Chaptef 1️⃣
👽YANAYIN RAYUWA 👽
Oumm Ashraf
Page 1️⃣
Bismillahir rahmanir raheem
Gudu take tana Juyawa don ganin bayan Ta Ko har Yanzu Suna binta , gudu take yi Suna bin ta a baya , je fa kafarta Kawai take yi ko ina dan ceton ranta , tun tana gudu da kuzari har Ta soma gajiyawa , karfin Ta ya kare , gudu Ta cigaba Dayi cikin gajiya wa, bata Ankara ba Ta ji ta gangara , wani ƙaton wuri ne ta fada , wanda suke binta kuma ganin ta faɗa wannan wajen ya saka suka tsaya , babban cikin sune wayar sa tayi ringing ɗagawa yayi ya kara a kunne yace: “ uwar ɗakina aiki yayi wannan yarinya sai dai uwarta ta haifi wata amma ita dai ta sheƙa” bushewa akayi da wata mahaukaciyar dariya daga cikin wayar kafin muryar wata mace ta ratsa ta cikin wayar tace : “Jaga nasan ai baka wasa , dan haka ka duba account dinka na tura maka ragowar kudin ka “, ihu ya saki tare da cewa : se dake uwar ɗakina ni nasan ba kya wasa da irin sabgar nan shi yasa nima bana sanyi wajen biya miki buƙatun ki” kashe wayar akayi daga ɓangaren wacca ya kira da uwar ɗakinsa……….******
HAMAD POV*********
Durƙushe yake gaban wani dattijo wanda aƙalla zeyi shekaru sittin a duniya, kwance dattijon yake , ƙoƙarin ɗago shi yake , wanda se wash wash yake ce wa , alamun ya jin ciwo a jikinsa , shi kuma Hamad ɗin se sannu yake jera masa , da kyar ya ɗago shi ,pillow yayi saurin sakawa a bayan dattijon yadda zeji daɗin zama da kyau,duba na kaiga dattijon, fari ne sol dashi kyakyawan ne duk da tsufa yazo masa amma kana ganin sa kasan ya zuba kyau lokacin samartaka , dukda har yanzu farin na shi na nan , se dai wahalar rayuwa da kuma rashin lafiya da yake fama da ita , wacca har yau an rasa sanadin wannan cuta , kuma babu kudin kaishi asibiti domin duba lafiyar sa , se dai a kwantar dashi kuma atayar amma yafi shekara uku da wannan cuta a tare dashi*************
Tafiya take da shanun ta da tafita kiwo dasu ,gangarawa suke yi , tana bi tana sake kaɗosu suna sake kaucewa, yan waƙe waƙen su takeyi na fulani , wanda inda sabo ta saba domin ko yaushe ita kaɗai take zuwa , saboda haka ta saba zuwa , murmushi take ta zubawa da ta tuno saurayin ta wato Gidado , tuntuɓe taji tayi da wani abu kamar dutse , kallonta ta kai wajen kwance taga wata mace , ja baya tayi da sauri cikeda kiɗimewa da kuma tsoro ,takai wajen mintuna uku kafin ta matsa kusa da wacce ta gani , mayafin da ya rufe mata fuska ta ɗan yaye , se dai me wata mace ta gani me kama da ita sak kamar wasu yan biyu , baya ta sake ja cike da tsoro da kuma mamaki wannan me kama da itan ****************
Daga alƙalamin ✍️
Oumm Ahsraf 026 #