MATAR GIDA PAGE 52
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P52
Washe gari tun safe Ɗalha ya fita ofis dalilin kiran gaggawa da ogansa ya yi masa,a ofis ya yi breakfast,a can wajen Unaisa kuwa tun karfe goma ta shiga kitchen ta fara girki ba ita ta gama ba sai karfe uku na rana,sabbin wormer's ta cire su daga kwali tare da dauraye su kafin ta zuba abincin ciki,sabbin plate da cokalai ta cire daga kwalayen su duk sai da ta dauraye ta goge da wata farar karamar towel mai tsafta kafin ta kai kan daining ta jera su da wormer's,kitchen ta koma tana bin ko ina da kallo ganin yadda kitchen ɗin ya yi kaca kaca,har ga Allah baza iya gyara kitchen ɗin yau ba hakan yasa ta ja kofar kitchen ta rufe daga haka ta wuce ɗaki bayan shigarta ɗaki zama ta yi bakin gado tana mayar da numfashi,ko sallar azahar bata yi ba kallon agogon wayarta ta yi taga karfe uku harda mintina ashirin,kunna datar wayar ta yi tana goge zufa da gefen rigarta,rabonta da wanka tun shekaran jiya,tashi ta yi tare da kunna fanka,tana nan zaune har karfe huɗu da wasu mintina ganin lokaci ya tafe yasa ta yunƙura ta tashi tsaye tare da nufar bathroom,bayan shigarta bathroom alwala ta yi ta fita zura hijab tare da shimfiɗa darduma daga haka ta tayar da sallah,tana cikin sallah ta jiyu muryar Ɗalha ya dawo, bakinsa dauke da sallama ya shiga ɗakin ganin tana sallah yasa ya juya ya fita,Ɗalha bai dade da fita daga ɗakin Unaisa ba, yana zaune cikin parlour ya kwantar da bayansa jikin kujera wayarsa ta yi ƙara alamar shigar kira daukar wayar ya yi ya duba ya ga Muhsin ne ke kira amsa kiran ya yi tare da ƙara wayar a kunne a takaice Muhsin ya ce ''mallam zo ka buɗe mana kofa'' daga haka ya kashe waya yunƙurawa Ɗalha ya yi tare da miƙewa tsaye, ɗakin Unaisa ya nufa lokacin ta idar da sallah idonsa a kanta ya ce ''sun ƙaraso zan je na buɗe masu gate'' gyaɗa masa kai ta yi tare da a ɗaga hannayenta tana addu'a fita Ɗalha ya yi daga ɗakin ya je buɗe masu gate,bayan ta shafe addu'a ta mike tsaye tare da cire hijab ɗin jikinta,Ɗalha ne ya shigo ɗakin a karo na biyu fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''ki fita ku gaisa'' daga haka ya juya ya fita,da ido Unaisa ta bi bayan sa,a hankali ta je gaban madubi tana ƙarewa fuskarta kallo,ta dauki a ƙallah sakan biyar tsaye gaban madubi sosai fuskarta ya nuna alamar rashin wanka maimakon ta shiga bayi ta wanke ko da fuska ne sai kawai ta dauki poda ta shafawa fuskarta wata ƴar karamar kwalbar turaren humra ta dauka ta buɗe ta dangwala turaren kaɗan a yatsar ta kafin ta rufe turare,bayan ta rufe kwalbar turare ta goga yatsarta a tafukan hannayenta,hijab ɗinda ta yi sallah ta dauka ta zura daga hakan ta fita daga ɗakin ta zura fararen kafafunta cikin takalma easy foot wear,bayan fitarta nan parlour ta tsaya ta shiga gaisawa da abokan aiki Ɗalha,mazaje tara cikin harda ogansu,sai mata biyu,bayan sun gama gaisawa ne Unaisa ta wuce kitchen da dauko masu zobo haɗe da kofuna ta ajiye gaban su fuskarta dauki da murmushi,bayan ta ajiye masu ne tana shirin zuba masu a kofi ɗaya daga cikin matan ta ce ta bari kawai zasu sa da kansu waje Unaisa ta samu ta zauna ita ma ta shiga hirar da suke harda ba wani ganewa ta ke ba, kasancewar hirar aiki suke,ganin lokaci ya fara tafiya Ɗalha mayar da dubansa ga Muhsin ya ce ''ba ku ci komai ba,bismillah ga abinci kan daining ko a kawo maku nan" duk suka ce eh amma banda ogansu da hankalinsa na kan wayar da yake,cike da nitsuwa Unaisa ta miƙe tare da nufar daining tana kwaso wormer's da ta zuba abinci ta dawo da su cikin parlour,daga haka ta wuce ɗaki dan bawa baƙin daman cin abinci ɗaya daga cikin matan ne ta yi sarving ɗinsu gaba ɗaya har ogansu,tun da suka fara cin abinci kirjin Ɗalha ke dukan uku uku ya shiga bin kowanne su da ido yana kallon yanayin fuskarsu,babu wata alama a fuskarsu da zai nuna abinci ya yi daɗi ko akasin haka,bayan sun gama cin abinci sun daura da meat pie ɗinda Unaisa ta yi nan ma Ɗalha ya kafe su da ido ya ga dai har sun gama ci babu wanda ya yi complain babu wanda ya yaɓi abincin,har suka gama ci Unaisa na ɗaki,bayan sun gama ci ne mutum uku daga cikin su suka ce.amarya ta yi ƙokari abinci ya yi dadi,karfe shidda daidai suka yiwa Ɗalha da Unaisa sallama,har gate Ɗalha ya raka su,a kan idanunsa suka shiga mota yana ɗaga masu hannu,da wani irin sauri ya koma ciki,da shigar sa ya diɓi abinci kaɗan cikin plate ya zuba miya kafin ya dauki tsoka ɗaya daga cikin pepper meat da ta yi masu ya daura kan shinkafa ba tare da ɓata lokaci ba ya samu waje ya zauna tare da fa cin abincin a hankali ya shiga tauna shinkafar,shinkafar ta yi laushi da yawa kadan ya rage ya zama tuwo,miyar shinkafa babu wani ɗanɗano na musamman ciki daga magi sai gishiri sai dai gishirin bai yi yawa ba haka ma magi,ga mutumin da yake jin yunwa sosai da kuma wanda bai saba cin abinci mai kyau da dadi ba zai yabi girkin Unaisa, amma Ɗalha sam abincin bai yi masa dadi ba kasancewar ba haka Amirah ke girki ba,a hankali ya ajiye cokali ya dauki namar kaza ya kai baki shima dai za a iya ci ba tare da korafi ba matsalar namar ɗaya gishiri ya yawa ciki,Ɗalha ya daure ya haɗeye wanda ya gutsur daga haka ya dauki kofi ya zuba zobo,babu wasu kayan ƙhamshi cikin zobon daga sugar sai sugar Allah ya taimaka bai yi tsami ba,yanzu ya fahimci dalilin da yasa wasu daga cikin abokan aikin sa basu yabi girkin ba,ba kuma su kushi ba,daukar plate ɗin shinka ya yi ya ƙarasa shinkafar bai iya cin namar ba kasancewar baya son gishiri cikin abinci
Karfe takwas daidai Unaisa ta shiga ɗakin Ɗalha ganin sa ta yi zaune kan wata kujera one siter dake ɗakin hannusa riƙe da waya,zuwa yanzu ta yi wanka shanye take cikin wasu riga da wando na bacci cotton kalar blue kanta sanye da baƙin hula,bakinta dauke sallama ta shigo, amsa mata sallamar Ɗalha ya yi yana binta da ido,cike da nitsuwa ta samu waje ta zauna kanta ƙasa ta fara magana kamar ba ita ba shi dai Ɗalha binta kawai yake da ido ''ƙawata Fadeelah ta haihu gobe za a yi suna ina son zuwa sunan in Allah ya kaimu gobe'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya gyara zama tare da ajiye wayarsa kan gado ''me zai hana ki kirata a waya ki gaishi ta in an kwana biyu sai ki tafi,gani nake kamar bai dace ki fara fita yanzu ba'' ya kare magana tare da jan hannunta ya zaunar da ita cinyarsa,taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta ce ''gaskiya ina son zuwa Fadeelah ce fa ba wata ba ko dai baka gane ta bane?" murmushi mai sauti Ɗalha ya yi tare da juyo da fuska Unaisa ya haɗa fuskarta da nasa murya can ƙasa ya ce ''na gane ta Fadeelah da ki ka yiwa ƙawar amarya,kafin ta yi aure islamiyyar ku ɗaya'' ya kare magana yana shafa lips ɗinta da yatsa,gyara zama Unaisa ta yi kan cinyarsa ta ce ''eh ita amma me yasa bazan tafi ba'' hannu Ɗalha ya kai ya riƙe ƙugunta ya haɗe goshinsa da nata ya ce ''saboda ke amarya ce bai dace ki fita sati huɗu bayan auren ki ba'' lokaci guda annurin dake fuskar Unaisa ya yanke ta shiga bin Ɗalha da wani irin kallo can ta tashi tana gyara rigarta,daga haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin,tana daf da fita daga ɗaƙin ta juyu ta kallesa shima ita yake kallo a takaice ta ce ''ba zan iya fasa zuwa ba na faɗa maka'' daga haka ta fita daga ɗakin,bayan fitarta dafe kai Ɗalha yana tunani kan halaiyar Unaisa,can ya dauki waya ya kira layin Amirah,ya dauki kusan awa guda yana waya da Amirah kafin daga bisani suka yi sallama,a can wajen Unaisa kuwa bayan shigarta ɗaki wayarta ta dauko ta kunna data tare da shiga group ɗin matan gida ta tadda messages da yawa nan ta shiga bi ɗaya bayan ɗaya da yawa yawan messages ɗin hira ne kan taron da za a yi gobe murya can ƙasa Unaisa ta ce ''haka kawai za ka hana ni zuwa taro'' har karfe sha ɗaya na dare Unaisa na riƙe da waya tana chating,ba ita ta kwanta ba sai sha biyu,bata dade da kwanciya ba Ɗalha ya shigo ɗakin sanye da jallabiya, tsayawa ya yi bakin kofar yana kallonta cikin duhu kasancewar ta kashe wutar ɗakin,ɗakin ya yi shiru baka jin motsin komai sai ƙarar fanka dake hura iska,ɗakin ya yi wani irin sanyi Unaisa na kwance ta rufa gaba ɗaya jikinta da bargo,a hankali ya karasa shiga ɗakin yana ƙarewa Unaisa kallo rabon shi da ita tun a Kano a halin yanzu a matse yake,drower bed side ya buɗe inda yake da tabbacin ta ajiye magunguna da aka bata a Kano ya buɗe ya ga ta shanye mayar da ledar maganin ya yi cikin drower tare da rufe drower,a matse yake sosai amma tunawa da abubuwan da take masa yasa ya ji gaba ɗaya ba zai iya kusantarta ba,jiki babu kwari ya fita daga ɗakin zuwa nasa bayan shigarsa ɗaki bathroom ya wuce ya sakarwa kansa ruwan sanyi,washe gari Lahadi karfe tara dai dai Ɗalha ne tsaye cikin kitchen yana bin ko ina da kallo bayan Unaisa ta gama yiwa abokan aikin girki bata gyara kitchen ba haka ta bar kitchen kaca kaca ga kwanuka cike cikin sink kasan kitchen baje da kwanuka da robobi,numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya nufi ɗakin Unaisa bakinsa dauke da sallama ya shigo ɗakin bayan shigarsa ya ga Unaisa kwance tana bacci nan ya shiga tashin ta yana kiran sunanta a hankali tare da buga kafarta,a hankali ta buɗe idanuwanta dake cike da bacci tana tashi zaune ''me yasa ba ki gyara kitchen ba bayan kin gama girki?" adunwanta rufe ta ce ''na gaji ne shi yasa, zuwa anjima zan gyara'' gyara tsayuwa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''me yasa ki ke da kazanta ne wai wacce irin mace na aura ne?" ya kare magana yana daura hannuwansa duka biyu a kai,taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta koma ta yi kwanciyarta,Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina biyu tsaye yana ƙare mata kallo can ya ce ''zan fita zan kai mota wajen gyara,bana son na dawo ba ki gyara kitchen ba,ban san dalilin ki na son datti ba na faɗa maki time without number bana son ƙazanta amma kin ƙi ji,kar na dawo ba ki gyara kitchen ɗin ki ba kin dai ji na faɗa maki,and maganar zuwa gida suna babu i da za ki in kin kuskura kin fita wallahi zan mugun saɓa maki zan ba ki mamaki''daga haka ya fita daga ɗakin cike da ɓacin rai,a garejin da ya kai gyaran mota ya siya kunu da ƙosai ya yi breakfast,bayan fitar Ɗalha da wasu ƴan mintina Unaisa ta tashi ta shiga bathroom,bayan shigarta bathroom ribbon da aka daura mata suma tun ranar dauren aurenta ta kwance kafin ta shiga warware sumarta tana rintsa idanu saboda yadda sumar ke mata zafi,ko sau ɗaya bata taje sumar ba tun ranar dauren aure rabon da ta taje suma,ta dauki sama da mintina sha biyar tana wanke suma sai da tabbatar ta wanki da kyau kafin ta yi wanka da brush,sosai ta mayar da hankali ta yi wanka mai kyau sanda ta zo brush ta wanke kowanne lungu da saƙo na bakinta,fita ta yi daga bathroom sanye da bathrope yadda ta daura karamin towel a kai,zama ta yi gaban madubi ta dauki hand drayer daga kayan lefen ta kasancewar unguwar da suke babu wahalar wuta yasa Unaisa ta gyara suma a gida,da hand drayer ta yi amfani ta busar da sumar kafin ta dauki straightener ta straighting suma,hair cream mai kyau ta shafawa sumar daga haka ta dauki body skin care ɗinta ta fara shafawa,bayan ta gama shafa mai hoda kawai ta shafawa fuskarta ta gyara girar ta,wata doguwar riga designer ta dauko ta zura ta yi rolling kanta da gyale kalar rigar,ɓakin simple shoe ta sa ta dauki wani hand bag shima designer bag,dubu talatin da ta siyar da rigar last week ta dauka ta sa cikin jaka daga haka ta fita daga gida,tafiyar mintina talatin ne daga gidan ta zuwa gidan da za a yi taron
*SHUUKRAN