MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 55

by @maimunabala209

MATAR GIDA BOOK 2



SHUUKRAN/022


YOTA ASSOCAITION




P55


Unaisa na can bakin fanfo tana wanken  tukwane ta ji ƙhamshin turaren wuta ya daki hancinta cike da ɓacin rai ta yi magana murya can ƙasa ta ce ''maiyya'' a can wajen Amirah karfe huɗu da wasu da ƴan mintina ta gama girki,flask ta dauko ta fara ƙulla tuwo cikin leda tana jera su cikin flask,wasu manyan tray guda biyu masu faɗi ta dauko ta sawa su Sudais da Ummu Abiha tuwo bayan ta gama shirya tuwo fita ta yi daga kitchen zuwa parlour inda ta tarar Ɗalha zaune ya mayar da hankali kan su Sudais dake cin abinci,ganin Ɗalha zaune wajen yasa su Sudais cin abinci ba tare da faɗa da junan su ba,kujera one siter Amirah ta zauna tare da faɗin ''ashe kana nan na zaci ka shiga ciki'' Ɗalha dake kallonta tun sanda ta fito daga kitchen ya ce ''a'a yanzu na dawo daga masallaci'' Amirah ta ce ''ok'' ta faɗa tare da miƙewa tsaye Ɗalha ya dakatar da ita ta hanyar faɗin ''ina nawa abincin? yaran ki kaɗai ki ka wa girki?" murmushi Amirah ta yi tare da mayar da dubanta garesa ta ce ''gaskiya ban dafa da kai ba'' gyara zama Ɗalha ya yi fuskarsa cike da mamaki ya ce ''ban gane ba'' murmushi kawai Amirah ta yi ta wuce kitchen Ɗalha ya bita da ido,bayan shigarta kitchen kwanukan da ta yi amfani da su ta haɗa ta fara wankewa tana nan tsaye wajen sink Ɗalha ya shigo,tun ɗazu yake zaune parlour yana jiran ta gama abinci,tun da ya ji ƙhamshin miyarta yawunsa suka tsinke yana Allah Allah ta gama ta sa masa,yanzu kuma ta ce banda shi cikin abinci shi da yake murna yau zai ce abinci mai kyau,sosai ya yi kewar girkin ta,kallo ɗaya Amirah ta yi masa ta mayar da hankali kan wanke wanke da take,a hankali Ɗalha ya tako har inda take tsaye kawai sai jinsa ta yi ya rungumeta ta baya tare da daura haɓarsa a kafaɗarta idanunsa kan kwanukan da take wankewa ya yi magana cikin wata murya sosai ya kwantar da murya ya ce '' Please save me some l'm very hungry'' ya kare magana yana wasa da hannusa a jikinta yadda yake yawo da hannusa a jikinta Amirah bata san sanda ta rintsa idanunta ba tare da dakatar da abinda take ganin haka Ɗalha ya manna mata ligth kiss a wuya cikin wani irin yanayi Amirah ta ce ''stop Please yara suna parlour'' cikin muryar da bai fita da kyau Ɗalha ya ce ''and so?" Amirah ta rasa yadda zata yi da shi kawai ta juyo a hankali suna fuskantar juna tana jan numfashi ta ce ''cika ni na sa maka'' babu musu Ɗalha ya cire hannusa a ƙugunta, yana nan tsaye kitchen ta dauki wormer zata sa masa tuwo ya ce a'a ta sa masa a plate,da to kawai Amirah ta amsa daga haka ta sa masa,ta kai masa parlour yana biye da ita kamar jela,zama Ɗalha ya yi cikin parlour ya fara cin abinci bayan ya wanke hannu cikin wata roba da Amirah ta zuba ruwa a ciki ta ajiye masa,kallo ɗaya Amirah ta yiwa Ɗalha ta fahimci ya daɗe bai samu abincin mai kyau ya ci ba ganin yadda yake cin tuwo,a can wajen Ɗalha kuwa albarka ya rinƙa sawa Amirah cikin zuciyarsa tuwon ya tuƙu da kyau ga miyar ta ji kifi ya kuma nuna da kyau,bayan su Sudais sun gama cin abinci sun kai tray kitchen Amirah ta wanke ta sa su wanke hannu sun goge baki daga haka ta haɗa kansu ta yi masu wanka,bayan ta gama masu wanka ta yi nata,karfe takwas daidai Amirah da yara ne zaune cikin parlourn,yaran suna wasa Amirah na zaune kan kujera ta rintsa ido tare da kwantar da bayanta jikin kujera gajiya ne cike jikinta tana nan zaune wayarta ta yi ƙara alamar shigar kira,daukar wayar ta yi ta ga Ɗalha ne ke kira kafe fuskar wayar ta yi da ido can ta amsa kiran tana sallama ba tare da ya amsa sallamar ta ba ya ce ''muna jira ki a main parlour'' daga haka ya kashe wayarsa a hankali Amirah ta cire wayar a kunne tana kallon wayar tana mamaki shi da wa suke jiranta a parlour can dai wata tunani ta faɗo mata kila sun yi baƙi ne, da wannan tunani Amirah ta tashi ta shiga ɗaki ta dauki wata koriyar hijab ɗinta har ƙasa ta zura daga haka ta fita daga ɗakin,bakin ta dauke da sallama ta shiga parlour, Ɗalha na zaune kan kujera one siter yana danna waya,daga can gefensa kuwa Unaisa ce zaune kan kujera two siter itama hannuta riƙe da waya tana dannawa, sweatsuit da ta sa tun safe shine a jikinta har yanzu kanta babu danƙwali,ga sumar ta ya sauka har kafaɗarta,ta daura fararen kafafuwanta dake cikin bathroom slippers ɗaya kan ɗaya,irin zaman da Unaisa ta yi ya kara fitar da kyau da diri da Allah ya mata mace har mace,wani irin sihirtaccen ƙhamshi mai kwantar da hankali da sanya nitsuwa ne ya gauraye gaba ɗaya parlourn,a hankali Ɗalha ya ɗago tare da mayar da dubansa ga Amirah yana amsa mata sallama ita ko Unaisa bata amsa sallamar ba kawai ta kafe Amirah da ido tun haɗuwar ta da Ɗalha bata taɓa ganin Amirah ba ko a huto hasalima bata gabanta,Unaisa ta ƙasa dauke idonta daga Amirah,sosai Amirah ta yi mata kyau da gani ba mai son hayaniya bace sai yanzu ta fahimci inda su Sudais sun sami hasken fatarsu,ɓoyayyar ajiyar zuciya Unaisa ta sauke cikin zuciyarta ta ce har ita ma ƙhamshin take,wai wani irin ƙhamshi ne haka Unaisa ta faɗa cikin zucuyarta tare da gyara zama ta sauke kafarta ƙasa,tana ƙara kallon Amirah,ƙhamshin da Amirah da yaranta ke yi ba irin kahmshin nan bane wanda daga ji zaka san mutum ya fesa turare a'a wani irin kahmshi ne dake nuna yawan ta'amali da turare da mutum ke yi da kuma tsafta,ɗazu bayan Ɗalha ya koma bangaren Unaisa ta ji kahmshin a jikinsa,ranar da su Sudais sun shiga ɓangaren Unaisa a kano saida parlournta ya yi kwana uku yana ƙhamshin jikinsu Sudais


















Kan Amirah ƙasa ta shiga cikin parlour ta samu waje ta zauna kan kujera one siter tana fuskantar Unaisa bayan Amirah ta zauna Unaisa ta yi saurin kawar da kai ta cigaba da danna wayarta, Amirah da tun shigar bata ɗaga kai ta kalle ko da mutum ɗaya cikin su ba,ta ɗago a hankali karaf idonta ya sauka kan Unaisa cikin wani irin yanayi Amirah ta kara buɗe ido da kyau ta kalle Unaisa cikin zuciyarta ta tambaye kanta wace wannan a ina Ɗalha ya samo ta,wani tunani ne ya faɗo mata ta yi saurin mayar da dubanta ga Ɗalha shima ita yake kallo yana sakar mata murmushi ita dai kanta ya ƙulle tana addu'a Allah a yasa ba abinda take tunani bane in har wannan ce kishiyarta tofa tabbas aiki ya same ta,lokaci guda Amirah ta ji ta ƙosa tana son sanin matsayin wannan buzuwar da Ɗalha ya shigo mata da ita ko shuwa ce oho,gaba ɗaya kyawun fuskar Unaisa da dirin jikinta yasa Amirah na shirin rasa nitsuwarta ko brazie babu jikin Unaisa amma kirjin a tsaye kam ga hips masha Allah ga hasken fata,gaba ɗaya fatar ta bata yi kama da ƴan Nigeria ba,cike da ƙarfin hali Amirah ta sakarwa Ɗalha murmushi ta ce ''barka da hutawa dear, ka kira ni'' ta ƙare magana tare da langwaɓar da kai cikin wani irin yanayi Unaisa ta ɗago tana kallon Ɗalha da Amirah gyara zama Ɗalha ya yi kafin ya mayar da dubansa ga Unaisa dake binsa da wani mugun kallo murmushin gefen baki Ɗalha ya yi ganin irin kallon da Unaisa ke masa kawai ya basar ya ce ''amarya ga yayarki matata Amirah Mumyns su Sudais'' be jira cewar Unaisa ba ya mayar da dubansa ga Amirah ya ce ''ga kanwarki Unaisa antyn su Sudais'' wani irin bugu zuciyar Amirah ya yi nan take ta ji jikinta ya yi mata wani irin sanyi,duk irin sanyi da ake cikin wannan daren ga kuma fanka dake hura iska a parlour harda ba wani gudu fankar yake sosai ba amma parlourn ya dauki sanyi sosai duk irin wannan sanyi ya riƙeɗa ya koma zafi a wajen Amirah wani irin zufa ya faso mata,bata san da me zata kira yanayin da take yanzu ba,tsoro ko kishi tana cikin wannan yanayi taji jikinta kamar ba nata ba gangar jikinta na niman rabuwa da ruhinta,daga Unaisa har Amirah ko wacce ta kafe ƴar uwarta da ido ko wacce da abinda zuciyarta ke karanto mata cike da kwarin gwiwa Amirah ta buɗe baki ta ce ''masha Allah'' ta faɗa tana kallon Unaisa,ita dai Unaisa ta yi shiru kamar bata parlourn Ɗalha ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ''ba ki gaida yayarki ba'' wani irin kallo Unaisa ta yi masa irin kallon nan na me ka ke nufi,ita dai Amirah sai faman murmushi take wanda ya fi kuka ciwo,ba da son ran Unaisa ba ta ajiye wayar hanunta tare da gyara sumarta ta mayar da shi baya, murya can ciki ta ce ''barka da dare ya yara ya kwana biyu'' da kyar Amirah ta iya amsawa Unaisa gaisuwa zagin murya Unaisa yasa hankali Amirah kara tashi amma sai ta danne zuciyata ta basar ta faɗaɗa fara'arta ta ce ''lafiya ƙlau amarya ya sabon wuri?" a daƙeli Unaisa ta ce ''alhamdulillah'' shi dai Ɗalha binsu kawai yake da ido abinda ya fahimta shine za a iya samun matsala daga Unaisa ga dukkan alamu tana da zafin kishi,gyara zama ya yi kafin ya shiga masu nasiha kan zamantakewar ya dauki sama da mintina talatin yana masu nasiha kan sun haɗa kawunansu su zauna lafiya daga karshe ya tambaye su maganar girki kwana nawa duke ganin ya dace, karaf Unaisa ta ce ''ni dai bazan haɗa girki ba zan riƙa yin nawa daban ita kuma ta yi nata da yaranta saboda ba zan iya daura babban tukunya ba'' ta kare magana fuska haɗe,cike da mamaki Amirah ke kallonta can ta mayar da dubanta ga Ɗalha dan jin abinda zai faɗa ganin yanayin da Unaisa ta yi magana cike da rashin kunya a tunanin Amirah Ɗalha zai tsawatar wa Unaisa sai kuma taga ya yi shiru bai ce komai ba,can ya mayar da dubansa ga Unaisa ya yi magana cikin kwantar da murya ya ce ''ki yi hakuri yadda Amirah ta faɗa haka za a yi ita ce babba ita ke da yara a gidan nan,sannan zuwa ki ka yi kika samita saboda haka ta fiki sanin yadda a ke riƙe gida da kula da gida'' Amirah dake zaune ta ji zantuka Ɗalha kamar a mafarki hakan yasa ta goge ido cike da mamaki take kallon Ɗalha ko dai mafarki ne hakan yasa ta kai hannu ta mitsile hannuta,bayan ta tabbatar ba mafarki take ba wani irin natsuwar zuciya ya ziyarce ta lokaci guda, can kasan zuciyarta kuwa farin cike ne fal,duk wani yanayin damuwa da fargaba da ta shiga ɗazu ta nema ta rasa,ta ji gaba ɗaya ta dawo hayyacin ta zuciyarta ta yi sanyi bata san sanda ta sake wani ƙawatatciyar murmushi ba, ita yau Ɗalha ya daukaka darajarta gaban kishiya,sunkuyar da kai ƙasa Amirah ta yi tana yiwa Allah godiya cikin zuciyarta,ita kanta ta ji daɗin maganar da Unaisa ta yi saboda tun sanda Ɗalha ya ƙara aure take tunanin yadda zata yi kan batun girki sanin kanta ne yaranta basu cika son cin abinci wani ba hasalima basa iya sakin jiki su ci abinci daga abincinta sai in sun je Kano gidan Ammi,abu na biyu da Amirah ke fargaba shine bata da tabbacin amaryar da Ɗalha ya aura ta iya girki saboda da yawa yawan ƴan matan yanzu basu iya girki ba,wanna dalilin yasa Amirah ta ji dadin kalaman Unaisa Ɗalha ya mayar da dubansa ga Amirah ya ce ''ki yi magana ke ce babba'' cike da sanyin murya ta ce ''na amince hakan ya yi kowacce ta yi girkin ta'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''batun kwana kuma fa kwana nawa ku ke son a raba?" duk suka yi shiru can Amirah ta ce ''l think two days will be fine'' Ɗalha ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ''ke fa?" wani harara ta banko masa kafin ta ce ''matar gidan ta yi magana wacce ni,kwanaki biyu ya yi tun da haka ta faɗa'' ta kare magana tana murguɗa masa baki,gyara zaman Ɗalha ya yi ya mayar da dubansa ga Unaisa ya fara magana in a very serious way ya ce ''kin san Allah duk rashin kunyar ki kar ki sake ki sa matata a ciki kina jina ki tsaya iya ni,in kuma kina son ganin ɓacin raina ki mata rashin kunya'' taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta ce ''na nawa kuma'' ta faɗa tana juya ido Amirah da ke zaune mamaki ya gama kashe ta sai binsu take da ido baki buɗe can ta saki murmushi tare da miƙewa tsaye ta mayar da dubanta ga Ɗalha cikin kwantar da murya ta ce ''in babu wani abu ina so zan shiga zan yiwa yara shimfiɗa'' Ɗalha da ransa ya gama ɓaci yana huci ya ce ''ok is fine'' cike da natsuwa Amirah ta wuce bangarenta tana ƙara mamakin halaiyar Unaisa kasan zuciyarta kuwa murna take Allah ya haɗa Ɗalha da maganinsa,bayan shigar Amirah cike da ɓacin rai Unaisa ta tashi ta bar parlourn murya can ƙasa ta ce ''munafuka''ta faɗa tare da shiga ɓangarenta 














SHUUKRAN