KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BA TA BUGA BA, SATAR DA AKAYI MANI
PART 2 KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BUGA, SATAR DA AKAYI MANI
PART 2
KAƊAN YA HANA ZUCIYA TA BATA BUGA BA SATAR DA AKAYI MANI
Wanda bai karanta PART 1 ba ya duba Comment Sactoin
Daga ƙarshe dai sai bayan kwana huɗu da yamma kuwa sai gashi ya dawo Hajaran-majaran, aka fara murna ana tambayar shi ina kaje? Me yasa baka dawo ba?"
Ya ce "Ku dai bari in samu wuri in huta tukuna, ai na sha wuya, an neme ni kuwa?"
Na ce "Nema na nawa ma kuwa? An nema-an nema har gidan rediyon Martaba, ana ta neman ka ana cigiyar ka, shin ina ka shige?"
Ya ce "Ba mun rabu da ku akan idan naje kasuwar Ɗan dume nayi ciniki in ranta maki naira ɗari inje wurin mai magani ba?
To da naje kasuwar sai nace bari in bari sai na gama ciniki na sannan inje wurin mai maganin, domin yana faɗa min ɓarawon inzo da rawar jiki in faɗa maki, domin kuwa na tabbatar mutumin nan sai ya tona ma ɓarawo asiri, saboda naga yanayi sosai kuma aikin shi kamar yankan wuƙa yake.
Sai da na gama ciniki na wurin ƙarfe uku, gashi nayi ciniki ranar sosai, wurin dubu goma sha biyar na ware na saka a cikin Aljihu na, na riƙe Naira ɗari ɗin da zamba mai magani.
Naje wurin mai maganin kuwa cike da mutane, masu karɓar magani da ƴan kallo, haka nima na ja layi, idan an sallami wannan a sallami wannan, har dai layi yazo kaina, na miƙa mashi kuɗin, ya fara bubbuga kuɗin domin fara gano matsalar data kawo ni.
Kamar ance in laluba Al-jihu na, na jishi a yage, alamar ansa reza an yanke, wata irin zufa data yanko mani, ban san lokacin da na kwarara uban ihu ba, na koma baya da gudu ina duba kuɗi na, ban ƙara komawa ta wurin mai maganin ba, ban taɓa jin tashin hankali irin na ranar ba, gashi kuɗi ba nawa ba, mai fodar kwari kuwa ba haƙura zaiyi ba.
Don haka dana gama kuka na, na yankema kaina shawarar zama cikin kasuwar intayin buga-bugar sana'a har saina tabbatar na haɗa ma mai fodar kwari kuɗin shi.
To dalilin da yasa kuka ga ban dawo ba tsawon kwanaki huɗu, ai a Kasuwar nan ba aikin da banyi ba, nayi dako-nayi sharar shaguna- nayi talla, duk ko inda na san zan haɗu da wanda ya sanni bana zuwa, ko hango mutum nayi sai in ɓoye, saida na tabbatar na haɗa ma mai fodar kwari kuɗin shi sannan na dawo."
Na kai mashi duka a kafaɗa, Faff! Sannan na ce "Amma kai sakarai ne! To me yasa ba ka koma wurin mai maganin ba, ka bashi ɗari biyu ya tona asirin ɓarawon waya ta, da kuma wanda ya yanke maka Al-jihu ba? Yanzu shikenan ka ja mana asara! Kayi wahalar banza! to ai shikenan ba komai Allah ya saka mana.
Ƙarshe! Ayi min comments da liking da sharing. kwana biyu kun jini shiru ba, to a ƙara haƙuri da ni
Fatima Dahiru Funtuwa Binta