MEERAH

012

by @oumfatima33

*MEERAH*

     *012*

   
    "Eh Yaya, gashi Momy sai kira na take yi a waya kuma ban san me zan faɗa mata ba."

   "Ka koma gida yanzu, ka san yanda zaka yi mata bayani, bari zan kira Sultan yanzu. Ina nan tahowa nima in sha Allah." Yana kammala faɗa ya katse kiran.

   Hajiya Na'imatu (Mamy) wacce shigowarta kenan Palon nata, taci karo da Ajmal ɗin da ke tsaye yana wayar cikin tashin hankali. Kallo ta gama ƙare masa cike da takaici, don ta fahimci inda wayar tasa ta dosa.

   Wuri ta samu ta zauna saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun Couches ɗin da aka ƙawata Palon da su ta harɗe ƙafa cike da ƙasaita ta zuba masa ido. Kallon ta yayi cike da ladabi yace.

   "Mamy ina so zan wuce Kano ne, Meerah ce ba'a gani ba kuma da alama ɗauke ta aka y, don an tsinci, kayanta yashe a ƙasa." Yayi maganar cikin damuwa, amma duk da haka sai da ya kwantar da murya ya tausasa harshe a gare ta.

     Tun da ya buɗe baki ya fara magana take watsa masa wani mugun kallo, sai da ya kammala faɗar abinda zai faɗa ɗin ya yi shiru kansa a ƙasa sannan tace.

   "To ba zaka je ba, babu inda zaka je nace. Wato an kira ka an faɗa maka ba'a ga ƴar gold ba, shine kai kuma jiki na rawa zaka kwasa ka tafi. Saboda kai ne zaka nemo ta idan kaje ɗin, to babu inda zaka je saboda gobe Jawhar zata zo gidan nan. Kuma ka sani sarai saboda kai zata zo." Ta ƙare maganar cikin nuna rashin damuwa da ɓatan yarinyar.

   Ɗagowa ya yi ya kalle ta, zuciyarsa cike da mamakin ƙiyayyar da take nuna wa mutanen da suka riƙe shi tamkar ɗan da suka haifa, suke nuna masa soyayya da gata fiye da nasu yaran da suka haifa a cikinsu. Miye laifin wanda ya nuna yana son naka? Amma sam Mamy ta kasa gane hakan.

  Kwantar da murya ya yi cike da rarrashi yace.

   "Please Mamy ba zan iya zama a nan ba, ban san wane irin hali take ciki ba. She is still young fa Mamy, ba'a san su waye suka ɗauke ta ba, za su iya cutar da ita." Ya ƙare maganar muryarsa ɗauke da tsan-tsar damuwa.

   Cike da takaici ta buɗe baki zata fara masifa Abby ya shigo Palon da sallama, shiru ta yi ta fasa maganar. Sai dai kallon gargaɗi da take jefa ma Ajmal. 

   "Barka da shigowa Abby." Ajmal ya faɗa cike da girmamawa. Amsa masa ya yi da kulawa sannan ya kalli Mamy da ta haɗe rai sosai.

   "Sannu da zuwa Abby." Ta faɗa a hankali fuskarta babu fara'a, don har yanzu ranta a ɓace yake.

  "Me yake faruwa ne?." Abby ya tambaya yana kallon su su biyun. 

  "Abby daman Jawad ne ya kira ni yace min wai ba'a ga Meerah ba, kuma ya tsinci kayanta yashe a hanya may be wasu ne suka ɗauke ta." Ajmal ya faɗa muryarsa ɗauke da tsan-tsar damuwa, don gaba ɗaya idanunsa sun kaɗe sun yi wani irin laushi na tashin hankalin da yake ta ƙoƙarin danne wa. 

    "Subuhanallah! Mamana ce ba'a gani ba, garin ya ya hakan ta faru?." Abby ya faɗa cikin tashin hankali yana miƙewa tsaye, da kallo Mamy take bin su cike da takaicin yanda duk suka bi suka damu kansu. Ita fa in dai abu ya tsallake kanta to ya faɗa kan ko waye ma ba damuwarta bace. 

   Mamy irin mutanen nan ne masu tsananin son kansu da abinda yake nasu iya su kaɗai.

   Wannan halin nata ne yasa bata zumunci da dangin su Abby sosai, musanman mutanen Gwangwazo da take ganin tafi ƙarfinsu. Bata shiga harkar kowa, bata son a shiga tata.

    Ita Bashir da ƴaƴanta kaɗai take so, saboda sune nata, babu abinda ya dame ta da danginsa. Wannan dalilin ne yasa ta zaɓi su zauna a Abuja inda zata fi sake wa ta yi rayuwarta yanda take so, ba tare da wani ya takura mata ba.

   "Bari na kira Abbas ɗin naji meke faruwa." Magar Dady ta ratsa su su biyun.


****** A can Kano kuwa bayan Jawad ya kira Ajmal ya sanar da shi, dole ya koma gidan ya sanar da Momy. Don bashi da wani zaɓin da ya wuce wannan ɗin, lokacin da ya koma ya samu Dady ya dawo, don yana zuwa yaci karo da guard ɗinsa a waje. Yaya Sultan da Aryan ma duk sun dawo suna tsai-tsaye suna jiran ganin ta inda zai shigo tare da Meerah, don Momy ta sanar da su halin da ake ciki.

   Jiki a sanyaye ya murɗa ƙofar Palon ya shiga da sallama, duk idanu suka zuba masa ganin ya shigo shi kaɗai ba tare da Meerah ba.

    Yaya Sultan ne ya fara nufar shi yana cewa.

   "Jawad ina Meerah take ne na gan ka kai kaɗai?." Ya masa tambayar da kowa ke son yi masa a cikinsu, kayan Meerah dake hannunsa ya zubar a ƙasa ya rungume Yaya Sultan kawai ya fashe da kuka. Momy dake tsaye tana bin kayan da ya zubar ɗin da kallo, jiri ne ya ɗebe ta sai da ta dafe kujera tsabar tashin hankalin da ya risketa.

   "Kayi bayani mana Jawad, ina Mamana take?!." Dady ya daka masa tsawa don shima hankalinsa ya yi ƙololuwar tashi, don tun kan ya iso Momy ta kira shi take sanar da shi abinda ke faruwa. Bayanin duk abinda ya faru ya yi musu, ya sanar da su inda ya tsinci kayan nata.

   Hawaye ne masu zafi suka shiga zuba a saman kumatun Momy, cikin sabbatu ta fara magana.

    "Shike nan wasu azzaluman ne suka ɗauke min yarinya Dady, don Allah ni dai kuke ku nemo min yarinyata kar wani abin ya same ta!." Ta faɗa kuka na ƙwace mata.

   "Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same ta in sha Allah." Dady ya faɗa don bata ƙwarin gwuiwa kawai, domin a zahiri shima yana cikin tashin hankalin da ya fi nata. Domin kai tsaye zargin sa kan abokan hamayyarsa na siyasa ne suka ɗauke masa ƴa.

   Idanun Yaya Sultan sun kaɗa sun yi jajir da tashin hankali yake cewa.

   "Me ya sa za'a barta ta fita ita kaɗai ne wai tun farko? Yanzu idan wani abin ya same ta fa?!." Ya faɗa zuciyarsa cike da tsoro. Aryan kuwa kuka kawai ya fashe da shi, don shima duk zafinsa bashi da ƙarfin zuciya a kan ƙanwar tasa.

   Dady kuwa wayoyi yake ta kira yana ɗagawa jami'an tsaro hankali, a kan a nemo masa yarinyarsa duk inda aka kaita cikin daren nan. Suna cikin wannan halin ne kiran Abby ya shigo wayar Dady, yayin da na Ajmal ya shigo wayar Sultan shima.

   Dukkanninsu yanda abin ya faru suke tambaya, da matakin da aka ɗauka. Shaida musu komai suka yi kafin suka yi sallama a kan su Abby ɗin za su biyo flights ɗin da zai tashi da asuba su iso Kano.

   Ammy dake zaune tana bin Uba da ɗan da wani irin kallon takaici, ganin yanda suka fita hayyacinsu tamkar waɗan da aka ce musu Fatima ce aka ɗauke. Da ƙyar ta iya danne abinda ke ci mata zuciya tace.

   "Don Allah ku kwantar da hankalinku mana, ba fa ayi 24 hours da ɓatan nata ba bare ku ɗaga hankalinku haka." Wani irin kallo Abby ya watsa mata, dole ta ɗauke kai tana ɓata rai. Shi dai Ajmal silale wa ya yi ya nufi ɓangarensa.

   Yana zuwa ya sake kiran wayar Sultan da tambayarsa ko an samu wani bayani, babu wani bayani har lokacin. Jami'an tsaro dai tuni sun fara gudanar da bincikensu a cikin unguwar.

   A wannan daren kasa runtsa wa Ajmal ya yi, har asuba zuciyarsa cike da tunanin halin da take ciki. Ana kammala sallar asuba jirginsu ya ɗaga zuwa Kano, in da suka je suka tarar da suma sunyi kwanan tashin hankali, don babu wanda ya iya runtsawa a cikin su....


>>>>>>>>>>>>>>

   A lokacin da ahalin Meerah ke cikin tashin hankalin rashin sanin halin da take ciki, ita kuma tana asibiti tana karɓar kulawar da ta kamata. Bisa jajircewar Nawaz Baffa wanda ya tsaya mata a kan duk abinda ake buƙata.

   Koda ya sayo panties ɗin da Doctor ta buƙata, yana kawo wa bai tsaya ba ya wuce masallaci don yin sallar isha'i da aka kira. Lokacin da ya dawo kuma da niyyar ya tambaye ta lambar wanda za'a kira a gidansu, don su san halin da take ciki sai ya samu an yi mata allurar bacci saboda rikicewar da jikin nata ya yi bayan fitar sa. 

   Ofishin Doctor ya nufa don jin halin da take ciki, samu yayi tana ƙoƙarin tafiya gida don ta tashi a aiki. Ganinsa ya sa ta zauna ta saurare sa.

   "Yaya jikin nata Doctor?." Nawaz ya tambaya cikin sanyin muryar da take halittarsa ce. Cire gilashin dake idanunta tayi sannan ta fuskance sa da kyau tace......

  Manage please.

   *Oum Fatima*
       ***