KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BA TA BUGA BA, SATAR DA AKAYI MANI
KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BA TA BUGA BA, SATAR DA AKAYI MANI
KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BATA BUGA BA SATAR DA AKAYI MANI
Shekarun baya kaɗan da suka wuce.
Na fara tara ƴan kuɗi na, kwatsam! Wani yaro ya kawo waya yace ta sayarwa ce gata idan zan siya.
Na ce "Nawa?
Ya ce "Idan kin siya dubu biyar."
Na ce "Kash! Gashi wayar kuwa tayi kyau, amma banda dubu biyar, idan dai ka bar min dubu uku."
Ya ce "Ba zata saidu haka ba, indai ƙara wani abu, kaka-kaka dai mukayi ciniki a dubu uku da ɗari biyar, ga wayar nan kuwa tocin mai kyau, na ba shi kuɗin shi, na kaɓi waya na saka layi na, naci gaba da sha'ani na.
Zanyi kusan wata huɗu da wayar nan ina amfani da ita ina jin daɗi, ko matsala ba ta ba ni, inyi Facebook inyi Tiktok inyi Whatsapp in shiga YouTube, wayar nan ba abinda ba tayi.
Rannan dai zan fita, tsautsayi yasa na bar wayar nan a gida, ni dai na san na ajiye wayar nan a cikin jaka, na dawo unguwa na nemi waya sama da ƙasa ta ɓace, da farko na ɗauki abin kamar wasa, daga baya dai ƙirji na ya rafa bugawa Dam! Dam!! Damm!! Na ji wani tashin hankali ya ziyarce ni, na tattaro duka yaran layi, irin waɗanda nasan ba sa jin magana, hada wanda ya siyar min da wayar, na fara yi masu kashedi
"Ina gargadin ku da duk wanda yasan ya ɗaukar min waya ya fito da ita tun kafin in ɗauki mataki! Domin kuwa ba haƙura zanyi ba, ayi maza-maza a fito min da waya ta tun kafin in jama yaro yasin! cikin shi ya ƙulle! kun dai san yaseen idan aka jama mutum ita sai ya lalace, don haka a fito min da waya ta tun kafin inyi!!!"
Yara suka fara rantse-rantse ba su ba ne, wasu hada kuka.
Nayi duk iya barazanar da zanyi, yaran nan ba su fito min da waya ba.
Naje na ɗauki buta nayi Alwala, na ɗauko Alkur'ani na karanta Yaseen, na ce "Zuwa gobe duk wanda akaji cikin shi na ciwo to shine ɓarawon wayar."
Washe gari, shiru ba wanda cikin shi ya yi ciwo.
Sai wani ƙani na ya ce "Binta ai Yaseen ɗin da kika yi ba zatayi aiki ba, ki ba ni kuɗi gobe zani kasuwar Ɗan dume, akwai wani mai magani duk ranar kasuwa yana zuwa, kuma idan yace abu yayi sai kiga yayi, mutumin nan har hular shi yana ajiyewa nesa kuma ya kira ta tazo, ko ya zuba ƙasa a kwano aga ta zama abinci, ko ya nannaɗa ganye ya zama kuɗi, idan akayi maka sata har kiran ɓarawon yanayi a gaban ka ka ganshi, don haka gobe kawai ki ba ni kuɗi inje wurin shi, ina miƙa mashi kuɗin ma zai gane abinda ya kawo ni, na tabbata wanda ya satar maki wayar nan dole saiya maido ta."
Na ce "Nawa ne kuɗi maganin?"
Ya ce. "Naira ɗari."
Na ce "To Ni yanzu banda kuɗi, amma gobe idan kaje kasuwar kayi ciniki karanta min ɗari ayi maganin."
Ya ce "To shikenan."
*********
To shi ƙanin nawa abinda yake kaishi kasuwar Ɗan dume ɗin shine, tallar fodar kwari yake, wani mutumi ne a layin mu yake basu fodar kwari bashi, suna bin kasuwanni, idan suka dawo su bashi kuɗin shi su cire ribar su.
Sai dai mutumin kwata-kwata bai da haƙuri, da sun dawo kasuwa yake binsu har gida ya karɓo kuɗin shi, shi baya yarda ayi mashi wasa da kuɗi, don har dukan yaro yake idan ya ɓatar da kuɗi, suna masifar jin tsoron mutum nan, shiyasa da sun dawo kasuwa suke yin saurin sallamar shi.
************
Toh! washe gari kuwa ƙani na ya shirya ya tafi kasuwar Ɗan dume, cike da kwarin gwiwa zai je wurin mai magani, don shima kanshi ya ƙosa a kama ɓarawon.
Abin tashin hankali shine har dare bai dawo kasuwar ba, shiru-shiru, duk abokan tafiyar shi sun dawo sai shi kaɗai, ga gari ba wata cikakkiyar lafiya ba.
Wasa-wasa dai har tsawon kwanaki uku bai dawo ba, hankalin kowa ya tashi, aka fara cigiyar shi, har masu zuwa kasuwar ake tambaya ko sun ganshi a cikin kasuwar? suce ba su ganshi ba.
Daga ƙarshe dai sai bayan kwana huɗu da yamma kuwa sai gashi ya dawo Hajaran-majaran, aka fara murna ana tambayar shi ina y'kaje? Me yasa baka dawo ba?
Kun san amsar da ya bayar kuwa?
To kuyi min comments da liking da sharing, anjima kaɗan in dawo in faɗa maku abinda ya hana shi dawowa da wuri. Amma idan banga ruwan comments ba da sharing ba, to gaskiya sai kun jira.
Fatima Dahiru Funtuwa Binta