MAKAUNIYYAR SOYAYYA

Page 1

by @mukarramat231

Wannan labarin kerariya ne,kama daga suna,waje,da guri.

Idan labarin nan yayi kama ceceniya da labarin ka/ki a yafe min,kafin alkalami ne.




BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM

   “MAKAUNIYYAR SOYAYYA”
 

    Written
By


       Mukaramat Yusuf

Page 1

INTER_NATIONAL MEDICINE AND SURGERY UNIVERSITY(LAGO'S)
Male hostel

Karfe 12 na dare, tele phone ne ya soma kada wa,da alamu kira ake,da sauri wani matashi ya tashi daga kan katifa'r da yake kwance ya nufi wajan da ya ji tele phone din na kara,sawa a kuni yayi,a dayan bangaren kuma yaji ance:way…wayy …..wayyo allah,aka qwarma ihu, sannan aka cigaba da magana,kazo ka taimaka min kaji,sir Kashim na san ya ci min zarafi,yash ka zo ka ceceni.

    Mutumin da aka kira da yash ya aje tele phone din a ma'ajiyar sa,fitowa yayi da gudu ya nufi female hostel dake makarantar.
  FEMALE HOSTEL
Kai,kai waye ya ce ka taba ta,wannan matashi dan saurayi me suna yash ya furta,lokaci guda yana shigo wa dakin ta,ganin sir Kashim a dakin yana da'go ta,lokaci guda yana jijiga ta,da alamu ta suma ko tana ƙoƙarin ta suma,da gudu yash ya kariso inda sir Kashim yake ya sha ke masa wuya,yana fadin sai na kashe ka,sai na hallaka ka,shi kuwa sir Kashim sai ihun niman a gaji yake,kan kace kwabo har Dalibai sun tashi,kowa ya nufi dakin sofeeya,a Male hostel kuwa karara wa suka ji ana bugawa a female hostel, sun San ba lafiya,da sauri ko wannan su ya tashi suka nufi female hostel,daker aka kwato sir Kashim daga hannun yash,don kuwa har ya suma,shi kuwa yash sake birkice wa yayi,tunawa da sir Kashim na kokarin yiwa feeya dinsa fyade, maganar ya kara ingiza shi,yasa ya koma tamkar mahaukaci,da taimakon security suka samu suka daure sa.
Masu makarantar kuwa female president ta kira aka sanar masu halin da ake ciki a makaranta,nan da nan chancellor din makarantar ta iso,motoshin en sanda da amblulance biye da ita a baya,sir Kashim da sofeeya aka sanya su cikin motar amblulance,aka yi gaba dasu,shi kuwa yash tambayan sa aka yi ,me ya faru?abun da feeya ta fada masa shi ya fada masu,hand copes aka sanya masa a hannun sa,akayi gaba dashi.


Ba zamu taɓa ka ba,har sai mun ji daga sofeeya Ade kunle, kafin mu dauki hukunci, washegari da safe aka sanar cewa sir Hashim ya farfaɗo daga sumar da yayi,da sauri polisa wa suka nufi asibitin,😀
Inspector yace:sir Kashim muna san ka fada mana gaskiya, sir Kashim yace:ok sir
Inspector yace:me ya kai ka dakin sofeeya Ade kunle?,sir Kashim yace: ina zaune ina yin makin,sai naga ɗaliba ta sofeeya na kira na,i was shocked akan abun da ta fada min, banyi wata -wata ba na nufi wajan security na tambaye number dakin sofeeya,shine suka bani inspector ya kara kusanto wa da wayansa,da alamu yana nadar komai,yace:amma me ta gaya maka? Sir Kashim yace:ta kira Ni ne tana kuka tana fadin kazo ka taimake Ni,yash ne zai keta mata hadin ta,da kuma Nazo sai na gan jini a jikin ta, da alamu an mata duka, har ta suma,shine nake kokarin ceto ta,naji yash ya shake min wuya,sir Kashim ya karike maganar yana share guntun qwalar sa, inspector yace: alright naji bangaran ka saura ita wannan yarinyar.

Sai bayan sallar isha sofeeya ta farfaɗo,nan da nan kawar ta sanan president din matar makarantar ta kira likita,nan likita ya duba ta yace:zuwa gobe zasu sallame ta,a daren inspector yazo dubiya sannan ya tambaye ta:me ya faru ?
Sofeeya tace: a jiya da misalin karfe 11 na dare yash ya shigo female hostel har daki na ya shigo yayi min rashin da'a,yace dani na sumbace shi,Ni kuma na kiye sai ya fara min wasu dabi'u da bansan sa da shi ba,dana ki basa hadin kai sai ya mun duka, inspector yace:wace ce room mate dinki? Sofeeya tace:female president ce:kallon female president inspector yayi yace:a lokacin da abun nan ya faru kina ina? Gyara zama ilham tayi sannan tace:bana school din,sati na biyu na koma gida sakamakon mahaifiya ta da ta rasu,sai jiya da dare,na dawo, shine na tarar da abun da ke faruwa,na buga kararawa sannan na kira masu makarantar, nan inspector din yace: mun gode da kika bamu hadin kai.ya kali sofeeya yace:Bamu address din gidan ku? sofeeya tace:sir kada a gayawa iyaye na batun nan,don mahaifina na da ciwon zuciya,muddun ya ji batun nan, ciwon shi zai tashi,nan inspector yace:toa maganar nan a rufe ta anan,amman sai an kai kotu,sosai a ranan yash yasha duka,ba kaɗan ba,yayi matukar kariya jin abun da feeya dinsa ta fadi,mace'n da ya dauke ta a matsayin mahaifiyar sa,don bai taba samun gatar mahaifiya a Duniyar sa ba,ya riga ya san babu wata mace da zata cika masa gurbin mahaifiya,amma yana buƙatar kulawa ta musamman daga wajan mace,a duk lokacin da yake tare da feeya toa ba ya jin ya rasa wani abu,akan ta yayi fada da abokansa ,harda abokin dakin sa,akan ta yayi komai,don kar su rabu.
  FLASH BACK

KANO
Da misalin ƙarfe 6 na yamma,wasu yara ne tsaye a wajan window din mahaifiyar su,sanye da uniform din islamiyya,da alamu da wowar su kenan,Yash,Ameer kar ku shigo ciki,wuta ne ke tashi,har ya cinye rabin falo,kuma na kira water service Amma har yanzu basu iso ba,na riga na san mutuwa zan , wutan na ta ci,su Abubakar ma kacewa wa suke,amma kamar ana kara wa wutar fetur,Ameer ka rike kanin ka yash,kada ka cutar dashi,Yash,ka rike ya'yan ka da hannu bibbiyu,kada ka cutar dashi,idan kuka samu mace, mai tarbiyya ku sota ku aure ta ,kada ku bari MAKAUNIYYAR SOYAYYA tayi galaba a kan ku, watakila wannan shine nasiha na na karshe a gare ku yarana, Sannan kuji tsoron Allah, nan ta jefa masu abin da yake hannun ta  
Ingo! Ku bar nan ,ta fadi lokaci guda tana jefowa wasu yara kayan su,tare da wani file,da alamu yana da mahimmanci a rayuwar ta,ta cigaba da cewa,ku tafi ku bar nan,kar wutan nan ya haɗa da ku,Abba na nan zuwa daukan ku,
Kar kuje da nisa,mama ki fito ,gamu mun dawo Ni danki Ameer da dan uwansa yash,ku tafi,kuce ma Abba ya yafemin,ta furta lokaci guda tana kallon wutan gobara dake tunkaro ta,ta kalli window ta ga yaranta na ta kwar ma ihun sunanta,ga wasu matasa na zuwa da ruwa a cikin robbar fainty,wasu kuma a cikin jarka,wasu na zubawa gidan kasa,Allah ya muku albarka,nan tayi kalmar shahada har wutan ya riske ta,nan da nan motar kashe wuta ya iso angwar,bayan da komai ya gama lafawa kamar ba a’yi gobara ba.
Sosai su Yash sunsha kuka kamar ba gobe,ganin yadda mace mafi soyuwa a zuciyar su ta rasu, Allah'n da yafi kaunar ta ya dauke masu ita,wanka aka mata aka mata jana'iza,aka kaita gidan ta na gaskiya,sai karfe 10 na dare abban su yazo ya dauke su,a ranar suka wuce Abuja.


Washe gari,A wani makeken daki suka samu kansu,da alamu ma basu san an kawo su ba,kwance a kan gado sunyi lublub,a kan gadon,a hankali Ameer ya tashi Yash daga barshi yace:yash,hanya wannan mutumin shine baban mu,mu bamu tapa ganin sa ba,sannan mama bata gaya mana waye mahaifin mu ba,sai dai tace shi din baban mutun ne,Yash ya sosa idanuwanshi sannan yace:ok,idan ka gama sai ka taso muyi Salan asuba, lokaci guda yana mike wa daga kan makeken gadon da suka yi barshi a kai.
Bayan sun hidar da Sallah,suka nufa falo,hotuna birjin suka gani a jikin bango,na mai gidan da matarshi,bana fada maka ba? Wannan mutumin ba shine mahaifiyan muba,fadin Ameer lokaci guda yana dakatawa daga tafi yar da yake yi,kafin yash yace wani abu, suka ga wata mata ta fito hannun ta rike da tray,wanda aka kawata shi da kayan lambu a ciki,Yash and amer right?matar ta fadi hakan dalla_ dalla,ta cigaba da fadin:You are higly welcome to commissioner of police house,tana kai wa nan tayi wuce War ta,Yash yace:dan uwa sai addu'a fa,ashe mahaifiyan namu police ne?fadin Ameer yana wani kalan murmushi,Yash Yace:ba yanzu ka gama tanta ma ko shi Mahaifin mune ko a'a ba?ko shi mahaifin mu ne ko a'a,Ni Ameer na dauke shi a matsayin mahaifi,yana kaiwa nan ya wuce daining. 

CIGABAN LABARIN


Ku haɗa shocking din Nan, inspector ya fadi, haɗa wa sukayi a ka jona masa,a ranan ya sha wuya sosai, washegari aka dibo en makarantar su dan kowa ya tofa albarkacin bakinsa, yana ganin Aliyu ya rikice watoa room mate din sa,yash yace:yawa Aliyu Dan Allah ka fada masu gaskiya,Aliyu ya zauna a gaban inspector yace:sir,kwana biyun nan yash na birki cewa ,idan aka bata masa rai,toa tamkar daba ya ke komawa,baya sauran kowa sai zuciyar sa,dan Allah inspector a karbar ma yarinyar nan hakin ta, yana kaiwa nan ya kalli yash sannan ya kalli inspector yace:zan iya tafiya sir? inspector yace:yh,You are free to go,shi kuwa yash aka kaisa dakin duhu,dukan yau daban na gobe daban.


Dan Allah sofeeya,ki janye case din nan,kinji, a'i naga ko a makaranta za mu iya warware matsalolin mu, sofeeya tace:ilham baza ki gane ba,idan kanwar kice a cikin wannan yanayin,shin zaki tsaya kallon ruwa ne e'? toa ki sani sai an kai maganar nan kotu, sannan a yanke masa hukunci,a matsayin ki na female president yaka mata ki fito zanga_zanga cewa sai an qwatowa wata hakin ta , amma kece kike cewa na janye case dina, ta karike maganar tana daga girar ta sama, lokaci guda tana fita daga dakin,don bata san ilham ta gane cewa dadi take ji ,mudun ta ga ilham din ta shiga damuwa.

  Bayan sati biyu,me girma me Shari'a, bisa da hujjar da muka kawo,ina niman alfarmar kotun nan mai albarka ya yanke masa hukunci a sauka ke, don kuwa lalai yaran nan na da ciwon ƙwaƙwalwa, a shekarar 1818 lokacin yana shekara 15 ya kace mahaifin sa, Watoa commissional of police na abuja,sir Ammar abdul rahaman,nan lawyar dake kare sofeeya ya mika ma barrister kundin case din commissional of police, a mamake en makarantar su ke kalan sa ,jin shi ya kashe mahaifin sa, barrister yace:kotun nan mai albarka ya yanke ma yash Ammar Abdul Rahaman,hukuncin zama a gidan yarii,na shekara 5,sannan wannan kotun zai tura sa gidan mahauka tai,har sai ya samu lafiya.


I rise,barrister din yafada lokaci guda yana buga abun bugawar sa ,kotu¡!!nan kowa ya mike tsaye.
,en sanda kuma suka tasa keyar yash zuwa waje.


 Dada,dan Allah kayi wani abu,kasan ina matuƙar sansa, soyayya ba wasa bane, zuciya ta belong to only him yash,fadin wata matashiyar budurwa,fara ce tsa'ul,kamar ka taba fatar ta jini ya fito, hannun ta rike da wata waya ipart,wanda ban taba gani ba,a saye take ,wani riga da wando ne punjamis a jikin ta, rolling veil tayi,ga gashin ta, wanda ya sha gyara baki wuluk kuwa malale a kan gadon bayan ta,daga ganinta an san jinin yar shuwa Arab ce,amma yadda take magana kasa kasa tare da izza a Muryar ta kasan yar kabilar yar’bawa ce ,Aikin gama ya gama don kuwa har an yanke masa hukunci,aka fada a dayan bangaren,Dada ya cigaba da cewa:ki kwantar da hankalin ki,ilham,kinji, kafin ta furta wani abu taji wayar ya dauke,da alamu babu chargy,da sauri ta juya ganin barrister na kokarin ciga mota,tace:sir can I see you for a moment? barrister yace:no way,here is my business card, message me in WhatsApp, barrister ya karike maganar da yake lokaci guda yana mika mata card number dinsa,amsa tayi da sauri tace thanks.dai dai lokacin aka fito da yash,sosai ya rame ,ya fita a' hayacin sa,tamkar bashi ba,sosai yayi duhu fatar nan tashi ya yi baki sosai,amma ba sosai ba,a idanuwan ta aka sanya sa cikin motar en sanda,yaya de,da fatan komai lafiya?fadin sofeeya,babu komai ,ilham ta amsa mata tambayar ta,amma na shiga sha’ku fa,fadin sofeeya, ilham ta kali sofeeya ta ce:i need to rest,bye 🙏🙏

  Rail high way,apapa Lagos

       (Jail) 
Bayan sati 2,ilham ta kawowa yash ziyara,tare da dada suka zo,amma bai bita ba,a office din I .p .s of police na jail a wajan dada ya zauna,yana kallon wasu case a cikin hand folder dinshi,a hankali aka kawo yash wajan kanta ,sosai wannan karon ya changer,kamar ba dan kwalissar nan ba,yana ganin ilham,abubuwa da yawa suka soma dawo masa ,ya soma ihu yana fadin ina feeyarh?eh ina take?nan ya soma ihu,ganin yadda soyayyar yarinyar nan ta gama haukace sa, daker aka samu aka mayar dashi dakin sa,kuka ta fashe dashi tana fadin nasan baka aika ta ba,amma soyayya ya rufe maka idanuwa ,ka koma tamkar mahaukaci,nan ta goge qwalar idanun ta,jin motsin kamar Dada na zuwa,don kuwa polisa wan gurin ta gani suna sara wa,yar kulan abincin da ta riko masa,ta mika ma wata sabuwar ma'i kaciya da umurnin ta basa inji ilham,tana juyowa suka yi ido biyu da dada'n ta , murmushi tayi masa,wanda bai kai zuciya ba,tsabar bata san Dada ya gane kuka take yi,a mota ta zauna har sanda ya gama ayukanshi ya fito,suka dau hanyar makarantar su,a harabar makarantar su motar Dada ta tsaya,fitowa tayi ta nufi dakin su, tana tunanin abun da ya faru a yau , lailai zamansa a ‘ jail zai kara haukatar da shi, gwara a kaisa” care and special mental health care hospital”.
 Business card din wannan barrister ta fito dashi,a whats'app suka hadu bayanin yash tayi masa, sannan tace tana da bukatar a sake sa,ko nawa ne kudin belin ita zata biya.











Wannan labarin kerariya ne,kama daga suna,waje da guri

Idan wannan labarin yayi kama da labarin ka/ki toa a yafe min,kafin alkalami ne.


  BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM


“MAKAUNIYYAR SOYAYYA”
    

Written

      By

Mukaramat Yusuf

   Page 2

Barrister yace:ko nawa fa kika ce zaki biya?
Ilham tace:eh barrister
Barrister ya cigaba da cewa:zan baki wasu takar du,ina bukatar a sanya hannu a kai, sannan ku biya kudin belin sa, ilham tace:toa ka turo min takar dun,ina Jira a faty coffee drinks,yace:toa zan turo miki,daga haka suka yi salama.


Karfe taran dare,babu motsin da ake ji a harabar makarantar,ko ina shiru yake,a daki mai lamba 25 upstairs, bulb din dakin kadai a kune yake,don kowa a makarantar bulb dinsa a kashe yake,da alamu sunyi barci,
Wayyo,Dada na kuma,wai ake buƙatar sanya hanun sa,watoa general sultan Usman, shugaban dss,fadin ilham lokaci guda tana buɗe next papper,Wanda ta amso a hannun barrister dazu, i ps of jail,sir Sadiq salis ade _ wole,sai inspector hassanu akanbi,kare wa hoton inspector tayi sannan tace:kai kadai ne zaka bani wuya,Amman akan masoyi na,zan iya yin komai,ba zan kariya ba,nan ta rufe files din,ta sanya su a cikin drower,wayar ta ta dauka,ta shiga contact din ta, number sofeeya ta kira,bugu daya,biyu,a na ukun ta daga, ilham tace:shin zaki dawo gida ko na rufe kofar?kida sama -sama takeji,tamkar a gidan rawa take,cikin Muryar maye sofeeya tace:ki kwanta abun ki, ki yi barci,sai gobe,diiii,diiiiii,diiiiii
Kuke ji da alamu ta katse kiran, addu'a ilham tayi ta kwanta.



Bayan sati Daya,sosai ta rame,tsabar aikin Beli da tasa a gabanta wanda yafi kara tunta mahimmanci a rayuwar ta, ta Bama maganar Beli mahimmanci a rayuwar ta,karatun ta ta aje a gefe,ta Bama case din 99.9percent,karatun ta kuma 1percent,tsaye take a gaban dada ,idanuwanta gwaje-gwaje da hawaye da alamu kuka take,Dada ka samin hannu kaji,Dada yace:duk abubuwan nan da nake gaya maki wai baki ji, lalai wannan shine MAKAUNIYYAR SOYAYYA,soyayyar da kike yi masa , baya gani, ilham tace:kasan Ni amana ce a gare ka,toa muddun baka san rasani,ka sa min hannu,tana kai wa nan ta fice,tamkar zata tashi sama.
Ranki ya dade:gashi nan fitowa,mun baku minti 3,fadin wata polis, ilham tace:toa nagode 🥰🥰🥰🥰💞💞💞
Nan aka shigo da yash,wani office inda ilham take,kalo daya ya mata , ya kauda kai,tace:kada kamin haka, ka san ina sanka,ina san ka bani wajan kwana a cikin zuciyar ka,ina son ko wani bugun zuciyar ka ya buga da suna na,No way,ya furta a hankali,a iya tsakanin lips dinsa.
Ka saurare Ni kaji, bana san rabuwa da kai,nan ta nuna masa rist watch din hannun ta,tace:na kamu da ciwon zuciya saboda kai,ko Dada bai sani ba,ka tai maka min,kaji🙆,wanka mata mari yayi sannan yace:ki fita harkana,bana san hadda hanya da ke,ki tambaye feeyarh mesa bata sona,kuka ta fashe dashi ,tace:ina matuƙar sanka,kada kace a'a,wanka mata mari ya kuma yi,a lokacin aka turo kofa aka shigo,Dada ta gani da alamu a fisace yake,mari ya wanka ma yash,kai baka da hankali ne,ya’r ta zaka mara,ba ki jin magana na,ya kali ilham ya cigaba da cewa:ba zan bari wannan ya wulakanta min ke ba,a yau zaki je London,Dada waye ya saka ka taba min shi?gani yash ya min duka, mudun haka zai sa ka so ni,sannan ka huce, a fisace Dada ya ja hannun ta suka fice,a mota ya sata sannan ya kulleta,sai bayan sallar azabar ya shigo motar,ki saurare Ni kinji,gobe da Misalin karfe 9’nsafe jirgin ku zai tashi daga Nigeria zuwa London, ilham tace:Ni Dada bazan je ba! Umurni nake baki,kafin 8 na safe ya yi ki tabbata kin shirya,don secetariya ta ce za ta zo daukan ki,kuje tare,fadin Dada lokaci guda yana tada motar sa.a harabar makarantar yayi parking,ya kalli ilham yace:bani wayar ki, wayan Tata ta bashi,tace:Dada shin har yanzu zaka cigaba da fushi da Ni?ina mai rokon ka, da ka sanya min hannu a wannan takardar,Ni dana zaci ba sai na baka hakuri kamin zaka samin hannu ba, sai gani ina baka hakuri , murmushi yayi,wanda ya fito da asalin kwarjininsa,yace:na riga da nayi signature a kan takardar, sannan kuma na biya kudin belin sa,ware baki ilham tayi da alamun mamaki,tace:Nagode Dada, Allah ya saka da alkairi 🫂🫂🫂, murmushi yayi yace:Amin




      Fitowa tayi daga cikin motarsa,dakin su ta nufa, kayan ta ta shirya a cikin box dinta,ta gyara daki,ta gyara katifar ta,ta je female toilet,wanka tayi tas sannan ta dauro alwala,tana cikin shirya wa, sofeeya ta shigo dakin,sanye take da half dress Wanda bai gama rufe taba, a'a ashe yau kina gida,ai Ni duk ganina kuna restaurant,fadin sofeeya lokaci guda tana shigo wa dakin, ilham tace: e'h yau ina gida,babu inda na je,amma me yasa baki je restaurant ba yau? sofeeya ta tambaye ilham lokaci guda tana zama akan katifar ta , ilham tace:babu komai,kawai na gaji ne, sofeeya tace: alright.
Sister,ina san nayi magana da ke,shin zaki iya bani lokacin ki kaɗan?fadin ilham, lokaci guda tana sanya kwalin ido, sofeeya tace:ina jin ki, lokaci guda tana cire rigar dake jikinta,ya rage daga ita sai half brass singlet,shin kina san yash? Ilham ta tambaye sofeeya 🙍🙍🙍sosai tambayan ya girgiza sofeeya,amma bata nuna ba,tace:ya da tambaya?so suddenly, ilham tace:babu,don ko za'a Shake ilham a tambayeta mesa tayi irin wannan tambayan zata ce bata sani ba,
Bana sansa, ilham taji sofeeya ta fadi hakan, amma toa mesa? ilham ta tambaye ta, sofeeya tace:kece silla,kece sillar komai,da baki fado rayuwar yash ba,ko tawa,toa da yanzun nan muna zaman lafiya,dukan mu,a lokacin da yash ya furta min cewa yana sona,nima nace masa ina san sa,nan muka fara soyayyar mu,me cike da ma'ana,a duk lokacin da na kalli idon sa sai inji wani kauna a cikin zuciya ta,muna cikin wannan soyayyar isham ya fado rayuwa ta,shi ya nuna min yadda duniya yake,da kudade,ya kara bude min idona tangarararr,shi ya koya min rayuwar makaranta, a nan ne naji yash ya fitar mun a cikin zuciya , a duk sa'illin da nace wa yash ina bukatar kudi,toa fa baya bani,sai dai yace dani in tambaye iyaye na,a wani ranar da na kira shi a waye ,don ban ganshi a class ba,yace dani yayi tafiya, a nan ne naje wajan isham don mu raya daren mu kamar ma’aurata,muna cikin wani yanayin feeling and emotional time,ya shigo dakin ,ina ganin shi na yi matukar firki cewa,amma sai nace masa isham ne ya tilasta Ni ,a wannan lokacn nayi amfani da dama na ,na sumba ce yash.nasan kina san jin mesa bana sansa ko? sofeeya ta tambaya, ilham ta gyada mata ka a hankali, sofeeya ta cigaba da magana: a lokacin da muke rubuta 2nd semester final year of 100 level,kin gan Ni ina kwafar amsa daga papper,sai kika gayawa Malama,ita kuwa Malama ta kai Ni wajan shugaban makarantar,aka yanke min hukuncin -35 marks in every exams,da yanzun nan muƙamin da kike Kai nice Nike,don Wannan abun da kika min yasa na dau alwashin sai na miki dubun sa,
Daga nan na fara bincike a kan ki,har naga wani diary na sirrin ki,shi na karanta na ga yadda kike san yash,daga nan ne na rike sa,gam dan kar ya subu ce mini,na sanya sa a cikin MAKAUNIYYAR SOYAYYA,wanda dukan abinda na masa baya taba ganin laifi na,da wannan saurin fushin nasa na tura sa jail,sannan na tura sa gidan mahauka tai,duk wannan abun nayi ne saboda soyayyar da kike masa,don na lura shine komai dinki a gare ki,yasa nayi wasa da zuciyoyin ku.
Amma shin da gaske ne yana kokarin ya miki fyade? ilham ta tambaye sofeeya lokaci guda tana share hawayan ta,ganin abun da sofeeya ta aika ta mata. 






Please like comment, 🌟,and share.