011
by @oumfatima33
*MEERAH*
*011*
Murƙususu nake yi cikin matsanancin yanayin da nake ciki, na tsananin azabar ciwon marar da nake jin tamkar zai yi gaba da rayuwata, saukar hannu naji a bayana ana ƙoƙarin ɗaga ni tare da faɗin.
"Hi Babe, wake up mana."naji saukar murya a cikin kunnena. Duk da yanayin da nake ciki bai hana ni saka hannu na doke hannun dake taɓa ni ba. Don wani irin tafarfasa zuciyata ke yi na taɓa nin da wani ƙato yayi, tabbas da ace ina da ƙarfin da zan iya tashi da babu abinda zai hanani wanke fuskar ko waye da mari.
"Da alama Babe ɗin nan zata yi taurin kai Nazzy, kaga sanƙameta kawai mu bar wurin tun kafin wani yazo wucewa ya ganmu a samu matsala." Ɗayan matashin mai suna Shamos ya faɗa.
"Naga alama kam, amma fa yau ina cikin alkairi. Don kana kallon wannan ka san zazzafa ce, duk da bata ƙarasa nuna ba." Nazzy ya faɗa yana cije baki cike da iya shege.
Wani irin matsanancin tsoro da fargaba ne ya shiga ratsa zuciyata jin maganar da suke yi, babu shiri na yunƙura da ƙyar na miƙe ina layi nayi ƙoƙarin gudu. Sai dai taku biyu nayi na ƙara zubewa ina fasa azabben kukan azabar dake ratsa har ƙwaƙwalwa ta.
Dariya suka sheƙe da ita suka rufa min baya, ina ji ina gani suka kamani duk da yanda nake tutturjewa. Ihu nake ƙoƙarin yi amma bani da ƙarfi, don da ƙyar nake iya buɗe baki na ina faɗin.
"Ku rabu dani!." Cikin mawuyacin yanayi nake furta hakan, hawaye na malala a saman fuskata, babu wanda ya saurareni sai ma dariya da suke faman yi tamkar wasu zararru.
Idan nace zan misalta irin tashin hankali da mahaifar da nake ciki ma ɓata lokaci ne, don yanayi biyu ne suka haɗe min lokaci ɗaya.
Tsananin ciwon da nake fama da shi, tare da matsanancin tsoron mutanen dake ƙoƙarin sace ni, wanda ban san ainahin abinda zasu iya min ba.
Na riga na gama sadaƙarwa don har sun samu nasarar tura ni cikin motar suna ƙoƙarin rufewa, jiri ne ya fara ɗauka ta idanuna suka fara ganin biyu biyu. Ni dai naga tsayuwar wani mutum a gaban motar ya riƙe murfin motar ya hana su rufewa.
Daga nan kuma ji da ganina suke ɗauke ɗif ban ƙara sanin abinda ya faru ba.
**** A hankali na shiga buɗe idanuna da suka yi matuƙar min nauyi, dishi-dishi na fara gani hakan ya sa na mayar da su na sake lumshewa. Sake buɗe su na yi na sauke su a kan mutumin dake zaune a gefena saman kujera ya zuba min duka idanunsa, yana kallon ko wane motsi nawa.
Lumshe ido na sake yi a karo na uku hawaye masu ɗumi suna zubo min, kamar an tsikare ni na sake buɗe ido saboda fuskar dana gani zaune kusa da ni ɗin ce ta bani mamaki. Nawaz Baffa ne, mawaƙin da ya yi wa Bestie na waƙa yau a wurin birthday party ɗinta.
"Kin tashi ne? Bari na kira Doctor." Muryarsa ta dawo dani daga tunanin da na tafi. Yana kammala faɗa ya miƙe ya fice daga ɗakin, idona na lumshe ina jin marata na mintsinina. 'me yake yi a tare da ni? Ko dai shine ya ƙwace ni a hannun waɗan can azzaluman?.' tambayoyin da nake yi wa zuciyata kenan.
Ana haka sai gashi ya dawo tare da likita Mace.
"Sannu, yaya jikin?." Ya tambaya cikin sanyin murya yana kafe ni da ido. Lumshe idanuna na yi na buɗe lokaci ɗaya, a hankali na buɗe baki nace masa.
"Da sauƙi." Matsowa Doctor ta yi ta cire min drip ɗin daya ƙare, tambayoyi ta yi min na amsa mata da ƙyar don ko kaɗan bana son yin magana. Rubutu ta yi a paper ta bawa Nawaz tace.
"Muna buƙatar waɗan nan yanzu."
"Okay Doctor." Ya faɗa yana amsar takardar ya fice, kai tsaye pharmacy ya nufa ya bada takardar. Magunguna da allurai ne aka bashi sai sanitary pads, koma wa yayi yaje ya kaiwa Doctor. Kayan ta amsa ta duba sannan ta ɗago tace.
"Okay kaje kazo mata da pant ɗin da za'a yi mata amfani da shi." Shiru ya yi yana tunani, har sai da Doctor tace.
"Ko akwai matsala ne, ba kace ƙanwarka bace?."
"No babu wata matsala yanzu zan je in kawo." Ya faɗa yana miƙewa ya fice daga ofishin.
^^^^^^^^^^^^^
A can gida kuwa hankalin Momy ya kasa kwanciya a kan fitar da Meerah ta yi, kuma ta san bata jin daɗi. Gashi shiru har yanzu bata dawo ba har an yi sallar magrib, kasa daurewa ta yi ta ɗauki waya ta saka kiran Jawad.
"Kana ina ne?." Ta yi masa tambayar cikin sanyin murya.
"Ina gab da shigowa gidan ne Momy." Ya bata amsa cikin ladabi.
"To kar ka shigo, kaje gidan su Zeezee ƙawar Meerah ka ɗauko min ita. Ta fita bata jin daɗi kuma har yanzu bata dawo ba." Momy ta bashi umarni.
"Okay Momy." Ya faɗa yana juya kan motar ya nufi hanyar gidan su Zeezee ɗin, kai tsaye gidan ya nufa kasancewar sun saba kai Meerah idan ana wani abu a gidan. Lokacin da ya isa tuni an tashi a wurin taron don har an yi sallar magriba ma.
Horn ya yi mai gadi ya leƙo ya ga waye kafin ya buɗe masa ƙofa, ciki ya shiga sannan ya buɗe motar ya fito ya jingina a jikinta yana duba wayarsa. Inda yake tsayen mai gadi ya ƙara so yana tambayar sa wanda yake son gani.
"Barka da dare Baba." Jawad ya gaishe sa, amsa masa ya yi da kula wa yana washe masa baki.
"Dama Meerah za'a yi wa magana ta fito mu tafi." Jawad ya faɗa masa yana gyara tsayuwarsa.
"Ai in dai Hajiya Meerah ce ta jima da fita a gidan nan gaskiya, don ba'a tashi a taron bama ta fita da alama dai akwai abinda ke damunta." Malam Maude mai gadin su Zeezee ya bawa Jawad amsa.
"Ban gane ta jima da fita ba, amma ai bata je gida ba, don Momy ce ta kira ni tace nazo na ɗauke ta." Jawad ya faɗa gabansa na faɗuwa, don basa wasa da al'amarin Meerah ko kaɗan.
"Gaskiya ranka ya daɗe sai dai a bincika wani wurin, don fita kam ta fita." Malam Maude ya sake faɗa.
"Okay to don Allah ka yi min magana da Zeezee ɗin." Ya faɗa yana ciro waya ya dannan kiran Momy, bugu ɗaya ta ɗaga don hankalinta ya kasa kwanciya da rashin dawowar Meerah. Ga Jawad ɗin data aika shima shiru basu dawo ba, dama tana ƙoƙarin kiransa ne nasa kiran ya shigo mata.
"Wai a ina kuka tsaya ne Jawad, baka ganin dare ya yi ne?." Momy ta faɗa lokacin data amsa wayar.
"Momy dama tambaya zan yi ko Meerah ta iso gida ne?." Jawad ya faɗa yana jin hankalinsa na ƙoƙarin tashi.
"Wace irin tambaya ce wannan Jawad? Ya zan aike ka ka ɗauko min yarinya ka kira ni kana tambayata wai ko ta iso, ce maka aka yi ta taho ne." Momy ta tambaya tana jin tashin hankali ya na kawo mata ziyara.
"Ba haka bane Momy ki kwantar da hankalinki, dama gate Man ɗin gidan ne yace min ta tafi gida. Amma na saka ya kira min Zeezee in tambayi abinda ke faruwa." Jawad ya faɗa cikin son kwantar mata da hankali.
"Wani irin kwantar da hankali Jawad an ce yarinya ta fito kuma bata zo gida ba?." Momy ta faɗa tana miƙewa tsaye.
"Yauwa Momy ga Zeezee ta fito zan kira ki." Ya faɗa yana katse kiran.
"Sannu da zuwa Ya Jawad." Zeezee ta faɗa lokacin data ƙara so."
"Yauwa Zeezee, murnar ƙaro shekara, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka." Ya taya ta murna fuskarsa ɗauke da murmushin yaƙe.
"Ameen ya Allah Ya Jawad, thank you so much." Zeezee ta faɗa. Kafin ya yi magana ta riga shi da cewa.
"Yaya jikin Bestie? Ta zo bata jin daɗi nace ta shiga ciki ta kwanta in sallami friends ɗin mu sai in zo mu mayar da ita gida. Ashe wai tafiya tayi bata jira ni ba, dama yanzu muke shirin zuwa mu duba ta ni da Yaya Abdul." Ta ƙare maganar cikin sanyin muryar dake nuna rashin jin daɗinta a kan jinyar Bestie ɗinta.
Wata irin zufar tashin hankali ce ta fara karyo wa Jawad, don ta tabbata dai Meerah ta bar gidan nan kuma bata ƙarasa gida ba. To tana ina kenan?, a ina ta tsaya?. Waɗan nan tambayoyin ne ke masa yawo a cikin kai.
"Lafiya kuwa Ya Jawad?." Zeezee ta faɗa ganin yanda yayi shiru yana tunani. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Gaskiya ba lafiya ba Zeezee, don Meerah ba ta je gida ba. Don yanzu ma haka ɗaukarta nazo."
"Bata je gida ba kuma? To ina taje kuma bata da lafiya fa?." Zeezee ta faɗa cikin damuwa.
"Bari kawai naje na duba ta." Jawad ya faɗa yana shigewa mota ya rufe.
"Okay Ya Jawad, don Allah ki kira mu idan ta koma ɗin. Gamu nan zuwa muma, dama zamu zo duba ta." Zeezee ta faɗa muryarta ɗauke damuwar rashin sanin halin da Bestie ɗinta ke ciki.
"Okay in sha Allah." Jawad ya faɗa sannan ya jan motar ya fice, a hankali ya rinƙa tafiya yana duba gefen hanya wai ko zai ganta. May be ko ta kasa tafiya ne, ta nemi wuri ta zauna tunda an ce bata da lafiya. Sai dai har ya kai gida bai ga ko mai kama da ita ba.
Kasa shiga ciki ya yi don bai san mai zai faɗawa Momy dake ta kiransa ba, yana ce mata ga su nan tahowa. Koma wa ya yi ya sake bin hanyar yana ƙara dubawa a hankali, a gefen hanya ya hango abu yashe a ƙasa.
A hankali ya gangara ya tsayar da motar ya fita ya nufi wurin da ya hangi kayan, ƙaramin mayafi ne yashe a ƙasa sai hand bag da waren takalmi. Wata irin bugawa zuciyarsa ta yi hankalinsa na tashi, don tabbas kayan Meerah ne waɗan nan. Domin kuwa jiya a gaban su ta fito da kayan tana nuna wa Momy, cewar kayan da zata saka a Birthday party ɗin Bestie ɗinta ne.
Duƙa wa ya yi ya kwashi kayan, sannan ya juya ya shiga dudduba wa yana kallon ko ina wai ko zai ga inda aka bi da ita. Don tabbas wani ne ya ɗauke musu ƙanwa. Gidan dake kusa da inda yake a tsaye aka buɗe, motoci guda biyu suka fito daga ciki suka wuce, gate Man na ƙoƙarin rufe ƙofar ya ƙarasa da gudu yana dakatar da shi.
"Bawan Allah lafiya kuwa? Me kake buƙata?." Mai gadin ya tambayi Jawad ganin yanda ya iso a rikice.
"Don Allah Malam baka ga waɗanda suka ɗauki wata yarinya a dai-dai can wurin ba?!." Ya yi masa tambayar cikin tashin hankali yana nuna masa inda ya ɗauki kayan.
"Wace irin tambaya ce wannan bawan Allah? Ta ya zan ga waɗan da suka ɗauke wata yarinya bayan ina cikin gida a rufe?." Ya mayar masa da tambaya.
"Ka ga waɗan nan kayanta ne a can na tsince su, tabbas wasu ne suka ɗauke Meerah." Ya faɗa hawaye na cika masa ido, domin kuwa suna da matuƙar rauni a kan Meerah. Suna mata wata irin soyayya mara misaltawa.
"To gaskiya ni ban gani ba kuma ban ji wani motsi ba, saboda haka sai an jima Allah ya bayyana maku ƙanwarku." Mai gadin ya faɗa cikin rashin damuwa, yana kammala faɗa kuma ya mayar da ƙofa ya datse.
Jiki a matuƙar sanyaye Jawad ya juya ya koma cikin mota, koda ya koma cikin motar kasa janta yayi. Dafe kansa ya yi kawai cikin matsananciyar damuwa da rasa abin yi.
Kamar an tsikare sa ya ɗauki wayarsa ya saka kira, bugu biyu aka ɗauka. Sallama ya yi cikin rawar muryar tashin hankalin da yake ciki. Amsa masa aka yi daga can ɓangaren cikin dakakkiyar murya.
"Jawad kana lafiya kuwa? Wani abu ya faru ne? Ameerah tana lafiya dai ko?." Ajmal ya jero masa waɗan nan tambayoyin, saboda muryarsa kaɗai da yaji ta tabbatar masa da akwai matsala. Da ƙyar Jawad ya iya saita kansa yace.
"Yaya Ajmal dama Meerah ce taje gidan su ƙawarta Zeezee wurin Birthday party ɗinta, to shine Momy nace in je in ɗauko ta. Kuma ko da naje sai aka ce wai bata da lafiya ta jima da tafiya gida. Kuma....Kum.... Ku...."
"Kuma me Jawad?!!!." Ajmal ya daka masa wata gigitacciyar tsawar da ta firgita shi, ta ƙara saka shi cikin tsoro a kan wanda yake ciki. A gefe ɗaya kuma kiran Momy ne ke ta shigo masa wayar.
"Talk to me mana Jawad, what is happening?!." Ya ƙara buga masa wata tsawar. Cikin rawar jiki data murya Jawad yace.
Bata je gida ba Yaya, kuma koda na duba hanya na tsinci mayafi, hand bag tare da waren takalminta. Tsoro nake ji Yaya kar aje wasu ne suka ɗauke mana ita!." Ya ƙare maganar cikin karyewar murya hawayen da yake riƙe wa tun ɗazu suna zubo wa a saman kumatunsa.
"What are you saying Jawad? Kana nufin Meerah aka ɗauke?!." Ya yi masa tambayar yana jin wani irin matsanancin tashin hankali, haɗi da tsoro suna kama shi kai tsaye........
Oum Fatima
***