MATAR GIDA PAGE 54
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P54
Washe gari karfe takwas dai dai Ɗalha ya fita zuwa ofis Unaisa na can tana bacci,yau ma kamar kullum karfe uku ta fita daga ɗaki ta samarwa kanta abinda zata,farar indomie ta dafa tsabar ƙiwa ko albasa bata sawa indomie ba haka ta dafata daga ruwa sai maggi,a nan kitchen ta ci abinci,tukwane da ta jiƙa su da ruwar omo jiya ta liƙa ta tagar kitchen suna nan yadda ta barsu,taɓe baki ta yi daga haka ta koma ɗaki,wasa wasa sai da tukwane nan suka yi kwanaki huɗu Unaisa bata wanke su ba,a ranar wata asabar an tashi da ruwan sama tun daren jiya ake ruwa har safiya ruwar bata tsaya ba,har da gari ya waye amma garin da hadari sosai sama ta yi duhu ga ruwa dake sauka a hankali hakan yasa garin yin duhu kamar dare,Ɗalha sanye yake cikin wasu riga da wando sweatsuit navy blue kafafunsa sanye da socks da takalmi hause slippers,tsaye yake cikin kitchen yana haɗawa kansa tea bayan ya gama haɗa tea hannusa riƙe da kofin yana juya tea,tsaye yake jikin tagar kitchen yana kallon compound ɗin gidan daga taga,idanuwansa ne suka sauka kan tukwane da Unaisa ta barsu bata wanke ba, a hankali ya ajiye kofin kan kitchen island daga haka ya buɗe kofar baya ya fita,tsayawa ya yi yana ƙarewa tukwane kallo ya dauki a ƙallah mintina uku tsaye wajen kafin daga bisani ya koma kitchen ya dauki kofin tea ya wuce ɗakinsa,sanin kansa ne ko ya yiwa Unaisa magana kan tukawane ba lallai ta wankesu ba karshe ta faɗa masa baƙar magana,a can wajen Unaksa kowa zaune take cikin ɗaki ta rabka tagumi,sanye take cikin wasu riga da wando sweatsuit kalar hoda,sumar kanta ya kwanta har gadon bayanta Allah ya taimaka yau ta yi wanka da brush ta kuma gyara suma dalilin ruwar sama da kuma tsananin sanyi da aka waye garin yau dashi,duk yadda ta yi dan kar ta yi wanka yau abin ya ci tura saboda yadda jikinta ke mata kaikayi hakan yasa ta hakura ta yi wanka ba dan ranta ya so ba,rabon da ta gyara suma da wanka tun ranar da ta tafi taron matan gida,fararen kafafunta ta daura kan bedroom slippers, ta yi nisa cikin tunani,tunani take kan yadda zata haɗa kuɗaɗe da zata siya mota,ta dauki sama da mintina goma zaune tana tunani kafin ta tashi ta nufi ɗakin Ɗalha,bayan shigarta ganinsa ta yi zaune can kuryar ɗaki kan wata kujera da tebir laptop daure kan tebir da wasu takardu a gefen laptop, ga kuma kofin tea daga can gefe da alama aiki yake cikin laptop,har ta shiga ɗakin bai sani ba idanunsa kan laptop,sai da ta sake sallama a karo na biyu kafin ya ɗago a hankali ya zuba mata idanunsa ba tare da ya amsa sallamar ba,sosai ɗakin ya dauki sanyi harda babu haske sosai amma hakan bai hana Unaisa ganin yadda ɗakin ke gyara tsaf ba, ga wani ƙhamshi air freahner da ɗakin ke yi,a hankali Unaisa ta taka ta je kusa da shi idanunta kansa kamar yadda shima yake kallonta,ta dauki a ƙallah mintina uku tsaye bata ce masa komai ba shi kuma bai mata magana ba can dai ya ce ''ya aka yi me ke faruwa'' sai a sannan ta samu waje ta zauna,so take ta yi masa maganar mota sai dai bata san yadda zata fitar masa da zance ba duba da yanzu ya ɗan sauya mata ba kamar da ba,kafin su yi aure kai tsaye take tambayar abu ya yi mata ba tare da ɓata lokaci ko da kuwa ta zagi sa,saɓanin yanzu da yake iya fushi da ita ya ƙi mata magana na tsawon kwanaki muryar sa ne ya katse mata tunanin yadda ya ce ''kin yi shiru ba ki ce komai ba me ke faruwa'' numfawa Unaisa ta yi har sannan bata san yadda zata faɗa amsa abinda ke damunta ba,nan ta shiga wasa da yatsunta idonta ƙasa can wata tunanin ta faɗo mata gyara zama ta yi tare da langwaɓar da kai,bayan wasu ƴan sakanni ta yi magana murya can ƙasa ta ce ''sanyi nake ji'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta daura da ''sanyi ya yi yawa ina ji kamar zan yi mura,ko kana da magani'' ta karasa magana a shwagaɓe tun da ta fara magana Ɗalha ke binta da wani irin kallo kamar yau ya fara ganinta,yanayin sanyi da kuma irin shigar da ta yi yasa Ɗalha shiga wani irin yanayi,rabon shi da ita yau kusan sati Uku,tun da yake da Amirah bai taɓa yin sati ɗaya ba,wannan dalilin yasa ya ƙasa riƙe kansa a yanzu,a hankali ya kashe laptop dake gabansa ɗakin ya kara yin duhu kaɗan,a hankali ya miƙe ya nufi inda take hannu ya mika mata alamar ta zo sai a sannan ta ɗago ta kallesa daga haka ta mayar da dubanta ga hannu da ya miƙo mata a hankali ta daura hannunta cikin nasa,ɗago ta ya yi tare da haɗa ta da jikinsa, lamo ta yi jikinsa tana shaƙar khamsin turarensa,bakinsa ya kai saitin kunnenta ya yi magana cikin wani irin yanayi yana jan numfashi ya ce ''ba magani ki ke buƙata ba..''look up'' ya faɗa yana ɗaga fuskarta goshinsa ya haɗe da nata yana goga hancin sa kan nata taɓe baki Unaisa ta yi ba abinda ya kawo ta ba kenan amma baza ta iya hanasa ba ta buɗe baki da niyar maganar Ɗalha ya yi saurin haɗe bakinsa da nata ya dauki sama da mintina biyar yana kissing ɗinta passionately a hankali ya dauke ta ya daurata kan gado,gaba ɗaya Unaisa ta gama sakarwa Ɗalha jiki ya dauki sama da mintina goma yana bin lungu da saƙo na jikinta,a hankali Ɗalha ya raba jikinsa da Unaisa ya sauka daga kan gado ya wuce bathroom daga shigar sa rage kayan jikinsa ya yi kafin ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi,bai san dalili ba kawai ya ji bazai iya kusantar Unaisa ba, lokaci ɗaya ya ji gaba ɗaya abin ya fita kansa,da ido Unaisa ta bisa har ya shiga bathroom ta dauki a ƙallah mintina biyar zaune kafin can ta dauki rigarta ta sa tare da gyara wandon jikinta,tsawon zaman ta da shi bata taɓa sanin abinda ake ji cikin abin ba,sai dai abinda Ɗalha ya yi yanzu ko kadan bai mata daɗi ba, a hankali ta gyara kwanciya tana lumshi ido tare da sauki ajiyar zuciya akai akai
Unaisa na nan kwance har Ɗalha ya fito daga bathroom daure da towel a ƙugunsa,Unaisa ta shiga bin dark skin ɗinsa ido har sannan jikinsa da ruwa,Ɗalha irin mazan ne karfafa masu tsawo da faɗi,har ya sa kaya tana nan kwance sai binsa take da ido,bayan ya gama shirya kansa zama ya yi kan kujerar da ya tashi ɗazu yana buɗe laptop ɗinsa,Unaisa dake kwance ta yunƙura a hankali ta tashi zaune tana kallon Ɗalha da ya juya mata baya yana danna laptop ɗinsa mamaki ne ya cika Unaisa me hakan ke nufi? haka zai barta kwance kamar wata marar galihu,gyara zama ta yi ta ɓude baki da niyya masa rashin mutunci sai kuma ta yi shiru ta ƙasa magana kamar wacce ta tuna wani abu,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta saita nitsuwarta, cikin kwantar da murya ta ce ''ina da magana'' idon Ɗalha kan laptop ya ce ''ina jin ki'' a sanyaye Unaisa ta sauka daga kan gado tare da ɗaukar stole ta je kusa da Ɗalha ta zauna,kamar wata mutumiyar arziƙi ta zauna tare da sunkuyar da kai ƙasa a ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa Ɗalha dakatar da abinda yake ya mayar da dubansa gareta ''talk'' ya yi magana a daƙeli da kyar Unaisa ta tattaro kwarin gwiwa ta ce ''daman da akwai abinda na ke so ne in bazan takura ka ba'' shiru ta yi tana jiran jin abinda zai ce,amma sai ta ji ya yi shiru bai ce komai hakan yasa ta ɗago a hankali ta kallesa a sace ganin ita yake kallo fuskarsa babu yabo babu fallasa, numfasawa Unaisa ta yi kafin da kyar ta iya faɗin ''mota nake so bana jin zan iya riƙa zuwa anguwa a motar haya ko adaidaita,ka ga dai yanzu ni matar aure ce bai dace na riƙa bin abin hawa ba'' ta kare magana kanta a ƙasa a natse Ɗalha ya ce ''haka ne amma bana da halin siya maki mota a yanzu ƙila sai nan gaba,ki yi hakuri''shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''matata Amirah a motar haya take zuwa aiki ta kuma kai yara makaranta sannan duk inda zata motar haya take bi..ina ganin ba wani abu bane in kin shiga motar haya'' ya kare magana tare mayar da dubansa ga laptop ko kaɗan Unaisa bata ji dadin amsar da Ɗalha ya bata ba cike da ɓacin rai ta ce ''ni ba matar ba ke? duk sanda za ka yi magana kan Amirah sai ka ce matarka me ka ke nufi da hakan?" ta kare magana cike da tsiwa sarai Ɗalha ya fahimci rikici take son yi hakan yasa ya mayar da hankali kan abinda yake bai sake cewa komai ba,Unaisa na zaune kan gado sai huci take tsabar ɓacin rai ji ta yi kamar ta fashe da kuka amma ta daure bata yi kukan ba,cike da ɓacin rai ta fita daga ɗakin,bayan fitarta da wasu ƴan sakanni Ɗalha ya fita daga ɗakin zuwa kitchen ya haɗowa kansa shayi,karfe biyu da wasu mintina Ɗalha ne zaune parlour ya jingina bayansa da kujera idanunsa rufe wani irin yunwa ke ɗawainiya da shi a wannan lokacin,tun safe babu wani abincin kirki da ya ci tea da buscuit ya yi breakfast,ruwan da aka yi ta yi yasa bai samu damar fita siyan abinci da safe ba,yanzu haka tunanin abinda zai ci yake,numfasa ya yi murya can ƙasa ya ce ''mata biyu amma ina rayuwa kamar marar mata,Allah ka yiwa Amirah albarka'' yana nan zaune parlour ya ji kamar an buɗe gate shiru ya yi tare da mayar da hankali kan muryar da yake ji daga nisa kamar muryar Suhail yake ji can kuma ya ji kamar Sudais,har ya tashi da niyyar zuwa duba sai kuma ya tuna kusan raba dare ya yi jiya yana waya da Amirah amma bata faɗa masa za su dawo yau ba,hakan yasa ya koma ya zauna,bai dade da zama ba ya je an buɗe kofar parlour entrance Ɗalha bai tsaya ɓata lokaci ba ya fita zuwa babban parlour cike da mamaki yake kallon yaran Ummu Abiha ce ta fara ganinsa hakan yasa ta sake ihu tana faɗin ''Dady oyoyo'' ta faɗa tare da yin gudu ta je ta rungume shi duka yaran hankalin su ya koma kan Ɗalha duk suka yu kansa da gudu suna faɗin ''Dady oyoy Dady oyoyo'' cike da farin ciki Ɗalha ya rungume yaran yana dariya nan ya shiga liƙe yana duba Amirah amma bai ganta ba,har ya buɗe baki zai tambaye yaran ina Amirah ya ga ta shiga parlour tana jan akwatin kayansu,a hankali Ɗalha ya raba yaran da jikinsa idonsa kan Amirah ya ce ''oya ya isa je ku zauna'' duk suka koma parlour sun zauna kamar zai haɗeye ta haka Ɗalha ke kallon Amirah wani irin kyau ta ƙara masa ta kara haske amma ba can can ba fatarta har wani glowing yake, har inda take ya ƙaraso tare da karɓar jakar kayan ya ce ''me yasa ba ki kira na zo na dauka ba?" murmushi mai sauti Amirah ta yi bata ce komai ba,fita Ɗalha ya yi zuwa compound sauran kayansu tare da dauka sauran jakukkunan,ita dai Amirah tuni ta wuce bangarenta bayan shigarta ɗaki ta wuce ta cire mayafinta daga haka ta shiga bathroom,bayan shigarta bathroom ganin ta yi bathroom ɗin ya yi mata ƙora hadda ba wani datti sosai ya yi ba amma ta ji gaba ɗaya baza iya amfanin da shi ba tare da ta wanke ba,sai da ta wanke bayin tsaf kafin ta biya buƙatarta,bayan fitarta daga bathroom bata tsaya ɓata lokaci ba ta shiga gyaran gidan gaba ɗaya,dake babu wani datti sosai da ɓangaren yasa cikin ɗan kankanin lokaci ta gama share ko ina har morping ta kunna turare cikin burner,Ɗalha dake zaune cikin parlour da yara ya ji wani ƙhamsi ya dake hancinsa,tun da can haka gidan ke ƙhamshi ko da yaushe wannan turaren Amirah ta saba amfani da shi bayan Ɗalha ya shaƙa ƙhamshin murya can ƙasa ya ce''my queen is back queen of the hause is back'' ya faɗa shi kadai yana saken murmushi,ita ko Amirah bayan ta gama gyara ko ina ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta shiga kitchen ta daura sanwar tuwon semonvita miyar bushasshiyar ƙubewa,Unaisa na kwance ɗaki ta ji wani irin sihirtaccen ƙhamshi mai kwantar da hankali shiru ta yi tana tunanin inda ta san wannan ƙhamshin kamar wacce aka tsikara ta tashi zaune tunawa ta yi da inda ta san ƙhamshin ta ce ''matarsa ta dawo ne? na ji ƙhamshin jikin yaranta'' shiru ta yi kamar me tunani can ta taɓe baki tare da faɗin ''aljanar tsaftar ta dawo kenan'' tsaki ta yi tare da ajiye wayarta daga haka ta fita daga ɗaki zuwa kitchen,bayan shigarta kitchen store ta shiga tare da ɗaukar robobi da ta yi amfani da su ranar da ta yi wanke wanke,ta haɗa girar sama da ƙasa cike da ɓacin rai ta buɗe kofar kitchen na baya ta tare ruwa cikin roba daga haka ta fara wanke tukwane,tana nan bakin fanfo tana wanke tukwane ta ji wani ƙhamshin turaren wuta ya dake hancinta murya can ƙasa ta ce ''maiyah''
SHUUKRAN