DA JININSA NAKE RAYUWA
by @legendspen
“Me zaku yi a T-Shima, ina tambayarki kin bini da idanu.”
Yaya Walid ya sake faɗa, ransa a haɗe.
“Mun faɗawa Mama zamuje gidansu ‘yan ajinmu, ta gidansu Aisha Sharif zamu fara sune a T-Shima tun da yafi nisa.”
Husna ta sami kanta da shirga lafiyayyar ƙaryar da bata san ta ƙware a kai ba sai yanzu.
“Shine ina miki magana kin yi min banza? To duk inda zaku ki tabbatar la'asar ta yi muki a gida, sannan wannan kayan da yake jikin ki kar na sake ganin kin fita da shi.”
“Tam, in sha Allah.”
Ta faɗa bakinta har rawa yake, zuciyarta na wani irin bugu da ƙarfi ƙarfi, ya sa hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa mata.
“Ku hau napep, kuma drop zaku ɗauka. Sannan idan baku san waje ba ku jaddadawa mai napep ɗin ku ce daidai waje kaza zai ajiye ku.”
“Tam Yaya, mun gode.”
Ta faɗa tare da amsar kuɗin, su Said Kibiya ma suka yi masa godiya suka tafi, Hafsat ce ta ce.
“Yayanki ne wannan?”
Husna ta gyaɗa mata kai, dan ita har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa da ƙarfi ba.
“Amma dai yana da kyau.”
Tsaki Said Kibiya ta yi, sannan ta ce.
“Kuma duk gidansu yafi kowa zafi ba.”
“Wallahi fa.” Husna ta faɗa suna ƙarasawa bakin titi, napep ɗin farko da suka tsayar ya ɗaga suka ce masa T-Shima zai kai su drop, ya ce dubu biyu, suka ce zasu bashi.
Tun da suka shiga cikin napep ɗin Husna ta ƙurawa titi ido, kawai fargaba take ji da kuma zaƙuwar haɗuwa da Uncle Dee, dafa kafaɗarta aka yi ta juyo ta kalli Said Kibiya, a hankali Said Kibiya ta ce.
“Husna Abubakar Sheshe, kisani duk wani abu da yake faruwa a rayuwar Ɗan-adam Allah ya tsara masa tun kafin zuwansa duniya, idan Uncle Dee alheri ne a gareki Abba da Mama da su Yaya duk zasu fahimta zaku dawo ku fahimci juna shima ya karɓi addinin Allah ku yo aurenku, idan har kika ga abubuwa sunyi tsantsani kowa ya gaza fahimta to da alama shi ɗin ba alheri ba ne, dan Allah Husna ke yi min alƙwari guda ɗaya.”
Said Kibiya ta ƙarasa maganar tana kama hannun Husna.
“Wane alƙwari.”
“In dai Uncle Dee yaƙi amsar addinin Musulunci zaki haƙura da shi, ba zaki yi gardama da iyayenki ba, kinsan dai Abba zai ba shi aurenki indai har ya musulunta da zuciya mai kyau ba da wata manufar ba.”
“Wai mene yasa bazan aure shi ba dan ba addinin ɗaya ba, naga al'ada ɗaya muke yi da shi ko? Kuma namiji musulmi ai yana iya auren macen da ba musulma ba.”
Hafsa ce ta bawa Husna amsa da cewa.
“Al'ada ai daban addini ma daban, kuma a cikin abubuwan da suka haramtawa mace musulma auren namiji da ba musulmi ba akwai. Rashin Bada Kariya ga Addininta, namiji Musulmi idan ya auri macen da take Ahlul Kitab, addininsa ya tilasta masa ya girmama Annabi Isa (AS) da Annabi Musa (AS) da Littafai tsarkaka. Amma mutumin da ba Musulmi ba, bai yi imani da Annabi Muhammad (SAW) ko Al-Qur'ani ba, saboda haka babu wata shari'a ta addininsa da za ta tilasta masa girmama ko kare addinin matarsa Musulma.
Sannan akwai tarbiyar ‘ya'ya, 'ya'yan da aka haifa a Musulunci suna binsa ne ta hanyar mahaifinsu wajen bin addini da sunaye da nasaba. Idan mahaifi ba Musulmi ba ne, a shari'ance 'ya'yan ba za su taso a matsayin Musulmi a ƙarƙashin shugabancinsa ba, ke kan ki zai zame miki abun baƙin ciki ki duba cikin ‘ya'yanki kiga suna wani addini daban, Husna wallahi wanna giyar soyayya ce ke ɗibanki, gaba ɗaya shekarki nawa? Nasan na girmeki amma har yanzu ban cike 18 ba.”
Shiru Husna ta yi ta mai da hankalinta ga kallon titi, ita a yanzu kawai so take taje ta yi ido biyu da shi, a yanda take jin soyayyarsa a zuciyarta ai zata iya zama da shi ba tare da sun haihu ba, sannan kuma ya ce zai kare mata addini, yanda ma yake da kyan mu’amala ai ko wani musulmin albarka.
Babu wanda ya sake cewa komai har suka iso T-Shima mai napep ɗin ya sauke su, tun anan suka dabarbarce sun rasa ta inda za su fara, sun kusa mintuna goma kafin suka yanke shawarar fara tambayar mutane, mutum na farko da suka tsayar tambayar da suka yi masa dan Allah Yasan Iliya D Musa, ya ce musu a'a, haka mutum na biyu shima amsar ita ce a'a. Sai da suka tambaya sama da mutane goma kowa amsar ita ce a'a, ɗaiɗaiko ne ma suke tambayarsu ba shi da wani sunan bayan wannan sai su ce Uncle Dee, suma ƙarshe su ce basu sani ba. Da suka gaji ne Said Kibiya ta ce ko zasu tambayar layin da gidajen arna suke, haka kuwa mutum na farko da suka tambaya ya ce su tsallake su yi tafiya kaɗan sai su sake tambaya.
Hakan aka yi suka tsallake suka yi tafiya kaɗan basu kai ga tambaya suka fara cin karo da arnaye, gasu nan su ɗau kwalliya sun dawo daga church, ta farko suka tambaya ta ce musu bata sani ba, ta biyu kuma ta ce musu tasan shi amma yanzu baya gari zata rakasu gidansu.
“Baya gari? Ina yaje?”
Husna ta tambayeta bayan ta faɗa musu, wani kallon banza matar ta yi musu, sannan ta ce.
“Ni ina zan sani?”
Ta yi maganar tana haɗe rai, cikin wata caɓɓiyar hausarta.
“Sorry sister, zamu iya samun contact na shi, ko wani close friend na shi?”
Hafsat ta faɗa, dan tafi su Husna wayewar mu'amala da mutane.
“Ni banda number ɗinsa, amma ina da na Moses best friend ɗinsa, amma ku su waye?”
“Students ɗinsa ne daga school ɗin da yake koyarwa.”
Hafsat ɗin ta sake bata amsa, wayarta ta zaro daga jaka ta ba su lambar aka sanya a wayar Hafsat, suka yi mata godiya ta wuce.
“Idan kika ce haka zaki yi wallahi babu abin da zaki samu.”
Hafsat ta faɗawa Husna, tana danna lambar Moses ɗin, bugu ɗaya ya ɗauka Hafsat ta ce.
“Hello, Moses how are you?”
“Am Fine oh, waye ke magana?”
“Esther ce, gani a unguwanku ina so mu gaisa ne.”
Hafsat ta faɗa, su Husna da Said Kibiya da ido suka bita, tafi su wayo da sune ba haka zasu yi masa ba kwata kwata.
Cikin hausar da bai wani iya ba ya ce.
“Wane Esther? Ko Esther Cafe.”
“Eyh ni.”
Hafsat ta yi magana ita ma da hausa kamar ta ‘yan koyo.
“Okay, okay where you dey?”
“T-Shima junction.”
“Okay 2 min.”
Ya faɗa tare da kashe wayar, kallonsu Hafsat ta yi sannan ta ce.
“Ku barni ni zan yi magana da shi, dole yau sai an sami lambar nan.”
“Ke kam Hafsat yaushe kika waye haka?”
Said Kibiya ta faɗa tana mamaki, ita kanta Husna mamakin Hafsat take yi.
“Ba waye ba ce, kawai darabar ce ta yaudara, wani lokacin sai an kwantar da kai ake samun biyan buƙata.”
“Ikon Allah.”
Husna ta faɗa dan ita bata san wannan karatun ba, rigima kawai ta sani da taurin kai sune kaɗai ke biya mata buƙata. Husna ce ta fara hangosa sabida ita tasan shi a zaman asibitin AKTH, ƙasa ƙasa ta ce.
“Gashinan shine yake tawowa.”
“To ki juya baya tun da ya sanki.”
Hafsat ta yi maganar itama ƙasa ƙasa, a hankali Husna ta juya baya ta yanda ba zai ganta ba, yana cikin waige waige Hafsat ta ce.
“Moses.”
Ya tsaya cak tare da ƙura mata ido, ita kuma ta ɗaga masa kai alamar ita ce, a hankali ya matso kusa da ita yana nuna ta yatsa.
“Kin ce Esther Cafe.”
“Ba Esther Cafe ba ce, kawai ina son ganinka ne shi ya sa na ce ma haka.”
“To me zaki yi min?”
“Iliya nake son gani.”
Ta faɗa kanta tsaye, Husna dai duk da kanta ajuye yake, amma mamakin ƙarfin halin Hafsat take, tana magana da ƙwarin gwiwa babu tsoro babu fargaba.
“Wace ke?”
Moses ya faɗa, Hafsat ta ce.
“Student ɗin shi ce daga makarantar da yake koyarwa ne, ya daina zuwa shine muka zo nemansa.”
“Iliya yanzu baya nan, ya tafi wajen prophet ɗinmu, yana wasa da addini shi dadynsa ya tura shi, sai je ya yi bauta na wata uku jinin sheɗan ya fita daga jikinsa, ya tsarkake addini.”
“Me ya sa?”
Hafsat ta tambaya kamar bata san komai ba, Moses ya sake cewa.
“Yana neman ya bar addini ne.”
“Bai kyauta ba, yanzu kira min shi a wayanka.”
“Banda enough card, amma bari na baki wayan a kira shi.”
Ba musu ta miƙa mai wayar, tana mamakin rashin wayo irin nasa, sai da ya sa lambar a wayarta ya miƙo mata ta ce.
“Bai ce ma komai a kan Husna ba?”
Ɗan dakatawa ya yi na wasu daƙiƙu, sannan ya ce.
“Husna? Tana ina?”
“Bata nan, amma bai ce ma komai a kan ta ba?”
“Bai ce ba, amma ya ce idan tazo nemansa ace mata KAR..TA.” Sai kuma ya yi shiru, yana ƙoƙarin haɗa hausar da ƙyar ya ce.
“KAR TA SARE.”
Maganar ta shiga Husna sosai, kawai taji hawaye sun fara biyo fuskarta, wai kar ta sare daman me zai sa ta sare? Ai bata fara dan ta daina ba.
Daga cikin wayar ya fara magana, murya ta fito cikin sanyinta a koda yaushe, wanda ya haifarwa da Husna wani irin tashin tsigar jiki, hawayen da ke fuskarta suka ƙara gudu suna zubowa babu ƙaƙƙautawa.
“Husna ungo.”
Hafsat ta faɗa tana miƙa mata wayar, daga can ɓarin Uncle Dee jin an ce Husna ungo shima ya haifar masa da mugun bugun zuciya mai ƙarfi. Husna ta karɓi wayar tasa ta a kunneta ba tare da ta ce komai ba, ta yi shiru. Shima ya yi shiru babu abin da suke ji sai bugun zuciyoyin junansu, da ƙyar ya ce.
“Husnahhh.”
“Uncle Dee.”
Ta faɗa, muryarta na rawa. Wani irin sanyi yaji ya mamaye duniyarsa bakiɗaya.
“Husnahhh.”
Ya sake faɗa, ita kam kuka ya ci ƙarfinta ta kasa magana sai kuka.
“Shiru please, Husnahhh bana so ki daina, dan Allah.”
“Na daina.”
“Ya jikinki?”
“Na warke.”
Ta faɗa, ya sake cewa.
“Ya school kin koma ko? Kinga saƙona wajen ƙawayenki ko?”
“Eyh nagani, kana ina? Nazo T-shima ɗin.”
“Na yi nisa Husna, na yi nisa sosai amma zan dawo, zan dawo yau ko gobe saboda ke, ki amince mu yi aure. Bazan iya rayuwa babu ke ba.”
“Nima haka, Jininka ne ke bawa zuciyata damar bugawa, son ka shine ke bani ƙwarin gwiwar rayuwa. Da jininka nake rayuwa Uncle Dee.”
“Nima haka Husna, zan dawo. Tsorona ɗaya kar ki sare ki bar zuciyata a gantale.”
“Har Abada Uncle Dee, har abada.”
“Thank you Husnahhh, na gode da kika bani zuciyarki, na yi alƙwarin ba zan taɓa barinki ba.”
“Nima ba zan barka ba, bambanci addini ko al'ada ba zai raba ni da kai ba.”
“I love you Husnahhh.”
“I love you too.”
Daidai lokacin kuma katin wayar ya ƙare, kiran ya katse sai dai ko cikakken minti ɗaya ba ayi ba kira ya shigo wayar, tana ɗagawa ya ce.
“Wayar waye wannan?”
“Ruƙayya Said Kibiya.”
Ta faɗa, daga can ya yi murmushi ya san ƙawayen Husna bazasu taɓa rabuwa da ita ba, sabida yaga zallan soyayya a tare da su.
“Ki gaisheta.”
“Okay, yanzu yaushe zaka dawo.”
“Ki ban House Addrss ɗinki kawai.”
“Tom, Sharadaɗa NNDC, gida mai lamba 144C.”
Sai bayan sun sake shiga napep zasu kuma gida, Hafsat ta ce da Said Kibiya.
“Ɗan bani kusa da Husna.”
Said Kibiya ta matsa mata ta shiga ciki, Husna tana daga ƙarshe ta jingina kanta a ƙarfe Napep ɗin tana kallon hanya.
“Husna.”
Hafsat ta yi mata magana, Husna ta kalleta ba tare da ta yi magana ba.
“Bakya ganin yakamata ku ɗanyi baya da wannan lamarin naku?”
Wani irin kallo Husna ta yi wa Hafsat, sannan ta taɓe baki ta ce.
“Baya, me ya sa?”
Murmushi Hafsat ta yi, sannan ta ce.
“Idan kin duba fa, kuna da bambancin addini ke musulma ce shi ba musulmi ba, idan soyayya ta rufe miki idanu, bai kamata ki rufe ƙwaƙwalwarki da tunanin ki ba, soyayya fa bata taɓa dauwama, wallahi duk ƙarya ne.”
“Hafsat, soyayya na dauwama mana, ko ba haka ba Said Kibiya?.”
“A'a, karki sakani a cikin lamarin soyayya dan bantaɓa ba. Amma ni dai nasan zaman aure ɗan haƙuri ne kuma sai anyi da ce.
Ke bari na faɗa miki abin da na sani, Namiji ko gida ɗaya kuke da shi ba addini ɗaya ba, ko ciki ɗaya kuka fito babu tabbacin idan kun yi aure zaku zauna lafiya.”
“Da wannan ma, amma magana nake miki ta faɗar Allah, ke dai kin san iyayenki ma baza su taɓa barin ki ba.”
Hafsat ta sake faɗa, Husna ta turo baki gaba sannan ta ce.
“Wallahi zasu barni.”
********
Bayan kwana biyu.
Husna na zaune a falo, bakinta sai rawa yake tun shekaran jiya da suka dawo take son yin magana amma takasa, ko jiya da ta je gidan Antyn Said Kibiya sai da suka sake bata shawara a kan ta daina zurfafawa a kan lamarin Uncle Dee, amma ba ta ji ba.
Ta buɗe baki za ta yi magana, Yaya Walid ya shigo yana faman faɗa.
“Wane irin iskanci ne wannan, shi wannan aina ya san gidan nan da har zai zo mana ƙofar gida?”
Wani irin bugu ƙirjjn Husna ya yi, Uncle Dee ne ya dawo kuma yazo gidansu, lallai Uncle Dee ya yi wa soyayyarta hallarci, amma wai a haka ake ce mata karta zurfafa, idan bata zurfafa ba me za ta yi?
“Mene haka zaka shigo babu sallama, kai da waye?”
Mama ta faɗa, ƙwafa Yaya Walid ya yi sannan ya ce.
“Waye idan ba wannan malamin nasu Husna ba, na ɗauka an gama da maganarsa?”
Alhaji ne ya leƙo daga ɗakin saman bene ya ce.
“Wannan arnen?”
Wani irin ɓacin rai Husna taji, ƙasa ƙasa ta ce.
“Dan yana Arne ai mutum ne.”
Kasancewar a hankali ta yi maganar ya sa ba wanda ya jita, Alhaji ya sake cewa.
“To me yake yi?”
“Ni ko sauraronsa na tsaye ne? Sabida ba shi da lissafi har zama na yi da shi na yi masa bayanin halal da haram, faɗar Allah da hukuncin wanda ya yi watsi da maganar ubangiji, amma da yake dusa yake ci ya kasa ganewa.”
Shiru Husna ta yi, daman Yaya walid ne ya hana Uncle Dee magana da ita a wancan lokacin kenan? Lallai mutanen nan.
Alhaji ne ya sauko zai fita Mama ta ce.
“A'a babu ruwanku da shi ku ƙyale shi, zai gama jiransa ya tafi.”
Komawa ya yi sama ya ci gaba da karatunsa, Yaya Walid ya ɗaura alwala kasancewar magariba ta haɗo kai, ita dai Husna tana zaune tana kallonsu ji take kamar ta yi tsintuwa ko ta ɓace ta ganta a waje, ina dalili rabin ranta na ƙofar gida an hanata fita ita.
Ko da Yaya walid zai fita Mama ta ce da shi.
“Walid, karka kuskura ka tanka masa, ko ya yi ma magana ka yi banza da shi.”
“Tam Mama, masallaci zanje na yi karatu kafin a tayar da sallah.”
“To Allah Ya bada ilimi mai amfani.”
“Amin, Amin.”
Ya faɗa tare da ficewa, Husna Allah Allah take Mama ta shiga ciki ta fita waje, dan ita babu abin da zai hanata fita. Kamar Mama ta san abin da Husna ke ayyanawa a ranta taƙi tashi, har aka kira sallah ta ce da Husna.
“Ta shi ki yi alwala mu shiga ɗaki.”
Kamar mara laka haka Husna ta tashi ta shiga banɗaki ta yi alwala ta fito, Mama kam anan tsakar gida ta ɗaura alwalal, dan Mama bata taɓa zama babu alwala tsakanin la'asar da magariba sai ta ɗaura alwala uku ko huɗu.
Tare suka shiga ɗaki, kowacce ta gabatar da sallarta, suna idarwa su Walid suka sake shigowa suna magana a kan Uncle Dee da yaƙi tafiya, Mama ta ce.
“Tun da ba zai tafi ba ku bar shi mana.”
“Mama ai mun bar shi, kawai muna mamakin zaman me yake yi har yanzu.”
Mamaki bai sake kama su ba sai da suka dawo daga sallar isha'i wai yana wajen a zaune, har Abba ma ya dawo yana ta mamaki da aka ce masa tun yamma yake wajen, wajen ƙarfe goma ma da Yaya Abdul ya sake leƙawa waje ya gan shi a tsaye, abun ya yi matuƙar taɓa shi har ya ji kamar ma ya yi magana da shi, amma dai ya kule gidan.
Kowa ya kwanta bacci aka bar Husna zaune ta rafka uban tagumi tana faman tunani, anya ana sonta a gidan nan? Anya ta yi hallaci barin shi a tsaye a waje taƙi fita, ta kyauta kuwa? A kanta ya baro can inda aka tura shi Tsarkake addini, amma ya bar tsarkake addinin ya tawo wajenta, gaskiyya ba zata saɓo ba.
Washe gari da yamma ma sai ga shi Ashir ya shigo yana cewa wai ya ga Uncle Dee a ƙofar gida, yana faɗa Husna ta yi zumbur ta miƙe, Mama ta ce.
“Ina zaki?”
“Mama wajena fa yazo, ya za ayi ace an barshi a tsaye tun jiya gashi har yau ma.”
“Koma ki zauna, wallahi ba zaki fita ba, baki da hankali ne ko wani abu na damunki?”
“Dan Allah Mama ki barni na je, wallahi wajena yazo kuma sona yake yi, Mama aurena fa zai yi.”
“Gidanku Husna, kar ki bari na taso fa.”
Kuka Husna ta fara yi tana bububbuga ƙafa, Mama ta ce.
“Ki bubbuga ƙafa da kyau, amma babu inda zaki wallahi.”
Mama ba ta rufe baki ba Husna ta kwasa da gudu ta yi waje tana faɗin.
“Wallahi sai na fita, sai dai duk abin da za ayi ayi.”
Tana fita kuwa ta ci karo da Abba na ƙoƙarin shigowa, a bayansa kuma su Yaya Abdul ne har da Uncle Dee. Baya ta yi da gudu zata koma Abba ya ce.
“Shiga a nutse.”
Legendspen
***