YANAYIN RAYUWA

Chapter 2️⃣

by @aishayakubuahmad811

👽YANAYIN RAYUWA 👽

Oumm Ashraf 


Page2️⃣


U.S.A 

Aji ne cike yake maƙil da student , wasu  fararen wasu kuma baƙaƙe , sit irin me haɗe da table a jiki irin dai na zaman mutum ɗaya, wani baturen lecturer ne yake bayani a gaban ajin yayin da kowa yake jotting kuma duk wanda ka gani hankalinsa na kan abunda lecturer dinann yake  faɗa , zagayawa lecturern ya shiga yi a class dinn , tsayawa yayi daidai wani sit , wata yarinya ce ta ɗora kanta a kan table ɗin , dukan table ɗin yayi a hankali kafin ya furta “ Amnah Dangi are you ok” ya fada tare da zuba mata idanuwansa , ɗago fuskarta tayi , tareda lumshe idanunta tana faɗin “ sorry sir , sannan da ɗauke kai , murmushi kawai yayi tareda cigaba da tafiya ,don yasan Dan Amnah D na bacci bashi da damuwa , dom yasan bata wasa da karatu ko kaɗan , shiyasa be nuna damuwarsa ba da yaga tana bacci***********



HAMMAD’S POV**********

Zaune yake ya zubawa waje ɗaya ido yana tunani ,dama haka mata suke , me yasa mata duka halinsu ɗaya , meyasa mata basu da adalci, meyasa mata suke butulu , tambaya yake yayinda idonsa ya ciko da kwalla wacca be san ta taru ba , indai haka mata suke baya sonsu , ya tsane su , baya kaunar duka wata mace a duniyar nan , siririn tsaki ya ja tare da kai duban sa ga tsohon dake kwance , idanunsa a lumshe suke , dukda yasan da wuya bacci ya ɗauke kakan nasa , matsowa yayi tare da saka hannun sa ya fara danna masa ƙafafuwansa , buɗe idon tsohon yayi tare da kafe Hammad da ido , wanda shi kuma danna ƙafafun kakan nashi kawai yake yi , muryar kakan shi ce ta katse masa tunani , yaji yana cewa “ muhammadu , “ ɗago kyawawan idanunsa yayi tareda kallon kakan nashi don yasan abunda ze saka Baffa ya kira shi da asalin sunan shi abu ne mai muhimmanci ,kallon Baffan yake ganin haka yasaka Baffan cigaba da magana dan yasan halin jikan nasa wannan kallon shi ke nufin amsa maganar tashi , maganar shi ya cigaba kamar haka ,” muhammadu  kamun wata alfarma mana , dan Allah kayi koƙari wajen yaƙi da sheɗan , ko bayan raina ka nemi Hafsa , ka koma wajen mahaifiyar ka , ka neme ta , sannan kace ni dai na yafe mata , kamar yadda mahaifiyarta ta yafe mata , kaima kuma ina roƙon ka yafe mata” cikin karyewar murya da sanyin jiki Hammad yace “ Baffa ka taimaka don Allah koda wannan ce alfarma ta ƙarshe da zaka mun , ka taimaka ka faɗa mun wane babana “ ya ƙarasa faɗa cikin rawar murya , alamu yana dab da fashe wa da kuka , idanun Baffa ne suka ciko da hawaye , be amsa masa tambaya ba , ya share zancen da cewa “ kaga an kira sallah a masallaci , kuma yunwa ma nake ji , shiru Hammad yayi kamar baze ce komai ba , miƙewa yayi tareda girgiza kai domin yasan Baffan baze faɗa masa ba , don ba wannan ne karon shi na farko ba wajen tambayar Baffan , amma kullum haka yake masa , alƙawari ya ɗaukar wa kansa , Insha Allahu baze sake tambayar Baffan ba , har se idan shine yayi ra’ayin faɗa masa da kansa*****************



Sauri tayi ta matsa wajen shanun ta , gorar ruwa ta ɗakko , buɗe murfin tayi tare da zuba mata ruwan a fuska , shiru bata motsa ba , har ta yanke tsammani , ta fara tunanin kodai ta mutu , se taji an saki ajiyar zuciya da ƙarfi , cikin sauri ta fara janta , cikeda dauriya ta ɗora ta akan ɗaya daga cikin shanun nata , sannan ta nufi hanyar gida tana ta tunanin wannan wacca ta gani din ***************

Daga alƙalamin✍️





Oumm Ashraf 026#