TSAURI COMPLETE
Introduction
TSAURI COMPLETE
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
GABATARWA.....
Bismillahir Rahmanir Rahim '
Wannan littafin na TSAURI qir qirarren labari ne kuma banyishi da niyyar cin zarafin wani a raye ko a mace ba ,
Idan kaci karo da wani abu da yake kama da rayuwar ka to arashi ne kuma ina me bada haquri ba nayine da niyyar 'batanci ko walaqanci ba .
GAR GA'DI
Wannan littafin na TSAURI mallaki nane kuma ban yarda wani ko wata yayi amfani da shi ta wata hanya ko ya juyashi zuwa video ba tare da izini na ba ,
Idan Kuma kayi amfani da shi ba tare da izini na ba to tabbas zaka fiskanci fushi na a dokance....
Yadda muka fara littafin nan lafiya ina roqon Allah yasa mu gamashi lafiya ..
Family ne masu matiqar ban sha, awa" gabaki da'yansu a zaune suke a dining, d'in da yakecikin wani qaton parlor wanda yasha kyau har ya gaji,
fentin parlorn fari ne me ratsin gold, sai wasu manyan kujeru Golding color" da wani carpet, shima fari me ratsin gold '
sai wasu manya manyan zanen floor's light blue da fari.
Su biyar ne xaune a dining d'in, wani babban mutum ne, fari tass, sanye da, wata babbar riga fara tasha aiki "
kansa sanye da wata hula, se wani siririn glass dake sanye a fuskarsa,
duk da kasancewar ya manyanta amma hakan be hana kyansa bayyana ba, ko ba a fad'amaka ba da kanka zaka yanke cewar shine mamallakin wannan gidan,
Alhj Ma aruf, bommoli,
Wanda naji dattijuwar matar da ke kusa da shi tana kira da major, ko ba a fad'a ba da alama itace matar gidan wato, hajiya ni ima, matar Alhj, Ma aruf bommoli.
Se wani saurayi dogo wanda suke kira da suna Zarban,
gefensa wata matashiya ce da bazata wuce shekaru 14 a duniya ba, Wanda fuskarta take yanayi da na Zarban, kallo d'aya zakayimusu kasan cewar jini d'aya ne su,,
bayansu sai wata " matashiyar wacce zasu iyayin sa annin da Nusaiba, wato qanwar Zarban, amma ita wannan yarinyar kallo d'aya zakayimata kafahimci ita ba d'aya bace dagacikin yarangidan,
Farace tass mul mulalliyar fuskarta na d'auke da, dara daran idanuwa farare tass" sai d'an qaramin baki da wani sihirtaccen dogon hanci,
Duk da cewar a zaune take, kanaganinta zakasan ba doguwa bace kuma kai tsaye baza a kirata gajera ba"
jikinta 'bul 'bul yake ko ina a ciccike duk da batada wani jiki sosai,
Doguwar rigar atamfane a jikinta milk me d'auke da manyan floor's brown color, rigar ta kar'beta sosai, sai dai kallon guda zakayimata kafahimci daga qauye ta fito.
Tayi wata kwalliya tamkar wata yar bori sai iyayi take wai ita a dole tayi kyau "
Zarban da Nusaiba ,ne suketa tsokanar ta suna dariya, itakuwa se mita takeyi tana kaiwa ammi qararsu,
Gabaki da'yansu break fast sukeyi tamkar ba a halicci damuwa a duniya ba,
dukkansu kallo d'aya zakayimusu kasan tabbas suna cikin matiqar farin ciki idan ka cire mutum d'aya, wanda fuskarsa take murtuke tamkar an aikomai da saqon mutuwa,
lokaci zuwa lokaci yana aikowa wannan yarinyar da naji Nusaiba ,na kira da suna Mahanur, da saqon harara kamar idanunsa xasu fad'o qasa,,
da alamar shine babban d'a a gidan,
Duk da bashida haske sosai amma yanada matiqar kyau sosai,
Gashin kansa yayi luf akansa kamar hula, kallo d'aya zakayimasa base ka qaraba zaka fahimci shi mutum ne me aji ga wani kwar jini da Allah yayimasa.
Gabaki da'yansu sun lura da irin hararar da yake aikamata amma babu wanda yabi takansa kasancewar inhar da sabo to yaci ace duk sun saba da hakan,
Dan kowa ya sani tunda yarinyar tazo gidan jininsu be had'u ba " indai har kaga wani abu yashiga tsakaninsu to baya wuce duka ko zagi da fad'a"
Kusan kullum sai ya sakata kuka sai dai in basu had'u ba...,.
duk gidan suna sonta saboda tanada shirme da quruciya sosai idan ka zauna da ita zakayita shan dariya har saika gaji,
Bayan sun kammala break fast d'in major ya miqe yana duba agogon hannunsa, yana fad'in yau kam na makara,
Bazan samu kai twins d'ina school ba, saboda haka, Rafiq ka wuce da su idan zaka tafi aiki ka ajiyesu a makarantar idan sun shirya .
Ya qarasa maganar yana kallon matashin tare da nunasa da hannu,
Wani sauti qirjin Mahanur ya bada , da qarfi ji kakeyi dumm....... dumm.....
jitayi kamar an bugamata guduma a qirji,
Kallon yaya Rafiq tayi da gefen Ido wanda taga ya sake had'e rai ya tsuke fuska ko kad'an babu alamar wasa a tattare da shi,.
Ta d'anyi nare nare da fuska cikin rawar murya tace,
Am Abba dan Allah kar kabari yaya Rafiq ya kaimu, ka kaimu da kanka kokuma kacewa yaya Zarban ya kaimu "
Jin yadda tayi maganar a tsorace sai da tabawa kowa dariya,
Abba yayi dariya sannan yace a'a mama na ai baza ayi haka ba Zarban tare da shi zamu tafi ze miqamin wani saqo ' saboda haka dole kuyi haquri yau yaya Rafiq ne zeci ladarku.
Gabaki da'ya sukayi dariya sannan suka miqe Zarban ya amshi jakar da ke hannun mahaifinnasu sannan suka sakai suka fice.
Ammi ma d'akinta ta nufa tana dariya,
Mahanur kam takasa cewa komai sai tunani kawai take a cikin ranta'
Ita daikam tasan yau ta shiga uku,
Wai yaya Rafiq ne ze kaisu makaranta"
mutumin da ko da wasa batason abunda zai had'asu zama guri d'aya,
Muryar Nusaiba ,ne ya katsemata tunaninta, mahanur kitashi ki shirya mun makara fa,
Miqewa tayi jiki a salu'be kamar kaxar da qoyi yafashewa a ciki,
Bayan sun gama shiryawa suka fito farfajiyar harabar gidan, yaya Rafiq na tsaye a jikin motarsa yana jiransu yagama qulewa, zuciyarsa taje har wuya,,
besan meyasa abban nasa yakeson sakashi a lamuran wannan bagidajiyar yarinya me renin tsiyanba,
har zuciyarsa baya qaunar ganinta balle har wani abu ya shiga tsakaninsu,
Turus ta ja ta tsaya ganin yadda yake harararta a kufule, cikinta yayi wani irin hautsinawa, na shiga uku...,.
Nusaiba ,wallahi nafasa zuwa makarantarnan indai wannan azzalumin yayannakinne ze kaimu,
dariya Nusaiba ,tayi tace kede da taku batazo d'aya ba, amma wallahi yaya Rafiq yanada kir ki sosai, kema rashin kunyarkine yake had'asa da ke kinsan shi bayason raini"
*Kixo mu qarasa *
Ya kaimu nikam kinga yanzuma mun makara ga home work d'inmu kinsa yau shine first period Kuma yace da wuri ze kar'ba,
ta qarasa maganar tana jan hannunta , cikin sauri ta fizge tana zare idanu haka sukaci gaba da musu akan itadai bazatajeba,
Qara ta sake tare da saurin wai wayawa saboda wani rankwashin da taji an sauqemata a tsakiyar kanta,
nantake hawaye suka shiga kai komo a idanunta' bata ankaraba sai ji tayi ya riqe kunnenta yanaja da qarfi.
nan da nan hawayenta suka qaru, takai hannunta ta riqe hannun da ya riqe kunnen nata , cikin kuka tana fad'in,
dan Allah yaya Rafiq kayi haquri kasakeni wallahi akwai zafi sosai.
Yad'an quramata ido ba tare da ya sassauta riqon da yayimata ba, yad'an sunkuyo kusa da fuskarta sannan yace ke ni sa an wasankine?
Yayi tambayar cikin tsawa tayi saurin gir gixamasa kai jikinta na rawa saboda tana matiqar tsoron tsawa sosai,
wata tsawar ya sake dakamata wacce tasa hantar cikinta kad'awa, ba magana nakeyimikiba ko bakida bakin da zakibani amsa ne ?
A'a a'a,
Ta fad'a cikin rikicewa da rashin sanin abunda ya kamata tayi,
Kunnenta ya qara ja har se da ta saki wata qara sannan yace duk randa aka sake cewa na kaiku makaranta kika tsaya kina 'batamin lokaci sena 'ballaki,
shegiya nunar rana kawai, yana gama fad'ar haka ya bud'e qofar motar ya shiga " fuskarsa a d'aure, suma suka shiga har suka isa makarantar kanta yana qasa tana kuka.
Ko da suka shiga cikin makarantar, Mahanur bata wani sakeba tunani kawai take akan yadda, Rafiq yake yawan kyararta,
ta rasa lefinta a gareshi da baya qaunar ta.
Akwana a tashi asarar me rai, yau twins d'in Abba, wato Nusaiba da Mahanur, suke bikin kammala senior secondary school,
Murna da d'oki kam ba a cewa komai musamman ma ga mahanur dayake dama bawani son karatun takeba kawai tanayine saboda takurawar Abba,
farin cikin ta d'aya shine abba yace " babu yarinyar da zata cigaba da karatu a gidansa, se de in tayi aure idan mijinta yanada ra ayin karatun se taje taci gaba a gidansa.
Bayan sun halarci taron gama makarantar da yamma, suka fara shirin tafiya wajen, partyn da Abba ya had'amusu, saboda farin cikin twins d'insa sun girma, kumasun samu sakamako me kyau, musamman Nusaiba, da tafi mayar da hankali akan karatun"
Su duka biyun suka shirya cikin, wani rantsattsen, leshi light blue,
se farin mayafi, takalma plat, suka saka shima fari ne, se wata yar qaramar jaka silver color, me kyau taji adon duwatsu qanana se kyalli take.
Sunyi kyau sosai kamar ka sacesu, musamman mahanur, wacce budurcinta ya qara bayyana, ta qara fari da kyau kai kace ba, renon qasar bace,
Ta tifke baqin gashin kanda me cika da tsayi sosai, gashi da duhu, da santsi ga laushi, wanda yazo har goshinta .
Parlor, suka fito se wani siririn qamshi sukeyi, kamar wasu amare, duk da Nusaiba tasan tayi kyau sosai se da ta rena kanta data kalli Mahanur '
Masha Allah, kawai ta furta tare da qara ware ido tana kallon Mahanur.
Suna fitowa parlon, idon kowa ya dawo kansu masha Allah Zarban ya furta tare da miqewa tsaye yana tsokanarsu,
Twins d'in Abba yau an girma se aure kenan, dariya sukayi dukkansu, Mahanur ta d'an zaromasa dara daran idanunta tana dariya, tace ,,
kai kai...
yaya Zarban ai mukam ba yanzuba tukunna ka manta gakunan ko haka kukeso mu tafi mu barwa Abba ku, wallahi munqi wayon semun fara aurar da ku tukunna saboda karma inzo ace bazan kwana ba a aurenku dan wallahi se munyi sati muna biki,
Gabaki da'ya sukayi dariya ammi tace, kede ba a rabaki da shiririta yanzu saboda auren Zarban ne zaki qiyin, aure salon ace mama ta tayi kwantai,
Ai wataqila auren Zarban kam se de kizo da yaranki biyu ko uku,
yara Kuma nid'in, mahanur ta fad'a tare da d'an zaro ido,
ta d'aura da cewa tab wallahi ammi gani nakeyi kamar qarya ake fad'a bazamu aihuba, haka sukaci gaba da hira suna raha.
Abba ne ya shigo tare da Rafiq, yace iyayen makara yau har an shirya kenan saboda d'oki?
gabaki da'ya suka gaisheshi kafin yace, wa ammi ki d'auki Nusaiba, ku tafi tare ni zan d'auki Zarban,
idan yaso se Rafiq ya wuce da mama na,
Saurin tsuke fuska Mahanur tayi a cikin zuciyarta tana fad'in shikenan na shiga uku Abba yau kam ka kasheni.
Taso tayi musu amma tariga tasan halin Abbansu'
tunda har ya fad'a baze canzaba, Rafiq ya harareta sannan ya mayar da dubansa ga Abba yace,
Abba ina ganin idan babu damuwa kufara wucewa tukun idan yaso mu zamu biyoku daga baya yanzu zan qarasa shiryawa,
Abba yace to ba matsala amma kuyi sauri kasan banson 'bata lokaci '
insha Allah Abba"
ya fad'a kansa na qasa, tana gani su Abba suka fice suka barta daga ita se shi a gidan,
Be ko dubi inda takeba yayi shigewarsa d'akinsa mahanur tun tana jiransa a zatonta yatafi shiyawane kamar yadda ya fad'a har ta gaji da jira, ta miqe cikin qarfin Hali " ta nufi dakinsa qirjinta na dukan uku uku .
Qofar ta shiga kwan kwasawa a hankali, qasa qasa ya bada umarni shigo,,
A hankali ta tura qofar d'akin amma ga mamakinta a kwance ta gansa akan gadonsa yana lallatsa wayarsa,
wani malolon takaici ne ya taso ya tokare qirjinta amma wannan ya renamin hankali '
ta fad'a a cikin ranta .......
kar karwa jikinta ya fara saboda tsawar da ya daka mata lafiya kikazo kikayimin tsaye kina kallona kamar wata sabuwar mayya??
Am,, amm,
Dama nazone na duba ko ka shirya mu tafi inda Abba yace ka kaini.
D'an yatsina fuska yayi ba tare da amsamataba yace cikin isa,
Maza kishiga kitchen ki d'an dafamin abunda zanci, yunwa nakeji Kuma naga su Nusaiba sunriga sun fita '
Wasu hawayen baqin ciki ne suka gangaro suka wankemata fuska, cikin d'acin rai tace amma fa yaya Abba ne yace,
Abba ne yace me??
Ya fad'a cikin tsawar da tasakatayin baya a hanzace, tare dajan bakinta ta tsuke, zuciyarta tashiga bugawa da qarfi kamar zata 'balle qirjinta ta fito "
Kukanta ya qara tsananta tanajin kamar ace tak ta kasa a guje,
tsuke fuska yasakeyi sannan yace inajin yunwa nace kidafamin abunda zanci.
da sauri ta fice jikinta na rawa har tana had'a hanya, ta nufi kitchen d'in, durqushewa tayi tacigaba da rera kukanta,
Se da tayi me isarta sannan ta share hawayenta ta miqe ta d'aura indomie, har ta gama tana sharar hawaye, tanajin wani irin tsanar Rafiq a cikin ranta, ji takeyi kamar ta nemo shinkafar 'bera ta sakamasa a cikin indomie d'in ya mutu kowa ya huta,
Haka ta gama ta d'auko plate ta juye a ciki, ta d'auko tana tura d'an qaramin bakinta ta nufo d'akinsa, xuciyarta tab da tsanarsa dajin haushinsa,
A hankali ta tura qofar, siririn qamshin turarensa ya daki hancinta, yayi wani irin had'ewa cikin wani rantsattsen yadi
brown color,
ya d'aura wata hula baqa a saman kansa wacce bata qarasa rufe lallausan gashin kansa ba, sajensa me laushi ya qara shumfud'owa a gefen fuskarsa,,
ya d'auko wani d'an siririn farin glass ya yasaka, yayi wani irin kyau kuma kwar jininsa ya qara fitowa sosai '
Duk da tana matiqar jin haushinsa amma yayimata kyau sosai.
Sallama tayi, a "hankali ya d'ago narkakkun idanunsa wad'anda a ko da yaushe suke kama da na mejin bacci,
Shigo, kawai ya furta tare da juyawa ya d'auko wani agogo me kyau yana sanyawa a hannunsa '
sunkuyawa tayi ta ajiyemasa plate d'in indomie d'in cikin rawar murya tace, gashi yaya, dan har yanzu sharar qwalla take,
kawar da kai ya d'anyi kamar bazece komai ba se kuma yad'an 'bata fuska ' cikin had'ewar rai yace
menene wannan kuma??
Saurin d'agowa tayi ta kallesa ganin yadda yasha mur, babu alamar wasa a fuskarsa yasata had'iye abunda tayi niyyar fad'a,
Indomie ce ta basa amsa a taqaice ranta nayimata wani irin quna.
taku biyu ya qara ya xauna a bakin gadon tare da sake had'e rai tamkar be ta'bayin dariya ba,
Da sauri ta juya zata fice daga d'akin ina zakije ?
ya fad'a a daqile, zanje na jiraka a parlor ne ta fad'a tana cigaba da tafiya,
to ban bada izini ba .
ya fad'a, sannan yakai hannu ya d'auki wayarsa da taketa faman ruri, sallama yayi cikin ladabi, bayan wasu yan secondni ya fara magana"
gamunan abba tun d'azu muka fito motarce tad'an samu matsala a hanya shine muka tsaya muka nemi wajen gyara amma insha Allah zamu qaraso nan bada jimawa ba "
Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi suka had'a Ido ya kashe mata Ido d'aya yana wani mur mushin zaki gane kurenki '
Da sauri ta kawar da kanta cikin ranta tace maqaryaci ko kunya bayaji ya saki baki yanata zubawa mahaifinsa qarya Kuma wai a gabana ko yaushene motar tasa ta 'baci oho.
shiru yad'an qarayi da alamar yana sauraron abunda ake fad'a ne se kuma yace,,
a'a Abba base tahau abun hawaba ankusa kammala gyaran insha Allah yanzu zamu qaraso yamma tayi kuma kaga ita macece,
"Okay "
to shikenan Abba se mun qaraso ya fad'a tare da ajiye wayar yana murmushin gefen baki,
Plate d'in ya janyo ya saka cokali ya d'ebo kamar zekai baki se kuma ya mayar ya ajiye ya d'ago ya watsamata wata harara da tasa gabanta fad'uwa,
Magani zaki banine?
Yayi maganar a kausashe, cikin hanzari ta kad'amasa kai alamar a'a,
to menene kika tsaya a kaina sekace wadda zatabani magani?
Kode kinaso na kware ne duk kinbi kin wani tsareni da ido.
sunkuyar da kanta tayi idanunta' suka ciko da hawaye amma batacemasa komai ba, se hannunta da ta saka tana share siraran hawayen da suke gan garowa a fuskarta,
alama yayimata na ta zauna ba tare da ya qara cewa komai ba "
can gefe ta samu ta zauna ta sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta '
Gabaki da'ya jinta takeyi a matiqar takure amma to yazatayi dole de tayi haquri ta jira har se sanda yagama isa da mallakarsa ya kaita,
yanakai loman farko yayi saurin furzarwa tare da jan wani dogon tsaki yana fad'in ko indomie d'in baki iya dafawaba a hakan wai ake maganar za a aurar da ku nan kusa"
Zanga wani d'an wahalanne ze d'aukeki a matsayin mata, dan wallahi seya gommaci ya kiwata kare da kud'insa akan ya auri macen da ko girki bata iya ba,
Maganganun sunyimata zafi sosai ji tayi kamar an zubamata narkakken dalma a zuciyarta,
wani abu me d'aci ya taso ya tokare maqogoronta, tasan kawai yaso zagintane amma tasan batada ganda akan girki hakanne yasa bata d'auki wani lokaci me yawa wajen koyan girki ba'
kowa yanason girkinta saboda kwarewarta a wajen iya girki, amma wai yau ita ake fad'awa irin wad'annan maganganun akan girki,
Wasu sabin hawaye masu ciwo suka sulalo akan kuncinta, ta d'ago fararen idanunta wad'anda suka rine i zuwa launin ja saboda kuka ta kallesa tasake sunkuyar da kai, wani abu yana yawo a cikin ranta "
Hannu ya miqa ya d'auko key d'in motarsa ya fice ba tare da furtamata uffan ba ,
miqewa tayi ta bisa a baya tanajin zuciyarta tamkar zata 'balle qirjinta ta fito'
Babu wanda ya qara cewa komai har suka isa jikin motar ya bud'e ya shiga, ta kai hannu zata bud'e qofar baya,
tsawa ya dakamata ke, ni driver d'in kine?
Saurin dakatawa tayi jikinta na wani irin kerma, yasa hannu ya bud'e mata qofar kujeranr me zaman banza'
shiga tayi tana 'bata fuska tare da turo baki, ta zauna ta janyo qofar ta rufe, wani irin kallo ya bita da shi wanda yasa lakar jikinta mutuwa,
Ke a haka zaki bini ?
Yayi tambayar yana wani mazewa,
me Kuma nayi ta tambaya cikin rawar murya"
ki wuce kije ki gyara fuskarki, wato zaki bini a haka salon Abba yace ina cutar da ke kinyi kuka fuska tayi kojai kojai neman ki jazamin bala i a wajen mahaifina koh,
toh wallahi baki isaba ki wuce nabaki five minutes kikoma ciki ki gyara fuskarki kifito mu tafi, idan kika kus kura kikabari su Abba sukagane kinyi kuka har sukayimin fad'a wallahi ni da kene se na 'ballaki a cikin gidannan kinsan halina Kuma kinsan bana maganar wasa,
Jin kukan da taketa qoqarin dannewa yana qoqarin su'bucemata ne yasata saurin fita daga motar da gudu '
'bangarensu ta qaraso, a guje ta shiga toilet, tayi kuka me isarta sannan ta wanke fuskarta, ta sabunta kwalliyar sannan tafito suka wuce,
Ga mamakinta harabar wani restaurant taga yashiga yayi parking,
be cemata komai ba kamar yadda itama batacemasa ba, bata kuma fito daga cikin motar ba,
ciki ya shige ba tare da yabi ta kanta ba, se da ya d'an 'bata lokaci sosai sannan yafito yaja motar suka d'au hanya"
Suna isa harabar Hall d'in ta yunqura da sauri zata fice daga motar ,
hannu yasa ya fizgota da qarfi , sosai ya matso daf da ita har numfashinsu na gaurayuwa da na juna,
Wani irin kerma jikinta ya farayi, se da yad'an kafeta da ido na d'an lokaci kafin yace,,
Kinde tina abunda na fad'amiki, idan kika kus kura su Abba sukaga canji a tare da ke kuma suka d'auramin har sukayimin fad'a to wallahi na lahira se ya fiki jin dad'i,
Yana gama fad'ar haka ya saketa a guje ta fice daga cikin motar, babu alamar hawaye a fuskarta amma zuciyar ta tanayimata wani irin suya me rad'ad'in gaske.
Da gudu tashiga cikin Hall d'in, hankalin kowa ya koma kanta '
bata wani jima da zuwaba aka yanka cake sannan aka watse da addu a ita da Nusaiba, sukayiwa baqinsu godiya da fatan kowa ya koma lafiya,
Bayan sun dawo gida wanka kawae tayi ta cire kayan jikita tasaka na bacci tabi lafiyar gado dayake dama ba sallah takeyiba "
se da takusa raba dare tana tunanin irin abunda Rafiq yayi mata ,
Washe gari da safe tana tashi ta shiga toilet tayi brush ta wanke fuskarta sannan ta fito ko kayan jikinta bata canza ba"
haka ta fito ko d'an kwali babu a kanta yalwataccen gashin kanta gaba d'aya ya cukur kud'e ta sauqo, dining ta wuce kai tsaye domin tasan acan zata samu kowa ,
tana isowa tad'an rungumi ammi ta baya tana gaisheta sannan ta gaida Abba ta zauna tana gaida Zarban cikin zolaya "
Wani lafiyayye rankwashi ya sauqemata a tsakiyar kanta had'i da dakamata tsawa,
Ke baki iya gaisuwa bane?
Cikin hawaye tace yaya Rafiq ina kwana, sake tsuke fuska yayi kamar be ta'ba dariya ba,
tashi kije kicanza kayannan kuma kinemi d'ankwali ki rufe wannan kannaki, ya fad'a ba tare da ya amsa gaisuwar ba,
Zum'buro baki tayi ta miqe tafara tafiya tana qun quni qasa qasa "
Se da taqarasa 'bangarensu ya rufamata baya , tsayawa tayi a tsakiyar d'akin tana magana a fili,
Aikin banza kawai mutum imbanda shegen takura babu abunda ya iya mugu kawai,,
kullum seya nemi hanyar da ze daki mutum, saboda mugunta, Kuma ina dai dai dashi wallahi duk abunda yakeyimin sena rama ,
dole ma na kawowa Abba wanda nakeso idan nayi aure senaga a ina ze ganni har yaci zalina zanganine idan zece ze bini gidan mijina yace ze,
Bata qarasaba taji ya fizgota da qarfi ya juyo da ita sosai suka fiskanci juna, wani rass qirjinta ya bada da qarfin tsiya,
hannu yasa ya riqe kunnen ta wanda ya haifarmata dayin wata y'ar qaramar qara, menaji kince d'an mai maita naji se nasamu isarwa Abba saqon yadda kikeso"
Kince kingaji da zaman gidannan saboda haka ke aure zakiyi bazaki jure, irin takurawar da Abba yakeyiminki ba,
Zakiganine idan ya isa yabiki gidan mijinki ya takuramiki,,
itama kanta ammi a dole kike zama da ita saboda haka idan kikayi aure zaki tattara gidannan ki watsar koh ?
itakuma Nusaiba idan ta kus kura tajemiki gidanki me gadi zakisa ya koreta kokuma ki sakarmata kare, koh "
Kai yaya Rafiq ni wallahi ba haka naceba cewa nayi,
Nayimiki qaryar da nasaba kenan ?
Ya fad'a a hasale a'a,
kawai ta furta idanunta na kawo ruwa, d'an quramata ido yayi kamar me tunanin wani abu, se kuma ya juya ya nufi qofar fita yana fad'in '
bari naje nafad'awa Abba saqonki nacewar kingaji da zaman gidannan aure kikeso,
Batasan sanda tayi wani tsalle ba tariqoshi ta baya sosai ta qanqameshi, ta fashe da wani marayan kuka,
Dan girman Allah yaya Rafiq kayi haquri ka rufamin asiri wallahil azim ba hakanan naceba, idan kaje ka fad'awa Abba wannan maganar wallahi bansan da wani ido zan kallesaba,,
bashi kad'ai ba harda ammi da sauran mutanen gidannan, me zan fad'amusu su fahimci ban aikata abunda kakeson fad'amusu a kaina ba ?
Ina kakeso insa kainane ni mahanur, zan iya jure duk wata uqubarka ta cikin gidannan " amma wallahi bazan iya amsa tuhumar Abba da ammi ba, please yaya Rafiq dan girman Allah kaji tausayina,
Shikam dariyace taso su'bucemasa, ganin yadda gabaki da'ya ta gigice ta fice daga hayyacinta taketa basa haquri ga wata iriyar cakwama da tayimasa ta baya, wanda yaketa qoqarin kwacewa, amma taqi basa damar hakan "
Wai dama haka yarinyarnan takeda masifar tsoro shikam bega matsala ba dan kawai anje ance aure takeso,
a hankali yad'an saki mur mushi ta gefen bakinshi, sannan ya sake 'bata fuska ya maze"
Hannunsa ya kai ya fara qoqarin rabata da jikinsa dakyar yasamu ya janyeta daga jikinnasa sannan ya juya yad'an sunkuyo da fuskarsa setin fuskarta yana kallonta,
itakuwa kanta na qasa tanta hawaye, itade fatanta kawai yajanye wannan sharrin da yake qoqarin yimata a gurin Abba,,
Qafafunta ne suke qoqarin kasa d'aukar saboda rawan da jikinta yaketa faman yi,
luuu, ta tafi zata fad'i ta baya, saurin riqeta yayi, se a lokacin ya lura da irin rawar da jikinta keyi, a hankali ya janyo hannunta '
akan gado ya zaunar da ita had'e da fad'in ki kula yayi saurin juyawa ya fice daga d'akin yabarta a zaune tanata faman saqawa da kuncewa .
Wata ranar asabar da safe kasancewar wicked ne gabaki da'yansu suna gida,
Abba ya tarasu a babban parlor gabaki da'ya, suka had'u parlorn yad'an yi shiru na wasu yan daqiqu kafin Abba yayi gyaran murya yafara da cewa,,
Gabaki da'ya kunsan dalilin da yasa na taraku a nan ?
gaba d'aya suka amsa da
a'a "
Yad'an numfasa, sannan yace, yazu lokaci yayi da ya kamata na sauqe wani nauyi daya jima a kaina tunda gaba d'aya yanzu kun mallaki hankalin kanku,
ina fatan zaku bani had'in kai ku sauqaqamin wajen sauqe wannan nauyin?
babu wanda yace komai "
Seda ya d'an yi shiru na wasu daqiqu kafin yace,
Nusaiba kinada wanda kikeso ne a cikin samarinki ?
sosai tambayar ta daki ransu gabaki da'ya,
jim ta d'anyi Abba yasake mai maita tambayar, kai ta duqar qasa cikin jin kunya tace,,
"Eh Abba "
dama, mufty, yace nayimaka magana yanason turo magabatansa, to dama inaso nayi maganar da ammi ne idan yaso se ita ta fad'amaka,
To Masha Allah kawai yace sannan ya juyo kan Mahanur"
se da yad'an yi shiru kafin yace, uwata cikin sanyin jiki ta amsa qirjinta na dukan tara Tara, ya sauqe doguwar ajiyar zuciya.
Yace wani matsayi nakedashi a gurinki?
Sosai tambayar ta daki ranta amma ta maze matsayin mahaifi '
ta basa amsa a taqaice kanta na qasa tana wasa da yatsun hannunta,
Wata tambayar ya sake jefomata "
Kin yadda ni mahaifinkine kuma bazan ta'ba za'bamiki abunda ze cutar da ke ba?
Eh.....,
ta fad'a har yanzu bata d'ago kantaba, yaqara cewa,
to kinajin ni inada iko a kanki kuma na isa da ke ta yadda zan iya za'bamiki abokin rayuwa ?
Jim ta d'anyi kamar bata fahimta ba,
Abba yad'an qara numfasawa, yace kina d'aukata a matsayin uba hakan yana nufin inada iKon yankemiki mijin da zaki aura, domin kinsa bazan ta'ba za'bamiki abunda ze cutar da ke ba"
Eh Abba ta fad'a tana kallon saman carpet d'in parlorn,
Mamata kinyadda na isa na za'bamiki abokin rayuwa ?
Ya qara tambayar yana kai dubansa gareta,
Kanada damar da zaka yanke ko wani irin hukunci a cikin rayuwar y'arka Abba bazan ta'ba kaucewa umarninka ba Abba komai tsaurinsa,,
duk wanda ka bani a matsayin miji wallahi bazance komai ba.
Abba, sosai yaji dad'in furucinta,
To Masha Allah Allah ya yimiki albarka " amin Abba '
ta fad'a idanunta sunayimata wani irin zafi da alamar kuka takeso tayi amma bataso Abba yagane saboda hukuncin da ya yankemata ne takesonyin kukan, saboda haka ta qara dakewa sosai,
Abba yacigaba da magana, mamata kafin zuwanki gidannan nariga nayimiki miji kuma ina fatan zaku bani had'in kai wajen sauqe wannan nauyin a kaina,,
insha Allah Abba.
ta fad'a idanunta suna ciccikowa da hawaye, dan bazata iya bijirewa umarnin Abba ba , amma damuwarta shine tasan wanene mijin da Abba nnata ya za'ba mata"
Batakai ga qarasa tunani ba taji muryar Abba yana cewa,
yakamata nafad'amiki wanene mijin domin inaso ne ayi komai nan kusa a gama babu 'bata lokaci'
shiru tayi tana sauraron Abba nnata dantaji wanene mijin da ya za'ba mata tun tana qarama,
amma jin abunda ya fad'a ya jijjiga nitsuwarta,
wani irin miqewa tayi jikinta na rawa, wasu siraran hawayen masu zafi suka sulalo mata"
dai dai lokacin da Rafiq ya d'ago kansa da sauri zuciyarsa na harbawa da qarfi nan take idanunsa suka kad'a daga launin fari zuwa ja,
jijiyoyinkansa sun mimmiqe saboda jin abunda Abba ya fad'a,
Ja da baya ta farayi tana furta yaya Rafiq yaya Rafiq fah,
Wai ni zaka aurawa yaya Rafiq why Abba?
Ta qarasa maganar tana durqushewa akan guiwar ta, ta fashe da wani marayan kuka me sauti tamkar ranta ze fita,
Shikam gogan kasa cewa komai yayi, yashiga nanata sunanta a zuciyarsa
Mahanur Mahanur,
wai ni Abba yakeso ya aurawa wannan yarinyar wani lefi nayiwa Abba haka wanda yakeso ya hukuntani ta hanyar tarwatsamin rayuwa da auren wannan yarinyar?
Kusa da ita Abba ya matsa ya dafa kanta kiyi haquri Fatima Zahra,
kinsan ni mahaifinkine bazan ta'ba za'bamiki abunda ze cutar da ke ba'
kince zaki kar'bi duk mijin da na za'ba miki ban ta'ba neman wata alfarma a gurinkiba amma dan Allah kiyimin wannan alfarmar kinji uwata kuma karki tambayi dalili please.
Toh... Abba.. toh... Abba... toh... Abba.
kawai take nanatawa tare da qan qame hannun ammi tana sake fashewa da wani sabon kuka me ta'ba zuciya,
kanta Abba ya shafa yace Allah yamiki albarka,,
Batacemasa komai ba haka taci gaba da rera kukanta,
ya miqe har yaje bakin qofa, yasake juyowa, yace '
Nusaiba ki fad'awa mufty ya turo iyayensa gobe inaso a had'a bikinku ke da Mahanur nan da wata d'aya"
kuma ku rubutomin duk abunda da kuke buqata, kama daga kayan d'aki zuwa na kitchen,
Nusaiba ta amsamasa da to,,
yasa kai ya fice,
Itade Nusaiba ta rasa farin ciki zatayi ko baqin ciki,
farin cikin ta shine gobe za a sakamata rana da masoyinta mufty'
daga d'ayan 'bangaren kuma tanajin babu dad'i ganin yadda Mahanur take ta rusar kuka saboda mganar aurensu da yayanta Rafiq,
amma ta wani 'bangaren tanajin dad'i tasan idan sukayi aure ko ba komai rashin fahimtar da take tsakaninsu zata ragu "
Gabaki da'ya su ammi da Nusaiba da Zarban sunata kwantarwa da Mahanur hankali,
Shikuwa Rafiq, dakyar ya ja jikinsa ya d'auki makullan motarsa, ya fice daga gidan zuciyarsa na lugude.
Dak'ayar ta ja jiki ta shige d'akin ta,
Zubewa tayi akan gado tare da qara rushewa da wani gigitaccen marayan kuka, tana fad'in'
aure ni da yaya Rafiq kuma, nashiga uku ayyo ni, wayyo Allah na, umma ta meyasa kika tafi kika barni?
Inada buqatarki nasan a yanzu babu wani wanda ze fahimci matsalata se ke kad'ai,
wayyo Allah na shiga uku na, ni Mahanur ya zanyi da rayuwata rana zafi inuwa quna ina zan saka raina inji sanyi ?
Haka taci gaba da kuka tana sambatu, a haka har bacci 'barawo yayi awun gaba da ita,
itace bata farkaba se qarfe 04:27 , na yamma "
yun qurawa tayi zata miqe da sauri ta koma ta dafe kanta da yayimata nauyi ga wani irin sara mata da yakeyi kamar ze fad'o qasa,
wani irin zafi jikinta ya d'auka kamar wuta, rintse idonta tayi hawaye na gangarowa ta gefen fuskarta,
Dak'ayar ta miqe a daddafe tashiga toilet ,ta d'auro alwala, ta fito ta rama sallar azahar da ta wuce ta sannan tayi sallar' la asar,
dak'ayar ta ja jiki ta koma kan gadon taja bargo ta rufu saboda wani irin sanyi da takeji har cikin 'bargonta, ga wani ciwo da takeji a cikin jikinta kamar ana daddatsa duk wata ga'ba na jikinta "
haqoranta tasaka ta datse lips d'inta a hankali ta lumshe ido tana mai maita kalmar innalillahi wa inna ilaehir raji 'un , a cikin ranta,
ganin shirun yayi yawa ne yasa ammi ta nufo d'akin, domin tunda safe bata qarajin motsintaba,,
tura qofar tayi tajita a bud'e hakanne yabata daman shiga tana kiran sunan Mahanur, amma shiru babu amsa, hakanne yasa ta yaye qaton bargon da taga Mahanur ta lullu'be jikinta da shi,
duk kuwa da irin zafin da akeyi .
Hannu ta kai ta dafa goshinta taji ya d'au zafi sosai, tayi saurin kama hannunta amma se taga ya sake, kamar wata matacciya,
tasaka hannu a setin qirjinta taji zuciyarta na harbawa da sauri, amma bata numfashi ko kad'an "
a rikice ta sauqo qasa ta kira number Abba ta fad'amasa zasuwuce asibiti da Mahanur,
Zarban tasaka ya d'aukota ya sakata a mota suka wuce asibitin, Nusaiba taso binsu amma, ammi ta hanata tace tabari idan Abba ya zo se suje tare,
haka ta zauna badan ranta yaso ba.
Asibitin, R M B medicine hospital, suka nufa , nan take aka fara bata agajin gaggawa duk da babban likitan asibitin bayanan,
se kusan 9 na dare likitan ya shigo cikin kayan aiki, sosai kayan sun kar'bi brown d'in fatarsa me sheqi,,
yayi kyau kamar ba kayan aiki ya sakaba, sajensa sun kwanta a gefen kunnensa sunyi lub, babu hula a kansa sumarsa ta fulanin mallawa, ta kwanta tayi lub a kansa se sheqi take,
Ya rufe fuskarsa da face mask, iya fararen lumsassun idanunsa masu d'auke da zara zaran gashi kawai kake iya gani,
Wanene wannan?
Dr. Rafiq Ma aruf bommoli,
Mamallakin asibitin R M B medicine hospital,
Round, yakeyi yana duba kowani gado, dayake dama kullum se yazo asibitin ya duba marasa lafiya koda ba ranar aiki bane,
komai dare se ya zo ya duba halin da asibitin yake ciki ,
Ko wani gado yakebi yana dubawa, amma kallo d'aya zakayimasa kasan baya cikin nitsuwarsa "
har ma aikatan asibitin se da suka karanto damuwa a kan fuskarsa,
Mamaki ne had'i da tsoro suka cikasa ganin ammi a cikin asibitin,
Me yake faruwa?
Ya tambayi kansa to wanene Kuma ba lafiya bayan na fita nabar kowa lafiya, ganin babu me amsamasa tambayar sa ne yasa ya nufo inda ammin take, zuciyarsa taf, da tambayoyi,,
Meyake faruwa, ammi?
Wayekuma ba lafiya ?
Yayi tambayar tare da maida dubansa i zuwa gadon ,
Mahanur ya gani wacce taketa bacci sosai saboda alluran da akayimata, fuskarta tayi jazur abunka da farin mutum.
Ammi tace kaga mahanur ce batada lafiya bansan me yake damuntaba, tun safe najita shiru banji motsinta a gida ba shiyasa naje zan dubata se kawai naganta a sume bata ko numfashi, shiyasa ni da Zarban muka kawota, nayita kiran wayarka amma bata shiga,
yad'an yatsina fuska, yanajin wani irin tsanar yarinyar yana tasomasa, amma ya danne"
Allah ya kawo sauqi, kawai ya fad'a ya juya ze fice daga d'akin,
ammi ce ta dakatar da shi da cewa, bazaka dubata bane kokuma an fad'amaka hutawa mukazo yi a asibitin ne da zaka sa kai ka fice baka dubata ba?
ai baka ta'ba fad'amin an mayar da asibitin ka wajen shaqatawa ba "
Da ba nan zamu kawota ba se mu wuce inda ake jinyar marasa lafiya, tunda mu lafiyar muka fito nema.
haka ya dawo ba dan yasoba ya fara dubata dan shi yanzu ko sunan yarinyar bayason ji,
a tsattsaye ya d'an dubata yace babu komai, ammi zazza'bi ne kawai da ciwon kai,,
Kuma rashin hutu ne ya haifarmata da su, idan ta farka daga bacci, zazza'bi da zafin jikin zasu sauqa,
kuma zan rubuta muku magun guna se ku kar'ba,
Zuwa gobe ko jibi idan akaga sauqin jikinnata se a baku sallama .
Yana gama fad'ar haka ya fice da sauri,
Be jima da fita ba Abba da Nusaiba suka shigo, suka dubata, ammi tayiwa Abba bayanin abunda yake damunta , sannan suka wuce '
itakam Nusaiba taso abarta ta zauna a asibitin amma su abba suka qi,
Bayan kwana biyu jikin mahanur yayi sauqi sosai, hakan yasa aka basu sallama suka dawo gida,,
Bayan sallar insha, ammi ta shigo ta samu Abba, a cikin d'akinsa ta zauna a gefensa tace major,
akwai maganar da nakeso muyi dama to saboda zaman asibitinnanne yasa nace, zan bari se mundawo gida se muyi maganar .
a nitse" ya numfasa sannan ya tattara hankalinsa ya mayar kanta,
Inajinki ya fad'a,
Jim ta d'anyi sannan tace,
major nifa ina ganin saboda maganar auren nan ne Mahanur tasaka damuwa a ranta har ya haifar mata da wannan ciwon ".
kaga dama ko a gidannan ba shiri sukeyiba "
se nake ganin kamar idan bataso a fasa maganar aurennan, a bari ta kawo wanda takeso da kanta, inaga kamar haka zefi "
Se da ya d'anyi shiru kafin yace,
kin de san wanene mahaifinta a gurina, Kuma kinsan matsayinsa a zuciyata da rayuwata,,
kinsan bazan ta'ba za'bawa y'ar sa abunda ze cutar da rayuwata kawai saboda son raina ba,
To saboda haka idan wannan maganar ce ta kawoki, garama ki barta dan wallahi idan kinga ba ayi wannan auren ba se de idan d'aya ne daga cikin mu babushi,
ko qasa ta rufewa d'aya daga cikin su ido kokuma ni qasa ta rufemin Ido, wannan dalilin ne kawai ze iya dakatar da wannan auren"
kuma koda babu ni a raye na umurceki da tabbatuwar wannan auren ban yarda a fasashiba '
Yana gama fad'ar haka ya miqe ya shiga toilet ya bar ammi tana jinjina kai tana qara jujjuya kalamansa a ranta.
Shin wacece Mahanur? Wanene mahaifinta? Menene alaqarsa da Alhj Ma aruf bommoli??
SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE,
Lokacin, Alhj Ma aruf bommoli, yana d'an qaramin yaro baze wuce shekara 8 a duniya ba,
se qaninsa me shekara 3 Ahmad, suna zaune ne a qauyen bommoli, tare da iyayensu,,
sunan mahaifiyarsu " Fatima, amma mutanen qauyen suna kiranta da Inna fatu.
se mahaifinsu malam yunus wanda ake kira da baffa,
Kasancewar su ba yara bane se da sukayi shekara 30 da aure sannan suka samu suka haifi Ma aruf, daga nan basu sake aihuwa ba se da ma aruf ya cika shekara 5 a duniya,
Zo kaga farin ciki a gurin ma aruf wai shima inna taje kasuwa ta sayomasa qani"
Tun daga lokacin ya d'auki duk wata soyayyar sa ya d'aura akan Ahmad, ko da yaushe yana tare da shi ko wasa baya iya fita yabar Ahmad,
haka kuma ko abu aka basa idan ba a basa na Ahmad ba to ze haqura baze kar'bi abun ba duk yadda yakai ga soyayyar abun "
Haka lokaci ya cigaba da tafiya har Ahmad yayi wayo, duk inda kaga Ma aruf, zakaga Ahmad,
shima Ahmad yana matiqar qaunar d'an uwan nasa kamar yadda yake qaunarsa, hatta bacci ma baya rabasu.
Se de d'abi unsu sun bam banta, da na juna'
Ma aruf tun yana qarami mutum ne shi me, taurin kai da kafewa akan maganar sa, idan har ya fad'a baya ta'ba canzawa komai wuya komai tsauri se ya aiwatar,
Shikuma Ahmad mutum ne me sauqin kai da sauqin Hali ,
se de wannan bambancin nasu be ta'ba shafar shaquwarsuba,
Haka sukaci gaba da girma cikin kulawa da qaunar junansu, ko ciwo d'aya yakeyi haka d'ayan ma ze dawo kamar majinyaci,,
Irin shaquwar da take tsakaninsu tana bawa kowa a cikin qauyen sha awa, domin duk yadda Ahmad yakeda sauqin Hali, bashida sauqi idan ka ta'ba masa yayansa, ballantana Ma aruf, sarkin zafin rai " saboda shi kowani yaro tsoron ta'ba Ahmad yake,
Wata ranar talata da safe, lokacin, Ma aruf yanada shekara 13 a duniya, Ahmad kuwa yanada shekara 10 ,
wani abokin mahaifin su yazo daga birni, Alhj Hamza dawaki ya kawomusu ziyara wanda kasuwanci ne kawai ya had'a su kasancewar Alhj Hamza dawaki d'an kasuwa"
yana kai kayansa kasuwannin qauye, anan suka had'u da malam yunus mahaifin su Ma aruf,
Duk da Allah ya basa dukiya amma be ta'ba samun aihuwaba shi da matarsa hajiya zulai.
tun suna neman magani har suka haqura suka fauwalawa Allah komai '
Sosai yaran suka burgeshi, domin sunada nitsuwa sosai ga ladabi da girmama manya kuma basuda kwad'ayin abun duniya,
Hakan yasa Alhj Hamza yayiwa malam yunus bayanin halin da suke ciki na rashin aihuwa shi da matarsa hajiya zulai,
ya kokamasa irin quncin da suke ciki had'i da roqonsa, ya temaka ya basa d'aya daga cikin yaran, ze kula da tarbiyarsa da karatunsa had'i da alqawarin zasu dinga ziyartarsu idan sun samu lokaci.
Abunka da kunya irin ta mutanen da, baze iya hanasa ba, haka badan ransa na so ba, ya amince ze basa Ma aruf,
da yamma aka had'a masa kayansa " haka suka rungume juna shi da Ahmad 'sunata kuka se da sukabawa kowa tausayi,,
domin kowa yasan irin shaquwar da sukayi inna fatu, d'aki ta shiga tana kukan rabuwa had'i da tausayin yarannata,
dak'ayar aka 'bam 'bare Ahmad daga jikin Ma aruf, yanata kuka yana cewa shi a dawomasa da d'an uwansa"
Haka Ma aruf yanaji yana gani aka rabasa da d'an uwannasa, tun yana iya kuka da hawaye, har hawayen ya qafe, se kukan zuci,
Gabaki da'yansu babu wanda ya iya barci a ranar, saboda basusan yadda zasu rayu babu junaba, dan basu ta'ba gwada hakanba ko sau d'aya.
Babu wanda beyi jinyar rashin d'an uwansa ba, daga qarshe dak'yar kowanne ya bawa zuciyarsa haquri, suka fara sabawa da rashin junansu'
amma duk da haka sunajin babu dad'i idan suka tina juna ko da yaushe suna cikin kewar juna,
Alhj Hamza da me d'akinsa hajiya zulai suna kulawa da Ma aruf sosai sun sakashi a makaranta suna qaunarsa sosai, kuma yaron yanada qoqari, hatta malaman makarantarsu suna mamakin irin qoqarin sa,,
Yana primary 5 hajiya zulai ta fara laulayin ciki, zo kaga murna da d'oki a gurinsu gaba d'aya,
Ranar jumma 'a da misalin qarfe 2 na dare hajiya zulai ta haifo kyakkyawar baby girl"
sunyi murna da farin ciki sosai, takanas, Alhj Hamza ya d'auki Ma aruf sukaje qauyen bommoli suka sanar da inna da baffa qaruwar da suka samu,
sunyi murna sosai, Ma aruf da Ahmad ma sunyi farin cikin ganin junansu, kamar bazasu rabu ba " da suka tashi komawa, sosai aka had'amusu tsarabar mutanen qauye, suka kamo hanya,
A kwan a tashi asarar me rai, Ma aruf ya kammala degree d'insa da masters, a makarantar sojoji,
bayan training na d'an qaramin lokaci ya fito da babban matsayi, gabaki da'ya sunyi farin ciki da haka, yanzukam yana yawan zuwa qauyensu gurin su baffa da Ahmad '
Duk lokacin da akayiwa Ahmad maganar aure, se yace shi bazeyi aureba har se yayansa yayi tukun,
Tun su baffa sunayimasa fad'a har suka gaji suka dena, dan sun fahimci da gaske yake
Shekarar Ma aruf d'aya da fara aiki lokacin qanwarsa ni ima tanada shekaru 18 a duniya,
ta kammala secondary school d'inta, a lokacin ' Alhj Hamza ya yanke shawarar had'ata aure da yayanta Ma aruf,,
Lokacin da yajewa su baffa da maganar
sunji dad'i kuma sunyi na am da hakan, murna kuwa a gurin Ahmad ba a cewa komai, yayansa zeyi aure.
Sati biyu aka yanke lokacin biki, tun ana saura sati d'aya bikin Ahmad ya tattaro ya dawo, garin Gombe, dan auren yayansa,
cikin nasara akayi biki lafiya "aka d'aura auren Ma aruf yunus bommoli da amaryarsa Ni I'ma Hamza dawaki kowa ya koma gida cike da murnar yin auren , Ahmad da su inna, ma suka tattara kayansu sukayi azaman komawa gida"
Cikin shekara d'aya da aure Ni I'ma ta sankato, qaton baby boy d'inta, me kyau sosai '
kasancewar ita black beauty ce shikuma Ma aruf fari ne, se yaron ya d'aukosu gabaki da'ya, shi ba fari ba sannan kuma bazaka kirasa da baqi ba , fatarsa chocolate color ce me kyau,
Ranar suna yaro yaci suna, Aliyu haidar, wanda sukeyiwa laqani da Rafiq.
Ma aruf yayi iya qoqarinsa wajen ganin ya d'auko su baffa sun dawo cikin gari domin bayason rayuwarsu a qauye,
amma duk yadda yayi sunqi yarda su dawo cikin gari duk sanda yayimusu maganar se suce sukam ai sunriga sunyi rayuwarsu anan yanzu qarshe ne anan sukafi wayo saboda haka kawai yabarsu anan.
Haka ya haqura ya barsu badan ransa na so ba "
shikuwa Ahmad duk lokacin da yayimasa magana akan yabiyosa su zauna a birni se yace shi ze zauna tare da su inna dan baze iya nisa da su ba,
Haka Ma aruf ya haqura badan yaso ba amma yana yawan kawomusu ziyara tare da matarsa Ni I'ma,
Watarana Ma aruf yazo dubasu" amma bezo da Ni I'ma ba, domin cikinta ya tsufa aihuwa yau ko gobe,,
lokacin ' Rafiq yayi wayo dan yanada kusan shekara 5 ,
Baffa yake fad'amasa, Ahmad ya samu yarinya a nan kusa da qauyensu har anje an tambayamasa aurenta Kuma, wata biyu akasa lokacin bikin,
Ma aruf yayi murna sosai dajin d'an uwansa yasamu mata, haka ya koma cike da farin ciki ze yiwa matarsa Ni I'ma albishirin qaramin mijinta ya samu mata zeyi aure.
Ya tarar da wani farin cikin, domin kuwa yasamu Ni I'ma ta aifo, baby boy, fari tass " qato'
farin cikin ya had'u masa biyu " se ma ya rasa ta ina ze fara.
Ai kuwa tun ana sauran sati d'aya bikin Ahmad Ma aruf ya tattara shi da iyalinsa suka tafi qauyen bommoli, domin yayi alqawarin shima se yayiwa Ahmad gata kamar yadda yayimasa a nasa auren,
lokacin Zarban kwata kwata watansa biyu ne a duniya.
Ai kuwa anga auren gata kaf garin da mak'waftansu , se da suka sheda auren Ahmad dankuwa Ma aruf ya kashemasa kud'i sosai ,
biki akayi kamar a cikin gari, ma aruf ya had'asu shi da amaryarsa Najiba, yayitamusu nasiha me shiga jiki' daga bisani suka kamo hanya suka dawo gida,,
Shekarar, Zarban 3 wata ranar jumma 'a da yamma , Ahmad ya kira Ma aruf gabaki da'ya jikinsa a sanyaye yacemasa inda hali yazo jikin baffa ya rikice,
A rikice ya tafi qauyen bommoli dan ko shiri be tsaya yiba " amma kafin ya isa, me afkuwa ta afku '
baffa ya amsa kiran mahaliccinsa , duk da a lokacin Ma aruf ya manyanta amma haka yadinga sharar qwalla yanayiwa baffa addu,a "
bayan anyi sadakan uku Alhj Ma aruf ya dawo garin Gombe ita kuwa hajiya Ni ima se da akayi sadakan bakwai suka dawo,
A lokacin daga ita har Najiba suna laulayin qaramin ciki .
Cikin iKon Allah hajiya Ni ima ta sankato qatuwar jaririyarta fara tass me kama da Zarban, gwanin sha awa,
ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Ni I'ma, zulaihat" suna kiranta da Nusaiba,
Kwanan Nusaiba goma a duniya, inna, ma ta amsa kiran mahalicci "
wata uku da rasuwar inna, najiba ta aifo yarinya fara tass kyakkyawa,
Alhj Ma aruf yanajin aihuwar, ya d'auki su hajiya Ni ima, suka tafi qauyen bommoli,
lokacin Nusaiba tanada wata 3 da kwana 10, Zarban yanata d'oki wai yaga sabuwar baby,,
shikwa Rafiq se fad'a yakeyimasa wai shi babu ruwansa da ita tunda ba babyn su bace babyn qauye ce, suka dinga yimasa dariya, a cewarsu wai haline na quruciya "
Ahmad ya miqawa Alhj Ma aruf yarinyar yace yaya da kanka nakeso kasakamata suna,
ka za'ba mata duk sunan da kaga ya dace da ita.
Alhj Ma aruf ya quramata ido yanajin wani qaunarta har cikin ransa domin tana matiqar kama da mahaifiyarsu " gashi uwa uba d'iya ce a gurin mutumin da yafi so a cikin rayuwarsa,
Yad'an numfasa sannan yace, na sakamata sunan mahaifiyarmu Fatima bintu, daga yau, zamu dinga kiranta da Mahanur, ma abociyar haske me kyau.
Mahanur tanata girma, amma ko kad'an Rafiq baya sonta koda gidansu sukaje ko su suka zo musu baya shiga harkata,,
mahanur tanada shekaru 12 sukayi hatsarin mota ita da mahaifinta da mahaifiyarta,
Najiba a take ta amsa kiran uban giji, shikuma Ahmad yasamu karaya a kafad'ar sa,,
kansa ya bugu sosai" qafarsa ta dama da hannunsa na hagu suka kakkarye, ita kuwa Mahanur ta samu tsagewar qashi.
Alhj Ma aruf yashiga damuwa sosai,,
watan Ahmad guda, a asibiti, Alhj Ma aruf ya shigo dubasa, Ahmad ya roqi mutanen gurin da su temaka subasa guri yayi magana da d'an uwansa '
Bayan sun fita ya riqe hannun dan uwannasa yace yaya na, nabar amanar mamata a hannunka nasan idan kananan bazatayi maraici ba,
Zaka kula da ita fiye ma da yadda ni zan kula da ita,
Banida shakka akan matarka Ni I'ma zata zamo mata mahaifiya"
dan Allah karku bari tayi kukan rashinmu, inada wani quduri na auramata babban d'ana Rafiq,
naso nayi tsawon rai harnaga aurenta, amma qaddara ta riga fata"
nasan ko bana raye zaka cikamin wannan mafarkin nawa na aure tsakanin Mahanur da Rafiq, domin yawaitar iyalinmu '
Kuma bazatayi kuka saboda maraici ba,
Dan Allah idan yarana sunyi Nisan kwana, ka auramusu juna domin tun ranar da aka haifeta na yanke cewar mata aka haifawa Rafiq.
Alhj Ma aruf yayi saurin tarar numfashinsa yace a'a d'an uwana,
babu inda zaka tafi kabarni zaka yi tsawon rai kuma zakaga auren, Mahanur da Rafiq "
kai kad'ai ne ka ragemin, a duniya kai kad'ai nake kalla naji dad'i, ciwo ai ba mutuwa bane zaka samu lafiya meye amfanin dukiya ta idan har ban temaki d'an uwana da ita ba?
Zan kashe koma nawane a kanka koda zan sayar da komai nawa na koma gidan haya wallahi inde zaka samu lafiya zan sallama komai nawa.
Ahmad ya rintse ido hawaye na gangaro masa yanajin wani irin azabar da tunda yake rayuwa be ta'ba jin irinta ba, ko ranar da sukayi hatsari beji irin wannan azabar ba,
Dak'ayar ya bud'e baki yace ina me baka haquri yaya na '
kuma nasan kanayimin son da yafi haka " koda rayuwarka ne nasan zaka iya bada ita saboda tawa rayuwar,
ka dinga kallon gudan jini na a duk lokacin da kayi kewata naji dad'i da ba kai zaka tafi kabarni ba"
domin inda kai ka tafi duniyarnan gaba d'aya bazata yimin dad'i ba.
Kalmar shahada ya farayi yana wani irin jijjiga wani kumfa na fita daga bakinsa, Abba yanaji yana gani rai yayi halinsa"
haka suka d'auki gawar suka koma gida sosai Alhj Ma aruf yake kuka kamar wani qaramin yaro,
hajiya Ni ima ta riqeshi tana rarrashinsa,,
Ni I'ma shikenan yanzu na rasa taqamata duk wani farin ciki na yana tattare da d'an uwana yau na rasa shikenan na rasa komai,
inama ace mutuwar ni ta d'auka ta k'yalesa , wayyo Allah qaddara meyasa zakiyimin haka?
Haka yaci gaba da kuka yana sambatu hajiya Ni ima tanata faman rarrashinsa, domin ita a karan kanta zata bada shedar irin qaunar da sukeyiwa juna shi da d'an uwannasa.
Rafiq da Zarban ne suka temaka masa wajen yimasa sutura,
aka fitar da shi akayimasa sallah" sannan suka kaisa gidansa na gaskiya,,
tun daga wannan ranar abba ya d'auki duk soyayyar da yakeyiwa d'an uwannasa ya meyar kan Mahanur"
har yafi qaunarta akan yaran da ya haifa.
Baya son ganin kukanta domin a duk sanda ya ganta mahaifiyarsa da d'an uwansa ne suke fad'o masa a ransa '
Haka yacigaba da kulawa da ita cikin qauna har aka kawo lokacin da yakeson cikawa d'an uwansa qudurinsa na aurawa y'a y'ansu juna.
Lokacin biki se qara gabatowa yake, saura kwana biyar, anata shirye shiryen biki amare se shan gyara suke "
duk da Abba yace baza ayi wata hidima ba aure kawai za a d'aura akai ko wacce d'akin mijinta,
Haka kuwa akayi, ranar auren tun da safe Abba ya sakasu a d'aki yayita yimusu nasiha me ratsa zuciya,,
gabaki da'ya se kuka suke, musamman Mahanur da ta mayar da kukan kamar al a darta tunda auren ya matso "
batada aikin da ya wuce kukan, ko abinci ma se ammi ta matsamata take d'an cakala ,
batawani cin na kirki se tace ta qoshi, idan ammi ta matsa se ta sakamata kuka haka zata haqura ta k'yaleta.
Da misalin qarfe 10 na safe aka d'aura auren,
Muhammad sani yalwa, wato mufty' da amaryarsa, zulaihat Ma aruf bommoli, wato Nusaiba,
Sannan aka d'aura auren,,
Aliyu ma aruf bommoli, Rafiq, da amaryarsa, fatima Ahmad bommoli,
da yamma aka miqa amarya Nusaiba gidanta sannan aka miqa Mahanur ma nata gidan'
wacce dakyar aka rabata da jikin ammi,
Tunda taji tsayuwar motocin d'aukan amarya ta daka tsalle ta qanqame ammi tana kuka, tana fad'in,
Wayyo Allah na na shiga uku ammi dan Allah karki bari su tafi da ni wallahi banason yaya Rafiq, kicewa Abba ya temaka yabarni naci gaba da zamana a nan gidan"
Wayyo na shiga uku ya zanyi da wannan qaddarar ?
Wani irin tausayinta ne ya kama ammi, itama batasan sanda ta fashe da kuka ba, tana rarrashinta,
kiyi haquri mama na " yanzu kin girma sabuwar rayuwa zaki fara rayuwar gidan miji ba kamar zaman gida yakeba '
Zaman aure d'an haquri ne,
Duk wanda kikaga aurensu yaje wani mataki to sunyi haquri da juna ne,
Ki kula sosai, ki kula da tsaftar gidanki harma da na jikin ki "
ki zama ma abociyar kwalliya a gidan mijinki, karki bawa matan waje gurbi a cikin rayuwar mijinki,
ki sauqemasa duk wani hakki nasa da yake kanki,,
kar ki ta'ba bari mijinki ya koka da ke, domin idan yayi fushi da ke hatta mala ikun Allah fushi suke da ke, ki kula da tsaftar abincinsa,
Ki kula da wuqa wajen girki karki yanke hannunki.
Shikam Abba d'akinsa ya shiga domin ya 'boyewa mutane hawayensa,
haka aka kaita gidanta tanaji tana gani kowa ya watse aka barta ita kad'ai a gidan.
kallon abun takeyi kamar almara , wai yau itace a cikin gidan yaya Rafiq, kuma wai a matsayin matarsa.
Se can kusan qarfe 10:40 na dare ya shigo cikin gidan,
mamaki ne had'i da tsoro ya kamata lokacin da taji ya nufo d'akin ta,,
Ajiyar zuciya ta sauqe had'e da yiwa Allah godiya ganin, daya shigo be cemata komai ba,
ledar hannunsa kawai ya miqamata, ya juya ya fice da sauri.
Bud'e ledar tayi dayake dama yunwa takeji dan rabonta da abinci tun daren jiya, da ammi ta matsamata ta d'an sha tea, da cake,
Kazace lafiyayya se yogurt me sanyi, da ruwan gora "
Sosai taci tasha yogurt d'in se da taji tayi qat , sannan tabi lafiyar gado ta kwanta
Washe gari tun 6 na safe ta tashi, ta d'aura break fast "
bayan ta kammala ta shiga toilet ta watsa ruwa, batayi wata kwalliya me yawa ba " powder kawai ta shafa sannan ta murza man baki.
Wasu riga da scate d'in atamfa, ta d'auko ta saka sun kama jikinta sosai sunyi kyau kamar a jikinta aka d'inkasu,
fitowa tayi ta zauna tafara karyawa bayan ta kammala ta tattare kayayyakin tabar masa nasa a gurin ta koma d'aki tayi kwanciyarta tana lallatsa wayarta,
Ko da ta fito haka ta tarar da abincin yadda ta barsu,,
to kode be fita bane ta tambayi kanta a hankali ta nufi d'akinsa ta tura qofar cikin sa a tasamu be rufeba ta shiga,
bayanan da alamar abincinne kawai be ciba'
ta d'an ta'be baki tace kayiwa kanka"
tattaresu ta koma tayi sannan ta shiga kitchen d'in dan ta duba abunda ya kamata taci da rana.
Shikam tun da ya fita ya nufi asibiti duk da weekend ne,
office d'in sa ya bud'e ya shige " zama yayi ya dafe kansa da hannayensa,,
ni wai nine yau na amsa sunan mijin wata, watanma wai Mahanur yarinyar da a duniya ko sunanta bana qaunar ji, impossible.
Ya fad'a a fili zuciyarsa na qisima masa wani abu"
Da sauri ya janyo farar takarda ya d'auki jan biro ya fara rubutu kamar haka.
Ni Aliyu ma aruf bommoli, na saki ' matata Fatima Ahmad bommoli, saki d'aya sakamakon anyimana aurene ba tare da muna son junanmuba,
Yana gama rubutun ya nad'e takardar ya cusa a aljihunsa , yana tunanin yaushe zeyi jaruntar bada wannan takardar ?
domin yasan duk randa Abba yaji labari , shikam kashinsa ya bushe dan yasan Abbansu da tsauri,
amma duk da haka ya quduri aniyar duk rintsi watarana seya bata wannan takardar domin shi ko a matsayin y'ar aiki bayajin ze iya zama da ita balle har matsayin mata.
Ita kuwa Mahanur tun tanayin abinci da shi tana ajiyemasa har ta gaji ta dena domin koda tayi ko kallon banza bata isarsa da ita da abincin nata,
Wata ranar alhamis da yamma, yana dawowa gidan wani irin qamshin abinci ne ya cikamasa hanci" da fari har ya maze ya shige d'akinsa"
jin qamshin yaqi qarewa ne yasashi fitowa ya nufi hanyar kitchen d'in dan yaga wace wainar yarinyar nan take toyawa,
Ido kawai ya tsaya ya zuba mata, sosai yake kallonta ta juya baya tana girki"
wata y'ar 'bingilalliyar riga ce a jikinta wacce iyakarta guiwarta ne, kanta babu d'an kwali ' ta tufke baqin gashinta a tsakiyar kanta,
Hannu ya kai ya riqota, wani ihu ta saki na tsoro domin ita batasan da tsayuwarsa a gurin ba,,
Saurin had'ata da jikinsa yayi yasa hannu ya matse bakinta, wannan girkin kuma na meye?
Ke da Wayene a gidan da zaki dafa wannan abincin haka ?
Ganin shine yasa ta sauqe ajiyar zuciya" ta d'an rausayar da kai dama kaine?
Wallahi yaya har ka bani tsoro,
Baki bani amsar tambaya taba, sosai ta fad'a d'a mur mushinta tace yau baqi fa zamuyi a gidannan '
cikin mamaki ya tambayeta su waye Kuma?
Dariya tayi ta juya manyan idanunta a hankali tace,
canka zakayi ai yaya, ki fad'amin mana su Abba ne?
Dariya ta sakeyi, ta d'an fara tafiya sannan tace na fad'amaka ai canka zakayi,
idan kuma maza sun kasa se abawa mata gari.
To shikenan karki fad'amin da kaina zan gano suwayene, ta d'anyi mur mushi me sauti tace zan ganine,
ga mamakinta mur mushi taga yayi wanda shi kansa besan sanda ya su'bucemasa ba, ya janyota jikinsa ya matso da kansa jinkin wuyarta,
cikin wata kasalalliyar murya ya rad'a mata a kunne '
Zamu ganine,
Yasaketa tare da kashemata Ido d'aya ya fice yana murmushi,
tsaye tayi tana mamakin wai yau yaya Rafiq ne ya kulata Kuma wai har yakeyimata dariya,
Anya ba gizo idonta yayimata ba kuwa.
Shima kansa mamaki yafara bawa kansa, dajin takaicin yadda yayimata magana,
dogon tsaki yaja sannan a fili ya furta, yanzu wannan yarinya me masifar kankanba da renin zata fara renani.
Toilet ya shiga yayi wanka, jallabiya kawai ya zura ya wuce masallaci "
bayan ya dawo Nusaiba da mufty' ya tarar '
sosai yaji dad'in ganinsu domin yayi missing d'in yar uwar tasa,
hira sukayi sosai se da akayi sallar insha sannan mufty' ya d'auki Nusaiba suka tafi"
sosai suka bawa Mahanur sha awa ganin yadda mufty' yake nan nan da ita yana bata kulawa,,
ko yaushene zan samu irin wannan kulawa da farin cikin a gurin mijina oho , ta fad'a tare da miqewa tashiga banda'aki ta qara watsa ruwa.
Wata fitinanniyar riga ta saka wacce ko guiwarta bata qarasa ba, ta kamata sosai " rigar shara shara ce me laushi pink color,
Ko d'an kwali babu a kanta ta fito,,
Rafiq yana zaune a parlor wani irin kallo ya bita da shi ko qiftawa bayayi itakuwa ko kula dashi batayiba, kitchen ta nufa " har se da ta shige ya d'auke idon sa '
a hankali ya lumshe idanunsa had'e da d'aura hannunsa akan qirjinsa, wani irin feeling yana fizgarsa,
yad'an lashi saman lips d'insa a hankali, ya salam ya furta a zuciyarsa ' yana bud'e idanunsa"
A de de lokacin da take fitowa daga cikin kitchen d'in,
qara lumshe idanunsa yayi ya bud'e ya zubasu a kanta,
Giftashi tayi zata wuce da sauri ya janyota,,
Zo nan ya furta cikin wata kasalalliyar muryar da tasa tsikar jikinta" zubawa.
A gabansa ya zaunar da ita dayake akan carpet d'in parlorn yake zaune,
ido ya zuba mata sosai yanayimata wani irin kallo "
sannan ya kai hannu ya fara, murza gefen kunnenta a hankali ya matso daf da ita, ya gangaro da yatsarsa saman lips d'inta yana wasa da shi,
Firgigit, ya dawo cikin nitsuwarsa ' da sauri ya saketa itakam duk jikinta rawa yake,,
da sauri ta miqe zata fice ya sake riqota ta fad'o jikinsa,
Inajin yunwa Mahanur ki samamin abunda zanci, mamaki ne ya kasheta.
Abinci kuma?
Ta furta a hankali be kulataba ta sake cewa,
Kamar abinci naji kace na kawoma, ka manta kace ban iya abinci ba " Kuma bazaka iya cin abincin da na dafa ba?
Rannan fa har cewa kayi kai ko karenkane yaci abunda na dafa se an kaishi asibiti,
Kuma naga watana nawa a gidannan tun da nazo baka ta'ba cin abunda na dafa ba.
tsawa ya daka mata,,
ke ni sa an wasankine?
Ni kike fad'awa wad'annan maganganun? Ashe bakida kunya ?
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta qasa,
To ki saurareni nan gidan gidanane, inada damar cin abinci ko naqi ci a lokacin da naga dama, Kuma babu wanda ya isa ya tambayeni dalilin yin hakan,
Kin fahimta?
Ya qarasa maganar cikin fad'a, shiru tayi masa batace komai ba ta miqe ta koma kitchen d'in tana turo baki .
Jollof d'in taliya da kifi tayimasa, yaji had'i sosai se qamshi yakeyi " ta ajiyemasa ta juya zata fice '
Zo ki zauna ya fad'a fuskarsa ba yabo ba fallasa,
Dawowa tayi ta zauna a zuciyarta tana fad'in, wai wannan wani irin Murd'ad'd'en mutum ne haka?
Duk abunda zakayimasa bazaka ta'ba gwanintaba,
wallahi nasan yanaso yaci mutunci na ne kawai da baqaqen maganganunsa kuma wallahi yanzu kam duk abunda yayimin ramawa zan dingayi tunda ai ba ubana bane shi.
Ta qarasa tana murgud'a qaramin bakinta"
Magana kike ne?
Ya fad'a yana qoqarin janyo abincin gabansa,
A'a
kawai tace ta juyar da kanta'
Ai kuwa de kamar tasan ya zaunar da ita ne dan ya fad'amata magana,
Yana kai loman farko, abincin yayimasa dad'i sosai amma duk da haka ya yatsina fuska had'e da ture plate d'in yana cewa "
ke haka ake girki a gidanku?
Shiru tayi bata bashi amsaba, yaci gaba da cewa,
ko abinci baki iya dafawaba amma ke har kinsan zama a gidan miji, kin dage se da kika aureni "
imbadan qaddara ba ma kekam ko y'ar aikin gidana baki kai ki zamo ba, wallahi yadda kikasan yadda kikayi aka had'a aurennan,
garama tun da wuri kije kisamu abba ki fad'amasa yayi gaggawar raba wannan auren kamar yadda ya had'ashi, dan ke ko boyi boyi bakida class d'in da zaki zama a gidana balle ki saka ran zakizo ki miqe qafa ke ga matar gida.
Sosai maganganun sukayimata zafi, amma se tayi mur mushi ta miqe tsaye tace'
Alhamdulillah nide banyi kwantai ba" a gaban kowa Abba ya nemi alfarmata da na temakesa na rufamaka asiri na aureka,
banasonka amma na duba matsayin Abba a gareni naji cewar yafi qarfin duk wata alfarma a gurina"
saboda haka ne na yadda na temaka na aureka karka mutu ba aure,
dan ansan babu macen da zata iya zama da kai a haka.
Shikam mamaki ne ya hanashi koda motsi,
wai shi da manyan mata masu class suke bibiyarsa shi wannan qaramar yarinyar takeyiwa gorin an roqeta alfarmar ta zauna da shi,,
Har ta juya zata fara tafiya ' se Kuma ta qara juyowa tace,
And kuma maganar raba aure ba hurumina bane kuma bazan fad'a ba "
idan kanajin hakan ya dameka da yawa to kaje kasamu Abba da kanka ka fad'amasa " idan yayi na am da maganar se nafi kowa farin ciki,
dan kuwa ko babu komai zan yasar da kwallon mangoro na huta da quda.
Tana gama fad'ar haka ta juya da gudu ta nufi d'akinta,
da sauri ya biyo bayanta amma kafin ya cimmata tayi nasarar, rufe qofar tasaka Key"
Da qarfi ya shiga bugun qofar yana fad'in, kizo ki bud'e qofar nan wallahi idan kika sake na kamaki na lahira se ya fiki jin dad'i ,
shiru tayi masa kamar bata gidan " haka ya gaji ya juya ya nufi d'akinsa zuciyarsa na tafasa '
Wai yau shi wannar bagidajiyar qazamar yarinyar, take fad'awa haka wai yayi kwantai,
Duk irin mata masu class d'in da suke bina wai ni take fad'awa haka?
Ya fad'a a fili , ya shige d'akinsa zuciyarsa cike da wata iriyar tsana da jin haushinta.
Itakuwa tana shiga d'akin , ta kife akan gado ta fashe da wani kuka, wasu hawaye masu yaji suka shiga gangaromata,
saboda maganganunsa, wai ni yakecewa ko y'ar aikin gidansa ban kaiba.
Me gayennan ya d'auki kansa ne kam?
Haka ta ci gaba da saqe saqe a cikin zuciyarta, har bacci 'barawo yayi awun gaba da ita .
Washe gari kuwa qin fitowa tayi daga d'aki,
a nata wautar wai ita jira take seya fita domin ta riga tasan halin Rafiq sarai baze kyaleta ba"
batayimasa lefi bama yaci zalita balle kuma tayimasa rashin kunya,
Tsoro taji sosai lokacin da ta leqo ta 'bulin qofar " taga Rafiq yana zaune a parlor ya gama karyawa se de bataga alamar yanada niyyar fita ba,,
Na shiga uku na lalace, shikenan yau idan yaya be fitaba nasan rayuwata ta d'ai d'aice"
Haka taja jiki ta koma kan gado, zuciyarta cike da tsoro da tunanunnuka kala kala,
itade roqonta d'aya shine Allah yasa ya fita '
dan kuwa tasan idan be fitaba itakam ta mutu ta lalace, ga wata azzalumar yunwa da taketa k'wak'ular cikinta.
Haka ta kwanta ta dafe cikinta " ta lumshe dara daran idanunta had'e da cije saman lips d'inta tanajin yadda yunwar take ratsata,
cikinta se wani irin qugi yakeyi, yana neman a sakamasa wani abu.
Har seda taga 12 na rana yayi ta qara saqqowa ta leqa a tunaninta zataga bayanan,
abunda ya bata tsoro shine har yanzu babu alamar ze fita guri ma ya samu ya kwanta yana danna wayarsa,,
Ai kuwa batasan sanda ta zube a bakin qofa ba ta riqe bakinta ta fashe da kuka tana cewa"
meya kaikine Mahanur?
Meya kaiki yiwa wannan baqin azzalumin rashin kunya?
Na shiga uku na lalace, haka taci gaba da kukanta domin tariga tasan saboda ita yaqi fita abunda tayimasa da darene be mantaba shine yakeso ya hukuntanta a kai,
Itade kam tariga tasan wallahi ko kwana zeyi a nan bazata iya bud'e qofar nan ba, se de yunwar tayimata duk abunda zatayimata " amma wallahi bazata fitaba dan ta gwammace zama da yuwa akan muguntar yaya Rafiq,
itade yaukam tasan tayi kus kure.
Se yau ta qara rena kanta ta tabbatar ita qaramar y'ar iska ce,
se yau tasan a cikin marassa kunya ita qaramace "
ji takeyi kamar taje tabasa haquri, amma tasan wallahi ko uban haquri ta basa ba abunda ze hanashi 'ballata a gidannan.
Har kusan 2 na rana babu alamar ze motsa daga inda yake har ta riga ta saddaqar yau kam soyake yunwa seta kasheta a gidannan,
Wani dogon ajiyar zuciya ta sauqe taji wani sanyi a cikin ranta " jin muryar su ammi suna sallama,,
Alhamdulillah.....,..
ta furta sannan cikin sauri ta d'auko wata doguwar riga ta zura.
Tayi qoqarin danne damuwarta had'e da qaqalo mur mushin qarya wanda iya fatar bakinta ya tsaya '
tayi saurin bud'e qofar da gudu ta fad'a jikin ammi tana dariya tace,
ammi wallahi nayi missing d'in ku sosai ji nake kamar na koma gida wallahi,
dariya sukayi sannan gabaki da'ya ita da Rafiq suka gaida Abba,,
Ammi ta d'an quramata ido sannan tace mama na me ya sameki naga gabaki da'ya kin rame kin lalace?
Ina fatan de ba wani abun yake mikiba ?
Qir qiro mur mushin yaqe tayi tace wallahi ammi babu komai lafiya muke " kwanaki biyunnan na d'anyi zazza'bi ne shiyasa kikaga kamar na rame,
Ammi tace amma ai Rafiq yana zuwa gidan be fad'amin ba.
Da sauri tace ammi nice nacemasa karya fad'a ai zazza'bi ne kawai ba wani babban ciwon bane, banaso hankalinku ya tashi ne .
Abba de yaji maganar ne kawai amma batayi kama da wacce za a yaddaba "
domin shi yariga yasan irin baqin halin d'an nasa,
Da sauri ta miqe ta shiga kitchen, tana fatan Allah yasa kar su ammi su tafi, shikuma Rafiq se Allah Allah yake ya samu su ammi su tafi '
Jollof d'in cous cous, da hanta tayi, yaji carrot da green beans, da albasa, tuni Rafiq ya fara had'iye yawu saboda yadda qamshin girkin yake dukan hancinsa.
A kula ta sakowa su ammi, ta d'aura plate a saman da cokala, ta jera akan tre, ta had'o da ruwa,
Bayan tazo ta ajiyemusu ta koma ta sakowa Rafiq, a plate tazo ta ajiyemasa shima harda ruwa,,
sannan ta koma ta d'ebo nata ta d'auki robar ruwa ta koma d'aki "
Se da taji tayi qat, sannan tasha ruwa se yanzu ta dawo hayyacinta ' domin dama ita tun a gida ba wani juriyar yunwane garetaba.
Tayi mamaki sosai yadda taga Rafiq yaci abincin da yawa,
Sun jima sosai suna hira da ammi, kafin su wuce Rafiq ya miqe da niyyar kaisu, amma Abba yace da mota suka zo,
gaskiya Mahanur kam ko kad'an bataji dad'in hakaba.
Suna fita, tayi saurin miqewa zata koma d'aki "
fizgota yayi, ta fad'o jikinsa,
Take jikinta ya fara 'bari' fashewa tayi da kuka tana fad'in'
yaya Rafiq dan girman Allah kayi haquri wallahi sharrin shed'an ne da na quruciya,
Na rantse bazan sake,
Bata qarasaba ya d'allamata babbar yatsarsa a kan le'benta, wanda yasatayin shiru da sauri takai hannunta tana sosa gurin hawaye na zuba "
Qara matseta yayi a jikinsa sosai " ya d'aura bakinsa a setin kunnenta sannan ya zagayo da hannunsa yad'an riqe wuyarta,
Kafin ya fara yimata magana cikin rad'a a kunnenta '
Ke bakida kunya koh?
Ya fad'a daga can qasan maqoshinsa, yanajin wani irin feeling yana fizgarsa,
Da sauri sauri zuciyoyinsu suke bugawa,
Ya lumshe idanunsa a hankali ya d'aura hancinsa akan wuyanta,,
shiru tayi batace komai ba se wasu hawayen tsoro, da suketa" ambaliya akan fuskarta '
Juyo da ita yayi, yana kallon cikin idanunta irin kallon da bazata iya jurewaba,
da sauri ta rintse idanunta, hakan ya basa damar zubawa fuskarta idao,
haka kawai ya tsinci kansa da son kallon ta.
Hawaye se malala suke akan fuskarta, ta tsuke d'an qaramin bakinta, har yanzu bata bud'e idontaba,,
Ya zubawa zara zaran gashin idonta, Ido yana kallonsu,
besan sanda ya qara janyota jikinsa ba" a hankali ya qara matseta sosai, a cikin faffafad'an qirjinsa.
Saurin bud'e idanunta tayi, jin wani abu me laushi yana yawo akan lips d'inta,
Wani irin duka qirjinta ya shigayi da sauri da sauri "
Bakinsa ya d'aura akan nata, a hankali yana tsotsan lips d'inta kamar sweet,
Yana sauqe wata ajiyar zuciya, a hankali" ya lumshe idanunsa, da alamar de ya manta da wacece a gabansa'
wannan y'ar qauyence da ko y'ar aikin gidansa batakie ta zamaba,
Kuka takesonyi amma yaqi bata dama domin yaqi sakin bakinta.
Turesa tashigayi hawaye na gangarowa, amma ko a jikinsa " wai an tsakuri kakkausa,
Yaguninsa ta farayi hakan yasashi saurin sakinta, ta miqe ta nufi d'akinta da gudu tana kuka.
Mayar da kansa yayi ya d'aura akan kujera, ya qara lumshe idanunsa,
ya salam wai me yake faruwa da nine?
Wani irin yanayi nakeji ne?
Kuma wai akan Mahanur,
Baze ta'ba yiwuba wannan abunda da nakeji, Kuma akan Mahanur to taya haka ze faru, ?
Ya jefowa kansa tambayar tare da cusa hannunsa a cikin lallausan gashin kansa yana furta impossible a fili tare da furzar da wani iska daga cikin bakinsa.
Nusaiba kam ta fara zuwa makaranta, ga cikinta yafara girma dan harya fara fitowa "
Mufty ya qaro kulawa fiye da yadda yakeyimata da,
dan ko girki baya bari tayi wai karta wahalar masa da babyn sa,,
Da yamma Rafiq ya dawo gida yayi mamakin ganin yadda parlon yake kaca kaca, Mahanur bata d'auke komai ba '
be ta'ba ganin hakaba domin beyimata shaidar qazanta ba,
D'akinsa ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fito ya nufi kitchen yayi mamakin ganin bata dafa komai ba,,
tun chips d'in da tayi na safema yananan bataciba"
parlor ya fito ya zauna da niyyar yayi banza da ita,
se Kuma ya kasa domin yariga ya saba da motsinta a kusa da shi duk da babu shiri a tsakaninsu amma yanajin takura sosai idan bejitaba.
Rabu da ita kawai yanzu kana nemanta zata nemi renaka ta d'auka ka damu da ita ne,
Zuciyarsa ta fad'amasa '
To idan kuma batada lafiya ne fah?
Idan wani abu ne ya sameta Kuma fah?
Wata zuciyar ta fad'amasa"
hakanne yasa ya miqe da sauri ya nufi d'akin ta, se da ya d'anyi jimmm, a bakin qofar "
ya jima yana kallon qofar kafin ya tura a hankali ya shiga da sallama.
A kwance a tsakiyar d'akin yatarar da ita, daga ita se d'an qaramin towel, a d'aure a jikinta, da alamar wanka ta fito bata canza kaya ba,
jin yadda ta amsa sallamarsa dakyar ne yasa yayi saurin qarasowa wajen da take kwance riqe da cikinta,,
yakai hannunsa ya ta'bata se yaji jikinta ya d'au zafi kamar wuta'
da sauri ya d'ago ta yayimata masauqi akan gado ya juya ya fita,
be jima sosai ba ya dawo d'auke da robar ruwan sanyi da d'an qaramin towel, a hannunsa "
ya ajiye ya tsoma towel, d'in a cikin ruwan ya cire ya matse ya fara d'aura mata a jikinta a hankali,
Se da yaji zafin jikin ya sauqa sosai, sannan ya miqe ya koma d'akinsa ya d'auko magani ya bata Tasha,
Waldorf d'inta ya bud'e ya d'auko wata doguwar riga ruwan powder marar nauyi, ya juyo ya kai hannu ze zare towel d'in jikinta"
Saurin riqe hannunsa tayi tana qara zaro manyan idanunta, magana takeson yi, amma se tayi shiru tare da sakemasa hannunsa ta rintse idanunta '
saboda wani mugun kallo da ya aikamata, se da hantar cikinta ta kad'a,
Tanaji ya cire towel d'in, sannan ya d'auko rigar ya sakamata ya gyara kanta akan filow "
duk se taji wata kunya ta mamayeta, kasa d'aga ido ta kallesa tayi,
Har yakai bakin qofa da niyyar fita se kuma ya dawo"
se da ya qaremata kallo daga kwanciyar da tayi, ya d'an ta'be baki sannan yayi qwafa yace,
ke har kina tunanin kinada abunda zan kalla ne ?
Kinata wani 'bo'b'boye jiki dan renin wayo,
to bari na fad'amiki ko tsirara kike yawo a cikin gidannan wallahi ko kallo baki isheniba balle har naji kin burgeni ,
Sosai maganar tayimata d'aci, amma batace komai ba " har ya fice se kuma ya sake dawowa,,
Yau nawa ga wata?
27 , ta amsamasa ba tare da ta kallesa ba, ya d'an qara matsowa kusa da ita,
Yau kinyi baqo ne?
Kallonsa ta danyi cikin rashin fahimta, baqo?
Baqo Kuma?
Ta mai maita cike da mamaki,
Ganin kamar bata fahimci abunda yake nufi ba ne yasa yace,
baqonki na wata nake nufi, domin naga yaune ranar zuwansa"
duk da kunyar da takeji kamar qasa ta tsage ta shige ciki, be hanata kallonsa da mamakiba,
Waya fad'amaka?
Tayi tambayar ba tare da ita kanta ta shirya yiba,
tashi kawai yayi ya fice daga d'akin ba tare da ya sake cemata komai ba.
Bayan kamar 40 , minutes da fitarsa ya sake dawowa d'auke da ledodi,
ya ajiye ya fita ya nufi kitchen "
plate ya d'auko ya sake dawowa cikin d'akin ' bata motsa daga yadda takeba har yaje ya dawo,
Take away ya ciro ya bud'e ya juye abincin a plate,,
jollof d'in shikafa ne me wadataccen mai da kayan had'i se rabin kaza,
ya miqamata hannu alamar ta saka nata a ciki,,
kallon hannun ta d'anyi batayimasa musuba ta d'aura hannunta a cikin tafin hannunsa"
ya janyota ta tashi zaune ya miqamata abincin .
Duk da yunwar da takeji amma se taji bazata iya cin abincin ba saboda yadda ya kafeta da ido '
loma biyu tayi ta ture plate d'in gefe.
Me kike nufi?
Ya fad'a yana 'bata fuska,
na qoshine yaya ta amsa muryarta na rawa.
Had'e rai ya sakeyi sosai fuskarsa babu wal Wala, yace"
Zakici ne ko sena d'uramiki da kaina?
Ganin fuskarsa babu annuri ne yasa dole ta janyo plate d'in, tafara tura abincin tana hawaye "
Se yaji gaba d'aya ya takura da kukanta, besan meyasa yakejin bayaso yaga tana kuka ba.
Bayan ta gama cin abincin yasa hannu a d'ayan ledar ya ciro magani, ya 'balla ya miqamata har lokacin be d'auke idanunsa daga kanta ba.
Banason magani yaya wallahi banaso, dan Allah kayi haquri ka kyaleni gobe da safe zan warke,
Ta qarasa tana qara fashewa da kuka me qarfi,,
haka kawai se ya tsinci kansa da son rarrashinta"
a hankali ya miqa hannunsa ya janyota jikinsa sosai ya riqeta yana shafa gashin kanta '
se taji bataso ya rabu da ita saboda haka ta qara shigewa jikinsa sosai tana kuka" har cikin ransa yakejin kukannata
Da gaske banason wannan kukan,
ya fad'a yana shafa fuskarta da hawaye ya gaba wankewa.
Sosai tayi mamakin ganin yadda yake kula da ita toh kodan yaga banida lafiya ne?
Tayiwa kanta wannan tambayar amma a fili se tace '
Zan dena yaya " amma wallahi banason magani "
kisha maganin kodan lafiyarki please,
Yayi maganar cikin wata muryar da ko shi kansa be ta'ba sanin yanada ita ba '
ciwon ba wani me tsanani bane dama nasabayi duk qarshen wata,
tayi maganar tana qara 'boye fuskarta a cikin qirjinsa wai ita a dole kunya takeji.
Shikuma haka yayita aikin lallashinta dakyar ta kar'bi maganin tasha ,,
se da yayimata alqawarin zasuje su gaida ammi da Abba idan ta samu sauqi kafin ta kar'ba Tasha.
Ya sake kwantar da ita akan gadon yaja bargo ya rufeta sannan ya kashe wutar d'akin ya fita yajamata qofa,
Se da ta tabbatar yabar 'bangarenta sanna ta sauqo daga kan gadon ta janyo ledar da taga ya ajiye a gefen gadon ta bud'e.
Qaton ledan pat ta gani, irin me guda 40 d'innan "
da sauri ta saka hannu ta rufe fuskarta tana dariya kamar yana ganinta,
Seda ta d'auka ta shiga toilet ta gama kintsawa sannan ta fito ta fad'a a saman gado tana murmushi '
A fili ta furta Allah sarki yaya na ashe yanada tausayi sosai,
gaskiya Nusaiba take fad'amin da tace yanada kirki"
haka tayita tunaninsa tana mur mushi wanda ita kanta idan aka tambayeta dalilin yinsa zatace bata sani ba.
Daga 'bangaren Rafiq Kuwa,
tunda ya fita daga d'akinta ya nufi nasa se da ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya saka kayan bacci "
shima kwanciya yayi a saman gadonsa yana tunanin abunda ya faru, dama haka yarinyarnan takeda rigima,
ya rasa meyasa yanzu yake yawan Tinata ko yana asibiti haka kawai se yaji yanason ganinta kokuma jin muryarta ko da a waya ne "
amma be ta'ba yadda ya kirataba domin shi bega amfanin hakanba, tunda ba son juna sukeba,
Haka kawai ya tsinci kansa dayin dariya lokacin da ya tino kalan rigimarta'
A hankali ya shafa saman qirjinsa yana mur mushin,,
" I like you "
Ya furta a hankali yana lumshe idanunsa, se kuma yayi saurin bud'ewa yana furta,
Noooooo.........,..
Baze ta'ba yiwuwaba, ni ko kad'an bana sonta Kuma abunda nayimata yau kawai na sauqe nauyi ne saboda naga batada lafiya"
haka ya kusan shafe daren yana tunanunnuka kala kala,
mafi yawa a cikin tunanin na Mahanur ne,,
idan ya tino wasu abubuwan da takeyi kawai se ya tsinci kansa dayin mur mushi '
Da safe , Mahanur batajin ko wani irin ciwo,
amma se taji yauma tanaso ya kasance tare da ita ko babu komai tanajin dad'in kasancewa waje d'aya da shi ba tare da sunyi fad'a ba"
saboda haka qin miqewa tayi daga kan gadon haka taci gaba da kwanciya tana tunanin anya ze tina da ita ya qara shigowa kuwa?
Bata qarasa tunanin ba taji ya turo qofar da sallama,
tayi saurin rufe idonta kamar me bacci '
yakai kusan 2 minutes yana kallonta kafi ya zauna a bakin gadon yasaka hannunsa a hankali ya d'ago ta yana kiran sunanta,
Kamar wata me baccin gaske tayi miqa tana salati, ya shafa fuskarta,
Ya jikin naki?
Da sauqi.
ta amsa sannan tace ina kwana,
Kamar baze amsaba se kuma ya amsa lafiya qalau '
kin warke d'in ne ko kuma se kinsha maganin?
Shiru ta d'anyi sannan tace eh na warke dan Allah karka bani maganinnan banaso na jiyanma ya isa,
Yasan bata gama warkewaba amma sanin hawayenta a kusa yake idan ya matsa zata iya yimasa kuka yasa ya kyaleta,,
ya fice daga d'akin ya nufi kitchen " dan nemamusu abunda zasuci.
Tea kawai ya had'a da wainar kwai se soyayyiyar plantain,
bazaka ta'ba cewa shi yayi wannan girkinba dan bazaka kawo tunanin ya iya girki bama,,
Ya kawomata nata....
be bartaba har seda ya tabbatar taci sosai sannan ya tattare kwanunkan da zummar miqewa ya fice,
Se tayi sauri ta riqe hannunsa tana kiran sunansa "
yaya Rafiq.
Menene?
Ya fad'a yana dawo da dubansa gareta,
am nace yaune zamuje mu gaida su ammi?
Shiru yayimata bece komai ba tasake damqe hannunsa please yaya,
No,
ba yauba se kin qara samun sauqi"
nariga na samu sauqi dan Allah muje yau,
toh kibari sae gobe muje kafinnan kin qara war warewa.Please yaya ta fad'a idonta na cikowa da hawaye, sanin yana bata fuska zatayita damunsane yasa ya had'e rai kamar be ta'ba dariya ba,,
Se gobe nace idan kuma kika matsamin to gobenma baza a jeba wallahi zan fasa,
toh kawai tace sannan ta sakemasa hannunsa yanufi qofar ya fice.
Inin ranar gabaki d'aya haka tayishi tanaji kamar taja lokaci ya wuce dan ganitake kamar gobe bazatayiba,
haka tayita d'oki " kayakam ta canza sunfi kala goma duk wanda ta saka se taga kamar beyiba .
Be shigo gidanba se da akayi insha ya shigo riqe da ledodi ya miqamata d'aya sannan yace taje ta d'auko plate,
guda biyu 'ta d'auko ta miqamasa d'aya ta zauna ta janyo nata ta bud'e '
gasasshiyar kaza ce qatuwa da chips, ta juye ta fara ci shima nasa ya fara ci babu wanda ya cewa kowa komai.
Can kuma kamar an tsikari Mahanur tace yaya,
inade bakamantaba ?
se kuma tayi shiru menene?
Yayi tambayar ba tare da ya kalleta ba.
Kace gobe zamuje gida "
nasani ya fad'a har yanzu be dago ya kalleta ba hakanne yabata damar cigaba da magana,
amma de da wuri zamu tafi koh? Tun 7 zamu tafi,,
Se a lokacin ya d'ago ya kalleta yace 7 fah kikace lokacin ko tashi a bacci ai basuyiba,Nasan sun tashi wallahi kasan ammi bata komawa bacci idan ta tashi tun asubah"
yasanta da shegen surutu da fitinar tsiya idan be amsamataba zatayita fitinarsane musamman da batada lafiyarnan yaga ta qaro rashin ji kamar ma tadena jin tsoronsa,
saboda haka yace kawai ki shirya da zarar natashi daga bacci zamu tafi.
Jitayi kamar tayi tsalle ta rungumeshi dan rabon da suje gida tun wata rana da sukaje da dare suka gaidasu ammi,
Wani tsalle ta daka ta miqe ta shige d'aki da gudu tana dariya, se abu takeyi kamar wata qaramar yarinya"
shikam da kallo kawai yakebinta yana dariya "
dan zuwa yanzu ya gama tabbatarwa a d'an zaman da sukayi yariga ya kamu da soyayyar ta me zurfi, amma besan ta ina ze fara mata ba,
gani yakeyi kamar qas qanci ne yafito ya fad'amata abunda yakeji a kanta.
Haka ya miqe ya nufi d'akinsa wani abu me wuyar fassara yana nuqur qusar qasan zuciyarsa.
Da safe tun 6 ta tashi ta gyara gidan ta shirya tsaf cikin wasu riga da scate d'in atamfa,
sun d'an kama jikinta sunyi mata kyau sosai kamar a jikinta aka d'inkasu"
ba wata kwalliya me yawa tayiba, powder kawai ta shafa ta murza man baki ta d'auko wani mayafi d'an dadai bashida wani girma ta yafa '
tayi kyau sosai kamar kasaceta ka gudu,
Ta zauna tana jiransa a parlor, amma taga har 9 be fitoba gabaki da'ya ta qosa taga sun tafi amma taga alamar bema tashiba saboda haka ta miqe ta nufi d'akinsa dan ta dubashi.
A hankali ta tura qofar tashiga de de lokacin da yake miqa alamar lokacin ya tashi daga bacci,
tsaye ta d'anyi a bakin qofar ganin ko riga babu a jikinsa"
se ta juya zata fice,
Zo nan ya fad'a cikin muryarsa da take cike da bacci '
se da tad'an tsaya kamar bazata shigaba kafin ta tattaro qarfin halinta ta sakai ta shiga cikin d'akin .
Seda yasakeyin miqa sannan ya zubamata Ido yana ganin yadda tayi kyau sosai ji yake kamar ya d'auketa ya sakata a cikin qirjinsa,
se da yad'an jima yana kallonta kafin yace,
Menene?
Turo baki ta d'anyi kamar zata fashe da kuka,
se yasakejin ta qara burgeshi sosai,,
yaya 09:40 fah har yanzu bamu tafiba kuma kace da wuri zamu tafi.
Ta qarasa maganar kamar zata fashe da kuka,,
Se da yad'an yi mur mushi sannan ya miqa mata hannunsa,
a tunaninta yanasone ta temakamasa ya miqe ne saboda haka se itama ta miqamasa hannu da niyyar d'agoshi "
Da qarfi ya fizgota ta fad'a jikinsa '
Damm....... Damm....... "
Zuciyata ta bada da qarfi.
Qoqarin miqewa take amma ta kasa saboda irin riqon da yayimata,
a hankali yace toh dama ba nacemiki sena tashi daga bacci zamu tafi ba?
Da kyar ta tattaro jarumta cikin rawar murya tace,
amma ai da wuri kace zaka tashi.
Da sauri yad'an zaro idanu ni d'in?
Yaushene na fad'i hakan?
Yayi maganar yana nuna kansa da hannunsa,
Kaine ka fad'a mana"
ta fad'a hawaye na qoqarin zubowa,
Y'ar dariya yayi har seda taji sautin dariyar ya kai hannu ya shafa fuskarta yace '
okay, bari na shirya se nazo mu tafi just 50 minutes,
50 minutes?
Ta fad'a da sauri tana dafe qirji tare da zaro idanu waje,
besan sanda dariya ta kubcemasaba ganin yadda tayi kicin kicin da fuska kamar ya fad'amata saqon mutuwa.
Seda ya gama dariyar sannan yace sorry, I mean 15 minutes.
Se a lokacin ta d'anji sanyi a ranta ta sauqe ajiyar zuciya har seda yaji"
seda ya qara kallonta ya shafa fuskarta yana mur mushi sannan ya miqe ya shige toilet.
Ita kuwa ta fito ta zauna a parlor,
ba a d'auki wani lokaci me yawa ba ya fito sanye da wata farar boyal, tayi matiqar kar'bar , brown d'in fatarsa sosai "
ya saka wata baqar hula a saman kansa wacce ta qara masa kyau da kwarjini,
se wani zuba qamshi yake kamar wani sabon ango.
Batasan sanda ta kafesa da ido ba ko qiftawa batayi,
firgigit tayi jin muryarsa yanacewa '
madam zamu tafi ne kokuma in nemi guri in zauna har sekin gama qarewa Kyau na kallo kin fara hango munina ?
Wata iriyar kunya ce ta lullu'beta da sauri ta saka hannunta duka biyu ta rufe fuskarta tana dariya "
batayi auneba taji hannunsa a saman nata yana qoqarin janyesu daga kan fuskarta,,
da sauri ta kallesa suka had'a ido tayi saurin sunkuyar da kanta qasa, muje?
Ya fad'a yana kallonta kai ta d'aga masa alamar eh,
se kuma yad'an 'bata fuska yace, a haka zaki tafi?
Da sauri ta kalli kanta sannan tace eh menene?
Ki cire mayafinnan ki saka hijabi,
Haba yaya dan Allah meye ne a ciki idan nasaka,
Bata qarasaba ya rufeta da fad'a,
wai me kike tunanine?
Kin d'auka har yanzu kinada damar yin irin shigar da kikaga dama ki fita waje ko wani qato ya qarewa halittarki kallo ne?
Ko a tunaninki har yanzu ke budurwace da zaki fita a yadda kikeso?
Idan kin manta wacece ke to bari na tina miki ked'in yanzu matar aure ce,kuma matata,
saboda haka yazama dole yanzu ki suturta jikinki "
ki koma kisaka hijabi yanzu.
Toh kawai tace ta koma d'aki bata jimaba ta fito sanye da hijabi ruwan powder yayi matiqar yimata kyau sosai '
se yaga hartafi yimasa kyau ma sama da d'azu.
Cikin sanyin jiki ta qaraso gabansa a d'an tsorace dan taga alamar yananan da baqin halinsa be canzaba .
A tunaninta ze qara rufeta da wani fad'an ne amma ga mamakinta se taga kamar ba shi yagama yimata fad'a yanzu ba,
Tana qarasowa ya miqe ya kama hannunta a hankali ya d'aura akan cikinsa yana lumshe idanunsa a hankali,
" I'm hungry "
Ya furta daga can qasan maqoshinsa sannan ya bud'e idanunsa ya zubasu akan fuskarta,
a d'an tsorace ta kallesa tana d'an zaro ido.
Dan Allah kabari idan munje se kaci wanda ammi ta dafa please yaya yaukam karkace nayimaka girki dan Allah nimafa kaga banci komai ba "
Ganin yayi shiru ne yasa a hankali ta zame hannunta daga kan cikin nasa tace shikenan toh bari na dafamaka kaid'in kaci tukunna se mu tafi.
Tana kaiwa nan ta juya jiki babu kwari zata nufi kitchen,
da sauri ya riqo hannunta "
no,
ba ke zaki dafa ba.
da sauri ta juyo ta kalleshi to kaine zaka dafa?
A'a ya fad'a yana qara janyota jikinsa, yace zaki rakani ?
ina?
Ta tambaya tana kallonsa ' se da ya juya ya fara tafiya sannan yace, ina kike tunani?
Yunwa fa nacemiki inaji, idan banci abinci ba to taya zan iya kaimu?
Batace komai ba tabi bayansa har suka isa harabar gidan suka shiga mota.
A qofar wani babban restaurant, yayi parking suka shiga yayimusu order,
sosai yaci ya qoshi itakam ko ci da yawa batayiba saboda ta matsu,,
damuwarta kawai taga sun isa gida" haka suka fito daga cikin restaurant, d'in suka shiga mota suka hau hanya'
Tunda suka kama hanya babu wanda yacewa wani uffan,
tafiya sukeyi kowa da abunda yake saqawa a cikin ransa,
Seda suka shiga harabar gidan ammi yayi parking, da sauri ta juya zata bud'e motar ta fita yayi saurin dakatar da ita , ta hanyar riqe hannunta "
da sauri ta juyo,
Seda yad'an quramata ido sannan yace,
idan Abba da ammi suka tambayeki yanayin zamanmu me zakice?
Jimm ta d'anyi sannan tace lafiya qalau babu wata matsala,
Kallonta Yayi sannan yace,
kin tabbata ta d'agamasa kai alamar eh,
Se ya miqomata hannu yace promise?
Promise ,
ta fad'a tana d'aura hannunta akan nasa alamar tayimasa alqawari.
Mur mushi ya sakarmata itama tayi mur mushi ta fito se shima ya fito suka nuci cikin gidan.
Suna shiga Mahanur ta nufi wajen ammi da gudu ta rungumeta, tanada dariya '
da gaske tayi missing d'insu sosai,
seda ta shiga suka gaisa da Abba sannan ta dawo suka zauna a parlor ita da ammi suna hira "
Nusaiba ta fito tana tura qaton cikinta a gaba"
gaba d'aya qafafunta sun kumbura ba iya qafafuba gabaki da'ya jikinta har fuskarta a kumbure,
Mahanur ta sau baki tana kallonta, kekumafa daga ina?
Guri ta samu akan carpet ta zauna batacemata komai ba,
ammi tace kwananta uku a gida batajin dad'ine likita ya hanata aiki, saboda tariga ta shigo watan aihuwarta,,
shiyasa ya kawota har seta aihu ta koma.
Mahanur ta kalli Nusaiba tana dariya tafara tsokanarta "
Me ciki wallahi banison sunannan me ciki wallahi zamu 'bata da mutum me ciki, gamunan muna tura ciki ciki yana turamu.
Dariya Nusaiba tayi tace wallahi zan rama ba ayiwa motar gawa dariya "
haka sukayita hira suna raha har, Zarban yazo yafara taya Mahanur sunata tsokanar Nusaiba,
bayan sallar insha Rafiq ya dawo ya d'auketa badan taso ba amma tasan ko tace abarta ta kwana ammi da Abba bazasu bartaba haka tabiyosa suka dawo gida,,
Babu lefi sosai ya rage abunbuwan da yakeyimata dan wani lokacin har hira yake zaunawa sud'an ta'ba.
Sosai itama tafara sabawa da shi duk sanda ya fita se taji tanaso ya dawo ko da bazasuyi magana ba '
shima daga nasa 'bangaren hakane, jiyake yanzu bayaso yayi nisa da ita ko kad'an"
ranar litinin yana asibiti zaune yake a cikin office d'insa,
gabaki da'ya hankalinsa nakan screen d'in wayar sa,,
ya zubawa wani hotonta Ido yanata kallo, yanajin wani irin soyayyar ta tana azal zalar, qasan zuciyarsa,
yariga ya yanke shawarar bayyanamata soyayyar sa a yau "
ze ajiye duk wani girman kansa ya fad'amata irin soyayyar da yakeyimata ko ze samu sauqin abunda yakeji a cikin zuciyarsa "
da sauri ya shiga cikin contact d'insa yafara ja, har seda yazo kan number ta kamar ze kira se wata zuciyar ta hanasa.
Zanyimata sayayya yau na koma mata dashi sena fad'amata,
yafad'a a cikin ransa sannan ya kashe wayar yana mur mushi I love you so much my only wife.
Tana tsaye a kitchen hannunta riqe da wuqa tana yanka albasar da zatayimusu abun karyawa,
wayarta tayi qara, da sauri ta duba ta saki mur mushi ganin sunan ammi a saman screen d'in '
da sauri ta d'aga ta kara a kunnenta tana murmushi,
bayan sun gaisa ammi ta fad'amata cewar,
Nusaiba ta sauqa lafiya ta haifi kyakkyawar baby girl"
ta shirya Zarban ze biyo ya d'auketa su tafi asibiti,
Wani irin wurgi tayi da wayar ta daka tsalle tana dariya,,
Ta aihu, ta aihu, ta aihu, tashiga mai maitawa tana tsalle kamar wata qaramar yarinya,
da gudu ta nufi d'akin Rafiq, wuqar tana hannun domin batasan ya tafi office ba saboda da wuri yafita yaga tana bacci shiyasa bekoyimata sallama ba ya fita.
Tana shiga d'akin ta tarar baya nan har zata juya ta fita se taga d'akin a wargaje,
da sauri ta dawo dan ta gyara, wata farar takarda ta hango akan dress mirror '
se taji qirjinta ya buga da qarfi"
takai hannunta ta d'auko takardar a hankali ta bud'e "
da sauri ta ja da baya qirjinta ya bada wani irin sauti da qarfi kamar sauqan aradu,
wasu hawaye masu zafi da ciwo suka shiga gangarowa daga idanunta kamar an bud'e famfo.
Jitayi numfashinta yana shirin barin gangar jikinta saboda tashin hankalin abunda ta gani a jikin takardar "
Ni Aliyu ma aruf bommoli, na saki matata Fatima Ahmad bommoli, saki d'aya sakamakon anyimana aurene ba tare da munason junanmuba,
bata ta'ba sanin ta kamu da soyayyar Rafiq sosai ba se yau"
da sauri ta juya jiri na d'ibarta ta fice daga d'akin hannunta na qanqame da takardar,
ko gani batayi sosai haka ta fito parlor tana gauraya hanya,,
Batayi auneba qafarta ta hard'e wani irin gigitaccen ihu tasake lokacin ta takai qasa"
kanta yayi wani irin mugun dakuwa a qasa,
wuqar hannunta tayiwa kanta masauqi a gefen cikinta '
Kafin kace me jini ya 'balle a gefen cikinta da goshinta, gaba d'aya ya wankemata fuska.
Zarban ne ya shigo cikin parlorn, da sallama fuskarsa d'auke da mur mushi "
Wani irin mugun burki yaja ya tsaya,
Da qarfi qirjinsa ya bada wani irin sauti Damm... Damm....,
hannu ya kai ya ta'ba fuskarsa dan ya farka daga mummunan mafarkin da yakeyi amma seyaga kamar ba mafarki bane,
domin yaga har yanzu be bud'e Ido ba.
Hakanne yasa ya nufo inda take da sauri dan yaqara tabbatarwa ido biyu yake kallon Mahanur a cikin wannan mawuyacin halin "
Gata a kwace kamar gawa dan ko motsi batayi ga jini yanata tuttud'owa daga jikinta kamar anyanka sa.
Da sauri ya kai hannu ya d'agota ya juya da gudu yafita yasakata a mota har lokacin wuqar tana soke a gefen cikinta '
se a lokacin yayi arba da takardar da take damqe a hannunta da sauri yasa hannu ya zare ya bud'e ya fara karantawa"
seda ya karanta yakai sau bakwai amma har yanzu be yadda da abunda yake gani a jikin takardar ba,
wata qila hausarsace ta su'buce masa har ya kasa karanta takardar de de,,
Kokumade ya d'imauce da ganinta a hakane shiyasa ya kasa karantawa da kyau '
saboda haka yasakata a aljihunsa sannan yashiga motar yaja yafice daga gidan da wani mugun gudu kamar ze tashi sama.
Rafiq kuwa tun 3 na yamma yafito daga asibiti ya wuce super market,
sosai yayimata sayayyar abubuwa ya nufi gida zuciyarsa cike da farin ciki da fatan itama zatayi na am da soyayyar sa"
Yana isowa gate d'in gidan qirjinsa ya tsananta bugawa haka kawai besan dalilin fad'uwar gabansaba,
amma se ya alaqanta hakan da,
wataqila saboda yau ya quduri niyyar fad'awa wata kalma me tsadar da mata da yawa suke son jinta daga garesa amma ko a cikin wasa be ta'ba furtata ba.
Hakade ya daure ya tura qofar parlorn '
wani irin wurgi yayi da ledodin sayayyar, ganin jini a malale a tsakiyar parlorn '
me ya sameta?
Ya aikowa kansa tambayar yana shigewa cikin bed room d'in ta a guje,
sede ko alamar ta be ganiba ya tura qofar band'aki, amma bata ciki da gudu ya shiga d'akinsa yana nemanta "
amma ko alamarta bejiba, hakanne yasa yashiga kwallamata qira yana duba ko ina "
amma babu ita babu alamar amsarta,
cikin sauri ya janyo wayarsa yashiga kiran layinta amma se yaji qarar wayar a bakin kitchen,,
Gabaki da'ya ya gigice baya cikin hayyacinsa"
da gudu ya fito ya shiga zagaye lungu da saqo na gidan yana kiran sunanta,
ganin babu alamar ze ganta ko yaji ta amsa ne yasa da gudu ya shiga motarsa yayimata wata muguwar fizga,
a d'ari uku da hamsin ya nufi gidansu dan yasan koda tafiya tayi batada inda zata nufa se can '
Yana isa ya fito da gudu ya shiga cikin gidan ko rufe motar be tsaya yiba,
kai tsaye ya nufi d'akin ammi sede yatarar batanan,,
hakan yasa ya ciro wayarsa yashiga dokamata kira amma babu amsa "
hakan ne yasa yafara Kiran layin Abba shima be amsamasaba.
Seda yayimusu kusan mist call 140 amma babu wanda ya amsa,
hakan yasa ya fara kiran layin Zarban,
seda yayimasa kira hud'u a na biyar d'in ya d'aga nanma seda takusa katsewa'
hello Zarban naje gidana naga matata batanan nazo gida natarar babu kowa inata kiran ammi da Abba babu wanda ya amsamin meya faru?
Dan Allah idan akwai wata matsalarne kafad'amin babu wanda nasamu balle yabani wata makama.
Seda Zarban yayi kamar baze amsaba se kuma yace wace matar taka?
Dama ashe kanada wata matar ne bayan wacce ka walaqanta ka lalatamata rayuwa tun da yarintarta?
Sosai tambayar da Zarban yayimasa ta jijjiga tunaninsa amma seya dake,
Okay yanzu su ammi suna ina?
Muna asibitin me zare,
yanakaiwa nan ya kashe wayarsa Rafiq yayi qoqarin sake kira amma se yaji layin baya tafiya "
Da sauri ya juya ya shiga motar ya nufi asibitin, me zare gabansa na fad'uwa.
Cikin emergency room ya nufa da gudu gaba d'aya baya cikin nitsuwarsa,
waige waige yakeyi yana duba inda suke se can ya hangosu gabaki da'ya a ta waje jikin wata bishiya,,
be qara tsinkewaba seda yaga ammi tana kuka,
na shiga uku karde ta mutu da baqin ciki na ?
Ya furta a fili yanajin yadda qafafuwansa suke qoqarin kasa d'aukarsa '
dak'ayar yaja qafarsa ya nufi gurinda suke kamar wanda aka zarewa laka yanaji kamar anyimasa mugun duka ,
saboda yadda ga'bo'bin jikinsa sukayi sanyi,
Yana isowa gaba d'aya suka zubamasa ido amma babu wanda yacemasa uffan,
cikin qarfin hali ya bud'e baki ya fara magana "
Ammi meyake faruwa ne ?
Ko kallon inda yake ammi batayiba balle yasakaran samun amsa daga gareta,
haka ya gama maganarsa ganin bazata bashi amsa bane yasa ya juya wajen Abba,,
Abba meyake faruwa ne Abba na ?
Gabaki da'ya naga,
shiru yayi saurin yi saboda wasu tagwayen maruka da Abba ya jeramasa ' lafiyayyu
tass, tass, da sauri ya dafe kuncinsa, yanajin wani irin azaba na ratsashi.
Kafin kace me jini ya yanke ta hancinsa saboda Marin da Abba yayimasa bana wasa bane.
Burinka ya cika yau kayi nasarar lahanta rayuwar mareniyar Allah,
Aliyu wani irin lefi Fatima ta aikata maka wanda kakejin bazaka iya yafemataba Kuma kake hukuntata a kai tun tana qarama?
Me ta tare maka a cikin wannan duniyar da har kakejin zaka iya neman rayuwarta?
Nacika wasiyyar d'an uwa na ta hanyar auramaka ita da tunanin zaka janye qudurin ka manta da qiyayyar da kakeyimata,
ka rungumi qaddara ka riqeta a matsayin matarka Kuma y'ar uwar ka"
nayi tunanin na isa da kai kamar yadda na isa da ita" shiyasa har na had'a aurenka da ita,
amma a yau ka nunamin ban isaba ban kai na yankewa rayuwarka hukunci ba,
babu komai ka saketa ' ni zanci gaba da zama tare da ita tunda kayan nama baya kashe kura,,
Kaje babu komai Allah ze saka mata Kuma ze kawo mata wanda ze iya riqeta tsakaninsa da Allah "
bazanji haushi dan ka saketaba domin ba saboda tayi kwantai aka auramaka ita ba,
amma wallahi idan kasake ka kashe y'ar mutane to wallahi Aliyu tabbas senayi shari a da kai .
Yana kaiwa nan ya juya yabar gurin da sauri.
Rafiq yaji kalaman Abba kamar sauqan aradu a kunnuwansa,
ya kasa fahimtar kan maganar Abba gabaki da'ya kansa ya kulle,,
juyowa yayi dan ya roqi ammi tayimasa bayanin abunda Abba yake nufi"
amma se itama ta juya ta nufi cikin d'akin da Abba ya shiga ba tare da tasake koda kallonsa ba.
Zarban ganin ya juyo kansa da niyyar tambayar sa se shima yayi saurin miqewa zebi bayansu "
cikin qarfin hali, Rafiq ya riqe hannunsa.
Kaima gujemin zakayi?
Bazaka iya fad'amin komai ba?
Kafad'amin abunda Abba yake magana a kai wallahi bansan komai ba '
haba Zarban, kaji tausayina mana ina kukeso nasa kaina ne?
Koda kaima zaka tafi aqalla de katemaka kayimin bayanin abunda yake faruwa .
Abunka da d'an uwa se Zarban yaji Rafiq yayi matiqar bashi tausayi duk da yanajin haushinsa "
takardar kawai ya zaro daga aljihunsa ya miqamasa sannan ya nufi qofar d'akin da su ammi suka shiga,
qarfin halin bud'e takardar yayi besan sanda ya sulale ya durqushe a gurinba.
Ya salam,
innalillahi wa inna ilaihir raji 'un, ya hayyu ya qayyum, yashiga nanatawa kafin ya fashe da wani irin kuka me qarfi kamar wani qaramin yaro.
Seda yayi me isarsa babu wanda ze rarrasheshi ,
Snnan ya tashi yanajan qafarsa dakyar saboda nauyin da yaji ta masa "
d'akin da su ammi suka shiga shima ya nufa dakyar yake iya tafiya.
Yana shiga ya hangosu a gaban wani gado da sauri ya nufi gadon,
Mahanur ya gani a kwance babu alamar numfashi a jikinta tana miqe kamar wata gawa"
ga wani tafkeken nad'i da akayimata a goshinta na bendeji,
Sannan gashinan a gefen cikinta ma'
hannunta ya riqe yana wani irin kuka me ban tausayi tun daga can qasan qirjinsa kukan yake fitowa,
ya d'aura kansa a gefen gadon.
Muryar Abba ce tasa yad'an tsagaita kukan ya d'ago yana kallonsa cike da tashin hankali ,,
me kuma kazo kayimata a nan?
Ka zone ka qarasa ta tunda kaga bata mutuba ?
Sosai kalaman Abba sukayimasa ciwo amma bece komai ba '
se kawai ya mayar da kansa jinkin gadon yacigaba rera kukansa kamar mace '
Abba yacigaba da magana kariga kakawo qarshen ko wace alaqa,
idan na fahimta ganintane gaba d'aya bakasonyi "
To burinka ze cika bazaka qara ganintaba balle har ka kusanci inda take kokuma ita ta kusanceka "
sannan kuma ka tashi kafita kabawa mutane guri kar ka qara zuwa nan wajen,
wallahi Rafiq idan nasake ganinka kazo asibitinnan senayimaka walaqancin da zakayi mamaki,,
Se a lokacin ya sake hannunta ya juyo dak'yar ya durqusa a gaban Abba yasaka hannayensa duka biyu ya riqe qafar Abba.
Abba dan girman Allah kayi haquri karka rabani da matata ina qaunarta wallahi ban shirya rasataba dan Allah Abba,
kaji tausayina kar kayimin hukuncin da ze tarwatsamin rayuwa,
da ita kad'ai na saba bazan ta'ba maye gurbinta da wata macenba 'Abba yaja wani uban tsaki yace nade fad'amaka idan nasake ganinka anan wallahi sena baka mamaki ko yanzu ma dakaganka a nan saboda Fatima bata far fad'o bane ,
idan har ta farka ta fad'amin cewa da sa hannunka a cikin wannan ciwonnata, wallahi senayi shari a da kai na d'aureka,,
maganata ta qarshe ' kar kasake na dawo nasameka awajennan senasa security's sun fitarmin da kai.
Yana gama fad'ar haka ya fizge qafarsa da qarfi yafita daga d'akin ko juyowa beyiba balle yaga irin halinda Rafiq yake ciki .
Betashi daga durquson da yayiba yacigaba da kukansa,
seda yagama kukan ya miqe ya fita batare da yacewa ammi ko uffan ba '
dan yariga yasan koda yayimata magana ma, bazata saurareshiba.
Yana isa gidan kai tsaye d'akin Mahanur ya nufa '
A qasa ya zauna ya jingida da jikin gado " ya takure jikinsa ya had'a kansa da guiwarsa ,
ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya har yana shid'ewa yana fad'in.
Allah kasani inasonta kuma na yadda da qaddarori da jarrabawarka,
ya Allah karka qadartomin jarrabawar da bazan iya cinyewa ba,
Allah kasani idan ka jarabceni da rashinta bazan iya jurewaba.
Sosai yake kukan kuma da qarfi gabaki da'ya zuciyarsa ta cunkushe da tunanunnuka kala kala wanda ya rasa wanne zeyi Kuma wanne ze bari "
Damuwarsa shine yasan taya akayi su Abba sukaga takardar sakinnan kuma me ya jefa Mahanur a cikin wannan mawuyacin halin,
a iya saninsa idan bayanan ita kad'ai take rayuwa a cikin gidan "
kuma a iyakar saninsa da ita yasan tanada tsoro sosai Kuma tana matiqar son jikinta '
babu yadda za ayi ta iya cutar da kanta koda zuciyarta ta tana fad'amata tayi hakan.
Ya zama dole su Abba su zargesshi da aikata mata hakan,
yariga yasan koda samace zata had'e da qasa su Abba bazasu ta'ba yadda besan komai a kai ba"
itace kad'ai zata iya war waremusu wannan rashin fahimtar,
gashi kuma bata cikin yanayin da zata iya hakan,
A haka bacci ya d'aukesa ba tare da saninsaba.
Da safe yana tashi, a cikin toilet d'inta yayi wanka sannan ya tafi d'akinsa ya canza kaya '
ya fito yashiga kitchen tea kawai ya had'a ya d'auko bread ya zauna yafara sha se yaji yayimasa d'aci sosai,
amma haka ya daure yacigaba da turawa yanajin kamar zeyi amai.
Saboda yunwar da taketa qwa qular cikinsa,
domin rabonsa da abinci tun safiyar jiya.
Yana kammalawa ya fito ya nufi asibitin '
cikin rashin sa a sukayi kici'bis da Abba yana qoqarin shiga cikin d'akin Abba Kuma yana qoqarin fitowa.
Yad'an risina ina kwana Abba,
kawar da kai Abba yayi ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace,
me ya kawoka nan Rafiq?
Wani busasshen yawun wahala Rafiq ya had'inya sannan yace "
Abba nazo na duba jikin mata ta ne.
Sosai Abba ya had'e rai babu alamar wasa a kan fuskarsa,
Yaushe kuma na zamo abokin wasanka Aliyu?
Idan ban mantaba ina tunanin jiya na fad'amaka cewar kar ka sake zuwarmin nan ,
idan kuma gaisuwace to mun yafeta bama buqatar ta saboda haka kakama hanya kasan inda dare yamaka "
sannan kuma ko bananan idan kayi kus kuren shiga inda Fatima take,
nabawa masu gadin gurinnan umarnin su fitar da kai waje da qarfi ,,idan kuma kayi taurin kai suyimaka duka su fitar da kai,,
yana gama magana yabi ta gefensa ya wuce.
Shikam Rafiq tsaye yayi kamar an dasashi a gurin,
beyi auneba se ji yayi wasu sabin hawaye masu d'umi suna gan garowa akan fuskarsa '
Wani d'an dakali ya nema a jikin d'akin ya zauna '
tun yana iya kuka da hawayensa har ya fara neman hawayen amma ya rasa ,
se wani tuquqi da zuciyarsa takeyimasa se idanunsa da suka kad'a sukayi jazur kamar jini ya kwanta a cikinsu,
tun zamansa ammi tana kallonsa tun yana bata haushi har ya dawo bata tausayi "
abunka da d'a da uwa se taji kamar taje tacemasa yashigo yaga Mahanur,
amma babu damar hakan saboda Abba yace be yafeba idan har ta sake ta barsa ya shiga,,
sannan kuma itama kanta tanaso ya horu ya gane muhimmancin yarinyar,
da wad'annan dalilan guda biyu ta tilasta zuciyata yin banza da shi kamar ma bata ganshiba.
Se wajen 5:36 na yamma Abba ya dawo asibitin "
har yanzu Rafiq na zaune a inda yake tun safe,
Ko kallon inda yake Abba beyiba yasakai ya shige cikin d'akin,,
Har kusan 10:30 na dare ammi ta fito tayi tunanin Rafiq ya tafi amma seta ganshi a zaune a wajen kamar an dasashi"
se taji wani irin mugun tausayinshi ya kamata,
se wani takurewa yakeyi yana rawar sanyi ga iska se kad'awa takeyi ta ko ta ina,,
suma kansu da suke ciki sanyi yayimusu yawa balle shi da yake waje babu rigar sanyi babu bargo, ga iska.
Sannan ga wasu sauraye qatti sun kusa kai quda girma se cizonsa suke "
Ji kawai tayi idanunta' sun ciko da hawayen tausayin d'an nata '
yana ganinta da sauri ya miqe ya nufo inda take,
ammi ina Mahanur?
Ya jikin nata? Ta far fad'o ne?
Kai kawai ta gir gizamasa alamar a'a dan batasonyin magana saboda kar kukan da take qoqarin dannewa ya su'buce mata.
Ze sake aikamata wata tambayar tayi saurin d'agamasa hannu alamar dakatarwa tasakai ta wuce"
komawa yayi ya zauna , seda 11 ta wuce ammi ta dawo riqe da ledar magungunan da ta sayo seda tad'an qaremasa kallo taga ya rame sosai ta shige,
wasu hawayen tausayinsa suna zarya akan fuskarta.
Kusan shafe daren tayi bata rintsa ba saboda tausayin d'an nata,
lokaci zuwa lokaci tana sharar k'walla gashi har lokacin babu alamar Mahanur zata farka,,
Bata qara tsinkewa da lamarin Rafiq ba har seda safiya tayi ta fito ta gansa a gurin a takure '
duk da bacci yake amma se rawar sanyi yake har haqoransa suna had'ewa da juna,
Batasan sanda wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa daga idanunta ba.
Saboda halin da taga yana ciki se taji bazata iya barinsa hakaba saboda haka ta koma ciki ta d'auko bargo tazo ta rufemasa jikinsa,
ta koma ciki tana sharar k'walla, bata Jima da komawa ba se tasake fitowa dan neman abun karyawa '
amma seta samu har ya farka ya takure a cikin bargon yanata kar karwa.
Yana ganinta amma seya kasa tashi daga gurin da yake saboda yadda yakejin wani irin ciwo a cikin jikinsa ,,
yakasa tan tance irin azabayakeji kawai se ya rintse idanunsa ya ciza le'bensa da qarfi hawaye nabin gefen fuskar sa,
Seda ammi tayi kamar zata wuce amma setaji bazata iya ba saboda haka ta dawo ta tsaya a kusa da shi '
har lokacin be bud'e Idanunsa ba " takai hannunta ta ta'ba goshinsa,
wani irin zafi yayi kamar wuta har wani irin huci yakeyi.
Da sauri ya saka hannu ya damqe hannun da ta dafa goshinnasa, dak'yar ya bud'e ido wasu sabin hawaye suka gangaro.
Ammi ina matata take?
Ina Mahanur?
Dan girman Allah kuyi haquri nasan nayi kus kure amma wallahi bazan sakeba,
ammi idan kuka rabani da ita wallahi bansan inda zansa kainaba,
ammi inajin zafi zuciyata kamar zata fashe"
jinakeyi kamar an huramin wuta a cikin qirjina,
Wayyo Allah ammi nashiga uku ina zansa kaina,
ya qarasa maganar da wata galabaitacciyar murya yana qara fashewa da kuka '
ammi ma batasan sanda ta fashe da kuka ba ta rungumeshi a jikin ta,
Abbanku yayi fushi da kai sosai hakanne yasa ya yanke hukunci hanaka ganinta Kuma kariga kasan halin Abbanku"
yanada kafewa akan maganar sa, kuma kasan baya magana ya canza.
Baki ya bud'e da niyyar yimata magana amma seya kasa hakanne yasa ya sake mayar da kansa jinkin ta ,
ya ciza lips d'insa da qarfi,,
jin yadda ya sake qan qame ta da qarfi ne yasa tace yanzu katashi ' ka koma gida kayi wanka kaci abinci ka huta kad'anyi bacci "
idan Abbanku yazo zan gwada yimasa magana.
Jin tace zata yiwa Abba magana ne yasa yayi qarfin hali ya yunqura ya miqe da niyyar fara tafiya amma se yaji jiri na d'ibarsa'
yafara ganin duhu ammi batayi auneba se gani tayi ya sulale a qasa sumamme.
Da gudu ammi ta nufi inda yake tana kuka tana kiran sunansa,
wasu nurse's ne suka temakamata suka d'aurashi akan gadon marassa lafiya suka turashi sukashiga cikin emergency d'in da shi"
anyi sa a lokacin likitan yananan se yayimasa allurai ya d'aura masa ruwa, yacewa ammi,
rashin hutu ne kawai na jiki da na zuciya yanzu ze samu bacci idan ya farka ze d'anji qarfin jikinsa "
se kuma ya rage damuwa kuma yad'an samarwa kansa hutu koda ba me yawa bane.
Ammi tayimasa godiya sannan ya tafi,
Rafiq be farka ba har se kusan 05:23 , yana farkawa yamiqe ya fice daga asibitin dayake lokacin an cire ruwan da aka d'aura masa '
gida ya nufa duk da yadda yakejin kansa nayimasa wani mugun sarawa haka ya daure,
Yana isa gidan kai tsaye ya nufi band'aki ya sakarma kansa ruwa ya fito ya canza kaya sannan ya koma ya d'auro alwala yadawo ya shumfud'a sallaya
ya fara jero sallolin da suka wuceshi.
Bayan ya gama se ya fita yasayo abinci ya dawo dak'yar yake iya ci ba dan yanajin dad'in abincin ba ,
se dan yasan itama kanta yunwar wata damuwar zata qara zama masa.
Yana gamaci a gurin ya kwanta yafara wani irin baccin wahala,
shine be farka ba se 9:16 na dare ya tashi yayi alwala yayi sallah sannan ya fito ya nufi asibitin,,
kamar jiya besamu yaganta ba amma yau ammi bata bari ya kwana a gurin ba ta korashi gida "
seda ta nunamasa 'bacin ranta sosai sannan ya yadda ya tafi badan ransa na so ba'
Haka yayita faman zuwa asibitin kullum amma Abba ya hanashi damar ganinta,
duk da irin haqurin da shi da ammi sukayita basa amma yaqi ya haqura yabari ya ganta,
Kwananta 4 a asibitin da yamma ammi na zaune a gefen gadon ta tana tofamata askar d'in yamma,,
Abba da Zarban suna tsaye a gefen kanta"
wani irin zabura tayi tana ihu had'e da kuka '
wayyo Allah yaya Rafiq,
ammi yaya Rafiq ya sakeni wayyo kaina dan Allah ammi ki dannemin kaina ze fita,,
wayyo Allah na ammi nashiga uku kaina.
se wani irin fizge fizge takeyi duk da irin riqon da Zarban yayimata,
Gabaki da'ya ta rikice se kuka takeyi gabaki d'ayansu suka shiga tofamata addu a,
dakyar ta dena zabura da ihun da takeyi amma har yanzu bata dena kuka qasa qasa ba.
Satinta d'aya a asibitin Alhamdulillah jiki yafara sauqi saboda haka Abba ya buqaci a canzamata d'aki "
akaita d'akin da babu mutane hakan kuwa akayi aka kaita d'akinta ita kad'ai,
Da yamma ammi taje gida Mahanur ce kawai a d'akin ta kishingid'a a jikin qarfen gado "
wani likita dogo ya shigo amma bata samu ganin fuskarsa ba saboda ya saka mask,
sannan kuma ya saka glass ya 'boye idanunsa,,
kallonsa takeyi har ya qaraso becemata komai ba kamar yadda itama batacemasa ba'
haka ya qarasa inda take a hankali yakai hannunsa ya ta'ba gefen wuyanta sannan ya shafa sumar kanta dayake ko d'an kwali babu a kanta"
itade kallonsa kawai takeyi dan tasan kaf zamanta a asibitin a cikin likitochin da suke dubata babu wanda yakai wannan tsayi '
gashi yanatayimata wasu abubuwa wad'anda takasa fahimtar su.
A hankali ya kai hannunsa kan setin ciwon da yake gefen cikinta yasaka d'ayan hannunsa ya zare glass d'in fuskarsa '
ji tayi wani abu me d'umi yana sauq'a akan cikinta saurin d'agowa tayi dan taga menene.
Masks d'in fuskarsa ya cire ya d'ago yana kallonta "
sosai taji babu dad'i saboda ganin hawaye akan fuskarsa"
Yaya Rafiq,
kawai ta iya furtawa se itama ta fashe da kuka '
gefen gadon yasamu ya zauna sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta,
Tanajin yadda zuciyarsa taketa faman bugawa da qarfi,,
Dan Allah kiyi haquri ki yafemin Mahanur,
a zaman da mukayi tare da ke nasan nacutar da ke cikin sani da rashin sani"
amma dan Allah kiyi haquri ki yafemin na gane kus kure na kuma zan nunamiki kulawa irin wacce koda a tarihi babu irinta.
Ina sonki Fatima ina matiqar qaunarki ban ta'ba sanin irin soyayyar da nakeyimikiba har seda kikayimin nisa,
dan Allah Fatima kice kina sona kice kin yafemini ko zanji sanyi a cikin raina.
Itade batacemasa komai ba sema kukanta da ta qarawa qarfi,
A hankali ya fara kissing d'in wuyanta yana shafa bayanta" bakinsa ya d'aura akan nata yana shafa saman cikinta,,
jin yana nema ya wuce gona da iri ne yasa ta tattaro dukkan qarfin ta ta tureshi yayi baya,
tasake fashewa da kuka qirjinta nayimata wani irin duka kamar ze fashe.
Har ya gama yimata magana ya tafi bata furtamasa ko uffan ba Kuma bata dena kukan da takeyiba.
Be jima da fita ba ammi ta dawo d'auke da abinci a kula,
ganin yanayin Mahanur ya canza ba kamar yadda ta tafi ta bartaba yasa ta tambayeta abunda yake damunta amma tace ba komai,,
haka ammi ta kyaleta dan tasan bazata fad'amata ba koda ta matsa,
Faten dankali da hanta ta zubamata dakyar ta iyacin d'an kad'an ta ture dan dama tunda sukazo asibitin bata wani iya cin abinci sosai.
Satinta uku a asibitin aka sallamesu suka koma gida, lokacin hanifa y'ar Nusaiba ta fara wayo.
Haka suketa fama kullum se Rafiq yazo yayita kuka yanayiwa Abba magiyan yayi haquri ya mayar masa matarsa '
Amma Abba yaqi koda sauraransa .
Wata ranar jumma a da yamma Rafiq ya shigo gidan,
A lokacin Abba da Zarban sun fita ammi kuma tana d'akin Nusaiba suna hira"
ganin babu kowa a parlor ne yabawa Rafiq damar shigewa d'akin Mahanur ' tana kwance ta kifa ciki a saman gado "
tsabar nisan da tayi a kogin tunani ko sallamarsa batajiba,
Ihu tad'an saki jin an ta'bata ba tare da taji shigowar kowa ba "
Rafiq ta gani gabaki da'ya ya rame idanunsa sun kad'a sukayi jazur jijiyoyin kansa sun mimmiqe kamar zasu tsinke.
A d'an tsorace take kallonsa.
Hannu ya kai ya damqota ya fizgota daga kan gadon yayimata masauqi akan faffafad'an qirjinsa,
Na gaji fatima wallahi yau sekin koma gidana babu wanda ya isa ya rabani da ke ina qaunarki matiqa,,
Inda zan, iya bud'emiki zuciyata wallahi babu ko shakka sekin tausayamin "
Tunda Abba yaqi fahimta ta kawai kizo mu tafi muje koma inane zamuyi rayuwar farin ciki '
bazamu dawoba har semun haifi yara da yawa yadda koda mun dawo babu yadda za ayi su rabamu dole su barmu tare da juna '
se a lokacin ta fahimci abunda yake nufi wato guduwa yakeso suyi kenan.
Yaya Rafiq guduwa kakeso muyi kenan?
A'a gaskiya bazan iya ba a'a, a'a a'a,
Noooooo.....
Yaya Rafiq ta qarasa maganar tana gir gizamasa kai hawaye na zuba tana qoqarin raba jikinta da nasa,
Riqeta yasakeyi da qarfi,,
wallahi sekin bini Fatima semun tafi munyi nisa da garinnan,
bazan ta'ba bari a rabamu ba saboda ina sonki"
Hannunta ya kama ya d'aura akan qirjinsa,
Fatima kiji abunda nakeji, soyayyar ki tana wahalar da ni wallahi ina mutuwar sonki '
Fatima zan iya haqura da kowa da komai mu koma wani gurin inda babu wanda muka sani babu wanda ya sanmu"
kallon cikin idanunsa tayi taga iya gaskiyarsa yake maganar hakanne yasa ta tattaro dukkan qarfinta ta tureshi ta fizge hannunta da qarfi,
qofar fita ta nufa da gudu zata fita "
Cikin zafin nama ya yunwuro ya fizgota da qarfi ya wurgata kan gado '
ganin ya nufota gadan gadan ne yasa ta saki wani irin ihu wanda yayi de de da shigowar Abba da Zarban gidan ,,
saboda haka har rige rige suke wajen shiga cikin d'akin.
Nusaiba da ammi ma jin ihunta ne yasa suka fito da sauri suka nufi d'akinta ,
Abba ne ya fizgo Rafiq da qarfi "
yana juyowa Abba ya wankesa da wasu kyawawan tagwayen maruka, seda yayi taga taga kamar ze fad'i,
amma yakoma ya tsaya da qafarsa dan yariga yasha alwashin yau ko ta yaya se an basa matarsa '
Tsawa Abba ya dakamasa,
ficemin daga gida Aliyu ..
yayi maganar yana nuna qofa amma madadin Rafiq ya fita se yasake gyara tsayuwarsa'
Abba yasake mai maitawa".
Nace ka fitamin daga gida Aliyu,
babu inda zanje Abba wallahi bazanje ko ina ba seka bani matata,
Ina qaunarta Kuma babu wanda ze rabani da ita "
babu wanda yafi qarfin yin kus kure a duniyar nan, kus kure ne nariga na aikata'
Kuma nayi kuka nayi magiya na kwana a waje cikin sanyi babu rigar kare sanyi balle bargo,
duk sanyi da sauron asibitinnan haka suka qare a kaina,,
na zauna da yunwa nayi ciwo nabada haquri " kaqi ka saurareni.
Abba me kakeso nayi ka fahimci nagane kus kure na ?
Rayuwata kakeso na badane kafin ka fahimci nayi nadama?
Saboda haka Abba ganinan a tsaye a gabanka na shirya kar'ba ko wani irin hukunci zakayimin,
amma bazan ta'ba rabuwa da itaba, kuma "
wani marin da Abba yasake sauqemasane yayi saurin dawodashi cikin hayyacinsa ,
yayi saurin yin shiru,
Aliyu nace kafitamin daga gida inde har babu k'wandalarka a cikin ginin gidannan.
Dak'yar yaja qafarsa ya fita yanajin wani irin ciwo har cikin ransa,
a wannan lokacin seda ammi taji kamar tabi bayan d'anta su tafi "
abun major ya fara yawa,
itama kanta Mahanur seda taji haushin Abba hukuncin nasa ya d'anyi tsauri da yawa.
Har Nusaiba da Zarban sunyi matiqar tausayawa yayannasu dan sunriga sunsan be iya saka rai akan abu ba,
Inde yariga ya saka rai to baya ta'ba haqura duk irin baqar wahalar da zesha a kai,,
haka suka fice daga d'akin sukabar Mahanur kwance a saman gadonta tanata rusar kuka kamar ranta ze fita "
har cikin ranta tana matiqar tausayin Rafiq,
sosai takejin babu dad'i akan abunda Abba yakeyimasa '
musamman yau jitakeyi kamar taje ta rufe Abba da duka '
har ga Allah batason abunda yakeyiwa Rafiq "
to amma yazatayi idan tayi wasa tayi magana tasan har ita Abba seyayi fushi da ita.
ranar labara da dare ammi ta shiga tasamu Abba a d'akinsa ta zauna a gefensa tafara magana kamar wata marar gaskiya '
am major dama nace nazone muyi magana game da lamarin yarannan Fatima da Aliyu ,
ni se nakeganin kamar zuwa yanzu ya kamata ace ka huce kamayarwa da yaronnan matarsa"
tunda yayi nadama yagane kus kuren sa,
Kuma itama yarinyar nan wallahi alamu sun nuna tanason mijinta sosai '
ko kad'an batajin dad'in abunda akeyimasa ,
duk ranar da yazo gidannan ka koresa ko ka fad'amasa wani abu marar dad'i saboda ita ,
ini takeyi a d'aki tana kuka wani lokacin kamma ko abinci bata iya ci'
Ba seta fad'aba yakamata ace ka fahimci tanason mijinta dan duk wasu alamu bayyanannu da boyayyu tariga tanuna a bayyane tanaso ta koma .
Ido kawai Abba ya zubamata har seda takai qarshen maganar ta sannan yad'an numfasa yace,
Ni I'ma inde akan wannan maganar kikazo to da kinyi shiru baki 'batawa kanki lokaci ba "
domin wallahi bazata koma gidansaba har seya girbi abunda ya shuka,
kinsani bana ta'ba magana na canza inde nariga na furta to tabbas sena cika "
ban damuba koda yarinyar tana sonshi ko a…