Chapter 1
JINKIRIN AURE
BY
Rashma
AREWA WRITER'S ASSOCIATIONđź’¦
بسم الله الرŘمن الرŘŮŠŮ…
{Iyaye kusani ƴaƴa amana ne a garemu kuma sai Allah ya tambaye mu akan amanar da ya bamu idan Ubangiji ya jarraɓi ƴaƴan ku kamata yayi kuja su a jiki ku nuna musu ƙauna ba wai ku haɗe kai da jahilan cikin al'umma ba idan ku kuka ƙyamace su hakan zai sa zuciyar su ta ƙara bushewa ta fanɗare Ubangiji ya shirya mana zuri'a.}
Page 1
Ruwan wanka ta saka a cikin bokiti sai sauri take domin kuwa ta makara dan dai bazata iya zuwa gurin aiki a haka bane har ta kai ƙofar ban ɗaki ta tuna bata ɗauko kwandon wankan nata ba haka ya saka ta ajiye ruwan a ƙofar ban ɗaki ta koma ɗakin ta ɗaukowa tayi ta fito ɗaga idon da zatayi taga anrufe ƙofar bandaki da karfi da sauri ta nufi gurin ganin bata ga bokitin ruwan wankan ta ba cikin ɓacin rai tace "wane ɗan rainin hankalin ne ya daukar min ruwa?"
Jin ba'a amsa mata bane ya sakata jijiga ƙofar bandaki amma shiru ranta ne ya kara ɓaci ta tsani raini bata son shi ko kadan fitowar ƙanwar ta Sadiya ne ya sakata jin mugun ɓacin rai "Sadiya miye haka kika yi kinsan sarai ruwan ni na ajiye su amma dan tsabar iskanci shine kika ɗauka kika yi wanka dashi gashi gawayin ya mutu kuma na makara."
Dogon tsaki da Sadiyar taja ne ya kara fusata ta har ta gota ta ta saka hannu ta janyo ta da ƙarfi ta dawo baya hannu ta daga domin kai mata mari Mama Shafa ta daka mata wata uwar tsawa "karki kuskura ɗaura wannan ƙazamin hannun naki akan ƴata ban haifawa kowane ɗan iska ita ba dan ya daka inda kinyi aure ai da baki zauna kina fada da ƴar cikin ki ba duka ƙannan ki sunyi aure sun bar ki kina yawon ta zubar ubawaye be san me kike aikatawa ba da sunan aiki...."
Ranta na mata suya ta bar gurin har yaushe ne mutane zasu fahimce ta a haka ta saka doguwar rigar abaya ta yafa mayafin ta, ta fito ɗakin nata ta kulle ta nufi ɗakin mahaifiyar ta da suke kira da Amma a falo ta same ta tana shan koko da ƙosai sai ƙanwar ta Hajara autar su a ɗakin Amma kenan tana shirin makaranta har ƙasa ta durƙusa tana gaida ta fuskar ta a ɗaure ta ɗago tana kallon ta "wato Khadijah kinfi gane ma kina yawo a gari da sunan aiki bazaki daina jamin zagi ba ki fitar da miji kiyi aure ba ko tunda shi Sulaiman yaƙi ya fito."
Kanta ta sunkuyar ƙasa tana danne hawayen dake son ɓalle mata "kiyi hakuri Amma yace ya kusan gama gidan shi ai kema kin sani."
Jin bata sake ce mata komai bane ya sakata miƙewa ta mata sallama ta fita har lokacin Mama Shafa na zage_zage ko kallon inda suke batayi ba tayi ficewar ta sauri take yi sosai har ta ƙaraso bakin titi ɗan sahu ta tare "malam Rabo building."
"KuÉ—in ki dari biyar."
"Dari uku ne fa haka ake zuwa."
"Kin san Maine ya tashi shiyasa ma kika ga ankara kuÉ—in ki bada dari hudu."
Shiga tayi tana cewa "Allah ya kaimu lafiya."
Shiru tayi ta jin gina kanta a jikin karfe É—an sahun tana tunani rayuwa me yasa mutane suke haka ne ya suke so tayi da rayuwar ta a bakin get din company ya sauke ta kuÉ—in shi ta bashi sannan ta shiga matakalar bene ta fara haurawa da gudu har ta karasa hawa na biyu tana haki signing tayi na shigowar ta kallon ta mutumin yayi inda sabo ya saba ganin ta a haka "kekam me yasa bakya son hawa liptar."
"Baba ai a wannan zamanin da ciwon sugar yayi tsanani ai dole saida motsa jiki suga nake ƙonawa."
Jinjina kansa yayi da fadin "haka ne."
Koda taje office É—in su duk sunzo sallama ta musu a tare suka amsa akan teburin ta, ta zauna "miss Khadijah yau kin makara."
FaÉ—in Fahad abokin aikin ta "wallahi Fahad kasan yanayin rayuwa."
Kai ya jinjina mata shiru sukayi ko wanne yana aikin sa Zainab ce ta kalli inda Khadijah take tana cewa "yawwa kin kammala aikin da Mr Faruk ya baki kuwa da ɗazu yazo yana tambaya aka gaya masa baki ƙaraso ba."
"Na kammala jiya na manta ne baje da laptop É—in gida ba shiyasa ban tura masa ta email ba amma bara na tura masa yanzu."
Miƙewa Zainab din tayi riƙe da takardu a hannun ta "kiyi sauri dan yanzu zakiga ya dawo kinsan bayada hakuri haka yake kamar zawo."
Dariya sukayi gaba dayan su tana cikin turawa sai gashi ya shigo akan teburin ta ya karasa ya dafa shi da duka hannayen shi "good morning sir."
"Morning how are you."
"Am fine sir."
"You keep me waiting yesterday you don't send me."
"Am so sorry sir I forget my laptop in the office."
"Don't worry my dear send me right now am waiting for you."
"Okay sir."
Mai makon ya fita sai ya zauna akan kujerar dake gaban teburin ta tsuke fuska dan bata son shi shigi tana gama tura masa ta dago "sir na tura maka."
Kai ya jinjina mata saida ya kara wasu ƴan mintuna sannan ya miƙe ya fita ajiyar zuciya ta sauke me kauri ta ci gaba da aikin ta sha biyu suka tashi break dan haka bayan taci abinci ne a restaurant ta wuce zuwa Masallaci ya gabatar da sallah azahar dan har daya tayi itace ta fara dawowa office dan haka wayar ta take dannawa amma gaba ɗaya tayi zurfi a tunani duk yanda take ƙoƙarin cire maganganu mutane kada suyi tasiri amma haka bai faru ba hawaye ne suka cika mata idanu ta yaya zata fahimtar da mutane cewa shifa aure lokaci ne sannan duk yanda taso tayi auren bazai faru ba saida miji tabbas tana da kyau kyan da ya amsa sunan kyau dan kaf gidan su ta fisu kyau sannan ga diri Allah ya bata amma duk wanda zai zo gurin ta sai yazo da wata manufa tashi lumshe idanun ta tayi hakan ya bama hawayen da suka tarar mata damar zubowa buɗe ƙofar da akayi ne ya saka ta saurin kai hannu ta share hawayen ta har suka tashi batada walwala biyar suke tashi gurin me gashin kifi ta tsaya ta siya gabanta na faɗuwa ta nufi gida a ƙofar gida ta sami Babanta yana tsaye har ƙasa ta duƙa "Bappa barka da yamma."
Fuskar shi É—auke da fara'a yace "Hadizatul kubrah an dawo."
"Eh Bappa."
"Masha Allah Ubangiji ya miki albarka."
"Amin ya Allah Bappana."
Izinin tafiya ya mata dan haka ta miƙe yana me jin daɗi dan a gurin shi ne kawai take samun malamai masu daɗi kamar kullum haka ta samu gidan a cike da yara sunata haniya ga uwayen su gefe suna aikin abinci dare sannu da gida ta musu duk suka bita da kallon banza har ta shiga ɗakin Amma dan bata tsakar gida a tsaye ta sameta tana jera zobo a cikin firij ɗinta gaida ta tayi cike da girmamawa "lafiya."
Ta amsa a taƙaice ta ci gaba da aikin ta ledar hannun ta, ta ajiye mata "Amma gashi ba yawa."
Ta mike har ta kai bakin ƙofa taji muryar ta a dake tana cewa "zo ki ɗauki kayan ki bana buƙata indai bazaki ɗauki maganata da daraja ba."
Hawayen da take ta danne wa ne suka zubo mata me zatayi Amma ta yarda da ita uwar ma da ta haife ta bata yarda da ita ba wa take tunani zai yarda da ita kuma ya mata uzuri cikin rawar murya tace "Amma wallahi bana aikata abinda ba daidai ba ki yarda dani idan ke da kika haifeni kinkasa bani yarda to waye zai yarda dani."
“ki fitar da miji kiyi aure kawai shine hankalina zai kwanta na gaji da maganganu da suke yawo akan ki Khadijah nagaji da cin mutuncin da ake zuwa har gida anayi min nace ki rabu da Sulaiman ɗin nan kin ƙi nasan ba masoya kika rasa ba......”
Da gudu ta fita daga ɗakin tana rusar kuka kamar ranta zai fita harma bata kula da Bappa ba dake tsaye a dokin ƙofar dariya su Mama Shafa suka kwashe da ita kallo ɗaya Bappa ya musu sukayi saurin gimtsewa ƙwafa yayi sannan ya daga labulen da karfi cikin Fushi “waike Fatima wace irin uwa ce ke keda ya kamata kijata a jiki domin samun sauki rayuwa amma ace ke kike hantarar ta akan ƙaddarar da Allah ya ɗora mata kisani fa ba'a yima Ubangiji shi shigi a cikin lamarin sa matsin da kuke mata bashi zai saka tayi auren ba kisani ita ɗin amana ce a gurin ki idan kika bari ya shiga wata rayuwa a dalilin matsi da takurar da kike mata kisani bayan yafe miki ba.”
Yana gama faɗin haka ya fita fauuu be tsaya jin me zata ce ba rufe firij ɗin tayi ta jingina da shi tana lumshe idanu su suke ganin takura ce amma ita a nata tunani hakan ne zai saka ta fito da miji tayi aure tunda ya daure mata yace sai takwo wanda take so da kanta, kuka take sosai har numfashi ta yana sarkewa me take aikatawa ne da mahaifiyar ta takasa bata yarda ɗari bisa ɗari kiran sallar magriba da aka fara ne ya saka ta miƙewa domin ɗauro alwala idanun ta sun kumbura sunyi jajir ga fuskar ta tayi ja anan ƙofar ɗakin nata tayi alwala ta koma ciki tana sallah tana hawaye banyan ta gama ne ta daga hannu domin yin addu'a sai ta fashe da kuka me karfi tama rasa me zata ce saida hannayen ta suka sanyaye sannan ta sauke su ta kwanta a gurin wani zazzaɓi me zafi ya rufe ta duk da Amma ta shiga damuwa akan rashin ganin Khadijah haka ta daure sai dare da Bappa ya shigo ne yake tambayar Hajara“ina Aunty ku banganta ba?”
“Baffa bata fito ba ɗazu dai naga ta fito alwala magariba taba kuka to ban sake ganinta ba."”
Kallo É—aya yayima Amma ya É—auke kai ya fita É—akin Khadijah ya nufa kai tsaye saida ya haska fitilar wayar shi dan É—akin duhu sosai a kwance ya ganta tana rawar sanyi da sauri ya karasa gurin ta ya tallafo ta "subahanallah Khadijah me yake damunki?"
Kasa magana tayi dan haka ya mayarda ita ya kwantar ya fito cikin murya me amo yake ƙwallawa Nafi'u da hanzari ya fito sauran ƴan mazan ma suna fitowa "yi sauri ka samo abin hawa mukai Khadijah asibiti kar na rasa ta da gudu ya fita Bappa ya koma ɗakin sauran suna biye dashi lokacin Bappa ya fito da ita su Mama Shafa duk sun fito suna tsai tsaye be kula ko waccen su ba haka ya wuce da ita duk da Umar yaso ya karbe ta amma ya hana shi sai kawai suka bisu a baya sun kusa ƙarshen layin saiga Nafi'u da ɗan sahu duka shiga sukayi a lokacin tana ƙoƙarin fisgo numfashi ta asibiti mafi kusa ya kaisu cikin sauri aka karɓe ta Bappa ya kasa zama sai Safa da marwa yakeyi likitan da ya duba ta ne ya fito da sauri ya ƙarasa gurin da yake “likita ya jikin nata?"
Numfashi ya sauke sannan yace "Alhamdulillah yanzu ta fita daga hadari amma Please adaina yi mata abinda zai ɗaga mata hankali domin kuwa jininta yayi mugun hawa yanzu dai mun ɗaura mata ruwa yanzu dai ta sami bacci kuna iya shiga ku ganta amma Please banda haniya.”
Godiya Bappa ya masa sannan suka shiga tana kwance tana bacci a hankali take sauke numfashi a bakin gadon Bappa ya zauna ya kamo hannun ta da babu ɗaurin ruwa akai ƙarasowa Kusa dashi Munir yayi “Bappa ko zaka tafi gida sai mu kwana da ita?”
“ba buƙata kuna iya tafiyar ku ko ni kaɗai na isheta rayuwa.”
Kallon junan su sukayi sai suka koma gefe duk sukayi jugum_jugum a haka har ƙarfe ɗaya ta buga sundai sami ɗayan gadon sun jeru akai Bappa be kula su ba ya miƙe ya shiga banɗaki kallon junan su sukayi “babah wai me yake faruwa ne a gidan naga ran faza ya hau sama.”
Faɗin Fahad da tunda suka zo beyi magana ba Umar ya ɗora akan lips ɗinshi alamar yayi shiru hannu ya saka yayi alamar zip a laɓɓanshi fitowar Bappa ne ya saka su sake nutsuwa kallon su yayi a taƙaice “kai ku tashi ku kama gaban ku kunzo kun cika mana guri.”
Yana gama faɗin haka ya ɗauki mayafinta dake gefe ya shimfiɗa ya tayar da sallah ɗaya bayan daya haka suka fita a harabar asibiti suka tsaya a Mudan ne ya kwashe da wata irin dariya Fahad na tayashi harar su Umar yayi dan shine babba a cikin su “kufa bakuda hankali menene abun dariya kuma?”
“sorry bro amma kalli fa a tsohon daren nan ya koro mu dan ma munyi masa kara mun tsaya akan ibilishiyar ƴar nan tashi yasin faza ji yake kamar ya rufe mu da duka kamar mu muka ɗaura mata ciwon.”
Tsaki Nafi'u ya ja yana yin gaba bayan shi suka bi a kafa suka taka zuwa gida Nafi'u yaja tsaki yafi sau shurin masaki saida suka kusan dambatawa shida Fahad Umar ne ya shiga tsakani suna rufe gida Amma ta fito ganin babu Khadijah babu Bappa ya saka ta tambayar “suna ina ne?”
Fahad ne ya amsa mata da fadin “anbata gado shine faza ya koro mu a tsohon daren nan kamar sheg......”
Talle masa ƙeya da Mudan yayi ne ya sakashi yin shiru yana sosa wajen “Amma ki kwantar da hankalin ki insha Allah zata sami sauƙi zazzaɓi ne kawai kije ki kwanta Bappa zai kula da ita yanda ya dace."
Jinjina masa kai tayi tana share hawayenta da kallo Umar ya bita har ta karasa shigewa numfashi ya sauke yana shafa kanshi washe gari misalin bakwai na safe suka dawo babu wanda Bappa ya kula ya shige ɗakin shi bayan ya raka Khadijah har ɗaki shirin zuwa kasuwa yayi be kula Mama Karima ba da take zaune kayan karyawar ma da ta kawo mashi be kula ba yayi tafiyar shi Amma ma sai bayan azahar ta shiga har ɗakin Khadijah ɗin tana kwance waya a kunnen ta alamar waya takeyi tana ganin ta tayi saurin sauke wayar tana tashi zaune “ashe lafiyarki ƙalau tunda har kina iya waya kedai burinki shine ki kashe min nawa auren tunda kinga mahaifinki yana goya miki baya.”
Rau_rau tayi da idanun da suka cika da hawaye nan take saukowa tayi daga kan katifar ta saka gwiwowin ta a kasa "Amma ba nufi na kenan ba a rayuwa ba nida burin da ya wuce na ganki a cikin farin ciki kiyi hakuri wallahi ba.....”
Hannu ta daga mata alamar tayi shiru dan haka ta haɗiye maganar da takeyi “kedai kika sani Allah na gani na sauke nauyin dake kaina har ɗan gurin Aunty Safeena na kawo miki amma ƙiriƙiri kika watsa min ƙasa a ido waike baki sonshi idan aka ce kece kike korar manema auren ki kice ba haka ba koba gida ba gashi nan sai ki zauna muna gwada ƙafaɗa.”
Tana kawai nan tayi tafiyar ta komawa tayi ta zaune tana zabga uban tagumi ta ma rasa wane kalan tunani zata yi ƙarar da wayar ta tayi ne ya sakata juyawa ta kalle ta ganin sunan Yaya Sulaiman na yawo akan screen ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗaga “my love ya naji kin katse?”
“Ba katsewa nayi ba inaga ko matsalar network ne.”
Murmushi ya saki me sauti Sannan yace “har hankali na ya kwanta kinsan tunda kika fara zuwa aikin nan banida kwanciyar hankali dan gani nake wani me kuɗi zeyi wuf dake a barni da sakaken baki.”
Duk ta bata cikin yanayi saida ta murmusa “kanada abin dariya Ya Sulaiman an gayama akwai wani namiji ne da zai burgeni ne bayan kai ka fa tuna tun ina secondary school muke tare shekara goma fa niɗin takace Ya Sulaiman yanzu dai ina zuwa zanyi wani abu sai munyi waya."
Tana faɗin haka ta sauke wayar tana lumshe idanun ta sannan ta miƙe ta fita tsakar gidan a yatsine fuska mama Karima tayi dan ba ƙaramin ɓacin rai ya kwasa da safen nan ba dan taso tambayar shi kuɗin da ya mata alƙawarin zai bata a yau ɗin nan gashi ta jagula komai gaida su tayi Mama Shafa ce kawai ta amsa amma Mama Karima juyarda kanta ma tayi gefe miƙewa tayi kawai ta nufi ɗakin Amma zama tayi a kasa kafin ta buɗe baki tayi magana ihun yara ya cika mata kunne juyo tayi dan ganin su waye ɗaga labulen wani ƙaramin yaro yayi da bazai wuce shekara biyar ba yayi akan jikin Khadijah ya faɗa “Mamana i miss.”
Murmushi tayi tana me ƙara rungume shi macen ma da ta shigo yanzu ta shiga ture shi “Afif matsa nima.”
Murmushi ta saki tana rungume su gaba É—aya a jikin ta shigowar mahaifiyar yaran ne ya saka Amma fara'a "Beenafa Ć´ar albarka kune a tsakar ranar nan?"
Zaune ta kai akan kujera sannan tace “wallahi kedai Amma daga gidan su muke shine nace bara mu biyo mu gaisa, Allah aunty Khadijah zasu jimiki ciwo bazaku ɗagata ba sai na zo na sameku a gurin.....”
“Babu ruwan ki tunda ba akan jikin ki suke ba.”
Taɓe baki Amma tayi sannan ta miƙe tana kawo mata zobo “gashi kisha rabu dasu tunda ko albarkar gaisuwa bazan samu ba nima na riƙe tawa ƴar.”
Ai kuwa suna jin haka suka bar jikin Khadijah suka yo kan Amma aikuwa ta ce “bazan bayar ba.”
Kallon Amma Khadijah take yi ko ƙyafta idanu batayi tana fatan Allah ya kawo ranar da hakan zata kasance tsakaninta da Amma takanga irin wannan fara'ar ne kawai idan ƙanenta suka zo gidan wato Beenafa da Aneeƙa a nan ne zataga zallan farin ciki akan fuskar ta har taka rasan inda zata ajiye yaran kiran sunan ta da Beenafa tayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula “me kikace Beenafa?”
“cewa nayi ina fatan zaki halarci meeting ɗin da za'ayi a watan nan Aneeƙa ma tace zatazo sannan munyi waya da Sareefa itama zata zo.”
"Yaushe ne za'ayi Allah yasa ba ranar aiki bane?”
Mtsww “kedai naga ranar da zakiyi hankali kisan kin girma koda ranar aiki ce bazaki ajiye ba ki shiga dangi."
Duk shiru sukayi sauke kanta ƙasa tayi kawai idanun ta na cika da hawaye wata magana Beenafa ta dauko dan haka a sanyaye Khadijah ta miƙe ta fita yaran Beenafa suka bi bayanta, Beenafa itace take bi mata su biyar Amma ta haifa Umar ne babba dan auren sa saura sati ɗaya sai ita sannan Beenafa tayi aure harda yara biyu sai Aneeƙa ita kuma yarinyar ta ɗaya tana shiga taga wayar ta na haske dan haka ƙarasawa tayi ta ɗauka kira ne amma har ya zama miss call dan haka ta buɗe taga Ya Sulaiman kiranshi tayi bugu ɗaya ya ɗaga “my love anjima zan shigo gidan aunty Saratu Allah yasa kina iya fitowa sai mu haɗu a gidan nata zuwa shida zanzo insha Allah.”
“babu wata damuwa.”ta amsa masa da zataje dan gidan aunty Saratu na kallon gidan nasu,
Batasan cewa ƙaddara ce zata buɗe mata wani babin shafi daga cikin shafukan ƙadarar rayuwarta ba da tana da masaniyar akan abinda zai faru a ranar ba da bazata amsa masa da zataje ba, a tare da yaran sukayi Sallah la'asar suna a ɗakin misalin biyar da rabi ta jiyo sallamar Zainab abokiyar aikin da sauri ta fito Zainab ɗin na hango ta ta saki murmushi ta fara takowa cikin takunta na ƙwalisa duk da kallo su Mama Shafa suka fita suna gulma da ido da zunɗe bata kula su ba ta tarbe ta cike da fara'a gudun laifi ya sakata yi mata jagora zuwa ɗakin Amma domin ta gaida ta sama_sama suka gaisa sannan suka fito ɗakinta suka shiga sannan ta koma ta siyo mata zoɓo gurin Amma dan tasan ko mahaukacin kare ne ya cije ta bazata fara ɗauka bata biya ba ta ɗan daɗe sannan ta ce mata zata tafi dan haka ta miƙe domin yi mata rakiya saida tayima Amma sallama ita kuma ta gaya mata zata mata rakiya sannan suka fito motar ta, ta buɗe ta shiga “gaskiya gobe ki dawo office gobe tunda naga jikin naki da sauƙi sam yau banji daɗin aiki ba."
Murmushi ta saki sannan tace "insha Allah gobe zanje ai yau ma dan Bappa ya hanani tafiya ne."
Da ƙyar dai sukayi sallama taja motar ta, ta tafi har zata shiga gida sai kuma ta ga babur ɗin Ya Sulaiman a ƙofar gidan aunty Saratu sai kawai ta juya ta shiga ciki a tsakar gidan taga aunty Saratu gaidata tayi cike da girmamawa amsawa tayi a taƙaice kawai dan haka ta miƙe ta shiga falon aunty da taga takalmin ya Sulaiman labulen ta daga bakinta ɗauke da sallama miƙewa yayi yana buɗe hannayen sa "oyoyo my love."
Kaucewa tayi tana murmushi ta zauna akan two siter shima karasowa yayi ya zauna akan kujerar fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi “amaryata takaina.”
Hannayen ta, ta saka tana rufe fuskar ta “Allah a matse nake naganki a matsayin matana."
"Insha Allah Ya Sulaiman lokaci ya kusa kaine ruhina farin cikin raina."
"Insha Allah kin kusa wuce tsangwamar mutane zan ɗauke ki gaba ɗaya sai kin shekara biyu baki fita ko ƙofar gida ba me ya faru ne jiya har aka kwanta dake asibiti a daren jiya?"
Labarin abinda ya faru tsakanin ta da Amma jiya ta bashi dan babu abinda take ɓoye masa a rayuwar ta tunda shiɗin dan uwane a gare ta ko yanzu kuka take sosai alamar abin na ci mata rai rungumota yayi jikin shi yana lallashi basu ankara ba sai jin kukan aunty sukayi akan su a zabure ta ƙwace jikinta daga nashi......