ƙasar Nigeria, su bayar ga 'yan kasuwa cikin rahusa mai sauƙi, a hankali companyn yayi ƙarfin da suke aika kaya a sassan ƙasar. Akwai ma'aikata a companyn da yawa, ɓangaren ofisoshi waɗanda suke shigar da komai a takarda da na'uwara mai kwakwalwa da adana kuɗin Company a banki daban, ɓangaren masu kula da store suma daban, ɓangaren masu rarraba kaya da fitar dasu suma daban, sannan masu kula da motocin company wajen delivery suma daban, ga securities da masu gadi, ko wannensu ana biyansa albashi mai kyau akan aikinsa, shekara uku kenan da Ali ya fara aiki dasu saboda ya samu matsala a gurin aikin da yake yi, Hamisu ya jawo shi Hazan company a matsayin assistant ɗinsa, wanda a yanzu Ali shike kula da komai na company shi kuma Hamisu yana can China wajen haɗo oder ɗin kayan mutane, kuma a can ɗin ma yana aiki a wani company na yin kaya shiyasa baya samun zama a Nigeria sosai.
**
Safiyya tayi interview cikin nasara dan ta amsa duk tambayoyin da aka yi mata, suka sallameta akan nan da kwana biyu zata ji sakamako, tayi godiya kafin ta wuce zuwa gida a napep, ta samu kanta a cikin farinciki musamman yadda ta jima bata fita ita kaɗai ba a napep sai hakan ya tuna mata rayuwar makarantar da ta yi na jami'a, tare da tuna farkon haɗuwarta da Jabir a sanadin napep, zata je makaranta ne ta tari napep ta shiga bayan ta sanar da mai napep zai kaita BUK, sun ɗan yi tafiya kaɗan sai Jabir ya tare mai napep ɗin ya tsaya ya shiga ba tare da ya faɗi inda zai je ba, sai da suka kusa kaiwa titin da zai sadasu da makarantar su Safiyya sai Jabir ya ce mai napep ya tsaya zai karɓo saƙo, Safiyya ta haɗe fuska.
Kamar ya malam zaka amsa saƙo, gaskiya mai napap zai ɓata min lokaci nayi latti sosai.
Haba kiyi haƙuri abu kawai zan amsa a shagon can.
Ai sai kayi kuma dan bana jin yaran haƙuri akan nayi missing lectures.
Ta faɗa tana kawar da kai, Jabir ya saki murmushi.
Muje mai napep ka sauke ta sai ka juyo dani na amsa mu wuce in da zani, ba musu mai napep ya wuce dasu, bayan sun isa ta sauka ta biya kuɗin ta sannan Jabir ya ce mata.
Allah ya yiwa karatunki Albarka ya cika miki burinki.
Ya ƙare da murmushi a fuskarsa, Safiyya sai da ta ji wani iri a cikin ranta duba da rashin mutuncin data yi masa sannan ya bita da addu'a, sai ta saki murmushin yaƙe.
Amin in da gaske kake.
Babu canjin dubu ɗaya.
Cewar mai napep,
OK na bar wa wannan canjin.
Ta faɗa tana nuna Jabir sai ta juya ta wuce hankali kwance, Jabir dama tun shigarsa napep ɗin ya shiga ayyana wani abu zuciyarsa akanta sai ya sauka yana cewa mai napep ɗin ya jira shi, sai ya bi bayan Safiyya yana cewa.
Sunana Jabir Aminu, nima tsohon dalibin makarantar nan ne, amma yanzu ina aiki a Abuja hutu na zo.
Safiyya ta tsaya tana dubansa kafin ta yatsine fuska.
Amma meya faru da zaka biyo ni kana faɗa min sunanka.? ko na tambaye ka ne.?
Ta ƙare maganar tana yin gaba, Jabir ya tsaya turus dan bai zaci zata kware masa irin haka ba, sai ya girgiza kai ya juya wajen mai napep ya shiga suka wuce, ya tafi da niyyar ba zai sake tuna ta ba amma zuciya ba tada ƙashi ya kasa jurewa, tunaninta yayi masa dabaibayi har sai da ya sake dawowa makarantar ya shiga nimanta amma Allah bai sake haɗasu ba, har ya cinye hutunsa ya koma da tunanin Safiyya. A wani hutu daya zo Kano, ya ɗauko Ikilima a motarsa ya sauketa a shagon wani saloon, sai ga Safiyya ta fito daga ciki, bai yi ƙasa a guiwa ba ya fito ya kuma yi mata magana, a lokacin bata yarfa shi ba ta amsa masa cikin mutunci domin ta gane shi, sai dai bata ɓata lokaci ba ta samu abun hawa ta wuce ta bar shi a tsaye to a dalilin Ikilima ƙanwarsa ya san inda Safiya take, domin yasa ta bincika masa Safiyya ta hanyar mai saloon har suka san sunanta da unguwar da take, wannan shi ne mafarin soyayyarsu har ya kaisu ga aure. A sannan ne Safiyya sauke numfashi ta saki guntun murmushi ta cewa mai napep.
Idan ka isa gidan dake gaban masallaci mai ash ɗin gate ka tsaya a nan zan sauka.
To yace mata, da suka isa ta sallame shi ya wuce sai ta shiga gida da sallama, ta samu Anty Indo ta zo muryarta kawai take ji tana bawa su Mama labari. Safiyya bayan ta samu gurin zama sai ta yiwa iyayensu sannu da gida, ta gaisa da Anty Indo, ta amsa tana mele baki.
Yana ganki sukuku, ke da zaki shigo da farinciki ta yadda zamu gane andace aiki ya samu.
Hmmm interview nayi fa sai nan da kwana biyu suka ce zasu kira ni.
To Allah yasa mu ji alkhairi wai ko Jabir sun dawo daga Ƙasar wajen daya je da amaryarsa.
Cewar Indo tana murmushi, Mama da mama ƙarama suka saka salati, Safiyya ta sakin guntun murmushi takaici.
Anty Indo ai kin san gidan Ummi zai fi kije can ki tambaye su, a nan ne zaki samu amsarki.
Amma wlh Indo ba kida girma, haka kurum ki tuna mata da abunda zai tashi hankalinta.
Cewar mama ƙarama cikin ɓacin rai, Mama babba ta girgiza kai.
In Indo bata yi haka ba ai bata cika sunanta ba, kin kyauta.
Tana gama faɗar haka ta miƙe rai a ɓace ta wuce ɗaki, Indo ta saki murmushi.
Dan Allah kuyi haƙuri na yi haka ne naga ko ta saduda, Ƙanwata da fatan kina cikin ƙoshin lafiya.? Muje ki faɗa min sirrin wannan kyan da kika ƙara, gaskiya zaman gidan nan ya amshe ki.
Ta ƙare maganar tana yunƙurawa ta mike ta nufi inda Safiyya take zata dafata, Safiyya ta goce tana gunguni ta miƙe ta bar mata wajen, Indo ta cigaba da ɓaɓatun magana mama ƙarama tana cewa.
Kin dai gama yada girmanki wlh, Allah ya sauwaƙe miki wannan sakarcin.
Indo tayi dariya ta bi bayan Safiyya, ita haka Allah ya halicceta da yawan zolayar mutane, gata ita ce babba amma ba ruwanta da ɗaukar girman, sai tayi ta tsokanar ƙannenta shiyasa Ali ya karɓe girmanta ya zama kamar shi ne babba a gidan.
*****
Mujaheed.
Kafin su baba su dawo daga masallaci mama ta ɗauko waya dan ta kira Inna ta sanar da ita an ɗaura, sai da ta zauna a gefen gado kafin ta kira, bugu biyu inna ta ɗaga da sallama, suka gaisa kafin Mama ta sanar da ita ɗaurin auren, Inna tayi ƙabbara cikin farin ciki sai kuma ta saka albarka tare da nuna tsantsar murnar ta, hakan ya faranta ran Mama ta kuma ji daɗin yadda Inna ta bada haɗin kai ba a samu matsala ba, haka suka taɓa hira wanda duk na Mujaheed ne na yanayin da yake ciki a nan Daura, daga bisani suka yi sallama, mama ta sauke numfashi cike da farin cikin burunta ya cika a sauƙaƙe ba tare da wata mishkila ba, yanzu babban abunda zata saka a gaba shi ne ta haɗawa Aina'u kaya na garari masu kyau da tsada yadda zata yi fice ta yi zarra ga matan Magami, dan ta kankaro mata mutunci ta yadda za a riƙa martabata a san cewa daga Kaduna take garin Gomna.
....
Daura.
Rayuwa kenan duk yadda bawa ya tsara lamarinsa to sai yadda Ubangiji ya shara masa ne zai kasance, Mujaheed ya samu kansa a wata nahiya da bai yi zato ba, kuma sai lamarin ya zame masa wani sabon abu domin ya samu natsuwar ruhi dama gangar jiki fiye da yana Kaduna, anan babu mai yi masa ihu, babu mai hantararsa babu mai kiransa da mahaukaci, babu mai yi masa kallon banza, kowa so yake ya jashi a jiki a kyautata masa, wannan ya saka shi samun sukuni daga wannan fargaba da tsoron da yake ɗawainiya da shi, babban damuwarsa Kaka bata barinsa ya fita sai da dalili kuma ba shi kaɗai ba sai tare da Ahmad, tun Mujaheed ya kasa sake jiki ga Ahmad har ya zo ya fara, yakan ja shi suje makarantar allo da safe idan an taso su koma gida su ci abinci sannan suje gona ko su je suyi kiwo, sannan ga magani Inna ta dage masa sosai, kuma ko da ta kai shi wajen malam babba ya tabbatar mata da in dai akwai shafin jinni a jikinsa to In Sha Allah zai warke.
A wata guda da yayi a Daura sai rayuwarsa ta fara setuwa daga wancen ƙalubalen da yake fuskanta na razani da tsoro, saboda tasirin ruwan addu'a da yake sha da kuma kyakkyawar kulawa da yake samu a gurin Inna, sam bata barinsa ya zauna cikin ƙazanta kullun sai yayi wanka da safe ya sauya kaya masu kyau, fitsarin kwance kuma bai yi ba duba da kullun sai inna ta tashe shi da asubahi yayi sallah, ita kanta ta kula da ya ƙara natsuwa duk da baya magana sosai da ita amma tasan akwai sakacin kulawa da ya rasa a baya, iyayensu basu tsaya sosai ba akansa sun sake yi a layi yana garari al-umma su tarbiyantar da shi, ta tabbatar da ace tun lokacin da ya fara fuskantar matsalar rashin lafiyar sun tsaya tsayin daka da abun bai yi ƙamari haka ba, sai take ganin kamar ma zata riƙe Muhajeed ɗin kawai a hannunta dan gaskiya taji daɗin sauyin da ta gani a tare da shi. A ɓangare guda kuma tana ta haɗawa Aina'u kayan gara danginsu kayan miya, wato ta yi mata garin daddawa, kuka, kuɓewa busasshe, da yaji mai daɗi dakan hannu mai yawa, ta kuma samu cukwi tayi mata haɗin wani maganin mata wanda idan taje gidan miji ta riƙa sha da nono, shiri take yi sosai wanda nan da sati biyu zasu tafi sai an gama biki kafin zata dawo, amma tana ganin tare da Mujaheed ɗin zata dawo kawai su cigaba da rayuwarsu a nan.
Inna mace ce mai haƙuri da kawaici tana son zumunci tayi da kuɗinta tayi da ƙafa, shiyasa itama 'yan uwa suke gwada mata ƙauna, dama auren zumunci aka yi mata da babansu Musa, kusan dangin guda ne shiyasa komai nasu baiɗaya ne. Babansu Musa ya rasu lokacin yana matashi wanda dalilin hakan ne ya bar Daura ya koma Kaduna wajen Alhaji Sanusi, shi ne babban ɗan inna sai Salaha ke bi masa tana aure a Sokoto 'ya'yanta bakwai ta aurar da huɗu, bata cika zuwa ba duba da auren nesa tayi kuma cikin ƙauye take, sai Nasiru shi ne na uku amma Allah bai ƙaddara zai yi tsawon rai ba dan yana ɗan shekara sha shida Allah yayi masa rasuwa, Inna bata sake aure ba ta cigaba da zama cikin dangi har Allah ya buɗawa Musa ya ware mata gidanta anan cikin gadon babansu, kuma da kuɗin gadonsa ya haɓɓaka kasuwancin da yake ciki a yanzu wanda ita Salaha tuni ta cinye nata a auren 'ya'yanta mata uku da ta yi, sai namijin daya yiwa kansa komai mahaifinsa ya taya shi. Inna bata da dogon buri bata da saka ido a sha'anin yaranta kullun addu'a take bin su da shi bata damu da suyi mata ba tunda ko wanne yana fama da iyali, ita tausayinsu ma take yi musamman Musa da yake zaune a binni tasan rayuwar nan da can akwai bambanci, babu abunda ya ƙara faranta mata rai sai lokacin da Musa ya sanar da ita yayi gidan kansa a Kaduna ga kuma ƙaruwar haihuwa da ya samu na Mujaheed dan lokacin baifi shekara ɗaya da rabi ba da yin aure, har gashi yanzu ya tara yara biyar shima har ya aurar da guda ɗaya, wannan ke nuna cewar lokaci ya tafi kuma ba zai dawo ba sai abunda yayi saura na rayuwar da ya rage musu.
...
Kaduna.
Duk wani shiri sun yi sun gama lokacin bikin tariya kawai suke jira ya zo, hatta lefe an gama haɗa wa dan musamman Idris ya zo ya kawo wa Mama kuɗi ta haɗa mata kayan lefe anan binni masu kyau, a cewarsu zasu yi mata komai na gata dan ta babanta da matansu na can. Hakan ya ƙara faranta ran baba ya kuma tabbatar da Aina'u tayi dace da gidan aure duba da yadda suke nuna kulawarku akan duk lamarinta, a yanzu ba shida haufi ba shi da fargaban inda ya kaita domin yasan zata yi rayuwa mai cike da 'yanci da kulawa. Mama kuwa abunda suka yi sun ƙara kankaro mata mutunci a gurin baba dan lokacin daya dinga yaba musu tayi farinciki ta kuma gamsu da cewar baba ya gama gamsuwa da mutanen kwarai ne su. Shiyasa itama ta yi abunda ya dace ta haɗa kaya masu kyau da tsada, akwati uku da kit shaƙe da kaya wanda sai da ta gayyato ƙawayenta suka zo suka gani suna yabawa. Sannan a wannan bikin tariyar tayi gayya sosai dan baba ya bata duk wata dama na abunda za a girka, kamar yadda take ƙaunar rayuwar ƙarya to ta gama shirya komai a wannan bikin tariyar, duk wani tattalin arzikinta sai da ta jijjiga shi, dan kaya kala huɗu ta ɗinka masu tsada, yaranta ma tayi musu kala bibbiyu.