SULTANIM

Chapter 28

by @msssamher590

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page28

Washe gari da Abba sukayi breakfast kuma tana gamawa taje ta shirya dan jarabawar safe ne, har taso ta makara saboda idan kana tare da Abba badai hira ba, drivern ta ya jima da zuwa tana fita wucewa kawai sukayi.

********

Daya idar da sallar asuba bai koma ba, waya ya amsa mai tsawu da MD na wani company da yakeso yasa hannun jarinsa a kamfaninsu dake Australia, yaci a ƙalla awa ɗaya da rabi a kan wayar, har sai da maganar ta fara hawa masa kai, ya bashi uzirin idan ga samu lokaci zai shigo su ƙarasa komai, a haka sukayi sallama.

Wayar ya ajiye yana lankwasa yatsun hannunsa, ya kalli agogo ƙarfe  bakwai da ashirin da biyar yana da meeting ƙarfe takwas, da sauri ya miƙe ya fara ƙoƙarin shiryawa.


Paper biyu suke dashi, dan haka koda suka fito na farko sha biyu da rabi masallacin dake cikin makarantar suka wuce, anan sukayi sallah sannan kowa ya fita ya siyo abinda zai ci , zuwa ƙarfe biyu suka koma class.

Cire rigan suit ɗin dake jikinsa na sama, ya saƙaleta a hanger dake cikin office ɗin, iska mai zafi ya furzar daga bakinsa, sai da ya isa ga fridge ya ɗau ruwa sannan ya ƙarasa tsakin office ɗin, saman kujerun dake gefe guda na cikin office din ya zauna wanda aka tsara wajan tamkar ba cikin office ɗin yake ba.

Kujerar dake kallonsa Hisham ya zauna, Faruq ya lura da kallon da Hisham ke binsa dashi amma ko a jikinsa ya bude roban ruwan ya fara tuttulawa cikinsa saida ya shaye duka.

Cire takalman dake ƙafansa yayi ya rage sai gajeran socks kawai a ƙafarsa.

“Anya kuwa kasan me dame ka faɗa wajan meetimg ɗinnan kuwa? Kwata kwata hankalinka baya gurin…. Lafiyarka kuwa?”

A hankali ya ɗago gajiyayyun idanunsa ya sauke su cikin na Hisham.

“I know…” ya amsa masa a taƙaice.

“Bana tunanin haka gaskiya..”

Janye idanunsa yayi daga kan Hisham sannan ya lumshesu na ƴan mintuna, kamar zaice wani abu sai ya fasa, ya miƙe a natse zuwa banɗaki dake cikin office ɗin dan yayi alwala.

Madaidaicin banɗaki ne amma ya tsaru sosai, hakan ya bashi damar lashe kuɗaɗe masu yawa, babban madubi ne daga wani side daban, a gaban madubin ya tsaya yana kallon kansa yana kuma murza gemunsa da hannunsa, ta ƙasan zuciyarsa yake tambayar kansa da kansa, me yake shirin faruwa dashi ne haka? Zuciyarsa da gangar jikinsa sun fara neman abu daban wanda a baya ko tunanin hakan babu a ransa, da wannnan tunanin ya samu ya ɗaura alwalarsa ya fito, ya samu Hisham har lokacin yana zaune a inda ya barshi.

“Ka shiga kayi alwalar muyi sallah, lokaci yana ƙurewa.” Miƙewa yayi ya nufi toilet yana murmushi a rasansa yana adduan Allah yasa abun da yake tunani, duk ta miskilancinsa amma shurunsa yayi yawa, haka suke tafe a hanyarsu ta dawowa daga masallaci, shi dai Hisham na biye dashi, gaba ɗaya kamar ba Faruq ba yau din, yana abu kamar bara lafiya.


Sannu a hankali take takawa zuwa gurin motan dake fake a haraban makarantar, a matuƙar gajiye take sosai, dubanta takai zuwa ga agogon dake maƙale a tsintsiyar hannunta, ƙarfe biyar da minti goma, ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin data jingina bayanta da kujerun motan.

Tana shiga ɗaki kayan jikinta ta cire ta shige banɗaki kai tsaye ta watsa ruwa sannan tayi alwala, koda ta fito sallah tayi ta saka kaya ta fito saboda yunwan dake damunta.

Gidan nan bashi da banbanci da nata, ko yaushe shiru indai bada safe bane ko da daddare, kitchen ta wuce tasa abinci anan ciki ta zauna taci, tana gamawa ɗakin Talatu ta wuce amma bata ciki hakan yasa ta wuce chan bayan gidan inda tasan Talatu na zama idan ta gama ayyukanta.

Ta tarar da ita zaune a tabarma tana gyaran ɗanyan zogala, kan tabarmar ta isa itama tasa hannu tana tayata suna hirarsu, ƙarar wayanta ya katse musu hirar Zaina ce da murmushi ta ɗaga.

Hira sukayi mai tsawo da ƴan matan Mami domin yaran Auntie Mama duka suna gidan.

Har bayan isha’i suna tare, a ɗakin Talatu tayi Magrib da isha sun dafa zogalan sun kwaɗata kuma suka cinye abunsu, cikin hikima Talatu ta dinga saƙawa Nadrah hikimomin kula da miji, da abun da ya kamata ace mace tayi wa mijinta.

Da wannan tunanin ta isa ɗakinta ta kwanta, abubuwa da dama suna kai kawo a cikin kwakwalwarta, tasan miji nada haƙƙi mai yawa akan matarsa amma dole sai ta samu dama kuma shi bai bata wannan damar ba, da wannan tunanin tayi bacci ranan.


Tsaye yake gaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa suka chanza launi ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa, rashin natsuwarsa ƙaruwa yakeyi a cikin ko wani minti, indai wannan yanayi ita ake kira sa soyayya to haƙiƙa ko Swafiyya ba santa yakeyi ba, shi kaɗai yasan halin da zuciyarsa take ciki anzo wajan da kuma bazai iya jurewa.

Kashe showern yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa ya fito daga banɗakin, a natse ya zauna a lallausan kujeran dake gefan gado, hannunsa cikin sumar kansa yana yamutsawa a hankali.

Saboda yadda yakejin jikinshi babu dadi sai karfe goma da rabi yayi shirin office, ko ɓangaran Mami be shiga ba ya wuce dan ya  makara sosai.

Ko kaɗan Nadrah bata samu matsalan zama da Umma ba dan bata wani zama a gida kwana biyun nan, idan ta fita tun safe sai  dare take dawowa gaisuwa kawai ke haɗasu, idan taje makaranta ta dawo suna tare da Talatu, lokaci zuwa lokaci kuma suna gaisawa da Mami yayi da su Zahra suka kasance abokan hiranta a WhatsApp, shi kuma ogan har yanxu basuyi maganan dashi ba.

Haka exams ɗinta yaci gaba da tafiya, yau ta kama juma’a kuma saura paper ɗaya ta kammala exams ɗinta wanda zasu rubuta shi ranan monday.……