Chapter 14
CHAPTER 14
...Kukan ma ya kasa fita sai faman nishi take cikin tsananin azaba. Jug ɗin ya aje a saman bedside tare da duƙawa.
"Me ya shigo da ke cikin dakin nan?"
Leɓe ta cije cike da radadin azaba. " Yar uwata ce me ya sa zaka tambayi dalili saboda na zo wurinta? Kasim ka ji tsoron Allah. Duk abin da kake yi lokaci ya baka idan ya tashi hukunta ka zaka sha mamaki. Ni ban isheka ba har sai ka je ka auro wata?"
Dariya Kasim ya yi bai ce mata uffan ba ya mikar da ita suka fita.
Ita dai Wasila duk ta rikice me ke faruwa haka. Sai kuma ta saki murmushi tunawa da tayi ashe ma ba son matar tasa ya ke ba. Ba shakka ita amarya, ita ce yar gaban goshi.
Shigowar sa ya sakata saurin sakin mayafinta.
Jug din glass din ya dauka masu ɗauke da jus din mango ya miƙa mata.
"Bude mayafinki kisha Jus" Shuru Wasila ta yi tana murmushi ba tare da ta bude ba.
Da kansa ya bude ya zuba mata cikin cup.
"Kada ki CI ko kisha abin da Kasim ya kawo miki"
Maganar matarsa ta dawo mata sabuwa da cikin kunnuwa.
Amsa tayi ba tare da tunanin komai ba ta ɗaya kai ta shanye tass!
Dariya mai ɗan sauti Kasim yayi.
"Jirani kaɗan ina zuwa"
Bai jira me zata ce ba ya fita ya barta tana faman rarraba ido.
Ajiyar zuciya Wasila ta sauke tana ji jikinta ya yi wani iri.
"Sai na shiryawa zama da matar nan. Saboda ga duk alamu lumbu-lumbu ce, ta iya kissa inda ma na samu sauki mijin bata ita yake yi ba." Ta ƙarasa maganar tana leƙa window. Komawa ta yi ta zauna
Tun tana jiran Kasim ya shigo har ta fara jin bacci daga karshe nan ta bingire.
Cikin bacci ta ji alamar tsayuwar mutum a kanta ana kallonta. A rikice ta bude ido.
Kasim ne tsaye a kanta sai kuma wani babban mutum wanda ga dukkan alamu mahaifinsa ne saboda tsananin kamanninsu.
Da sauri ta diro daga saman gadon tana gaishe da shi.
Kallonta ya ke ba tare daya amsa ba.
"Daddy gata nan"
Kasim ta Furta.
Da sauri ta ɗago ta kallesa tana mamakin me ya kawo mahaifin Kasim cikin daren nan?"
Kokarin fita da taga Kasim nayi ne ya sakata mikewa a dan rikice.
"Ina zaka je?"
Ta karasa maganar tana kokarin bin bayansa.
"Ki zauna tare da shi zuwa safiya zan dawo"
"Ban gane ba, mahaifinku fa ne me zai yi a wajen mu cikin daren nan?"
"Kai da ita kuna ɓata mana lokaci"
Mutumin ya fada cikin kakkausar murya.
Kafin tayi wani yunkuri Kasim ya fice ya datse kofar da karfin tsiya. Yunkurawar da zata yi duhu ne ya mamaye idanuwanta sulalewa ta yi ƙasa...
DUTSIN-MA
Maƙera
Tsabar yadda baccinta yayi nauyi sallar asuba ma bata samu ta yi ba. Maganar da taji ana yi mata saman kai ta sakata tashi a rikice tana kallon kofa.
"Sannu amarya. Malam ne ya ce a a sa miki ruwan wanka shi ne na zo in fada miki na kai miki"
Murmushi Nadiya ta kirkiro tana mai washe haƙora.
"To na gode yar uwa. Amma baki fada mini sunanki ba"
"Sunana Suwaiba ni ce matar Malam Bawa ta uku."
Shuru tayi sakamakon kukan daya ci karfinta.
Kallon mamaki Nadiya ke yima suwaiba.
"Kukan na meye ko na fada miki wani abu da bai yi miki dadi ba?"
Hawayen fuskarta ta share. "Aa ba kaina nake yiwa kuka ba ke nake yi nawa. Ina tausayin irin rayuwar da za ki fuskanta saboda na kula kaddararmu iri daya ce"
"Ƙaddara kuma? Wace irin ƙaddara?"
Nadiya ta tambaya cike da zakuwa.
"A yanzu ba za ki gane ba. Saboda abin da yayi mana shi yayi miki, sai a hankali za ki dawo cikin hayyacinki. Amma ki fara zuwa kiyi wanka da alamu ko sallah ba kiyi ba"
"Eh banyi ba bari in Fara zuwa inyi sallah sannan sai In yi wankan"
A tsora ce Suwaiba ta kalleta.
"Gaki dai wayayyiyar yar boko da an kalleki. Kada ki ce mini Baki gane irin wannan da nake nufi ba?"
"Wane wanka kike nufi ban fahimceki ba"
"Wankan tsarki mana"
"Wankan tsarki? To ai naga ba abinda ya shiga tsakaninmu da Malam bare in yi"
Ajiyar zuciya Suwaiba ta sauke. "Hatsabibancinsa ya kai ba zaki taba sanin abinda ya faru a tsakaninku ba. Kamar dai yadda yanzu kike jaddada mini, Amma kuma a zahiri komai ya faru ba zaki gane yana kusantarki ba sai kin ga bullowar ciki a gareki. Ki rufamin asiri ki je kiyi wankan nan kafin Malam ya fito ya iske mu a tare"
Jiki a sanyaye Nadiya ta shiga ruɓaɓɓen toilet ta yi wanka sallah tayi ta kara kwanciya tana ji kamar zazzaɓi ya zubo mata.
Suwaiba ce sake shigowa dauke da zazahen tuwon dawa miyar kubewa tasha man shanu sai kamshi take.
"Ki tashi ki ci abinci don naga da dukkan alamu kema kin hau layinmu"
Da sauri Nadiya ta tashi zaune lullube da hijabin jikinta.
"Wane layi kenan?"
"Ciki mana"
Zaro ido Nadiya ta yi a rikice.
"Na shiga uku. Wallahi a kaf tarihin rayuwata ban taba yin iskanci ba wallahi ba da shi na zo ba"
Murmushi Suwaiba tayi tana dafa kafadar Nadiya.
"Ba da shi kika zo ba. Alamomin samuwarsa ne a jiya. Kuma duk haka yayi mana In kika haihu ɗan bazai rayu ba a gaban Malam za ki haihu jikina na bani shi ke yin wani aikin tsubbu da abinda ka haifa"
Murmushi Nadiya tayi saboda kaf gaskiyar da Suwaiba ke fada mata a kan Malam, ji take kamar tana yi mata tatsuniya. Fahimtar halin da Nadiya take ciki Suwaiba tayi. Wasu sabbin hawayen tausayin Nadiya ne suka dubi mata.
"Ubangiji ya kubutar da ke kinji. Bani fata ki ƙare rayuwarki a cikin gidan nan kamar yadda tawa rayuwar ta zo ƙarshe.
Ita ta taimaka mata ta ci abinci kokon kadai ya iya shiga cikinta ta koma ta kwanta. Baccin wahala ne yayi awon gaba da ita. Kwanciya Suwaiba ta gyara mata ta ja mata kofar.
Almajiran Malan ne suka cika gidan da ruwa sauran yaran gida kuwa sai wasansu suke yi. Masu hankali kuwa kowace taba kofar dakin su. Burinsu daya su ga fitar mahaifinsu zuwa wani aiki da zai yiwa wani dan siyasa su fada dakin Amarya.
Gyaran Muryar da yayi ne ya saka kowace fitowa ta zube tana kwasar gaisuwa.
Rarraba ido ya ke ko zai hango Nadiya amma shuru.
"Ke Suwaiba!"
"Na'am Malam gani"
Ta karasa maganar cikin ladabi kanta a ƙasa.
"Kije ki fitomin da ita saboda in gabatar da ita kamar yadda na gabatar da ku a lokacin da kuke baki."
"To malam an gama"
Da gudu-gudu ta shiga dakin Nadiya dake sharar baccin wahala.
"Nadiya! Nadiya!!"
Ta shiga kiran sunanta.
Da kyar ta iya bude idanuwanta
"Ki zo Malam na kira, ko baki iyawa ki daure"
Jin an ambaci Malam zabura tayi ta mike ta riga Suwaiba fitowa ta zube gaban Malam.
Bayan sun gaisa ya fara bayani kamar haka;
"Ke baƙuwar zuwa ce don haka ke ce baki san dokoki da ƙa'idojina ba. Kamar yadda kika gani wadan dan mata na ne. Kande uwar gida ita ce mata ta ta fari sai mai bi mata Jummai sai ta uku Suwaiba. A yau zaki fito ki ci gaba da aiki domin ke ce da aiki sai kinyi kwana biyu kina aiki. Wadda ta ga zata iya ita ce zata tayaki. Yaranta su ashirin da tara ne, na aurar da goma sha ɗaya saura goma sha takwas. A cikin goma sha takwas ina da kwara daya da nake masifar kauna mai sunan mahaifiyarta wato iyalle. Ta kasance tana fama da tabin ƙwaƙwalwa sakamakon abubuwan da muke aiki da su sun ɗan taba ta. A kaf duniya baki da wanda nake kauna kamar Iyalle. Ko kasheki ta ce zata yi bance kiyi mata musu ba ko gardama"
Da sauri ta amsawa da "to Malam an gama. Yadda ka ce haka za a yi"
"sannan haihuwa duk shekara ne. Hatta uwar gidana bata jima da gama haihuwa ba sakamakon manyan ta da tayi"
"To malam Allah ya bamu masu albarka"
Da Amin suka amsa haka ya fice shi da almajiransa.
Uban garin dawa suka miko mata zai yi tiya biyar.
Tana kallonsa wata sabuwar masassara ta zubo mata.
Suwaiba ce ta matso ta riketa ganin tana niyyar faduwa.
"Ko ki koma ɗaki Ni sai inyi miki?"
"Ba shakka uwar iya wadda tafi iya iyawa. Kin manta halin malam ne ko kuma son iyawa ne ya rufe miki ido?"
Kande ta karasa maganar tana mai riƙe ƙugu.
"Bari ba shegiyar ba ce uba ke gareta. Ai da barinta kika yi ta amsar mata girki idan Malam ya dawo mu yan kallo ne"
Cewar Jummai.
"Na yarda baku da imani. Kuna ganin halin da yarinyar nan take ciki amma kuke so a barta ta yi wannan uban aikin ita ɗaya?"
Rufe bakin Suwaiba sai gani suka yi Nadiya ta yanke jiki ta zube masu a wurin...