MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 51

by @maimunabala209

MATAR GIDA BOOK 2



SHUUKRAN/022


YOTA ASSOCAITION



P51



Idanun Ɗalha kanta ya ce ''o..k..y'' ya faɗa a rarrabe yana sosa kai kafin ya ce ''me ya kamat a dafa masu'' Unaisa ta buɗa hannu alamar ko ma me kafin ta ce ''duk abinda ya yi maka'' murmushi kawai Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ki dai yi tunani zuwa gobe'' ya faɗa yana miƙewa tsaye da shirin barin ɗakin,sai da ya kai bakin kofa kafin ya waigo ya mayar da dubansa gareta ya ce ''sai da safe'' ba tare da kallon inda ya ke tsaye ba Unaisa ta basa amsa ya yin da take hawa gado ta ce ''Allah ya kaimu'' washe gari juma'a karfe takwas da wasu ƴan mintina Ɗalha ya fita ofis ya yinda Unaisa na can tana baccin asara,bayan tafiyarsa ofis ne kiran Amirah ya shiga wayarsa bai amsa kiran ba ya kafe fuskar wayar da ido har kiran ta katse bai ɗaga ba,kiranta ya sake shiga a karo na biyu nan ma har ya gama ringing bai ɗaga ɓa,bayan wasu ƴan sakanni ya kai hannu ya dauki waya ya kira layin har ya katse ba a daga ba yana shirin sake kira sako ya shiga wayarsa,Amirah ce ta tura masa yadda ta ce tana son zuwa gida ita da yara ta gaida mahaifinta, Ɗalha ya rubuta mata ok babe Allah tsare hanya daga haka ya tura mata,misalin ƙarfe ɗaya na rana Ɗalha na zaune ofis Unaisa ta tura masa list ɗin abubuwan da zata bukata wajen girkin gobe,kallon list ɗin ya yi kafin ya kira sectary ɗinsa,ƙudi ya tura masa a account tare da list ɗin ya ce dan Allah ya yi maza ya je ya yi siyayyar ya kaiwa Unaisa,daga haka ya cigaba da aikinsa,a can wajen Unaisa tana nan zaune tana jiran zuwan Aina'u har karfe uku Aina'u bata zo ba a lokacin sactarey ɗin Ɗalha ya kawo mata cefane,wayarta ta dauko ta kira layin Ɗalha bugu ɗaya ya ɗaga nan Unaisa ta shida masa Aina'u bata zo ba Ɗalha bai ce mata komai ba kawai ya kashe waya tare da kiran layin Aina'u sai da ya mata kira uku bata amsa ba a kira na huɗu ne ta amsa,cike da girmamawa ta gaida Ɗalha, amsa mata ya yi  tare da tambayar ta lafiya bata je taya Unaisa aiki ba hakuri ta basa kafin ta shida masa cewar ƴarta ce bata ji daɗi ba yanzu haka suna asibiti ana mata ƙarin ruwa nan Ɗalha ya jajanta mata daga haka suka yi sallama,bayan Ɗalha ya kashe waya ne ya turawa Aina'u ƙudi har naira dubu goma,bayan mintina kaɗan Ɗalha na zaune yana aiki yaji saƙo ya shiga wayarsa daukar waya ya yi tare da duban saƙon,Aina'u ce ta tura masa saƙon godiya,ajiye wayar Ɗalha ya yi bayan ya gama karanta saƙon ya cigaba da aikinsa,misalin ƙarfe biyar daidai Ɗalha ya shigo gida bakinsa dauke da sallama, Unaisa dake tsaye kitchen tana aiki ta amsa masa sallama tana rage wutan gas tsaye Ɗalha ya yi bakin kofa kitchen yana ƙarewa kitchen ɗin kallo gani ya yi gaba ɗaya kitchen ɗin ya hargiste ko ina kwanuka ga kayan miya gefe guda,gefe ɗaya kuma kaje ne guda uku cikin tukunya ta zuba masu kayan ƙhamshi da ɗanɗano,da alama bata dade da gama gyara kajen ba,wasu abubuwan ma bata cire su daga ledar cefane ba,ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauki tare da faɗin ''sannu da aikin'' a takaice Unaisa ta amsa masa tana kunna gas tare da daura tukunyar kajen a kai,mayar da duban ta ta yi garesa kafin ta ce ''tare ku ke da Aina'u?" Ɗalha ya karasa shiga kitchen hannusa riƙe da jakar laptop ɗinsa yana jingina bayan sa da bangon kitchen ya ce ''a'a ni kaɗai ne, ƴarta ce ba lafiya bayan mun gama waya na kirata shine ta faɗa min'' idon Ɗalha kan ledar zubo da abarba ya ce ''za ki iya duk wannan aiki?" murmushi Unaisa ta yi kafin ta ce ''zan iya''





















Ɗalha ya taɓe baki kawai cikin zuciyarsa yana addu'a Allah yasa abinci ya yi dadi,fita ya yi daga kitchen zuwa ɗakinsa,rage kayan jikinsa ya yi kafin ya yi wanka,bayan fitarsa daga bathroom ya shirya kansa cikin wasu ƙananan kaya daga haka ya fita daga ɗaki, bayan fitar sa kitchen ya nufa Unaisa na shirin daura zobo wuta bayan ta wanke ta zuba duk wani abinda ya kamata Ɗalha ya shigo kitchen yana ƙare mata kallo shi dai mamakin ta yake daman ta iya dafa abinci duk tsawon zaman sa da ita amma ko sau ɗaya bata taɓa dafa masa abinci ba sai dai ta yi masa order? ko ko kame kame take? naɗe hannu ya yi a kirji yana kallonta gaba ɗaya bata san yana yi hankalinta na kan zobo da ta daura kan gas,gyarar murya ya yi kafin ya yi magana cikin kwantar da murya ya ce ''da akwai abinda zai taimaka maki ne?" mayar da dubanta ta yi garesa bayan ta rufe tukunyar zobo ta kunna fanfon sink tana wanke hannu ta ce ''a'a ba sai ka taya ni ba zan iya'' numfasawa Ɗalha ya yi can dai ya ce ''ok shikenan Allah ya taimaka'' Unaisa ta amsa da ''Ameen'' daga haka ya fita daga kitchen ɗin ya nufi hanyar fita daga gidan,bayan fitar sa wani eatry ya je ya siya abinci take away biyu  nashi da Unaisa daga haka ya nufi hanyar komawa gida,yana daf da shiga layinsu aka fara kiran sallar magrib hakan yasa ya samu  waje ya parking motar gefe wani masallaci,Ɗalha bai koma gida ba saida ya yi sallar isha'i kamar yadda ya saba,bayan komawarsa gida ya tarar har sannan Unaisa na kitchen cike da mamaki ya shiga kitchen,Unaisa dake tsaye wajen gas ta buɗe oven tare da fidda meat pei,dai dai lokacin da ta ajiye meat pie ɗin kan kitchen island idonta ya haɗo da Ɗalha cike da mamaki Ɗalha ya ce ''har yanzu?" numfasawa ta yi kafin ta ce ''na kusa gama'' karasa shiga kitchen Ɗalha ya yi yana ajiye ledar take away kan kitchen island ya ce ''no no is oky ki bar aikin haka sai gobe in Allah ya kaimu,ba da wuri za su zo ba sai irin karfe huɗu haka so ki bari kawai ki je ki huta'' ya faɗa yana riƙe kafaɗar tare da juyo da ita suna fuskantar juna lumshe ido Unaisa ta yi kafin a hankali ta buɗe su kan Ɗalha tana kallonsa hada ta yi ya yi da jikinsa a hankali yana buga bayanta,sosai ta gaji rabon da ta yi aiki irin wanda ta yi yau har ta manta,a hankali ya raba jikinsa da nata yana kallon fuskarta ya ce ''kin yi sallah? alama ta yi masa da kai alamar a'a ya ce ''ok je ki yi wanka ki yi sallah ga abinci nan na siyo mana da kin ci ki kwanta''ya ƙare magana yana shafa gefen fuskarta gyada masa kai kawai ta yi daga haka ta nufi hanyar fita daga kitchen ɗin tana tsallaka robobi da ledojin cefane da ido Ɗalha ya bi bayanta har ta fita daga kitchen ɗin,bayan fitarta wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga bin kitchen ɗin da kallo yadda Unaisa ta hargitsa kitchen kamar wacce aka bawa babban aiki abinci ƙala ɗaya zata daga farar shinkafa da miya sai salak da zoɓo sai kuma meat pie ya so ta dafa kala biyu amma ganin list ɗinda ta tura masa yasa bai ce mata komai ba kawai ya aika aka siyo mata abinda ta rubuta,yadda kitchen ɗin ya fita hayyacin sa za ka rantse aiki dafa namar sa aka bawa Unaisa kitchen kaca kaca kamar aikin sallah murya can ƙasa Ɗalha ya ce ''Allah shi kyauta'' 




















Daga haka ya shiga gyara kitchen ya dauki a ƙallah awa guda wajen gyaran kitchen,bayan ya gama gyara ne ya fita parlour,nan ya tadda Unaisa zaune kan kujera tana bacci riƙe da take away ɗin abinci bata gama cin abinci ciki ba amma ta ci ya fi rabi,a hankali Ɗalha ya shiga kiran Sunanta tare da buga gefen kujera inda ta daura kanta a hankali sai da ya kira sunanta kusan sau uku kafin ta buɗe ido a hankali,hannu ya kai ya karɓi take away da take riƙe da shi yana ajiye kasan parlour mayar da dubansa ya yi gareta ya ce ''kin yi sallah?"gyada masa kai ta yi alamar eh Ɗalha ya ce ''wanka fa'' ya faɗa yana bin jikinta da kallo cikin muryar bacci Unaisa ta ce ''sai gobe na gaji bazan iya wanka yanzu ba'' ta faɗa tare da barin parlour zuwa ɗakinta da ido Ɗalha ya bita har ta shiga ɗaki,Allah ya sani yana son Unaisa sosai sai dai munanan halaiyar da ɗabi'unta da ta fitar tun satin farko na aurensu yasa ya ji gaba ɗaya ta fara fice masa a rai,sosai kuma ya yi nadamar aurenta,sai bayan aurenta ya fahimce Amirah mace ce ta gari ya yi kuma yi nadamar duk wani cin mutunci da ya yi mata,da Unaisa zata cigaba da haka kamar yadda ta yi yau, ya mata magana sau ɗaya ta amsa masa babu jayayya ta kuma yi abinda ya ce gashi har karfe takwas tana kitchen da zata cigaba da haka yana da tabbacin zasu zauna lafiya dukkan su ukun zai kuma yi iya bakin kokarin sa wajen wajen ganin ya sauke duk wani nauyin su dake rataye wuyansa amma halaiyar Unaisa sai ya ke gani kamar zaman ta da shi ba zai yi tsawo ba,wata doguwar ajiyar zuciya ya sauki kafin ya tashi ya nufi kitchen, tea ya haɗuwa kansa kafin ya dauki take away ɗin abinci ya fita daga kitchen,zama ya yi nan cikin parlour ya ci abinci tare da shan tea bayan ya gama ne ya kunna TV ya shiga kallon labarai karfe goma sha ɗaya dai dai ya kashe TV tare da wutan parlour da wutan kitchen,daga haka ya wuce ɗaki ya kwanta, karfe sha ɗaya na rana Amirah ce tare da yara zaune cikin ɗaki gidan mahaifinta tun ɗazu suka zo amma bata samu Abba gida ba Anty ce kadai da yarinyar karama mai shan nono duk sun takura daga Amirah har yara,ko kaɗan su Sudais sun ƙi sakin jiki da Anty kasancewar ta saba hantarar su duk sanda suka je gidan,sai dai yau ta yi ta jan su da wasa,duk sun ƙi sakar mata fuska sai ma sun koma bayan Amirah sunbɓoya,da ƙyar Amirah ta samu ta shawo kansu suka biyo ta ko kaɗan basu son jin Amirah ta ce za a je gidan Abba,da Amirah ta ga haka sai ta fidda wayarta ta kunna masu carton har ita suka haɗu suna kallo tana kwance kan gado yaran na kewaye da ita,har karfe biyu Amirah da su Sudais suna cikin ɗaki a lokacin ne Anty ta shigo ɗakin hannunta riƙe da kolar abinci ta dire shi gefen gado da su Sudais suna kwance lokacin Amirah na zaune kan darduma ta idar da sallar azahar,haka Anty ta cigaba da jansu da wasa duk suka zuba mata ido ta gama ta fita,Abba bai dawo ba sai karfe huɗu da rabi na la'asar nan su Sudais suka cika gida da hayaniya Amirah na zaune parlourn Abba suna hira kan kuɗaɗen da ta bawa Kabir yana juya mata tana fadawa Abba yadda ta samu riba mai yawa sati biyu da suka gabata,Amirah ta dauki 50k ta bawa Abba, Abba ya ce mata ya yi yawa ya dauki 20k ya ce sauran ya bawa su Sudais,Amirah ta yi murmushi,su Sudais sai faman tsalle tsalle suke cikin parlour duk sun cika Abba da surutu, ganin hakan yasa Amirah cewa Abba zata je wajen Anty Abba ya ce to,dubu goma Amirah ta bawa Anty bayan ta yi mata bayanin yadda aka samu kuɗi sosai Anty ta yi murna ta sa hannu ta karɓi kuɗi tana washe baki tare da sawa Amirah albarka,Amirah ta amsa tare da yi mata sallama ta ce za su wuce Anty ta ce Allah tsare hanya,daga haka Amirah ta koma ɓangaren Abba ta sallame shi kafin suka fita da yara,Abba ya cika su Sudais da sweet buscuit daman baya rabuwa da su,siya yake ya tara a ɗaki duk sanda jikokinsa suka zo ya basu,dan su yake siya,har kofa Anty ta yi wa Amirah rakiya tana ƙara sa mata albarka 













SHUUKRAN