MATAR GIDA PAGE 53
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P53
Bayan Unaisa ta isa gidan taron duk wanda ya kalleta sai ya ƙara kallon ta,irin shigar da ta yi duk wani abinda ke jikin me tsada ne gashi ta yi wani irin kyau,nan dai ƴan kungiya suka shiga yabon outfit ɗinta kowa cewa yake ta yi kyau Unaisa tana ta jin daɗi,sau ɗaya Fadeelah ta kalle Unaisa ta dauke kai,Fedeelah ƙawar Unaisa ce tare suka taso dalilinta Unaisa ta shiga kungiyar matan gida,kafin Fadeelah ta yi aure tare suke zuwa islamiyya da Unaisa,Fadeelah marainiya ce a wajen ƴaƴanta ta taso,ko kaɗan ƴaƴanta baya ganin laifin ta duk abinda ta aikata dai-dai ne,wannan dalilin yasa Fadeelah ta taso babu cikakkiyar tarbiyya,bayan Fadeelah ta yi aure ne ta canzawa Unaisa gaba ɗaya duk wata alaƙa dake tsakaninsu ta datse Unaisa ta sha zuwa gidanta amma zata cewa ƴan aikinta su cewa Unaisa bata gida,da fari Unaisa bata gane ba,bayan ta fahimce Fadeelah bata son mu'amala da ita Unaisa ta bawa banza ajiyarta ta cigaba da sabgoginta,dalilin da yasa Fadeelah ta yanke alaƙa da Unaisa,me kuɗi ta aura hakan yasa tana ganin kanta,Unaisa bata daɗe da fita ba Ɗalha ya kira layinta amma bata ɗaga ba sai da ya yi mata kira uku a na huɗu ta amsa kiran,tashi ta yi daga inda mutane suke ta samu inda babu kowa kafin ta amsa kiran,bayan ta amsa kiran ne Ɗalha ya ce ba zai dawo gida da wuri ba saboda ogansa ya kirasa zai je ofis ya ce mata sai la'asar zai dawo,nan Unaisa ta saki jiki ana ta hira da dauke dauken hutona, bayan sun gama hutona aka ci abinci,karfe uku da wasu ƴan mintina Unaisa ta je ta sami wacce aka taro a gidanta ta ce mata zata tafi sosai matar ta yi mamaki a tunanin ta sai dare Unaisa zata tafi kamar yadda aka saba,hakan yasa ta tambaye Unaisa lafiya take son tafiya da wuri alhali lokacin tashi bai yi ba,Unaisa ta yi mata karya ta ce mijinta zai dawo daga tafiya shi yasa take son komawa gida dan ta dafa masa abinci baki sake matar ke kallon Unaisa can sauran mata dake wajen suka saki dariya suna kallon Unaisa ɗaya daga cikinsu ta ce ''lallai da sauran ki wai wannan rawar jiki miji ki ke yiwa a lallai da sauran ki'' duk suka fashe da dariya ita dai Unaisa bata bi ta kansu ba kawai ta dauki kuɗi dubu talatin ta tamƙawa wacce a aka yi taro gidanta daga haka ta je ta sami Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u dake zaune cikin ɗaki ta ce masu za ta wuce duk suka kalleta Hajiya Bilƙisu ta ce ''lafiya za ki tafi da wuri ko sallar la'asar fa ba a yi ba'' Unaisa ta sosa kai kafin ta ce ''ba da izninsa na fita ba shi yasa nake son komawa kafin ya dawo'' Hajiya Zulfa'u dake riƙe da wani glass cup cike da juice ta ce ''wa?" ta faɗa tana gyara zama har sannan kan Unaisa ƙasa ta yi magana cikin kwantar da murya ta ce ''me gidan'' cike da mamaki Hajiya Zulfa'u ta ce ''kina nufin mijinki?" Unaisa ta gyaɗa kai da sauri,wani irin dariya suka sake Unaisa ta shiga bin su da kallo sai da suka yi me isarsu kafin Hajiya Bilƙisu ta ce ''kina tsoron miji ki ka shiga cikin mu?daman ana niman izinin miji in za a fita unguwa?lallai yarinya da sauran ki'' ta faɗa tana dauka gashasshen nama,duk suka yi banza da Unaisa ganin haka yasa Unaisa faɗin ''ni zan wuce'' bata jira cewar su ba ta fita daga ɗakin duk suka bita da ido,Unaisa na daf da fita daga ɗakin Hajiya Bilƙisu ta kira sunanta a hankali Unaisa ta waigo tare da komawa cikin ɗakin tana amsa kiran, har inda suke zaune Unaisa ta ƙaraso ta samu waje ta zauna tana faɗin ''gani''
Gyara zama Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''maganar mota ya ake ciki?" da wani irin sauri Unaisa ta ɗago ta kalle Hajiya Bilƙisu,tana sane da maganar mota amma a tunanin ta ba za a yi mata tuni da wuri haka ba,Hajiya Bilƙisu ta daura da ''bai dace kowacce tana hawa mota ke kuma ki riƙa yawo adaidaita ba hakan ƙaskanci ne garemu'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta daura da ''taron da za a yi karshen wata da zata kama zai zama taro na karshe da za ki halarta a adaidaita,taro da za a yi watanni biyu masu zuwa in ba ki mallaki motar kan ki zuwa wannan lokaci ba kungiya zata yi maki gargaɗi za kuma ki biya tarar naira dubu hamsin,in ba ki siya mota ba bayan watanni shidda kungiya za ta kore ki,sannan akwai wata makarantar koyan mota da yawa yawan ƴan kungiyar nan a can suka koya mota,sabida haka in kina buƙata sai na ba ki lambar shugaban makaranta ki yi regester da kin yi regester sai ki fara zuwa anan koya maki '' ajiyar zuciya Unaisa ta sauke kafin ta ce ''ina kan haɗa kuɗaɗe ne da sun kammala zan sanar da ke'' Hajiya Bilƙisu ta dauki kofin glass dake gabanta ta kurɓi juice ɗin ciki kaɗan kafin ta ajiye kofin tana mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''to Allah ya taimaka,zan tura maki number ta whatsapp'' Unaisa ta masa da to daga haka ta fita daga ɗakin,bayan fitar Unaisa daga ɗakin ba tare da ɓata lokaci ba ta fita daga gidan gaba ɗaya cikin sauri take tafiya har ta kai bakin kwalta nan ta tare abin hawa lokacin karfe huɗu saura ƴan mintina,wayarta dake jaka ta fara ƙara alamar shiga kira ciro wayar ta yi daga jaka ta ga Ɗalha ne ke kira,wani irin bugu kirjin ta ya shiga yi bata amsa kiran ba kawai ta mayar da wayar cikin jaka,Allah Allah take ta ga kanta a gida,ko da zai Ɗalha ya dawo ya tarar bata nan da ta yi masa tsiwa shikenan sanin kanta ne yana shakkar ta amma harda haka hankalinta ya ƙasa kwanciya cikin zuciyarta sai faman addu'a take Allah yasa ta riga sa koma gida,dai-dai kofar gidan ta mai adaidaita ya yai parking cikin sauri ta sauko tare da miƙa masa kuɗi da ita kanta bata san ko nawa bane, makullin gidan ta ciro daga jakarta tare da buɗe gate,bayan shigarta ciki da sauri ka kalle inda Ɗalha yake pakin mota wata doguwar ajiyar zuciya ta sauki ganin babu motar Ɗalha a compound ɗin hakan yana nufin bai dawo ba,Unaisa bata tsaya ɓata lokaci ba ta nufi kofar entrance tana ciro makulli daga jakarta bayan ta buɗe kofar bangarenta ta nufa ta yi wurgi da hand bag ɗinta kan gado tana kwance gyalen da ta yi rolling tana lumshi ido, numfawa ta yi dai-dai lokacin da ta gama kwance gyale ta zauna bakin gado tana cire ƴan kunne da sarƙa,motsin ta ji daga waje alamar buɗe gate haɗe da karar motar Ɗalha babu shiri ta tashi da wani irin sauri ta dauki hand bag da ta yi wurgi da shi ɗazu tare da gyale da ta kwance ta wuce bathroom,a nan cikin bathroom ta cire doguwar riga da take sanye da shi,bathrope ta dauko ta sa kafin ta dauki sabulu ta fara wanka fuska,tana nan cikin ta je Ɗalha ya buɗe kofar ɗaki motsin ruwa da ya ji daga bathroom yasa ya ja mata kofa ya rufe kafin ya wuce parlour ya zauna yana mayar da numfashi ba karamar gajiya ya yi ba ga wani irin yunwa da take ɗawainiya da shi a hankali ya rintsa ido yana jin yadda iskar fanka ke huro iska mai dadi,a can wajen Unaisa bayan fitarta daga bathroom wata doguwar riga shadda ta dauko daga saif ta zura ta ɗiɓi body lotion kaɗan ta shafa fuska daga haka ta fita ɗakin, nan parlour ta tarar da Ɗalha zaune idanunsa rufa kamar yana bacci a hankali ta fara takawa gudun kada ta tashi shi daga bacci abinda bata sani ba shi ne ba bacci yake ba idonsa biyu kawai ya rufe ido ne yana hutawa har ta kai kofar kitchen Ɗalha bai buɗe ido ba hakan yasa ta buɗe kofar kitchen a hankali ta shiga,bayan shigarta tsayawa ta yi ta shiga bin kitchen ɗin da kallo ita kanta tasan bata kyautawa kanta ba kwanuka jibgi ta ko ina wasu ma har sun fara bushewa,sanin kanta ne in har ta ce za ta yi wanke wanke a kitchen tabbas Ɗalha zai farka in kuma ya farka to babu mamaki ya tambayeta dalilin da yasa bata yi wanke wanke da wuri ba,wannan dalilin yasa ta shiga store ta dauki wata babbar roba ɓaka irin wacce ake wankin kaya a ciki,cike da nitsuwa ba tare da ta yi wani motsi ba ta shiga kwashi kwanuka tana zuba su cikin roba,sai da ta zuba kusan rabin kwanukan dake kitchen kafin ta buɗe kofar baya dake kitchen ta fita hannunta riƙe da roba dauke da kwanuka masu datti,Allah ya taimake ta akwai fanfo a wajen,a bakin fanfo ta ajiye robar tare da kunna fanfon daga haka ta koma ciki ta kwashe saura kwanuka, bayan ta gama fitar da kwanuka ne har tukwane duk ta jiƙa su da ruwar omo wasu sabbin robobi ta dauko daga store guda biyu ta tara ruwa cikin daga haka ta koma kitchen,share kitchen ɗin ta yi tare da goge ko ina kama daga kitchen carbinate zuwa kitchen island duk ta goge su tsaf bayan ka gama goge goge ta yi morping kitchen lokacin karfe huɗu harda mintina arba'in ko sallar azahar Unaisa ba ta yi ba,bayan ta gama morping fita ta yi zuwa inda ta zuba kwanuka tana kare masu kallo,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauki,ba a son ranta ba ta koma cikin store ta dauke kujera ƴar tsuguno zama ta yi kan kujerar ta fara da ke kwanuka,a can wajen Ɗalha kuwa bayan shigar Unaisa kitchen ya buɗe ido motsin kwanuka da ya jiyu ya sa ya fahimci bata yi wanke wanke da ya ce ta yi kafin ya dawo ba shiru ya yi yana tunani kan halaiyar Unaisa zuwa yanzu Ɗalha ya fara tunanin Unaisa bata da cikakken hankali ya za a yi matar da ta san abinda take tun jiya da safe ta yi aiki da kwanuka amma ta bar su sun kwana sai yanzu take wanke kwanuka,karfe biyar saura na yamma anya bazai kai Unaisa asibiti a duba lafiyar kwakwalwar ta ba kowa abubuwan da take sun fara yawa da zai mata magana yanzu sai ta yi masa rashin mutunci har cikin zuciyarsa baya son yawan tashin hankali makullen motarsa dake daure Centre table tare da wayarsa ya dauko ya fita daga gidan,Unaisa na can tana wanke wanke ba ita ta gama ba sai karfe biyar harda mintina hamsin ta wanke gaba ɗaya kwanuka amma banda tukwane da ta cika masu ruwa sai zuwa gobe zata wanke su,daga haka ta kwashe kwanuka ta kai su cikin kitchen ta ajiye inda ya kamata,ɗaki ta koma ta dauro alwalah ta gabatar da sallar azahar da la'asar,bayan ta idar da sallah ne tana zaune kan darduma ta dauki waya ta shiga whatsapp nan ta ga Hajiya Bilƙisu ta tura mata lamba,daukar lambar ta yi ta yiwa lambar magana ta whatsapp cewar tana son ƙoya mota nan dai mutumin ya yi mata bayani inda ya faɗa mata kuɗin da ake biya in za a koya makawa mutum tsawon watanni uku kuɗin shi daban ina kuma watanni shidda ne shima kuɗin sa daban,Unaisa ta zaɓi wata uku saboda kuɗinta bai kai na watanni shidda ba,bayan ta tura masa kuɗi ne ta shiga tunanin yadda za a yi ta riƙa fita koyan tuƙi sanin kanta ne Ɗalha bazai taɓa bari tana fita kullum ba,ta dade zaune tana nazari can dai ta tashi ta yi sallar magrib bayan ta idar ta fita daga ɗakin ta nufi hanyar kitchen,jollof ɗin macaroni ta dafa ya ji kifi da kayan lambu ya yi kyau a ido sai dai gaba ɗaya ta manta bata sa manja ba,sai bayan ta gama girki ta yi sarving kanta har ta fara ci kafin ta tuna bata sa manja ba,zaman ƴan bori ta yi tana tunanin yadda zata yi saboda sosai take jin yunwa,ta dauki sama da mintina biyar zaune a haka tana nan zaune Ɗalha ya shigo parlour bakinsa dauke da sallama kallo ɗaya ya yi mata ya dauke kai da ido Unaisa ta bi shi yana daf da shiga ɗaki ta ce ''sannu da dawowa'' a daƙele ya amsa mata ya ce ''yauwa sannu''
SHUUKRAN