SULTANIM

Chapter 34

by @msssamher590

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page34


Da sauri ta kammala aikinta ta kuma shirya kanta cikin wani luxury abaya baby blue color wanda yayi matuƙar amsar fatanta, already sunyi da safe zasuje dan haka taje ta samesu a shirye suna gaisawa da Mami suka fitowa driver ya kwashesu.


Tunda suka bar gidan daga Zahra har Zaina waya sukeyi har suka isa, da idanu kawai take binsu tanajin sha’awar abun har cikin ranta, sunane kawai tana da aure amma sun san abubuwa da yawa da ita bata sani ba, har gara yanzu da suke chat da Nafisat ta kuma sata a groups kusan guda uku, wanda tun tana shiga da marmari harta daina saboda maganganun da akeyi a ciki kanta baya iya ɗauka.

Batasan mai Nafisat ɗin ta gani ba amma ko ranan suna magana saida tace mata

“Shi namiji da kike gani babu abu mai sauƙi wajan sarrafawa kamar shi, sau da yawa zakiga dama kawai suke jira ka basu….”


Saloon ɗin yayi mata kyau saboda komai nasu a tsare yake babu hayaniya hakan ne ya ƙara burgeta, sun ɗauki lokaci a wajan saboda yadda ake wanke kan mutun kamar baza’a gama ba.


Saidai suka gabatar da azahar a wajan sannan driver ya dawo ɗaukarsu dan ƙarfe biyu ya wuce, suna shiga sukace masa gudan Anty Mama zai kaisu, Nadrah batace komai ba tunda itama zaman waje ɗayan ya isheta.


Anty mama taji dadin ganinsu karma Nadrah da bata taɓa zuwa, haka taita nan nan da ita, sai dab da magrib suka dawo gida tagaji sosai kamar wanda tayi zirga zirgan a ƙasa, shiya ko sashen Mami bata shiga ba ta wuce ɓangaranta.

A ƙoshe suka dawo dan haka ta shige ɗakinta tayi wanka tayi alwala, ana kira kuma tayi sallah bata tashi kan sallayarba saida ta gabatar da isha.

Bata saka Faruq a idanunta ba tunda ko falon bata fita ba, tana gamawa ta haye gado tayi kwanciyarta.



              Daran ranan lahaɗi duk suna sashen Mami harda Faruq wanda daga sallan isha’i nan ɗin ya taho kai tsaye, bayan sun ɗan taɓa hirarsu ya dubi Mami yace

“Mami zanyi tafiya gobe kuma in sha Allah bazan wuce kwana ɗaya ba indai na samu yadda nakeso”

Shiru Mami tayi naɗan lokaci sannan tace

“Anya Umar, yaushe zaka sama ma kanka hutu ne wai, daga nan sai nan babu wani wadataccen, yanxu fa ba kamar da bane kana da iyali.”

Satar kallon Nadrah yake yaga yanayinta saidai sam taƙi ko kallon inda suke duk da kuwa tanajinsa.

“Mami kwana ɗaya fa nace miki, abin da zanyi bashi da yawa kawai dan ya zama dole ne zuwan”


“Shikenan, Allah ya taimaka, Allah ya ƙara tsarewa.”

Ya amsa da “Amin Mamina”


              Tunda tayi sallar asuba batama koma ba tunda tasan da tafiya, lafiyayyan breakfast ta haɗa masa, hakan ya mata daɗi sosai yadda ta gama ta shirya masa a dinning bai fito ba, kitchen ɗin ta koma dan fara gyarawa.


Daga inda yake zaune yana iya hangota, sanye cikin soft night gown ne a jikinta farare tas kamar ba dasu ta kwana ba, gashinta mai laushi da santsi nannaɗe cikin sleep bonnet, yadda kwantacciyar sumar girarta ya sake ƙawata fuskarta kamar ba daga bacci ta tashi ba, jikinta na fidda ƙamshin turaren baccinta data jima da warewa musamman saboda bacci kamar yadda Nafisat ta koya mata, fararan santala santalan hannunta dukka a waje suke saboda yanayin hannun rigar ɗan ƙatami ne sosai, ƙafarta farin slippers ne mai taushi da aka yiwa adon gashi gashi daga sama.


Da ƙyar Faruq ya haɗiye wani abu mai tauri, tare da ɗauke idanunsa daga kanta.


                   A bakin dining ta sameshi a tsaye da alama ya gama shirinsa tunda har jakarsa na ajiye a ɗaya daga cikin kujerun, riga da wando ne a jikinsa na kamfanin tom ford, sai ƙafarsa dake sanye cikin rufaffen takalmi na fata slip on, batasan yadda kayan maza suke ba amma ita kanta takalmin ya tafi da ita, kayan sun dace dashi sosai kuma sun fitar da ƙirar sa wanda suit da banyan kaya ke boyewa, kana dubansa zaka san yana shiga gym sosai.

Da ita dashi a tare suka ɗauke kansu dukkansu suna ƙoƙarin basarwa, duk sanda ta tashi a bacci sai idanunta su ƙara masa wani irin kyau su kuma firfito wanda hakan yake matuƙar burgeshi.


Ta tako a hankali tana basarwa, sai ƙamshin turarensa daya cika falon yana kaɗa mata hankali

“Good morning” ta faɗa da muryanta da ko da yaushe take tuna masa da mafarkinsa, ko a yanzun ma sai dayaji tsigar jikinsa ta tashi

“Morninnnng” ya amsa yana ɗan jan kalmar, har yayi shiru sai kuma ta tsinci muryansa yana faɗin

“Dawa kike waya ranan?” 
Manyan idanunta ta ɗago ta dubeshi, sai dai kamar bashi ne yayi maganan ba saboda idanunsa na kan agogon da yake ɗaurawa a hannunsa.

“Don’t let me repeat my question”

Sai data kauda kanta gefe cikin muryan kuka tace

“Ya Mahmud ne”
“Who is Mahmud?” Ya faɗa yana goge hannayesa da tissue.

“Ya Mahmud dai….”
Tayi maganar hawayen daya cika idanunta suka fara sauka saman fuskarta.

Dama kawai magana yakeso yayi da ita kuma yaji dawa take wayan, sai ya ɗanji dadi, amma kukan da takeyi ne sam bayajin daɗinsa dan haka ya gyara tsayuwarsa, kanta yana ƙasa tana ƙoƙarin tsaida hawayenta don haka batasan ya iso inda take ba har sai da turarensa ya shaida mata.

Ranƙwafowa yayi dai dai fuskarta, ta kasa jurewa hakan dan haka ta ɗago kanta hakan ya masa yadda yakeso
A mamakance Faruq ya ɗaura bakinsa saman fuskanta kuma yayi amfani da harshensa ya ɗauke hawayen saman fuskanta….

“Da shi zan dinga share hawayanki duk sanda na miki magana kika kuma yimin kuka” taku biyu yayi ya koma baya murmushin gefen baki na suɓuce masa  ya ɗau jakarsa yana faɗin 

“See you soon, take care” daga haka ya fice abinsa yana jin zuciyarsa fes kamar an masa bushara da aljannah.


                Baki buɗe ta bishi da kallo har ya fice, ruwan da jinin dake jikinta saida suka daskare na wucin gadi, shikam ko kunyarta ma bayaji wani irin iskanci ne kuma wannan, tunawa tayi da maganar da Zahra tayi mata

“Mijinki ko? wallahi Anty nadrah Ya Faruq ya iya nuna soyayya, shiɗin na dabanne, saidai yana da wani irin aji da kamewa wanda zaisa ki kasa fahimtar inda ya dosa, amma idan ya kwace ko ya salammmmm, zakice na faɗa miki”
Ajiyar zuciya ta sauke batasan ko kaɗan abun ya tsaya mata a rai dan haka ta tattare kayan ta koma kitchen ta ƙarasa aikinta.


              Ƙarfe uku da rabi a cikin company tayi wa Faruq, tafiyar tayi masa sauri sosai kuma yaji dadinta, hakan yana nufin zai iya juyawa a gobe kenan tunda ya iso kafin su tashi.


Ƙarfe bakwai daidai Faruq ya fito daga cikin company ɗin dare da wani bature a gefenshi, shiya buɗe masa gidan baya ya shiga sannan ya shiga mazaunin driver yaja motar suka nufi hotel ɗin da  Faruq ɗin zai kwana.


Saida yayi ordern abinci a hotel reception ɗin kafin ya amsa key ɗin ɗakin ya wuce, wanka yayi da ruwa mai zafi sosai kafin ya fito yayi sallan magrib da kuma ishan dayaji wayarsa ta kira.


Abincin da aka shigo masa dashi yaci sannan ya shiga banɗaki yayi brush, yana fitowa kiran Zaina na shigowa wayarsa yasan Mami ne dan ita sam bata yarda da saka data ba saidai idan amfanin hakan ya taso


Ya isa lafiya kawai ta tambaya, kuma yace da ita goben dai zai juyo in Allah ya yarda, yaso tambaya ko Nadrah tana ɓangaran amma sai Zaina batayi magana ba Mami na gamawa suka kashe, hakanan ya haƙura ya ajiye wayarsa, yaso kiran Swafiyyah amma sai ya barta da tunanin zaiyi mata bazata.

                Kwanciya ce ta isheshi ga babu bacci a idanunsa, kamar wanda aka tsikara ya tashi ya ɗau lemon kwali mai sanyin gaske ya zuba a cup, ya buɗe tagar a hankali wata sassanyar iska ta dake shi, ya shanye lemon tare da lumshe idanunsa.

Sannu a hankali idanunsa suka fara bin wajan tagar da kallo, kasancewar a tsakoyar city ya sauka ya sanyashi samun wani katafaran hotel dake fuskantar wani babban mashaya (bar).


Yammata da samari ne keta kai kawo ga hasken fitilu daya haske ko ina kai kace rana, ƙarfe sha biyu ne da kusan arba’in amma kamar ba dare ba.

Tsaki yaja yana ƙara kallon haraban bar ɗin, gefe guda ƴan sigari wani gefan kuma ƴan giya ne, hankalinsu kwance suke shagalinsu, domin kuwa har da police officers zaka gani a wajan, wannan kalar rayuwar ba baƙonsa bane a turai amma ya kasa saɓawa da ganin hakan, a ransa ya kanyi hamdala da Allah yayishi musulmi kuma mai addini

“Alhamdulillah” ya faɗa a bayyane.

Har yayi taku biyu da ƙoƙarin barin wajan gizon da idanunsa suka hango yanasa shi komawa baya tare da duban wajan da kyau, ya kasa gasgata abin da yake gani, hannun ya kai ya goge idanunsa kafin ya rintsesu ya kuma budewa

“Swaffiyah……..” ya faɗa cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa…….