GA SANI GA SHAGALA

21-22

by @zahrasurbajo

Ana saura kwana uku a ɗaura auren Ayat, sai Ayra ta tashi da zazzaɓi. Cikinta yana mata ciwo, ga amai da tashin zuciya da suka addabe ta.

Da Ayat ta ga halin da take ciki,sosai ta damu.

“Anty ayra, mu je asibiti. Kina bukatar likita ya duba ki.”

Ayra ta girgiza kai.Tace“A’a, zan samu sauƙi.”

“Amma kina amaifa kuma cikinki yana ciwo. Bai kamata ki zauna haka ba.”cewar ayat cikin damuwa 

Ayra ta ƙara ƙin yarda da batun asibitin,dole ayat ta ƙyaleta,tunda ta kafe kan zata samu sauƙi,kuma ta gargaɗi ayat ɗin kan cewa karta faɗawa ummansu.
  A zuciyarta kuwa, wani tunani ne yake damunta. Tana tsoron ko ciki ne, kuma ba ta son a je asibiti a gano hakan agaban wani nata..

Sai kawai ta yanke shawarar zuwa wajen Ayan. Idan ya ga ya kamata su je asibiti, za su tafi tare dashi.

Da misalin ƙarfe tara na safe, Ayra ta shirya ta fito daga ɗakinsu tana rƙe da niƙab ɗinta a hannunta

Ummasu ta tambaye ta:

“Ina za ki kuma da safiyarnan alhudahuda?”

Ayra ta amsa cikin dauriya dan batason umma ta gane bata jin daɗi tace

“An gayyace ni taron buɗe wata Islamiyyane.Shine  Zan je na halarta.”

Umma ta yi mata fatan alheri.“To, Allah Ya kiyaye. Ki dawo lafiya.”

Ayat ma ta ce:“Allah Ya kai ki lafiya anty ayra ki kula min da kanki.”

Ayra ta amsa musu, sannan ta fita.

Amma  tana fita daga gidan, kai tsaye gidan Ayan ta nufa.

---
tana isa, ta shiga bedroom ɗinsa. Ayan yana kwance a kan gadonsa yana jin wani irin feelings na taso masa. Da ya ji motsinta, ya buɗe ido.

Koda ya gan ta, nan take ya lura cewa akwai wani abu da yake damunta,amma halin da yake cikine abinda yafi damunsa,hakanne yasa yajata kawai zuwa kan gadon ba tare daya bata damar yimasa bayanin abinda ke damuntaba.
Haka ya afka mata dan a buƙace yake da ita,ya dinga ci yana ƙarawa,seda ya samu biyan buƙatarsa sannan ya ƙyaleta.
Haka ya ɗauketa suka shiga wanka,bayan sun fitone

Ta zauna gefen gadon, tana dafe cikinta.

Ayan ya dubeta cikin kulawa yace

“Me ya same ki? 

Ayra ta sauke numfashi daƙyar sannan tace.

“Tun safe nake jin bana jin  daɗi. Ina zazzaɓi, cikina yana ciwo, sannan ina yawan amai da tashin zuciya.”

Ayan ya kalleta cikin damuwa.Yace 

“Kin sha magani?”

Ta girgiza kai.

“A’a.Ban sha ba”

“to Kin je asibitine?”

“A’a.”

Ayan ya yi shiru, yana kallonta.Sannan yace

“to Me ya sa?”

Ayra ta ɗan yi shiru kafin ta ce:

“Ina tsoron ko ciki ne.”ta bashi amsa tana rawar sanyi.

Ayan ya kasa magana na ɗan lokaci. Ya kalleta sosai, sannan ya ce cikin natsuwa:

“Ba za mu zauna muna zato ba. Sai an tabbatar sannan”

Ayra ta kalle shi.

“in Za ka raka ni to mu je asibitin?”

“Eh. Zan rakaki mana sa kayanki”

Ayra ta sauke ajiyar zuciya. Aƙalla yanzu tana tare da mutumin da ta fi yarda da shi, kuma duk abin da za a gano, za su fuskance shi tare.Cikin ƙwarin guiwa tasa kayanta,shima ya shirya suka tafi.

Bayan sun je asibiti aka duba Ayra, likitan ya tabbatar musu da cewa tana da ciki. Da jin wannan labari, sai farin ciki ya bayyana a fuskar Ayra, har ta kasa ɓoye murmushinta. Amma a wajen Ayan, abin ya kasance kamar an jefa masa wani babban dutse a zuciya. Hankalinsa ya tashi, domin yana iya fahimtar irin hatsarin da wannan cikin zai iya jefa shi a ciki.

Haka suka bar asibitin suka nufi gidansa. Ayan kuwa jikinsa ya yi sanyi,fuskarsa cike da damuwa, yayin da Ayra ke tafiya kusa da shi cikin farin ciki.Na hango cikar burinta.

A ɓangaren da gidan Ayan yake acikin barikin sojojin , mutane da dama sun san Ayra a matsayin ƙanwarsa. Hakan kuwa ya samo asali ne saboda yadda take sanya kaya na mutunci da kunya duk lokacin da za ta zo gidansa, tare da yadda sukan yi mu'amala a gaban mutane. Hatta wasu daga cikin sojojin da ke aiki tare da Ayan suna kallonta a matsayin ƙanwarsa, ba tare da sun taɓa tunanin akwai wani abu da ke ɓoye tsakaninsu ba.

Da suka shiga gidan, Ayan ya kasa zama. Ya yi ta kai-komo cikin ɗakin na ɗan lokaci, kafin ya tsaya ya dubi Ayra da kallon dake nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki yace.

"Me ya sa kike murna haka da jin an ce kina da ciki?" ya tambaya cikin murya mai ɗauke da damuwa.

Ayra ta ɗaga kai ta kalle shi, murmushin da ke fuskarta bai gushe ba.Tace
"Saboda yanzu na san babu abin da zai raba ni da kai,Tunda ina ɗauke da cikinka, dole ne ka hanzarta aurena kafin asirinmu ya tonu."

Ayan ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci. Maganarta ta ƙara masa tsoron da yake ciki maimakon ta kwantar masa da hankali.Yace

"Kin san abin da kike cewa kuwa, Ayra?" ya tambaya.

"Na sani mana."

"To abnda kike tunani,Ba haka abin yake ba. Idan har mutane suka gano wannan ciki kafin aure,to ina me tabbatar miki da cewa bazaa barni in aurekiba"

Ayra ta yi shiru tana kallonsa.Seda ya gama sannan tace"to ay dama wani satinne bikin ƙanwata kaga bashikenan se a haɗa da nawaba tunda cikin na sati ukune"

Ayan ya ja numfashi mai nauyi sannan ya ce, "ba batun muyi aure bane ayra sabida ko munyi aure be ɗauruba tunda da ciki,kawai Akwai wani abu da nake so ki yi.Wanda nake ganin shine mafita"

"Menene shi abun?"cewar ayra

"Ki amince mu zubar da cikin."cewar ayan

Da jin wannan magana, murmushin da ke fuskar Ayra ya ɓace nan take.Tace

"Me ka ce ayan?"

"Ki zubar da cikin, Ayra. Wannan shi ne mafita mafi sauƙi a yanzu."ya maimaita

 girgiza kai da ƙarfi.Tayi gamida cewa

"A'a.Bazan iyaba"

"Ayra, ki saurare ni."ya faɗi yana ruƙota

"Na ce a'a.Bazan iyaba"

"Ba za ki fahimci halin da muke ciki ba ne ayra. Akwai auren  da yake gabatowa acikin familyna a halin yanzu,familyna suna da girma da daraja akwai mutane da suke kallona da wani irin matsayi na musamman ayra,mahaifina mutumne da ake girmamawa. Idan aka gano wannan cikin yanzu, asirinmu ya tonu.Girma da darajarmune ze zube"cewar ayan araunane

Ayra ta kalli ƙasa, sannan ta ɗaga idanunta cike da hawaye.Tace

"duka nasan wannan sede Ni kuma bana son in mutu."

Ayan ya tsaya cak.Yana kallonta taci gaba da cewa

"Ba zan yi abin da zai sa rayuwata ta shiga hatsari ba. Wannan cikin naka ne, kawai de yana jikina ne. Ni ce zan ɗauki wahalar abin da za a yi min. Ban shirya mutuwa ba saboda kawai kana tsoron kada a gano sirrinmu."

"Ba wai ina son ki mutu ba ne," Ayan ya yi saurin cewa. "Ina son mu nemo mafita ne kafin komai ya lalace."

"To wannan ba mafita ba ce a wajena."cewar ayra

Ya matso kusa da ita.Da sauri yana sake ruƙota

"Ayra, don Allah."

Ta sake girgiza kai.

"A'a, Ayan bafa zan kashe kainaba wallahi."

Ya zauna kusa da ita, ya kama hannunta.Yace muryarsa na rawa

"Ki yi min biyayya a wannan karon. Zan kula da ke, ba zan bar ki ba ayra kuma ko nawa kikeso wallahi zan baki."

"Idan da gaske kake ba za ka bar ni ba, to ka aure ni mana kawai."cewar ayrar

Maganar ta sa Ayan ya yi shiru.Ayra ta ci gaba da magana cikin kuka, "Tun da dadewa nake jiran ranar da za ka ce za ka aure ni. Yanzu ga shi Allah Ya ba mu abin da zai sa ka kasa guduwa daga gare ni, sai ka ce in cire shi.Tabɗijan wallahi bazan cireba"

Ayan ya rasa abin cewa.Ya sake ƙoƙarin lallashinta, yana bayyana mata irin matsalolin da za su iya tasowa idan ciki ya bayyana kafin aure. Ya roƙe ta, ya yi mata alkawarin zai kula da ita, ya kuma yi ƙoƙarin nuna mata cewa abin da yake nema shi ne su kare kansu daga abin kunya.

Amma Ayra ta kasance mai taurin kai a wannan karon,taki yarda da duk wata kalma da zata fito daga bakinsa.

"Ko me za ka ce, ba zan yarda ba," ta faɗa tana hawaye. "Ba zan kashe ɗana ba. Kuma ba zan yarda a yi min wani abu da zai jefa rayuwata cikin haɗari ba in bakason tonon asiri muyi aure mana."

Ayan ya yi shiru.Yana  kallon cikinta, sannan ya ɗaga kai yana kallon fuskar Ayra. A wannan lokacin ya fahimci cewa babu yadda zai iya tilasta mata yin abin da ba ta yarda da shi ba.

Ya yi ta lallashinta na dogon lokaci, amma Ayra ta ƙi amincewa.

Daga ƙarshe Ayan ya sauke ajiyar zuciya, ya jingina bayansa da kujera yace.

"To shikenan," ya faɗa cikin murya mai rauni. "Ki bar cikin tunda dama ajikinki yake."

Ayra ta kalle shi.Tana share hawaye

"Amma ki sani,daga yau komai ze iya canzawa daga yadda kika sanshi."

Ba ta amsa ba.Ta dai share hawayenta a hankali, tana riƙe da cikinta, yayin da Ayan ya nutse cikin tunani mai nauyi.
Auransa ya matso,ga kuma ayra nada ciki,da take ikrarin nashine,kuma yace ta zubar taƙi amincewa,muryartace ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.
"na baka nan da sati ɗaya kazo muyi aure,ko kuma wallahi in je gutin mahaifinka da wannan cikin ya bani inda zan zauna in kula dashi"bata jira amsarsa ba tasa kai tai ficewarta agidan ta koma gida,ranta fess domin tasan lokacin nata auran itama yazo ko ba shiri.

*Tirƙashi!!!.*

*Ya wannan dambarwa zata kasance?*

*Wa ayan yake aura tsakanin ayat da ayra.*

*me ze faru idan ayra ta gane ayat shi zata aura,?*

*Ya ayat zataji asanda ta gane ayan shine yayiwa yayarta ayra ciki?*

*Shin da gaskema cikin na ayan ɗinne?*

*me yasa ayan ya kasanc masanin addini,dake faɗaƙarwa akan shan giya da zina amma kuma shi yake aykatawa?*

*Wainnan dama sauran wasu tambayoyin duka ku tara cikin littafi na biyu domin jin amsoshinsu.*

.