GARIN KALLON RUWA

Introduction

by @yargidanimam

GARIN KALLON RUWA BOOK 1

Tun dare ake hada hadari yana washewa. A garin Kanon Dabo, har gari ya waye bai sakko ba. Amma gaf, da fara sallar juma'a gaba daya sai hadarin ya taso gadan-gadan da iska mai karfi. Tamkar ana jiran a idar da sallar juma'ar ne. Gaba daya sai ruwan ya sakko da karfi ba sassautawa, kamar da bakin kwarya, wanda hakan ya tilasta ma jama'ar dake tafiya a kasa samun mafaka, wadanda suke kan abin hawa kuma, sai kara ma kansu gudu suke. Domin su tsira daga dukan ruwan saman. A daidai wannan lokacin ne Mallam Habibu da matarsa Salaha da ƴarsu Khaleesa, suke kokarin tsallake titi, domin su ma su samu mafaka, kamar yadda sauran jama'a ke yi. Duk da kasancewar sun fi awanni hudu da sauka a garin Kanon a matsayinsu na baki, wadanda Basu san kowa ba a garin. Amma har zuwa wannan lokacin da ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, basu sami wanda ya dubesu da idon rahama ya taimaka musu da wajen zama ba, ko duban tausayi da mutunci basu samu daga kowa ba. Ga yunwa da kishi, ga rashin kuɗi da zasu sayi abinda zasu ci. A daidai lokacin da suke kokarin tsallake titin. Wata farar mota kirar (Honda Hala), ta fisgo da gudu, wanda hakan yayi sanadiyar gigicewar Khaleesa, tayi saurin yarfar da hannun Inna Salaha dake rike da ita, ta ranta da gudu wai zata tsallake titin, kafin motar ta wuce. Cikin tsautsayi kwatsam!! Motar nan tayi awon gaba da Khaleesa. Iya rudewa da gigicewa mahaifan Khaleesa sun yi. Sauran jama'ar wajen kuwa sai salati da neman dauki. Yayin da mai motar ya tsaida motar tasa da kyar, sa'annan ya fito a gigice ya nufi Khaleesa wacce tuni mahaifanta da sauran jama'a suka dagata. Ba inda take. Hasalima a sume take, sai jinin dake fita daga kafafunta da gefen kanta. Alhajin na isowa, bai yi wata wata ba. Ya dauki Khaleesa ya nufi motarsa, a yayin da su Malam Habibu suka bi shi, duk suka shige motar. Sauran jama'a na fadin Allah ya kyauta. Allah ya kiyaye gaba. Cikin damuwa da gigicewa Alhajin ya figi motar, kai tsaye asibiti ya nufa da Khaleesa. Kasancewar babban asibiti ne na kudi, yasa ana isa da Khaleesa. Nurses suka dauketa da sauri zuwa dakin taimakon gaggawa saboda jinin dake fita a jikinta, sai a lokacin hankalin Alhaji ya ɗan kwanta har ya sami karfin guiwar matsowa kusa da Malam Habibu. Ya mika masa hannu suka yi musabaha. Ya kara da cewa ''Ni sunana Alhaji Jafar''. Malam Habibu yayi kokarin hadiye damuwarsa yace ''Ni kuma sunana Malam Habibu, na kuma gode da kokarin ceto rayuwar ƴata da ka yi''. Alhaji Jafar ya girgiza kai yace ''Haba Mallam Habibu, Meye na yi min godiya, me nayi na godiya? Don na kawo 'yarka asibiti? A ganina ai hakkina ne yin hakan, tunda ni ne silar komai. Ni ne ma da godiya Allah kuma ya takaita mata wahala''. Malam Habibu ya langwabar da kai yace ''Amin na gode''. Daga nan Alhaji Jafar ya dubi Inna Salaha da take matsar ido, yace ''Ki yi hakuri da izinin Ubangiji ba Abinda zai sami diyarku, asibitin yana da kyau, na san kuma za su yi iya bakin kokarin su na ganin sun ceto rayuwar ta''. Inna Salaha ta tsagaita da matsar ido, tace ''To Allah yasa haka, na gode''. Zuwa wani dan lokaci. Likitan ya fito. Cike da girmamawa ya mika ma Alhaji Jafar hannu. Suka gaisa, sa'annan yace ''Alhaji ba wata damuwa a yanzu, dama inda ke fitar da jinin a jikinta yankewa ce, kuma mun yi nasarar dinke wajen. Sai sauran kananan ciwurwukan wadanda ba zasu dauki wani dogon lokaci wajen warkewa ba. A yanzu ma ta dawo hayyacinta, sai dai firgitar da take ciki ne yasa ba zamu bar kowa ya shiga inda take ba a yanzu. Sai dai zuwa anjima''. Alhaji Jafar yayi ma Likitan godiya. Daga nan likitan ya juya zuwa office. A yayin da Alhaji Jafar ya waiwayi Malam Habibu da matarsa wadanda a yanzu hankalinsu yake kwance. Yace ''To tunda na ga alamar daga tafiya kuke. Yana da kyau ku isa gidanku, ku aje kayanku, ku dan natsa, tunda ba zamu sami damar ganinta yanzu ba. Zuwa anjima sai ku dawo, ina iya ajeku a gidan, saboda nima na ga inda kuke'' Malam Habibu ya dubi Inna Salaha. Sannan ya maida kallonsa ga Alhaji Jafar cikin taushin lafazi yace ''Alhaji, ai mu baki ne a garin. Babu wanda muka sani, mun dade da sauka a garin, amma mun rasa inda zamu tsoma kanmu. Kowa muka bukaci ya taimaka mana. Sai ya nuna cewa ba zai iya ba, me yuwuwa ko don Saboda halin da muke ciki ne, na rashin yarda da kanmu. To muna cikin wannan halin ne tsautsayi ya faru, don haka Alhaji mu kam bamu da wajen zuwa, sai dai mu zauna anan mu jira''. Alhaji Jafar ya jinjina kansa gami da kara kallon Malam Habibu, sai yanzu ya lura kwarai alamun wahala da jigata gami da damuwa a jikin Malam Habibu da matarsa. Don haka ya gyara tsaiwarsa yace ''To idan babu damuwa, ina da sha'awar taimaka muku''. Nan da nan Malam Habibu ya matso yana yi masa godiya ''Mun gode. Allah ya kara arziki da girma, mun gode'', Alhaji Jafar ya katse shi ta hanyar daga masa hannu da cewa ''Ba komai, kada ka manta kowa ya taimaki wani. Allah yana taimakon sa, saboda haka ne zan taimakeka tsakani da Allah''. Malam Habibu ya ɗan rissuna yana kara yi masa godiya. Lokaci daya Alhaji Jafar ya wuce, ya ba shi umarnin ya biyo shi. Nan da nan Salaha ta yayibo buhun kayansu tana yi ma Alhaji Jafar godiya, wanda tuni ya fice daga asibitin. A yayin da Malam Habibu da Salaha suka biyo shi a baya, zuciyarsu cike take da farin ciki da godiya ga Allah daya yanke musu wahalarsu da suke ciki. Suna shiga motar. Alhaji Jafar ya ja motar zuwa unguwar da yake zaune tare da iyalinsa (Nasarawa G.R.A). Zuwa wannan lokacin kuwa gaba daya an dauke ruwan saman, idan ka ɗebe jikewa da cabewar da garin yayi, sai ka dauka ma ba ayi ruwan ba. Garin yayi haske Gwani ban sha'awa, ga wata 'yar sansanyar iska da take busawa, kowane kusurwa na garin Kano. Yadda hakan yake dasa annashuwa a zuciyar al'umma Garin Kanon.

********************** Gidan Alhaji Jafar Faruq, babban gida ne me matukar kyau da kyawun fasali. Gida ne ginin zamani, bene wanda yana daya daga cikin manya, kuma kyawawan gidajen unguwar. A katon falon kasa na Alhaji Jafar Malam Habibu ne da matarsa Salaha zube akan kafet a natse. Kan doguwar kujera kuwa Alhaji Jafar ne zaune kusa da shi uwargidansa ce Hajiya Zulfa'u. Wacce aka fi sani da Hajiya Zulfa. Alhaji Jafar ya gyara zamansa gami da duban Malam Habibu yace ''Na yi nufin saukar daku a gidana, muddin zamanku zai kasance da zuciya daya. Amma kafin nan ina son jin dalilin barowarku garinku da abinda ya kawo ku Kano? Malam Habibu ya numfasa fuskarsa na bayyanar da tsantsan damuwa da alhini, ya fara yi masa bayani da cewa: ''Mu 'yan asalin wata babbar Ruga ce mai suna Rugar Dumau a cikin jihar Adamawa. Nan 'yan-uwa da abokan arzikinmu suke, dalilin barowarmu Rugar Dumau kuwa. Ya zama dole ne, don mu kanmu ba haka muka so ba, yawan ruwan da ake tafka mana kullum kamar da bakin kwarya yai sanadiyyar fara ruguje mana gidaje da bukkoki. To yau kimanin kwanaki biyar kenan da suka wuce. Annobar ruwa ta balle a Rugar Dumau. Saboda tsananin ruwan da aka kwana aka wuni ana tafkawa babu sassauci, shine yayi dalilin da ruwan ya cinye mana gidaje, ya tafi da bukkoki da gonakinmu da dabbobinmu. Hatta Shanunmu da muke kiwo, suka zamar mana tamkar gatanmu, ba mu tsira da su ba, balle fa kaji. Ba karamar asara muka tafka ba. Hatta wanda kwanansu ya kare sun rasu. Domin ni kaina Na rasa babban Dana Tasi'u. Mu kuma Allah yasa akwai sauran shan ruwanmu mun kasance cikin matsananciyar wahala kwarai da gaske, a cikin kwanaki biyar din nan, bamu da wajen kwanciya, ba mu da abinda zamu ci. Rayuwa tayi mana matukar tsauri. Da yawa sun kamu da rashin lafiya, saboda yunwa. Gwamnatin jihar tayi alkawarin taimaka mana da wajen zama da abinda za mu ci. Manyan namu sun zo mota guda, sun duba sun ga irin matsanancin halin da muke ciki. Sun ce zasu turo da taimako. Amma har na yanke shawarar barin Rugar, ba wani taimako daya iso garemu. A dalilin hakan na bar ruga, saboda bakin ciki da jimamin halin da muka tsinci kanmu a ciki''. Malam Habibu ya numfasa ido jajir!! Ya ci gaba da cewa ''Daga nan kai tsaye Kano muka yi, duk da kasancewar ban san kowa ba, kuma bani da kowa a Kanon. Amma dole ne na bar kauyen na mu, saboda kuncin da muka shiga. Wannan shine dalilin barowarmu kauyenmu da kuma zuwana Kano''. Hakika Alhaji Jafar ya tausaya ma Malam Habibu da iyalinsa, jin kuma labarin nasa ya kara masa karfin guiwar son taimaka masa. Domin tabbas labarin da Malam Habibu ya fada masa, ya ji a rediyo. Ya kuma karanta a jaridun mako. Don haka ya sami kansa da gasgata labarin Malam Habibu. Sabanin Hajiya Zulfa, da sam zancen Bai gamsheta ba. Shi yasa ma ba tace uffan ba. Kallonsu kawai take daya bayan daya, suna bata haushi. Alh. Jafar ya nuna ma Malam Habibu tausayawarsa, yayi masa ta'aziyar dansa Tasi'u gami da jajen abinda ya faru da su. Sannan yayi alƙawarin zama da shi a bisa amana da tausayawa. Tunda ya fuskanci Malam Habibu ba shi da kowa, don haka Alhaji Jafar da kansa ya dauki Malam Habibu ya kai shi inda zai zauna tare da iyalinsa. (Boys Quarters) ne. Me dauke da dakuna biyu, da bandaki da kicin, sai dan matsakaicin fili daga waje, wato tsakar gida, komai dai ya ji a can. Gwanin ban sha'awa. A zahiri Malam Habibu ya rasa bakin godiya, sai hawaye, domin iya rayuwarsa bai taba mafarkin zai zauna a irin wannan muhallin ba, shi dai kam a yanzu ya ɗauki Alhaji Jafar shi ne uwarsa, shi ne kuma ubansa. Shi ne komai nasa. Don duk wanda yayi maka irin wannan abin alheri, ba tare da ya sanka ba. Ai tabbas ba ka da kamarsa duk duniya. Cikin kuka yayi ta ma Alhaji Jafar godiya mara misaltuwa. Yayin da Alhaji Jafar ya bar bangaren, domin su samu su natsa, ko sa sami damar komawa asibiti su dubo Khaleesa. A falon ya tadda Hajiya Zulfa, ta hade rai, yana shigowa ta dube shi tace ''Ni ina mamakin saurin yarda irin taka. Kawai daga mutum ya gaya maka magana. Sai ka hau kai ka zauna, kana sane dai Fulani mugaye ne''. Nan da nan Alhaji Jafar ya fusata yace ''Idan zaki zagi Fulani, ko ki aibatasu. To ki tabbatar ba dasu kike ba, da ni kike. Don Fulani su ne ni. Don sune suka kawoni duniya''. Hajiya Zulfa tace ''Kada ka fassara min maganata Alhaji. Ni dai maganar zamansu a gidan nan bai yi min ba, domin komai na iya faruwa. Ka cika saurin yarda''. Ya dubeta sosai yace ''Gidana ne, baki da iko da umarni ko hani. Ni ke da wannan ikon. Saboda haka zan zauna dasu, baki isa ki hana ba. Na yi niyyar taimako, domin Allah. Ke ko tunda ba ki da wannan zuciyar irin bayin Allah. To ki yi hakuri, ki sa ma bayin Allah ido''. Yana gama fadin haka. Ya juya cikin fushi ya haye sama, ya barta tana binsa da kallon takaici, domin dai sam zamansu Malam Habibu tare da su, bai kwanta mata a rai ba. Domin dai daga ita har Alhaji babu Wanda ya san asalinsu ko halinsu.

*********************

Khaleesa ta ci gaba da zaman jinya a asibiti, har tsawon mako biyu. Sa'annan aka sallameta. A sakamakon warkewa da tayi tsaf! Don ko akwai abinda ke damunta a yanzu, bazai wuce kafarta ta dama ba. Da bata iya takata inda ya kamata. Ita kanta Khaleesa dawowarta daga asibiti da ganin inda Allah yayi da rayuwarsu ya burgeta. Ta kuma ji dadi kwarai da gaske. Duk da tana fama da jimamin rashin wanta Tasi'u wanda ruwa yayi sanadiyyar ajalinsa, domin dai ta shaku da Tasi'u. Saboda kulawar da yake bata. Bata tsammanin zata taba mantawa da wannan babban rashin da suka yi. Malam Habibu shi ke kula tare da gyaran fulawowin gidan. Duk da Alhaji Jafar yana yi masa nuni cewa ya daina. Amma Malam Habibu ya riga ya daukar ma kansa. Ita kanta Inna Salaha ta kan shiga cikin gidan ta taya Hajiya Zulfa aiyukan gida, duk da ba fuska take bata ba. Kuma tana da masu aikinta. Amma da yake Inna Salaha bata da son jiki da lalaci, ta kan je ta tayasu aikace -aikace. Shi ma kuma Malam Habibu ba zama haka yake yi ba, don bayan ya gama duk ayyukan daya dora ma kansa. Ya kan fita cikin gari, ya nemi dan aikin yi. Kamar dako da sauran ayyukan neman kudi, wanda da su zai ganganda yayi cefenen da za'aci abinci. Yana da matukar kokari kwarai da gaske. Ba'a taba zama ba'a ci ba a gidansa. Alhaji Jafar Faruq mutum ne dan kasuwa mai tarin arziki da kadarori. Allah ya rufa masa asiri ta ko wane bangare, yana da matukar tausayi da taimako ga masu karamin karfi. Ya mallaki matar aure daya. Uwargidansa Hajiya Zulfa, ita ko ta ɓangarenta mace ce isasshiya mara son raini. Mai kuma nuna kyama ga talaka. Domin ita ta fito gidan kudi, Bata san talauci ba. Ita ce ta Haifa ma Alhaji Jafar *'Ya'ya shida*. Umar Faruq, shi ne babba, kasancewar ya ci sunan Kakansa, yasa iyayensa ke kiransa da Magajin gida. Duk da yayi matukar Sa'a su kadai ke kiransa da hakan. To fa baya son sunan Faruq. Nagartaccen saurayi ne kyakkyawan gaske. Mai sanin darajar mutane, ga kwarjini domin komai yawan jama'a. Idan Faruq ya shiga cikinsu, sai ka ga gaba daya ya bambanta da su. Komai nasa daban ne. Kyakkyawa ne kwarai. A yanzu yana karatun (Law ne a A.B.U Zaria). Sai Hassana da Hussaina wadanda aka aurar da su bayan sun kammala diflomarsu. Sai Kabir wanda a yanzu ya kammala sakandire, yana shirye shiryen ci gaba ne. Sai Ibrahim yana aji hudu a sakandire. Daga nan sai Hauwa'u tana aji biyu a sakandire. Sa'annan sai auta Bilkisu, wacce take tsarar Khaleesa. Ta zana jarabawar gama firamare. Tana zaman jiran fitowar jarabawar. Tun daga kan Bilkisu haihuwa ta tsayawa Hajiya Zulfa cak! Sai dai fatan Allah ya raya abinda aka samu. Kimanin wata daya da fara zaman Malam Habibu a gidan Alhaji Jafar. Faruq ya dawo daga Zariya. Ya kuma tadda labarin zaman nasu a gidan. Kwarai shi ma ya tausaya ma labarinsu. Ya kuma goyi bayan taimakon da mahaifinsa yayi musu. Haka zalika Alhaji Jafar ya umarce shi daya kyautata musu, kada ya sake ya nuna musu kyama ko banbanci. Faruq yayi murmushi yace ''Alhaji ai wannan ba halina bane, zan kuma kasance mai kyautata musu''. Ita dai Hajiya Zulfa ba tace uffan ba, illa ma yi da tayi kamar bata san maganar da suke ba. Da yammaci Faruq yana sanye cikin lallausan farar doguwar riga, sumar kansa ta kwanta luf a saman kansa. Dan sajensa ya kara fitowa da ainihin kyawun fuskarsa. A daidai lokacin da ya shigo (Boys Quarters) din su Malam Habibu cikin sallama. Khaleesa na cikin sharar dan filin tsakar gidan, ta dago daga sharar tana kallon Faruq. Duk da bata taba ganin Faruq ba. Ranta ya raya mata cewa shine babban dan Alhaji Jafar, wanda mahaifanta suka gama maganar dawowarsa. Ta tuna da yadda mahaifinta ke nuna ma Inna Salaha. Jin dadin yadda ya karbe shi, ita ma tana gaya masa yadda suka gaisa da shi a cikin gidansu cikin karamci da girmamawa tamkar ya sansu. Tana wannan tunanin. Shi ko Faruq na tsaye ya zuba mata ido, kamar yadda ita ma ta kura masa idon. Shine ya katse 'yar kallo-kallon da suke yi. Yace ''Hello Pretty ''. Khaleesa tayi kasa da tsintsiyar tana dan murmushin rashin Sanin abinda yace. Cikin taushin murya tace ''Sannu da zuwa''. Yayi murmushi yace ''Yauwa, sannu da tsaftace gida. Ya sunanki? Tace ''Khaleesa''. Ya gyada kansa ya ce ''Sunanki yana da dadi, amma duk da haka kin fi dacewa da a kiraki Pretty, kuma hakan zan dinga ce miki. Ina Innar? Kafin ta bashi amsa. Inna Salaha da take kokarin fitowa daga daki, tace ''Ke da waye ne Khaleesa? Khaleesa ta ɗan dube shi. Ta rasa amsar da zata ba Innarta. Faruq ya ɗan yi murmushi gami da matsowa kadan kusa da ita. Yace a hankali ''Yaya Faruq''. Tayi murmushi tace da karfi ''Inna Yaya Faruq ne''. Da sauri Inna Salaha ta karasa fitowa daga daki. Jikinta na rawa tana cike da fara'a tace ''A'a Faruq kai ne, ka tsaya daga waje. Shigo ciki, don Allah''. Faruq yayi murmushi yace ''To''. Ta juya daki cike da farin ciki. A yayin da ya bita a baya. Sun dauki dan lokaci suna kara gaisawa, gaba daya Faruq ya saki jikinsa da Inna Salaha. Ita kanta ta ji dadin ganin yadda Faruq ya maidata mutum. Ya kuma saki jikinsa da ita tamkar sun dade tare. Babu shakka halin Faruq irin na mahaifansa ne. Akwai son mutane tare da sanin darajarsu. Khaleesa na gama sharar, ta shigo dakin, har kasa ta durkusa ga gaida Faruq. Ya amsa mata cike da kulawa. Daga karshe yayi sallama da Inna ya fice. Washe gari da safe Faruq na zaune akan fararen kujerun harabar gidan. Littafi ne a hannunsa irin na (Law) yake dubawa. Dama akidarsa matukar yana gida. To baya wasa da lokacin da yake da shi. A kullum yana cikin karatu da bitar abubuwan da suka gabata. Wannan karon doguwar rigar dake jikinsa baka ce, mai sheki. Garin ya hade da hadari. Cikin kankanin lokaci aka fara yayyafi, mai karfi, yanayin garin ya kara dasa annashuwa a zuciyar Faruq. Turo get din da aka yi da sauri. Da kuma karfi, yasa Faruq Kallon get din. Khaleesa ce ta shigo da gudunta kanta na dauke da kwanon kosai. Kafafunta ko takalmi babu, ga 'yar atamfar jikinta, duk ta yage, ruwa kuwa yayi mata sharkaf! Duk kayan sun manne a jikinta. Dan kirgan dangin data fara, duk sun bayyana kansu. Nan da nan Faruq ya tsinci zuciyarsa cikin kuna. Bai ji dadin yadda ruwa ya daketa ba, kamar yadda bai ji dadin ganinta haka yarkace-yarkace ba, cikin kayan da basu rufe mata komai ba. Ya zuba mata ido, har ta zo daf da shi, wanda sai a lokacin ne ma ta gan shi zauna yana kallonta. Da sauri ta durkusa har kasa, ta gaida shi cike da murmushi ya amsa. Ya kara da cewa ''Pretty, ina kika fita haka, ba takalmi ba dan mayafi? Sai ka ce kwailar kauye''. A tausashe tace ''Wajen sayo kosai ne''. Me yasa to kika fita cikin ruwa, ba ki tsayawa ya tsagaita. Sannan ki taho? Tace ''Ai san da na fita, ba'a fara ruwan ba''. Ya gyada kai gami da gyara zamansa yace ''Ina fatan idan ruwan sama ya dakeki, baya haddasa miki komai Irina? Don ni idan ruwa ya dakeni, ko yaya ne, sai nayi zazzaɓi''. Tayi dan murmushi tace ''Ni ma dukan ruwan na sa ni zazzaɓi. Amma sai idan ya dakeni da yawa''. Ya jinjina kansa yace ''Allah ya sauwake''. Har ta daga durkuson zata wuce gida. Faruq ya kara dakatar da ita da cewa ''Pretty, ba kya zuwa makarantar boko da Islamiyya ne? Don jiya da yamma ki na gida. Ya kamata kuma ace kina Islamiyya ne a lokacin. Yanzu kuma ga ki a gabana, wanda ya dace ace ki na makarantar boko ko? Khaleesa ta gyada kanta a hankali, tace ''Ko lokacin da muna garinmu, bana makaranta, don haka ma anan bana yi. Ba wacce nake zuwa''. Nan da na Faruq ya ji rashin dadi a zuciyarsa. Ya dubeta sosai, duba na natsuwa yace ''Ki na da sha'awar yin makarantar Pretty? Da sauri ta daga kanta tace ''Ina matukar sha'awar yin makaranta. Musamman idan an aikeni sayo kosai da safe, na ga 'yan makaranta suna ta tafiya makaranta cikin kayan makarantarsu, sai na ji kamar ni ma na bisu mu tafi tare''. Faruq yayi murmushi sosai, ya kuma ji dadin furucinta. Ya gyada kansa yace ''To shi kenan, maza je ki kai ma Inna kosan, kada ya huce, zan shigo anjima kadan''. Tace ''To''. Ta juya a tsanake ta tafi. A yayin da ya bi ta da kallo. Shin wane irin kyau Allah ya ba Khaleesa ne? Tambayar da Faruq yayi ma kansa kenan, tun farkon ganinsa da ita. Ita kuma yake kara yima kansa yanzu. Tun tana yarinya ma kenan kyau kamar ruwa. Jajir take kowa ya ganta ya ga bafillantanar asali. Iya gane-ganensa tun daga manyan mata 'yan jami'a, har zuwa mata yara sa'annin Khaleesa. Bai taba katarin haduwa da kyakkyawa irin Khaleesa ba. Tabbas idan Khaleesa ta sami karatu gami da gogewa, za'ayi manyan mata. Ga abinda ya ke kara burge shi da Khaleesa shine ga ta dai yarinya karama. Amma tana da matukar natsuwa da mutunta duk wanda yake gaba da ita. Nan take Faruq ya sami kansa da sha'awar sanya Khaleesa a makaranta. Amma me? Khaleesa tayi matukar girma a firamare, don akalla yana kimanta shekarunta zasu yi sha hudu. Baya ga haka kuma tana dan girman jiki, don haka a zahiri Khaleesa ta wuce firamare school. Daga bisani ya yanke shawarar samo malamin da zai dinga koyar da ita, idan an fara daukar sabbin daliban sakandire, sai ya nemo mata. Ya san zuwa wannan lokaci, ta fahimci wasu abubuwan da dama. Zuwa lokacin ta san me karatun ke nufi. Faruq bai sami shiga bangaren su Khaleesa ba, kamar yadda ya gaya mata, har sai washegari da yamma, yana cikin kwalliyarsa ta kananan kaya. Hannunsa rike da bakar leda. Yana shiga, ya tarar da Inna Salaha na sharar falonsu, ta dago daga durkason cike da fara'a tana yi masa sannu ada zuwa. Bayan sun gaisa. Yace ''Da kanki kike sharar, ina Khaleesa ba ta ji dadi ba, zazzaɓi take fama da shi''. Faruq ya bata fuska yace ''Dukan ruwan da ta sha jiya ne ya haddasa hakan. Tana ina?'' Inna Salaha tace ''Ga ta can kwance a dakinta, ta ki cin komai''. Ya ratse ya shige dakin da ta nuna masa da sauri. Kwance kan tabarma ya hangota, ta lulluba da katon zani sakar fulani, amma duk da haka sai rawar sanyi take yi. Ya matso gareta ya tsuguna. Ya dora hannunsa a saman dogon wuyanta, zafi rau rau ya cire hannunsa yana cewa ''Sannu Pretty ''. Ta bude idonta a hankali tana kallonsa. Zuwa can tayi murmushi a hankali, cikin rawar baki tace ''Me yasa ba ka shigo ba jiya, kamar yadda ka ce? Faruq ya maida tsugunnonsa zama a gabanta, yana murmushi yace ''Ki yi hakuri, na tsaya nemo Malamin da zai fara koyar dake ne, tunda kina son ki zama 'yar makaranta. Ko na yi laifi ne? Ta make kafada tace ''A'a, Yaya Faruq ne gode'' Ya girgiza kansa yace ''Ke ba kanwata bace? Idan nayi miki abu, ki daina yi min godiya ''. Tace ''To''. Yasa hannu ya janyo zanin yana kara lullube mata kafafunta. Lokaci daya yana tambayarta ''Wane irin magani kika sha? Ta girgiza kai ''Ban sha magani ba, tun dazu dai Baba ya fita, ya sayo amma har yanzu bai dawo ba''. Faruq ya jinjina kansa yace ''Ga rashin cin abinci, ga rashin shan magani? Ki na tsammanin za ki warke da wuri? Ta girgiza kai, ya dubeta yace ''Zazzabi kadai ke damunki? Tace ''Eh, har da ciwon kai''. Lokaci daya ya mike ya fice. A lokacin Inna Salaha ta zaga bandaki, kai tsaye wajen da ake damun furar Yogot ya nufa. Yasa aka dama ma Khaleesa. Gefe daya kuma kaji ake gasawa. Ya sayi guda daya, sa'annan ya karasa kemis ya hado mata nagartattun magunguna masu kyau. Ya dawo ya tadda Inna Salaha, zaune kusa da Khaleesa tana kokarin muttsuka wani ganyen magani da zata Bata. Nan da nan ya dakatar da ita, ta hanyar mika mata daurin maganin. Inna Salaha ta amsa cike da jin dadi, tana godiya. Ta tashi tsam! Ta je ta debo ruwa, ta dawo Faruq ke ballo magani adadin yadda ya kamata. Ita kuma Inna Salaha tana bata ruwa, har ta gama sha. Ta koma ta kwanta. Faruq yace ''Ba kwanciya za ki yi ba. Ki tashi ki sha fura''. Ya mika ma Inna Salaha daurin nama da fura. Ta amsa tana godiya. Da kanta ta samo kofi da faranti ta sa mata. Faruq kuma ya tsareta da ido, a dole ta tashi ta fara sha. Ganin hakan yasa Faruq ya sami damar yi ma Inna Salaha maganar idan Khaleesa ta sami sauki zata fara daukan karatu a wajen wani Malami da yayi magana da shi. Zai dinga zuwa kullum, amma ban da alhamis da juma'a, za kuma ta dinga bin su Bilkisu Islamiyyar da suke zuwa ta yammaci. Ita ma kullum ce ban da alhamis da juma'a. Ya riga ya je makarantar jiya da yamma yayi ma Malamin bayani. Har ma ya sai (Form) ya cike. Idan ta fara zuwa za'a sa ta a ajin daya dace da ita. A zahiri Inna Salaha ma ta rasa bakin da zata yi masa godiya, Faruq ya mike tsam yace zai tafi. Ya dubi Khaleesa ya nuna mata ledar da tun farko ya shigo da ita, yace ''Idan kin ji sauki, ga takalmi nan cikin leda, ki gwada. Allah yasa kintacena ya zama gaskiya. Allah yasa yayi miki. Kuma kada ki kara zuwa ko'ina, ba tare da takalmi ba''. Yana gama fadin haka. Ya fice. Bai tsaya jin sa albarka da godiyar da Inna Salaha ke masa ba. Inna Salaha ta jinjina kai tace ''Kai wadannan mutane ba mu da abinda zamu ce da su. Sai godiya. Suna dawainiya da mu''. Ta janyo ledar ta fito da takalmin, me kyau ne sosai da alama kuma zai yi karko. Tunda na roba ne.

Bayan kwanaki hudu. Khaleesa ta warke tsaf!! Saboda kulawar da take samu daga Yaya Faruq, har ta fara bin Bilkisu makarantar islamiyya. Sai dai ba a sa ta ajinsu Bilkisu ba, domin sun wuceta. Aji daya aka sa ta, tana kuma daya daga cikin manyan ajin. A yanzu duk yamma Khaleesa na makarantar Islamiyya. Sannan da safe karfe bakwai da rabi, tana gaban Malaminta na boko tana daukar darasi. Koda yake tunda Hajiya Zulfa ta lura da hakan, ta kira Faruq har daki tana yi masa fada. Ina ruwansa da rayuwarsu Khaleesa? Da ta ga alamar yana zakewa. Faruq ya nuna mata yana son kyautata rayuwar ta ne, ta sami ilimi, saboda gaba. A ganinsa kuma ai ba wani abu bane na damuwa. Daga nan bai kara sauraronta ba, ya fice, a dalilin hakan yasa Hajiya Zulfa take tura Bilkisu ita ma wajen (Lesson) din, kada Khaleesa ta sami karatun ita kadai. Khaleesa yarinya ce mai wayau da natsuwa, da yin amfani da damar da duk ta zo mata. Saboda ne ta bada himma kwarai wajen karatunta. A yayin da ta maida Faruq babban Yaya gareta. Tana mutunta shi. Ta dauke shi da muhimmanci a rayuwarta. Domin shine mutum na farko daya fara inganta mata rayuwarta. Shi ne ya fara mayar da ita mutum. Su kansu mahaifanta ba su da wanda ya fi Faruq da mahaifansa. Faruq da kansa ya dinka mata kayan makarantar Islamiyya. Ya kuma tanadar mata duk littafan da ake bukata na Islamiyya da kuma na (Lesson) dinta. Mako uku da fara makarantar Khaleesa. Faruq ya koma makaranta Zariya, ya bar Khaleesa da kewarsa da kuma tunaninsa. Khaleesa ta ci gaba da karatunta gefe daya, kuma a zuciyarta tana kewar Yayanta Faruq, kusan watanni uku rabonta da Faruq. Amma duk ta kosa ya dawo saboda ya ga irin kokari da bajintar da take yi, domin dai a cikin 'yan watannin nan, Khaleesa ta iya karatu da rubutu. Ko Bilkisu da tayi firamare ba abinda zata kwada mata, sai dai shiga ajin. Hatta a makarantar Islamiyya, an canja mata aji. Saura aji daya ta kamo Bilkisu. Khaleesa ta kara natsuwa. Abin ka dama da natsattsiyar. Ranar wata juma'a da yamma. Faruq ya dawo daga Zariya. Khaleesa bata jira ya shigo wajensu ba, tunda ta ji labarin dawowarsa, da murnar da doki cikin kwalliyar juma'arta ta shiga cikin gidan nasu. Kicibis suka yi da juna a filin tsakar gidan. Duk suka tsaya suna kallon juna. Sai Faruq ya ga Khaleesa ta kara masa kyau. Cikin murmushi yace ''Hello Pretty, how are you? Ba zato balle tsammani ya ji Khaleesa ta amsa da cewa ''I an fine''. Nan da nan ya hangame baki gami da dariyar mamaki yace ''Pretty ki ce min kin zama baturiya? Amma kin bani sha'awa. Hakan kuma ya tabbatar min da cewa ''Ki na maida hankali sosai kan karatunki, ba za ki bani kunya ba''.

Tayi murmushi a ladafce, tace ''Yaya Faruq ina kokari sosai, kaga har a Islamiyya sun kara min aji''. Faruq yayi tafi da hannunsa yace ''Da kyau Pretty, haka nake so, dama yanzu nake shirin shiga wajen ku, na kai miki tsarabarki. Saboda haka ga shi, tunda kin hutasshenie''. Ya mika mata bakar leda. Ta amsa cike da murna, ta durkusa har kasa tayi masa godiya, yace ''Idan kin koma, ki ce ina gaida Inna. Sai anjima da daddare zan shigo''. Khaleesa ta amsa da ''To''. Ta juya cike da murna, ta koma bangarensu, tana shiga kai tsaye Inna Salaha ta nufa. Ta mika mata ledar, tana gaya mata ''Yaya Faruq ne ya bani tsarabata''. Inna Salaha ta amsa tana farin ciki tace ''Dan makaranta yana tsaraba ashe? Lallai Faruq baya gajiya da hidimarmu. Allah ya saka masa da alheri''. Ta zazzage kayan akan cinyarta, doguwar riga ce mai kyau, hade da dan-kwalinta. Sai takalmi mai kyau na kwalliya. Nan da nan Khaleesa ta tsananta ma kanta murna, ta dauki kayan ta gwada. Gwanin ban sha'awa. Komai yayi mata cif! Tamkar Faruq ya gwadata. Sai tafiyar yana take tana murna. A daidai lokacin Malam Habibu. Ya shigo rike da rake a hannunsa. Shi ma Malam Habibu Khaleesa ta burge shi. Kayan sun amsheta, yayi murmushi yace ''Na san dai wannan aikin Faruq ne''. Inna Salaha tace ''Aikinsa ne fa Malam, ai Na rasa karamci irin na Faruq, yaron yana kaunarmu''. Malam Habibu ya mika ma Khaleesa raken hannunsa, ta amsa yana cewa ''Faruq yana da mutunci da karamci. Irin abubuwan da yake mana, musamman akan Khaleesa, ba mu da abinda zamu ce masa. Don haka nake jin Faruq a raina da jikina, tamkar marigayi Tasi'u. Saboda mutuntani da yake yi''. Inna Salaha ta mika masa kujera 'yar tsuguno. Ya amsa ya zauna yana ci gaba da cewa ''Kafin shigowata din nan da muka hadu a waje da shi muka gaisa. Salaha kin san me yake gaya min da muka gama gaisawa? Ta girgiza kai, yayi murmushi ya ci gaba da cewa ''Wai dama ya dawo ne akan maganar Khaleesa. An fara daukar sabbin dalibai, har kuma ya gama cuku-cukun samo mata makarantar. Sai dai bai sani ba ko yayi daidai. Domin makarantar kwana ya samo mata can inda yake karatu Zariya. Nace masa ai duk abinda yayi akan Khaleesa, daidai ne, ko Salaha? Inna Salaha ta gyara zamanta cike da fara'a tace ''Haka ne Malam. Duk abinda yayi a rayuwar Khaleesa daidai ne. Allah kuma ya saka masa da alherinsa''. Khaleesa dake gefe daya tace ''Amin''. Lokaci daya gami da lumshe idanun ta. Kwarai Yaya Faruq ya zama haske a rayuwarta, bata da kamarsa, yadda yake kokarin inganta mata rayuwa. Bata da wanda ya fi shi. Shi yasa ta sami kanta da kaunarsa matuka. Washe gari da rana Khaleesa na tsaka da cin dambu a tsakar gida. Gefen ta Inna Salaha ce, ita ma dambun take ci kan kujera 'yar tsuguno. A daidai lokacin Faruq ya shigo cikin sallama. Nan da nan Khaleesa ta mike ta dakko masa kujera, ta mika masa, ta amsa. Lokaci daya ya zauna, yana gaisawa da Inna Salaha. Bayan sun gama gaisawa. Ta dubi Khaleesa tace ''Debo ma Yayanki dambu ya ci, ko da yake Allah ma yasa yana cinsa''. Faruq yayi murmushi yace ''Haba Inna, ko bana ci ai na koyi ci, tunda ke kika dafa, balle ma ina ci. Amma ba sai an debo min ba, wannan na Khaleesa ma ya ishemu, ko Pretty? Khaleesa ta dawo tana murmushi. Ta dakko masa cokali ta dauki kwanon abincin, ta matsa kusa da shi, ta zauna ta mika masa cokalin. Ya amsa ya fara ci tare da Khaleesa. Inna Salaha na kallonsu cike da sha'awa da jin dadi sosai. Lokaci daya Faruq ya fara maganar makarantar Khaleesa da Inna Salaha, yace ''Inna da nayi tunanin kai Khaleesa makarantar kwana ne, tunda an fi samun karatu sosai, sai dai kuma ban yi shawara da ku ba, har na gama komai. Sai daga bisani nayi tunanin kamar idan na dauke miki Khaleesa, banyi miki adalci ba, don na ga tana tayaki aikace-aikacen gida, da kuma debe miki kewa''. Inna Salaha tayi murmushi, gami da girgiza kai tace ''Haba Faruq, ai ba wani abu, neman ilimi duk inda ya kama aje, ai sai aje. Ni kam don tani, ba komai Faruq, ka Kaita duk inda kake ganin ya kamata. Matukar dai ba takura ma kanka za ka yi ba''. Yayi murmushi yace ''Haba dai, ba wata takura, ai ni na daukar ma kaina''. Inna Salaha tace ''An gode Faruq, irin wannan hidima daka dauka ta Khaleesa. Ba abinda zamu ce sai dai nace Allah ya biyaka, ya kuma saka maka da alheri duniya da lahira''. Faruq yace ''Ba komai Inna, shi ilimi ya zama dole a neme shi, saboda aji dadin rayuwa, kuma Khaleesa ta cancanci a taimaka mata ta bangaren karatu, tunda tana da hazaka. Kuma tana son karatun''. Inna Salaha tayi murmushi gami da kallon Khaleesa da bakinta ya kasa rufuwa saboda jin dadi, tace ''To Faruq an gode kwarai da gaske''. Khaleesa ta dago suka hada ido da Faruq. Gaba daya suka yi murmushi, tace ''Yaya Faruq na gode''. Ya ɗan harareta, ta sigar wasa yace ''Bana hankali yi min godiya ba, idan nayi miki wani abu? Ta daga kanta, yace ''To kada ki kara, ni dai abinda nake bukata daga gareki, shine ki tsaya ki yi karatu, ki mori basirar da Allah ya ba ki. Tunda sau daya take zuwa a rayuwa ko? Khaleesa tace ''To Yaya Faruq''. Daga nan hira suka ci gaba da yi, gami da cin dambunsu. Har Faruq ya koshi, ya ake cokali, ya sha ruwa gami da yin hamdala. Sannan yayi sallama da Inna Salaha, ya fice. Inna Salaha ta raka shi da sa albarka da addu'a. Ita ma Khaleesa zuciyarta ta kara cika da kaunar Faruq tare da mutunta shi. Ya kuma kara yi mata kwarjini. Kwana biyu da dawowar Faruq. Babban abokinsa Usman ya iso daga Zariya da takardun makarantar Khaleesa wanda yake tabbatar da cewa an dauki Khaleesa a matsayin daliba a makaranta 'yan mata ta (F.G.C Basawa Zariya). Dama da zai taho a hannun Usman din ya bar komai, kasancewar bai da aminin daya wuce Usman. Tare suke karatu a (A.B.U). Aminaine sosai, kamar yadda mahaifin Usman Alhaji Mustapha da mahaifin Faruq suke abokan juna, tun suna kanana har kuma yanzu suna tare da juna cikin amana. Duk wani (Business). Tare suke yi, sun yarda da juna sosai. Hakan ce kuma ta dasa aminci da kakkarfan kawance tsakanin Hajiya Zulfa da matar Alhaji Mustapha Hajiya Juwairiyya. Su ma sun dinke da juna, suna kasuwanci tare. Duk da Hajiya Juwairiyya da Alhaji Mustapha zaunannun garin Zariya ne, to ba abinda ya rage a zumuncinsu da su da Alhaji Jafar da iyalansa. Usman da yake tsarar Faruq shi ne babban dan Alhaji Mustapha. Sai mata uku da suka biyo shi a baya. Sai namiji. Sannan sai tsararsu Khaleesa. Salamatu da zata fara aji daya a (F.G.C Basasa). Shine ma dalilin da Faruq yayi sha'awar sa Khaleesa a makarantar, don haka tare da Salamatu aka samo ma Khaleesa makarantar. Faruq tun fara karatunsa a Zariya a gidan Alhaji Mustapha yake zaune da Usman, babu inda aka yi masa shamaki a gidan. Babu kuma irin mutuncin da Alhaji Mustapha ba yayi masa a matsayinsa na dan amininsa. Ita ma Hajiya Juwairiyya duk mugun halinta da isarta, bata bambanta Faruq da Usman. Wani abin m da bata yi ma Usman ba, sai tayi ma Faruq, gaba daya an zama daya.

A daren da Usman ya kawo masa takardu, ya sami Alhaji Jafar a falonsa da maganar, tun kafin ya gama bayaninsa. Hajiya Zulfa ta katse shi, a fusace tace ''Kai Magajin gida, ni bana son tattaga da sa kai a uku irin naka, ka cika shiga sharo ba shanu. Irin wadannan fulanin da wuri suke ma 'ya'yansu aure, su ma don dai sun sami wayewa ne. Ai da tuni sun aurar da ita, kada ka sake ka shiga sabgar da ba taka ba. Bayan haka, me ka aje, wanda zai isheka daukar nauyin karatun Khaleesa? Kuma me zata iya? Yarinyar da ko firamare bata yi ba, za ka dauketa, ka kaita babbar makaranta, don daukar ma kai wuya? Ni bana son irin wannan halayyar, abinda zai yuwu shi ake yi''. Faruq ya girgiza kai gami da dubanta yace ''Hajiya duk abinda zan yi akan Khaleesa ko nake shirin yi. Sai na shawarci iyayenta, sai kuma sun bani goyon baya. Sannan zan yi. Kuma ina da tabbacin cewa ko wane irin karatu ne, Khaleesa zata iya, don tana da hazaka da basira. Ko yanzu idan ba wanda ya sani ba, babu wanda zai ce Khaleesa ba tayi firamare ba. Ta iya komai, shi yasa nake da sha'awar taimaka mata, saboda gaba''. Hajiya Zulfa ta tabe baki, tace ''Wane irin gaba? Kai dai ka yi a sannu. Wadannan mutanen, ba abinda muka hada dasu, ba mu san asalinsu ba, don haka wannan shigewar da kake musu, tayi yawa, ya kamata ka san haka''. Alhaji Jafar da bai sa musu baki ba. Furucin Hajiya Zulfa ya ishe shi ya dago a fusace yace ''Wai wace irin magana kike yi ne, mara kan gado? Khaleesa tamkar 'Ya take a gareni, ban bambantata da dan cikina ba. Meye laifinsa? Don ya tunatar damu abinda ya kamata ace mu muka yi''. Ya juya ga Faruq yace ''Allah yayi maka albarka. Wannan abu da ka yi niyya. Kamata yayi ace nayi. Amma na sha'afa. Na kuma gode da ka tunatar dani, kuma ni zan dauki nauyin karatun Khaleesa, tunda kai karfinka, bai kai na yadda zaka iya daukar nauyin karatun ta ba. Tunda kai ma dan makaranta ne, don haka ba damuwa. Tunda ka yi me wuyar ka samo takardun shiga makarantar. Ina kuma fatan Allah ya kara tabbatar maka da tausayi da taimako''. Faruq yace ''Amin''. Alhaji Jafar ya gyara zamansa yace ''Hakan kuma sai ya sa min tunanin hadata da Bilkisu a makarantar, don zata fi jin dadin karatun, tunda tana ganin na gida''. Hajiya Zulfa tayi karaf tace ''Ban gane ba? Gaskiya bana son a hadata da Bilkisu, ko wa ya zauna a matsayinsa'. Alhaji Jafar ya watsa mata harara gami da jan tsaki, bai bata amsar maganarta ba, illa kallon Faruq da yayi yace ''Don haka ina Usman yake? Faruq yace ''Yana daki''. ''To ina bukatar ita ma Bilkisu ku samo mata makarantar, duk sai su tafi tare''. Faruq ya ji dadin haka. Yayi murmushi yace ''Hakan yayi daidai. Alhaji Allah ya kara girma. Gobe sai mu tafi Zariyan''. Hajiya Zulfa ta saki wani uban tsaki, ta mike tana kunkuni, ta fice. Daga gani, ka san bata ji dadin wannan hukuncin da aka yanke akan Khaleesa ba. Balle fa hadasu makaranta daya da Bilkisu. Shi ko Faruq nan ya zauna suna ci gaba da tattauna maganar, tsawon lokaci. Sannan Faruq ya fice, ba tare da ya nemi Hajiya Zulfa ba. Cikin kankanin lokaci ita ma Bilkisu aka gama mata komai na tafiya makaranta. Wani abu ma fi dasa farin ciki ga Faruq, shine yadda Alhaji Jafar bai bambanta Khaleesa da Bilkisu ba. Duk abinda ya sai ma Bilkisu, shi ya sai ma Khaleesa. Hatta kayan makaranta dinkin irin daya ne, hakan ko ba karamin bata ma Hajiya Zulfa rai yayi ba. A ganinta ai Bilkisu da Khaleesa ba daya bane kowa da matsayinsa. Don haka tabbas ya kamata a ga banbanci. Sai dai bata furta komai ba, illa ci gaba da sa musu ido da tayi. Don kada Inna Salaha ta shigo yi mata godiyar hidimar Khaleesa da ake yi. Kwata-kwata Hajiya Zulfa bata sakar mata fuska ba, wanda hakan bai sa Inna Salaha ta fahimci komai ba, domin dai ta saba. Wani lokacin Hajiya Zulfa nayi mata irin wannan rashin sakin fuskar.

******************** Da lokacin tafiyarsu makaranta yayi. Faruq da kansa ya kaisu Khaleesa Zariya. Sai dai aka gama musu komai, ya gama musu komai, ya gama yi musu nasihohinsa, sannan yayi sallama da su, shi ma ya wuce makarantarsa. Hankalinsa kwance na ganin ya sauke nauyin daya daukar ma kansa, sai dai har zuwa lokacin daya isa(A.B.U). Bai daina ganin dan guntun hawayen Khaleesa ba da take yi, na rabuwa da shi. Sau tari idan ya tuna yadda Khaleesa ke daga masa hannu da hawayen ta a fuska, sai ya sami kansa da yin murmushi, yayi sha'awar ta kwarai a lokacin, musamman yadda ta nuna damuwarta da shi, fiye da kanwansa Bilkisu. Wacce sam bata damu ba, balle har ta tsaya tana wani kukan rabuwa da shi. Khaleesa Habeeb ta sami matsala kamar yadda daliban farko kan samu. Wadanda ba su san kan makarantar ba, kamar bakunta da sauransu, amma ba'a dade ba Khaleesa ta fahimci kan makarantar. Bata da wata damuwa, tunda dama can tana da ladabi da biyayyarta. Ta fuskanci karatunta sosai, bata wasa, balle bata lokaci. Kullum tana cikin karatu. Don bata son ta ba Yaya Faruq kunya, sabanin Bilkisu da bata damu da karatu ba. Ba ruwanta, ba abinda tasa gaba, daya wuce wasa, domin sau tari ko tana aji. Idan Malamin (Maths), ko na (Biology) ya shigo. Sai ta fita wai ita bata ganewa. Tsawon lokaci Khaleesa na lura da ita, tun bata mata magana. Har ta fara yi mata Magana. Wanda hakan ya fara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu, dama Yaya lafiyar kura dama. Domin hutunsu na farko da suka koma gida suka dawo. Bilkisu ta ki zama wuri ɗaya da Khaleesa. Dama umarnin Hajiya Zulfa kenan, ba ruwanta da ita, matukar ba Khaleesa bace tayi mata magana ba. To ba za ta yi mata ba. Duk masu tunanin Bilkisu da Khaleesa 'Yan-uwan juna ne. Bilkisu tayi ta gaya musu cewa bata hada komai da Khaleesa ba. Ita dai Baban Khaleesa dan aikin babanta ne. Tun abin bai damun Khaleesa har ya fara damunta, saboda yadda (Class mate) dinsu ke yi mata wani irin kallo na kyama da raini. Ita ko Bilkisu tuni ta dinke da Salamatu kanwar Usman, su ka koma zama da tafiya da 'Ya'Yan masu kuɗi ajinsu. Babu ruwansu da Khaleesa, kuma duk da haka Khaleesa bata daina kulata ba. Akwai wata rana ziyarar dalibai da Hajiya Zulfa ta zo tare da Hajiya Juwairiyya, domin sai da ta biya ta dakkota. Anan fa Bilkisu da Salamatu suka sasu a gaba da korafin Khaleesa ta sa musu ido. Ta takura musu, ba su da damar da zasu yi wani abu. Khaleesa ta dinga sa musu ido kenan, tana zaginsu. Nan da nan Hajiya Zulfa ta fusata. A yayin da Hajiya Juwairiyya ta saki tsaki tace ''Ai ke ma kin yi wauta da kika yarda aka hadasu makaranta daya. Ke fa kika ce ba ki san asalinsu ba. Yaushe zan iya, bari ta zo nayi ma ta katangar karfe da Salamatu. Ba ruwanta da ita. Kowa yai harkar gabansa ''. A daidai lokacin Khaleesa ta karaso wajen da kawayenta cike da farin ciki zasu gaidasu Hajiya Zulfa. Nan da nan Hajiya Zulfa ta dakatar da ita, a gaban kawayen nata tayi mata kaca-kaca. Ta kuma yi mata katangar karfe da Bilkisu. Wannan bai isheta ba, har da gori tayi mata, wanda shine yasa Khaleesa kuka. Hajiya Zulfa na gamawa. Ita ma Hajiya Juwairiyya ta ɗora, tayi mata iyaka da Salamatu da kakkausar lafazi. Khaleesa ta kara tsananta ma kanta kuka. Kawayenta suka jata cike da tausayi, suka bar wajen. A ranar Hajiya Zulfa bata ba Khaleesa komai ba, hatta kudin da Alhaji Jafar yace ta bata da sauran (Provisions). Duk Bilkisu da Salamatu ta hada ma. Ta kuma gargadesu da ko dafaffen abinci kada su sam mata. Hajiya Juwairiyya sai kara iza Hajiya Zulfa take. Haka dai suka tafi suka bar Khaleesa tana kuka. Kawayenta na lallashinta, gami da bata shawarar ta fita harkarsu Bilkisu kwata-kwata. Ita kanta Khaleesa shawarar da ta tsayar ma kanta kenan. Saboda a zahiri Hajiya Zulfa da Hajiya Juwairiyya sun yi mata tijarar tsiya. Don haka ta daukar ma kanta alkawarin fita harkar Bilkisu. Har da za'a gama ziyara. Khaleesa na zaune ta buga tagumi. Aka aiko kiranta. Inji Faruq. Nan da nan ta ji wani dadi ya rufeta, wanda ya kori bacin ran da take ciki. Sam bata son Faruq ya fuskanci tayi kuka, ko tana cikin damuwa, saboda haka ta koma (Hostel). Ta sanya hoda da kwalli. Sannan ta fita da saurinta ta nufi inda aka gaya mata yana jiranta. Yana zaune kan wata kujera, sanye cikin riga da wando na kananan kaya. Yayi matukar kyau. Gefensa kuma Usman ne, cike da farin ciki, Khaleesa ta karaso tana yi musu sannu da zuwa. Gami da dariya tana kiran sunansu ''Yaya Faruq, Yaya Usman ''. Faruq ya dago yana wurga key din hannunsa, yana murmushi yace ''Pretty kin ga na kusa makara ko?'' Khaleesa tace ''Na yi zaton ma ba za ka zo ba''. Usman yayi murmushi yace ''Ai abinda zai hana Faruq zuwa ganinki, ba ma fatan ganinsa Khaleesa''. Faruq yayi murmushi yace ''Wani dogon (Lecture) muka tsaya dauka. Tun safe, sai yanzu muka fito. Ko wanka ban tsaya yi ba, muka taho, saboda ina gudun kada a rufe ziyarar ''. Tayi dariya lokaci daya, ta tsuguna har kasa ta gaishesu. Cike da kulawa suka amsa. Sannan Usman ya kara da cewa ''Hajiya ta zo ko? Khaleesa ta daga kai a sanyaye tace ''Ta zo har da Hajiyarsu Yaya Faruq''. Faruq yayi murmushi yace ''Ki ce ku yau garau da ku? Ina su Salamatu fa? Ta dago daga tsugunon tace ''Bari na je na kirasu''. Faruq ya dakatar da ita yace ''Kyalesu, don yanzu za mu tafi. Na ga an kusa kada tashi ''. Ta dawo da baya, ta lura da yadda Faruq ke kallonta. Zuwa can yace ''Ba dai wata damuwa ko?'' Ta girgiza kai, tace ''Ba komai Yaya''. Yace ''Kada ki boye min, wace damuwa ce makale a fuskarki? Ko an gaya miki bana gani ne? Ta yi murmushi tace ''Allah Yaya bani da wata damuwa. Da da akwai, ai kai ne mutum na farko da zan gaya ma''. Ya gyada kai yace ''Shi kenan Pretty''. Usman ya ci gaba da kallonsu. Kallo na sha'awa. Sannan ya ce ''Faruq yakamata mu tafi, don bana son a kada tashi, muna cikin makarantar nan''. Faruq ya sakko daga kujera, ya mika ma Khaleesa bakar leda tare da kudi dubu daya. Ta amsa tana yi masa godiya. Usman ma ya mika mata wata dubu dayan. Ta amsa tana kara yin godiya. Daga bisani suka yi sallama. Suka tafi. Ita ma ta nufi dakinsu, zuciyarta cike da mutunta Faruq da kuma kaunarsa gami da girmama shi. Domin dai daga Faruq har Usman, babu wanda ya dakko halin mahaifiyarsa. Domin abinda mahaifiyar Usman tayi mata yau, Hajiya Juwairiyya bata taɓa tsammani ba. Haka rayuwa ta ci gaba da gudana ga Khaleesa. Tana fuskantar nunin so da kauna da kulawa daga Yaya Faruq. Yayin da take fuskantar kiyayya daga Hajiya Zulfa. Sai dai bata taba gaya ma kowa ba, har mahaifanta. Domin karamcin da Yaya Faruq ke mata, yasa dole ta kaunaci mahaifiyarsa. Haka kuma kulawar da Alhaji Jafar yake bata, ita da mahaifanta, ya kara tilasta mata mutunta matarsa da kowa nasa. Kwanci tashi, rayuwa na ci gaba da gudana. Da umarnin Ubangijin talikai. Komai na ci gaba da tabbata, kamar yadda Ubangiji ya rubuta, ya kuma tsara. Har ga shi yau Khaleesa tana aji biyar, wanda zuwa wannan lokacin, ko Khaleesa ta cika mace. Komai nata ya ji. Shekarunta goma sha bakwai, kyawun fuskarta da kyawun dirinta, sun kara bayyana. Khaleesa kyakkyawar 'Yar Fulani. Ta kara zama abar sha'awa a wajen kowa, saboda kyawunta da kuma kamun kanta. Ladabi da biyayya da uwa uba kwarjini, ga ta dai 'yar talaka gaba da baya, amma duk inda ta shiga, sai ka ga ta fita daban. Saboda kwarjininta. Haka zalika zuwa wannan lokacin. Shakuwar Khaleesa da Faruq ta kara matukar ƙarfi a tsakaninsu. A wannan lokacin ne kuma Faruq ya kammala karatunsa. Ranar daya dawo Zariya domin kwasar kayansa. Ya biya makarantarsu Khaleesa shi da Usman. Sun dan jima tare da Khaleesa kafin su yi sallama da zummar sai anyi musu hutu. Zai dawo ya daukesu, ita da Bilkisu. Akan hanyarsu Faruq ta zuwa gidansu Usman dake (G.R.A Zaria). Faruwa ya danna kaset din wakar Hausa ta Dr. Mamman Shata Katsina. A wakarsa ta Hassan Sarkin Dogarai. Mawakinsa kenan da yake kauna, wanda har yanzu bai ga kamarsa ba. Wakar na fara tashi. Faruq ya shiga gyada kai. Yana bin wakar. Sannan ya kara ma motarsa gudu. Kamar kullum idan yana jin wakar Shata, ya kan rasa lokacin da yake kara ma kansa gudu a mota. Usman ya ɗan dube shi gami da girgiza kansa yace ''Faruq''. Bai ji shi ba, har sai daya kara kiran sunan sa da karfi gami da rage karar Rediyon. Wanda hakan yasa Faruq ya kula da Usman yace ''Ya aka yi ne Shehu Usmanu, ya za ka rage min karar wakata? Usman yace ''Saboda ina son nayi magana da kai. Wacce ta shafeka, duk da ina ganin katsanlandan zan yi''. Faruq yayi murmushi yace ''Usman in dai da gaske abinda ya shafeni ne. Ai bana zaton katsanlandan zaka yi min. Domin dangantakarmu da kai, ta wuce haka. Ni da kai duk daya ne, don haka ina sauraronka ''. Ya karasa maganarsa gami da kara rage Rediyo. Usman ya dan muskuta ya fara magana a hankali, wacce ba alamar wasa a cikinta ''Faruq tsawon zaman rayuwata da kai a makaranta, tun daga farkon karatunmu har zuwa yanzu da muka kammala. Na san halinka fiye da kowa, tunda nake da kai, ban taba ganin ka yi soyayya da wata daliba ba. Duk da kullum sai ka sami sakon tayin soyayya daga 'yan matan jami'a. Amma ba ka bi ta kansu har zuwa yau da muka bar makarantar. Ba ka da wata tsayayya, kuma a kullum kana ikirarin baka san soyayya ba. Amma da dadewa tuntuni na tabbatar ma da kaina cewa kana cikin soyayya tsuundu!! Amma na ga alamar kana zolayar kanka da gangan''.

Faruq ya ɗan dubi shi lokaci daya. Ya mayar da idanunsa kan hanya yana murmushi.Yace ''Ban fahimci maganar ba Usman. Da wace yarinyar nake soyayya, wacce ni da nake soyayyar ban Santa ba? Usman yace ''Ka santa Faruq, illa kana neman ka yi wasa da tunaninka, da tunanin ita kanta yarinyar da na tabbatar ita ma tana sonka. Sai dai duk kun ki gasganta junanku ''. Faruq yace ''Ban fa fahimceka ba Usman ''. Usman yayi dan murmushi yace ''Ina nufin Khaleesa''. Faruq yai murmushi gami da lumshe ido, yace Khaleesa! Usman ya gyada kai, yace ''Kwarai, ko ka yarda, ko kada ka yarda kana son Khaleesa. Ban sani ba, ko ka sani kana boye min ne. Ka damu da Khaleesa fiye da komai, baka kaunar bacin ranta, kana kaunar duk abinda zai sanyata farin ciki. Kowane lokaci bakinka na aikin furta sunanta, zuciyarka na aikin tunaninta. Duk kuma ranar da ka je, ka ganta a ranar kana wuni cikin farin ciki. Shin Faruq meye wannan? In ba so ba? Faruq dai yana jin Usman, ya ci gaba da cewa. ''Khaleesa kyakkyawa ce kwarai da gaske, tana da hali na kwarai tana da ladabi. Me kake tunani a kanta, kake kuma jira da har yanzu ba ka gaya mata gaskiyar zuciyarka a game da ita ba? Ina son ka gaggauta yin hakan, don bana son ga-rin kallon ruwa........Kwado yayi maka kafa. Ka yi tunanin maganganuna''. Faruq ya numfasa gami da gyada kansa yana dan murmushi yace ''Na ji Usman, na kuma gode da fahimtata da ka yi, kwarai da gaske ina son Khaleesa so mai tsanani. Wanda ba zan iya kamanta shi da kowane irin so ba, tun tana karama. A rana ta farko dana fara ganinta na sami kaina da kaunarta, kiwonta nake Usman. Ina kokarin na inganta mata rayuwa, na maida ta abar sha'awa. Saboda na ji dadin zaman aure da ita''. Ya nisa gami da dan murmushi. Sannan ya ci gaba da cewa ''Bana son garaje, ko kuma na shiga karatun Khaleesa. Bana son na fara da sa mata tunanin soyayyata yanzu. Domin ina son ta maida hankalinta sosai akan karatu, domin ina kwadayin ta sami sakamako mai kyau. Saboda ina da burin Khaleesa tayi karatu mai zurfi. Don ina son ni kaina na dinga alfahari da ita, don haka ba zan sanar da ita gaskiyar soyayyata ba. Sai ranar da ta kammala makaranta, ta dawo gida''. Usman ya dube shi, yace ''Da kake cewa ba za ka gaya mata yanzu ba, saboda karatunta. To ita kana da tabbacin bata tsayawa da kowane saurayi? Faruq yayi murmushi yace ''Ka Sanni da kishi. Da hakan na faruwa. Da tuni na fayyace mata matsayinta a gareni. Khaleesa ba karamin sha'awa take bani ba. Usman bata tsayawa da kowa. Ba ruwanta da samari, karatu kawai tasa a gaba. Hakan ko ba karamin burgeni yake yi ba''. Usman ya gyada kai cikin fara'a yace ''Duk dai yadda ka ce, Khaleesa dai ni na san taka ce''. Daga nan suka ci gaba da hirarsu, wacce tafi tafiya akan Khaleesa. Suna isa G.R.A. Bai tsaya bata lokaci ba, kasancewar yamma ta fara yi. Bayan yayi sallama da Hajiya Juwairiyya. Kawai sai ya kamo hanyar Kanon Dabo, ya bar Usman a Zariya. Bayan yayi masa alkawarin zai ziyarce shi mako mai zuwa. Faruq ya koma Kano cike da tunanin Khaleesa. Ta bangaren Khaleesa kuwa, bayan tafiyarsu Faruq, tana kwance rigingine kasan gadonta. Cikin zurfin tunani, kamar kullum, idan Faruq ya ziyarceta, ta kan tsinci kanta cikin irin wannan zuzzurfan tunanin da abinda yake haddasa mata. Face dumin jiki da radadin zuciya. Shin ya zata bullo ma zuciyarta da take neman daukar mata Dala ba gammo? Ya zata yi ta yaki muguwar soyayyar Yayanta Faruq da ta zamar mata tamkar ciwo a zuciyarta. A hankali ta dan saki tsaki, wanda ya jawo hankalin kawarta Raleeya da take aikin shirya kayan da Faruq ya kawo ma Khaleesa a locker. Da suke aje kayan abincinsu. Raleeya tayi 'yar ajiyar zuciya gami da kiran sunan Khaleesa. Amma Khaleesa bata san abinda take ba, har sai da Raleeya ta bugu katifar da take ka, sa'annan tayi firgigit ta dubi Raleeya gami da gyara kwanciyarta, tace 'Ya aka yi ne Raleeya? Raleeya ta taso ta dawo kusa da ita ta zauna, tana kallonta tace ''Kullum Yaya Faruq ya zo, ya kan tafi ya barki cikin matsala. Kin fa san abinda kike yi, don ke ba karamar yarinya bace. Kin san baki, kin san fari. Yakamata ki san halin da kike ciki game da Yaya Faruq. Don wannan danne-dannen da kumumun, ba abinda zai kareki da shi''. Khaleesa ta yunkura ta tashi ta zauna cike da damuwa, tana kallon Raleeya tace ''Raleeya na rasa lokacin da nayi saken da zuciyata ta fara kaunar Yaya Faruq, na rasa lokacin, illa dai na wayi gari tunda na san kalmar so. Na ji gaba daya ba ba Yaya Faruq tawa soyayyar. Raleeya kin fi kowa Sanin yadda zuciyata take tafasa da kaunarsa, amma me? Na yi wauta, domin Yaya Faruq ya fi karfina ''. Ta dubi Raleeya ido cikin ido. Ta ci gaba da cewa ''Yaya Faruq dan masu kuɗi ne. Ya hada komai na jin dadin rayuwa. A karkashinsu muke. Shi da mahaifansa. Sune gatanmu, bamu da komai sai su, ba mu da kowa. Sai su. Mu talakawa ne gaba da baya, a gidansu muke zaune muke kuma cin arziki. Tun bayan barowarmu garin mu. Raleeya to ta Yaya zan yi? Tunanin cewa ni 'Yar Fulanin nan. 'Yar talakawa ta dace da mutum kamar Yaya Faruq? Ta karasa maganar idanunta cike da kwalla. Raleeya ta dafata ita ma cike da damuwa tace ''Haba, ya kike irin wannan maganar? Sai ka ce ba ki da ilimi? Dan Fulani da talaka ba mutum bane? Don me kike tunanin kudi da jin dadin Yaya Faruq zai sa ya fi karfinki. Allah shi yayi talaka da me kudi. Kuma kamar yadda kike tunanin Yaya Faruq yana da baiwa. Haka ke ma ki na da shi. Khaleesa Allah yayi miki baiwar kyau, ki na kuma da hali na gari, ga ladabi da hakuri. Wannan ma baiwa ce babba. Allah ya ba ki. Sai ki gode masa''. Khaleesa ta dubi Raleeya tace ''Na ji Raleeya, amma kina tunanin Yaya Faruq ni ma zai so-ni? Raleeya tayi dariya tace ''Me zai hana? Ba kya ganin yadda ya damu dake ne. Don haka ki kwantar da hankalinki, kina zaune a shararren waje. Yaya Faruq zai turo miki tayin soyayyarsa. Wannan tabbas ne. Da ikon Allah ''. Khaleesa ta ji dadin maganganun Raleeya. Don ko ba komai, sun sanyaya mata zuciya, ta ji sauki. Ta kuma yi addu'ar Allah ya tabbatar da hasashen Raleeya. Yasa Yaya Faruq dinta ya so-ta, wanda shine kadai burinta.

*Zuwa* wani lokaci kankani. Su Khaleesa suka sami hutun makaranta, wanda idan suka dawo zasu shiga ajin karshe. Faruq da kansa ya aje duk wani uzurinsa ya shirya ya je ya dakkosu zuwa gida. Tun bayan daya kaisu gida. Bai kara shiga wajensu Khaleesa ba. Sai washe gari da rana. Khaleesa na zaune a tsakar gida tana gyara ramar da Inna Salaha zata zuba a faten tsakin da take dafawa. Ya shigo kai tsaye tabarmar da Khaleesa ke zaune, ya nufa ya zauna. Lokaci daya ya fara tayata tsinkar ramar, ba tare da yayi murmushi tace ''Yaya Faruq nawa. Wa ya koya maka aikin mata?

Ya dago ya dubeta gami da turbune fuska yace ''Ba ruwanki da ni, ki daina yi min magana. Ko tunda na shigo, kin ga na kulaki ne? Khaleesa ta dafe saman kuncinta tace ''Kai Yaya na, me nayi maka, kuma daga rabuwar mu jiya? Ko dai don ni bani da wuyar laifi? Ya dago ya sakar mata wani irin kallo wanda ya haddasa ma jikinta jin sanyi. Yace ''Wato ma ba ki san laifinki ba? Ta girgiza kai a sanyaye tace ''Ban san nayi ma laifi ba Yaya. Don a rayuwata babu mutumin da bana son nayi ma laifi irinka. Don idan nayi ma laifi. Na kan rasa inda zan sa kaina. Ka ga kenan ba zan yima laifi da gangan ba''. Furucinta ya sanyaya zuciyar Faruq. Ya dan matso kadan kusa da ita yana kallon yadda yanayinta ya koma, na damuwa. Yace ''Pretty me yasa kika ki zuwa kirana jiya? Khaleesa ta dube shi da sauri tace ''Kiranka? Ni ban san maganar ba''. Ya ɗan harareta yace ''Jiya na aiko Bilkisu ta kira min ke, don na ga sakamakon jarabawarki. Ki ka ce mata ba za ki sami damar zuwa ba. Saboda kina aiki. Sannan ki ce min ba ki san maganar ba? Khaleesa tayi kasa da kanta cike da bakin cikin karyar da Bilkisu tayi mata. A sanyaye tace ''Ka yarda da ni Yaya. Ko Inna za ka tambaya, ka tambaya, tunda muka dawo. Bilkisu bata shigo gidan nan ba. Ta yaya za'ayi ka aiko kirana, ko wane irin aiki nake yi, na kasa ajewa na zo? Ai ka fi karfin haka, don haka, don Allah ka yi hakuri. Ban sami sakon kiranka ba. Bari na dakko maka sakamakon nawa ka gani''. Kafin ta tashi. Faruq ya aje ramar hannunsa, ya mike a fusace ya fita. Ba tare da yace ma Khaleesa komai ba, illa ita da take ta kiransa. Wanda hakan yasa Inna Salaha fitowa daga daki. Tana tambayarta, don me zata dinga kwala masa irin wannan. Kiran sai ka ce sa'anta? A ladafce Khaleesa ta gaya mata komai, ta kara da cewa ''Bana son ya sami Bilkisu da ko wacce irin magana, yadda kuma na ga ransa ya baci, tabbas na san sai yayi mata fadan karyar da tayi masa''. Inna Salaha ta jinjina kai tace ''Kai Allah ya sauwake, na ki jinin ƙananan maganganu. Ni bani ramata kin ji, na zuba a fatena, ku kuka sani''. Khaleesa ta mika mata farantin ramar, ta amsa da sauri ta shiga dakin girki. Bilkisu na kwance kan doguwar kujera tana aikin kankare jan kumbar da tasa a yatsunta. Faruq ya fado falon ransa a matukar bace, ya tsaya a kanta ya shiga yayyafa mata ruwan fadan. Don me zata yi karya akan aiken da yayi mata wajen Khaleesa? Meye dalilinta? Bilkisu ta kasa cewa uffan, illa jikinta daya dauki rawa, don bata taɓa katarin ganin bacin ran hakurarren Yayan nata irin na yau ba. Fadan da Faruq ke yi ne, yasa Hajiya Zulfa fitowa daga daki da sauri tana tambayar dalilin fadan nasa? Da abinda Bilkisu tayi masa. Nan da nan ya juya gareta ya gaya mata komai. Ya kara da cewa ''Don me zata yi ma Khaleesa karya? Kuma sanin kanta ne, na tsani mutum makaryaci, idan ba zata je aikena ba. Ai sai ta gaya min, ba wai tayi min karya ba''. Hajiya Zulfa dai tsayawa tayi tana kallonsa, cike da jin haushi da mamaki. Ta yamutsa fuska tace ''Yanzu Magajin gida, saboda Khaleesan ne kasa 'Yar-uwarka a gaba da wannan masifar. Sai ka ce za ka ga bayanta. Khaleesan me? Na fa gaji da wannan halayyar taka da kake nunawa akan Khaleesa. Me ka haɗa da ita? To tsaya ka ji. Bilkisu tana jin maganata, don haka bata shiga sabgar wadannan talakawan. Bata shiga wajensu, don haka kada ka kara aikenta, kuma anyi mata karyar''. Faruq ya jinjina kansa cike da jin haushi yace ''Yanzu Hajiya, Bilkisu ba laifi tayi ba? ''Eh, ba laifi tayi ba, kuma kada ka kara yi mata irin wannan hayagagar. Koda hakan ta kara kasancewa''. Faruq bai iya cewa uffan ba, saboda maganganun Hajiya Zulfa sun kona masa rai. Saboda haka yasa kai ya fice daga falon, yana hadiyar bacin ransa. Bayan fitarsa Hajiya Zulfa ta ci gaba da sababin fadanta. Bilkisu kuma matsar kwalla take yi. Da safe da Khaleesa ta shiga gaida Hajiya Zulfa. Da kyar ta amsa mata, sannan ta shiga yi mata fada ''Abin baki ya fara yin yawa Khaleesa. Tunda har kiyayyar da kike ma Bilkisu ta kai ki fara hadata da dan-uwanta. Ashe abin arziki ya taba zama na tsiya? Na rasa abinda Bilkisu tayi miki. Bayan cin arziki kike a gidansu. To ki yi hankali da ni. Nan da nan Khaleesa ta ladaftar da murya, ta shiga ba Hajiya Zulfa hakuri. Daga bisani ta juya ga Bilkisu ta bata hakuri, amma har ta fice. Babu wanda ya amsa mata. Cikin bacin rai ta fito. Daidai kofar fita tayi kicibis da Faruq. Nan da nan ta kori damuwar dake makale a fuskarta, ta duka ta gaida shi. Shi ma ya tsuguna a gabanta, yana kallonta, tayi murmushi tace ''Yaya lafiya? Faruq ya gyada kai, yace ''Lafiya lau, hakuri kawai nake ba ki, saboda zargin da nayi miki jiya''. Khaleesa tayi murmushi tace ''Haba Yaya, ni har na isa ka bani hakuri. Ni ban dauki komai ba Yaya''. Suka mike lokaci daya, suna kallon juna. Faruq yace ''Na gode Pretty''. Ta sake yin murmushi tace ''Kuma sakamakon jarabawata da kake don sani. Na yi na biyu ne''. Faruq ya zuba mata ido yace ''Da kyau Pretty. Amma ya aka yi keda kika saba yin na daya, kika zo na biyu? Kar dai ko kin fara wasa ne? Ta girgiza kai tace ''Bana wasa Yaya, haka dai sakamakon ya kasance, amma kayi hakuri zan dage''. Ya lumshe ido ya bude yace ''Ba komai Pretty, duk da haka kin burgeni, ina kuma alfahari dake. Kuma har kullum zan ci gaba da alfahari da ke''. Daga bisani dai Faruq ya shige cikin gida, ita kuma ta nufi bangarensu, zuciyarta cike da kaunar Yaya Faruq. Kimanin makonni biyu da dawowarsu Khaleesa hutu. Makarantarsu Faruq ta nemi wasu hazikan dalibanta, wadanda suka gama. Ciki kuwa har da Faruq da Usman. Usman din ne ma ya buga ma Faruq waya, ya gaya masa. Tun safiyar ranar da Faruq za shi Zariya, ya shiga wajensu Inna Salaha yayi musu sallama. Har bakin mota Khaleesa tayi masa rakiya gami da addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya. Sai da ta ga tafiyarsa. Sannan ta tsaya shiru ta bi sawun motarsa da kallo, gami da lumshe manyan idanunta. Tabbas duk duniya, babu wani da namiji da yake burgeta, yake tafiya da dukkan tunaninta, irin Yaya Faruq ba. Shin anya maganar Raleeya gaskiya ce? Na cewa Yayanta Faruq zai so-ta? Ita dai kam ta fada tsaka mai wuya na kaunar wanda bata da tabbas a kansa. Daga karshe dai ta takura ma kanta aje wannan tunanin. Ta kada kanta ta koma gida. Domin karasa wankin kayanta da tayi samnakon tashi da shi. Sai yamma likis Faruq ya dawo daga Zariya. Zuciyarsa cike da farin ciki da annashuwa, anma bai sami damar shiga bangarensu Khaleesa ba. Har sai bayan sallar issha'i. A lokacin Khaleesa na aikin gugar kayanta a tsakar falo, kasancewar Nepa sun yi adalci, sun bar wuta. Duk da dama ba'a wuni da ita ba. Daidai lokacin Faruq ya shigo ya gaisa da Inna Salaha da Malam Habibu da suke zaune kan tabarma a tsakar gida. Suna hira, Khaleesa duk ta kosa Faruq ya shigo wajenta amma sababin hakan. Sai Faruq yayi zamansa a gunsu Malam Habibu. Aka ci gaba da hirar da shi. Zuwa can Khaleesa ta ji Faruq yana shaida ma Malam Habibu abin arziki daya same shi. A sakamakon kiran da aka yi musu a makaranta yau. Ya gaya musu cewa yana daya daga cikin dalilan da suka fita, wadanda akayi nasarar turasu babbar makarantar koyon aikin Shari'a dake Hong-Kong. Domin gabatar da wani kos na shekara daya, wanda idan suka sami damar yi wannan kos din. Za su fito da wani babban matsayi, darajarsu zata karu kuma har da Usman shi ma ya sami damar zuwa. Hakika Malam Habibu da Inna Salaha sun yi matukar murna, sun ji dadin wannan ci gaba da Faruq ya samu, domin ci gabansa. Shine ci gabansu, sun yi masa addu'a gami da fatan alheri. Ita kam Khaleesa jikinta ne yayi sanyi. Ta tsaya shiru tama manta abinda take yi. Abu na farko daya fara fado mata a rai, shine ta yaya zata iya jure rashin ganin Faruq har na tsawon shekara daya? Mutumin da ko wuni tayi, bata gan shi ba, ta kan rasa inda zata sa kanta saboda rashin jin dadi. Balle tayi shekara daya, bata gan shi ba. Tana cikin wannan zuzzurfan tunanin ne. Kam! Ta ji an rike hannunta da take huta da shi gami da daga dutsen gugar data dora akan rigarta da sauri. Kafin ta san ko waye. Muryar Faruq ta ji daf da kunnenta ''Pretty kanki daya kuwa, kina jin kayanki na kauri. Amma ko a jikinki? Da sauri Khaleesa ta dubi rigar atamfarta. Tuni har dutsen gugar ya kwashe rabin rigar. Sai kauri kawai wanda ya cika falon. A kunyace ta dawo da kallonta ga Faruq wanda ya durkusa daf da ita. Ya dauke rigar ya daga yana kallo, lokaci daya ya wurgar da ita a kasa. Gami da kallonta, yace ''Haba Pretty, ki rasa rigar da zaki kona, sai wannan? Kin san ko yadda take miki kyau''. Khaleesa tayi dan murmushi, ta kama kunnanta biyu ta rike tace ''Ka yi hakuri Yaya, tuna nake''. Ya gyada kai yace ''To shi kenan, na san gajiya ce ta saki yin hakan. Saboda haka bari na tayaki''. Ta yi saurin girgiza kanta, tace ''A'a Yaya, ka bar shi kawai, kada ka wahalar da kanka''. Yayi mata wani irin kallo yace ''Ke kika sani''. Ba tace komai ba, illa ido da tasa masa, har ya dakko wata doguwar rigarta ya fara gogewa. A yayin da Khaleesa ta koma gefe ta zauna, tayi tagumi tana kallonsa. Shi kuma ya ci gaba da gugarsa, ba tare da ya kula da ita ba. Zuwa can Khaleesa tace a sanyaye ''Yaya Faruq, yaushe zaka tafi kasar wajen? Ya ɗan waiwayeta yace ''Wato ki na jin maganar da muke yi ko? Ta gyada kai tace ''Ina jinku Yaya, ka san duk abinda ya shafeka. Bana wasa da shi. Na kuma tayaka murna. Allah ya sanya alheri. Ya kuma tabbatar maka da samun nasara''. Kwarai ya ji dadin addu'ar Khaleesa, ya kuma kara kaunarta. Ya ɗan dubeta yace ''Na gode da addu'ar ki. Tafiyarmu kuma ba zata wuce nan da wata daya ba''. Gaban Khaleesa ya fadi. ''Nan da nan haka? Ta fada a ranta, a fili kuwa gyada kai tayi tace ''Allah ya kaimu Yaya''. Ya ɗan kara dubanta yace cikin girgiza kai ''Ya na ga duk kin canja ne Pretty? Ko har kin fara tunanin yin kewata ne, kamar yadda na fara tunanin rashinki? Khaleesa ta jinjina kai tace ''Ai dole na fara tunanin rabuwa da kai, shekara daya ba wasa bace''. Faruq yayi murmushi yace ''Idan da rai da lafiya Pretty shekara ai kwana ce. Kamar yau ne, za ki ga na dawo''. Daga nan suka ci gaba da hirarsu. Sannu kan hankali har Faruq ya gama goge ma Khaleesa kayan ta tsaf! Daga bisani yayi sallama da su Inna Salaha. Khaleesa tayi masa rakiya har waje. Sannan ta dawo gida. A wannan daren Khaleesa baccinta ƙalilan ne, ta zurfafa cikin tunanin Yaya Faruq da take zolayar kanta da cewa zai so-ta. Tabbas ta san Faruq ya damu da ita fiye da komai. Yana kuma kaunarta, sai dai ta kasa gasgata cewa zai iya sonta. Soyayya irin wacce zata kaisu ga aure, domin idan har zai so-ta, ko yana sonta. Don me zai yi jinkirin sanar mata? Alhalin shi kadai take jiran ya furta mata kalmar so. Ko zuciyarta zata fita daga rudanin da take ciki na kaunarsa. Domin shi kadai zuciyarta take so da kauna. Ba zata iya son kowa ba, sai shi. Washegari da rana Khaleesa, na wanke-wanke Faruwa ya shigo, Khaleesa ta juyo cike da fara'a tana gaida shi. Ya amsa lokaci daya gami da mika mata bakar leda. Ta amsa a lokacin da yake cewa ''Ki kai a dinka miki irin dinkin da kika kina jiya. Dayar kuma ki dinka irin doguwar rigar nan da na ga 'yan mata na yayi. Akwai kuɗin dinkinki a ciki''. A tausashe Khaleesa ta shiga yi masa godiya. Amma bai tsaya sauraronta ba. Ya juya ya tafi, yana barin mata sallahun ta gaida Inna Salaha idan ta fito. Khaleesa tabi bayansa da kallo, har ya fice. Lokaci daya ta dawo da kallonta ga atamfofin cikin ledar. Ta fito da su, guda biyu ne. Daya (English), Daya (Diamond), ta tsaya shiru tana ci gaba da kallon atamfofin. Tana yima Faruq addu'a a zuciyarta. Daga bisani ta shige daki ta kai ma Inna Salaha atamfofin. Inna Salaha ta sa ma Faruq albarka kamar kullum. Da daddare kuwa Khaleesa ta fita sayo ashana, tana dawowa ta shiga dakinta, za ta kunna fitila, turus tayi ta tsaya cike da mamaki. Tana kallon dandamemiyar katifar dake shimfide a tsakiyar dakinta. Da gudu ta fito tana kiran Inna Salaha wacce idar da sallarta kenan ta magariba. ''Inna katifar waye a dakina? Wa ya kawo ta? Inna Salaha tayi murmushi gami da cire hijabinta, tace ''Khaleesa fitarki keda wuya Faruq ya shigo da ita. A gaskiya na rasa bakin godiya ga Faruq. Al'amarinsa ya fara daure min kai''. Ta dago ta dubeta tace ''Khaleesa na tambayeki mana? Tace a yayin da take kallonta ''Tambayeni Inna''. Inna Salaha tace ''Faruq bai taba furta miki cewa yana sonki ba da aure? Khaleesa ta lumshe ido, ta so a ce amsar da zata ba Inna shine eh, amma ina. Ta bude idanunta sosai a hankali tace ''Inna makamanciyar wannan maganar bata taɓa shiga tsakanina da shi ba. Bai taba cewa yana sona ba''. Inna Salaha ta gyada kai tace ''To shi kenan, maza ki je ki yi masa godiya''. A sanyaye Khaleesa ta fita. A dakinsa ta tarar da shi kinshingide kan kujera, tayi sallama ya amsa mata sannan ta shiga, ya dago ya zauna sosai yace ''Pretty ya aka yi ne? Khaleesa ta zube a gabansa tace ''Lafiya lau Yaya, na zo nayi ma godiya ne, na ga katifa, na gode Allah ya kara arziki''. Ya ɗan tsareta da ido, cike da sha'awa yace ''Meye nayi min godiya? Ina son ki sani, A kullum na shiga dakinki, na ga tabarmar da kike kwana akai, na kan sami kaina cikin rashin jin dadi. Tsawon lokacin nan, ina burin sai miki katifa. Amma ban sami sarari ba, har gashi ina shirin barin kasar, wanda ba zan so shekarar da zan yi, ke ki yi ta akan tabarma ba. Shi yasa na sai miki, don haka ki daina yi min godiya, kinji Pretty? Cikin mutuwar jiki tace ''To''. Daga nan ya kara dubanta yace ''Kuma bana son fitar magariba, ki daina. Duk inda magariba tayi, to ina fatan ta riskeki a gida''. Ta gyada kai tace ''To Yaya, ba zan kara ba, na gode''. Ya gyada kansa, ta mike tana kallonsa tace ''Ban yi sallah ba, zan je nayi''. Ya dubeta yace ''To Pretty''. Ta juya ta fita, a yayin da ya bi ta da kallo. Khaleesa ita ce kadai burinsa, ita ce kuma matarsa da izinin Ubangiji. Khaleesa tana komawa gida ta fada kan katifarta, haka nan ta sami kanta da barkewa da kuka kamar wata karamar yarinya. Kowane lokaci Faruq kara mata kaunarsa yake yi. Domin dama ita zuciya tana son mai kyautata mata ne, tare da kin mai munana mata, to ko tabbas dole ta kaunaci Faruq, tunda yana kyautata mata kwarai da gaske. Kasancewarsu Khaleesa dogon hutu suka samu, Yasa duk akan idonta Faruq ke ta shirye shiryen tafiya Hong-Kong. Domin a kwana a tashi har ga shi yau ta kasance saura kwanaki biyu ya tafi. Har kuma zuwa wannan lokacin Khaleesa addu'a take yi Allah yasa kafin ya tafi, yace yana sonta.

*********************** Daren washegarin tafiyar tasa kuwa, ya dauki Khaleesa a mota. Sun zazzage gari, domin acewarsa yana son kafin ya tafi ya bar mata wani abu da zata dinga tunawa da shi a kullum. Kuma tabbas haka ne domin ya kawata ma Khaleesa wannan ranar da nuna mata lalle shi ma zaiyi kewarta. Sai dai ya ki furta abinda take ta fatan ya furta. Misalin ƙarfe bakwai na dare ya tsayar da motarsa a bakin wani tankasheshen (Supermarket) da ba abinda babu a ciki, ya umarceta data fito su shiga ciki. Bayan shigarsu ya umarceta da ta dauki duk wani abu da take bukata ko take da sha'awa''. Amma Khaleesa ta kasa daukar komai kunyar tasu ta Fulani ta motsa. Ganin hakan yasa Faruq ya zage da kansa yayi ta zabar mata kayan da ya san tabbas zata bukata domin kamar yadda ya santa haka yasan duk wani abu da take so, don haka ya yi ta dibar mata kaya. Tun daga kayan sawa, har zuwa takalma da kayan kyale-kyalen mata, ya kuma sai mata (Provisions) na makaranta kasancewar ya san sun kusa komawa. Kwarai da gaske Khaleesa tayi mamakin irin wannan babbar hidimar da Faruq yayi mata, ina ya sami kudi haka? Shin wane irin tattali yake yi mata? Duk wani tanadinsa nata ne, shin idan bata so Yaya Faruq ba wa za ta so? Idan bai shiga ranta ba wa zai shiga? Kwata-kwata bata sami bakin yi masa godiya ba, har sai da suka shiga mota suka fara tafiya, tana fara yi masa godiya kuwa ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu da cewa ''Don Allah Pretty ki daina yi min godiya akan duk abinda nayi miki, bansan sau dubu nawa nawa kike so na gaya miki ba, shin idan ban yi miki ba wa zai ma ki? Kuma da kin san yadda na dauke ki a zuciyata da ba ki dinga bata min rai ba, kina yi min godiya akan duk abinda nayi miki''. Tayi dabarar matse kwallarta tace ''To na daina'', yace ''Na gaji da jin hakan, ni dai abinda nake so dake duk bai wuce ki ci gaba da kama kanki, ki ci gaba da bada himma a wajen karatunki, don ina son ki yi ilimi mai zurfi don likita nake son ki zama, don haka kada ki sa wasa a karatunki ta hanyar fara soyayya''. A tausashe tace ''To, Yaya''. Ya ɗan waiwayeta gami da kiran sunanta, bata iya amsawa ba saboda yadda muryarsa ta kashe mata jiki, shi ma bai tsaya ta amsa ba ya ci gaba da cewa ''Sannan ina son ki yi min alkawari daya''. Da sauri tace ''Wane irin alkawari? Ya dauki dan lokaci bai yi magana ba, daga bisani yace ''Ina son ki yi min alkawarin cewa, zaki ci gaba da rayuwarki yadda na sanki, ma'ana ba za ki fara bata lokaci akan samarin banza 'yan yaudara ba, ki yi min alkawarin har na dawo ba za ki ba kowane saurayi kofar da zai tunkareki da batun soyayya ba balle har ki fara soyayya, saboda karatunki ya fi komai muhimmanci a gareni da ke kanki. Maganganun Faruq sun tsuma zuciyar Khaleesa, ta dago da sauri ta kura ma kyakkyawar fuskarsa ido ''Baki ce komai ba, ko kina ganin ba za ki iya yi min alkawarin ba ne? Ba za ki iya bin umarnina ba. A tausashe tace ba tare da ta dauke idonta a kansa ba ''Bin umarninka Yaya ya zama dole a gareni, don haka nayi maka alkawarin ba zan yi soyayya ba har ka dawo matukar hakan zai saka farin ciki, amma me yasa kake so nayi maka irin wannan alkawarin? Faruq ya gyada kansa gami da murmusawa yace ''Saboda ina son ki fito da sakamako mai kyau, tsayawa yin soyayya kuwa yana iya hanaki fitowa da sakamako mai kyau, don ba'a hada gudu da susar duwawu, na biyu kuma ina da wanda nake miki sha'awar ki aura don haka ni ma nayi miki alkawarin ranar da duk na dawo zan gabatar miki da masoyin daya dace dake, zan gabatar miki da wanda ya cancanci ki aura saboda so da kaunar daya dade yana miki, da kuma damuwarsa a kanki, kin ga a lokacin kin gama makaranta. Na kuma tabbatar da cewa wanda zan gabatar muku shi ne wanda ba za ki taba dana sanin auransa ba, don yana yi miki kauna mai tsanani, ai na san dai za ki yarda da zabi na ko Pretty? Cikin tsananin mutuwar jiki da tashin hankali tace ''Zan yarda da zabinka Yaya komai muninsa, don na san ba za ka taba zaba min abinda zai cutar da Ni ba''. Kin yi min alkawarin? Cikin kwalla ta daga masa kai lokaci daya kuka ya ci karfinta, ta kifa kanta a jikin cinyoyinta ta shiga kuka, Faruq ya girgiza kai yace ''Bar kuka, bana sonsa, kada ki karyar min da guiwa yau da farin ciki nake son mu rabu, saboda ba zamu kara samun dama irin wannan ba har sai nan da shekara daya, don haka bana son kuka kin ji kanwata? Ta gyada kanta kan dole ta goge hawayenta har suka isa gida, Faruq ya danne damuwarsa, tausar Khaleesa yake tare da son kawar mata da damuwa wanda mawuyaci ne idan zai iya kawar mata da damuwarta. Bayan isarsu gida da kanta tayi ta jidar kayan da Faruq ya sai mata zuwa gida har ta gama, bata tsaya gunsa ba tayi masa saida safe ta shige gida saboda ta sami damar yin kukanta wanda take tunanin shine kadai zai iya sanyaya mata zuciyarta. Tana shiga falo ta tarar da Inna Salaha tana daga kayan da Faruq ya sai mata daya bayan daya. Tana jinjina kai, tana shigowa ta dago da sauri ta dubeta tace ''Ke Khaleesa duk wannan kayan Faruq din ne ya sai maki? Ta zauna tana cewa ''Inna duk duniya wa zai yi min irin wannan hidimar? Idan ba Yaya Faruq ba, shi ne ya sai min komai'' Inna Salaha ta girgiza kai tace ''Kai, Allah me yadda yaso, Ni kam na rasa irin wannan haduwar jini naku ke da Faruq? Kullum bai da wata hidima sai ta ki, ko gajiya ba yayi ga tafiya a gabansa gobe, amma yake irin wannan hidimar, kai amma Allah ya saka masa da alheri''. Khaleesa tace ''Amin''. Daga nan ta tashi zata debi kayan zuwa daki, Inna Salaha ta dakatar da ita da cewa ''Na shigo dasu, idan Babanki ya shigo ya gani, don daf yake da shigowa tunda lokacin kulle gida y kusa''. Ta gyada kai. Sannan tayi mata saida safe ta shiga dakinta, cikin yanayin damuwa. Tana shiga daki ta fada kan katifarta ta lumshe idanunta wadanda basu jinkirta ba wajen fara bulbulo da hawaye masu dumi, shin wace irin rayuwa ce wannan ta jefa kanta na kaunar Faruq, wanda a yau ta tabbatar da cewa so da kauna na tausayi ne kawai a tsakaninsu, ba irin son da take addu'a ba. Shin waye wannan da Yaya Faruq ke don hadata da shi idan ya dawo? Waye wannan da Yaya Faruq ke kururunta mata irin son da yake mata? Alhalin bai taba gabatar da kansa gareta ba. Shin waye shi? Ta tambayi kanta lokaci daya hawaye ya kara balle mata, ita kam ta san duk duniya babu wanda zata so kamar yadda take son Faruq. Sai dai ko waye Faruq din ya gabatar mata a matsayin zabinsa ita kuma zata aure shi domin ta faranta ma masoyinta rai domin kuwa ta cika masa alkawarinsa. A wannan kuntataccen dare ga Khaleesa tayi kukan da bata taba yin irinsa ba, kafin gari ya waye kuwa tuni idanunta da fuskarta ta kumbura fuskarta ta kara jawur! Dama abin ka da farin mutum. Bayan ta idar da sallar asubah, ta jima bata bar kan sallayarta ba, tana ci gaba da lazimi, har gari ya karasa wayewa tangaran! Ta tashi ta fice cikin matsanancin ciwon kai, ta nufi bangaren dakin Yaya Faruq ta tarar da kofar Faruq a kulle saboda haka sai ta sami bakin kofar ta zauna gami da dora kanta a tsakanin cinyoyinta. Zuwa wani kankanin lokaci Faruq ya fito daga cikin gidansu a hanzarce ya karaso wajen Khaleesa ya dora hannayensa a saman kanta, lokaci daya yana mai kiran sunanta ''Pretty''. Tayi firgigit! Ta dago kanta tana kallonsa, suna hada ido zuciyar Faruq ta tsinke, komai ya kwance masa sanadiyyar ganin yadda fuskarta ta koma saboda tsabar kuka. Ya girgiza kansa ba tare da yayi mata magana ba. Ya kamo hannunta ya mikar da ita lokaci daya ya bude dakinsa suka shiga, ya zaunar da ita kan daya daga cikin kujerun dakin. Sa'annan ya durkusa a gabanta ya zuba ma kyawawan idanunta ido. Ya fara magana a tausashe ''Ban taba tsammanin za ki kauce ma umarnina ba, tunda na gargadeki da cewa bana son kuka amma dubi yadda kika maida fuskarki saboda kuka. Shekara daya har wani nisa gareta yanzu Pretty? Ta dube shi a hankali tace ''Ni ma ban lokacin da kukan ke zuwa min ba Yaya''. Maganarta ya sa shi yin dan murmushi, yace ''To idan kin ji kukan ya zo, ki dinga mayar da shi, ko kina son ni ma ki karyar min da guiwa ne ni ma ki fara ganin hawayena? Ta girgiza kai, yace ''To ina son kamar yadda na daure, kema ki daure, kin ji kanwata? Ta kara daga kai, yayi murmushi yace ''Good! To tashi ki tayani shirya jakata''. Ta dago ta zuba ma kyakkyawar fuskarsa ido tace ''To''. Suka mike lokaci daya tare suka hada kayan tafiyarsa, tun daga kan sutura har zuwa duk wani abu da zai bukata. Sai da suka gama tsaf! Sa'annan Faruq ya dawo gaban Khaleesa ya tsaya yana kallonta kasa kasa yace ''To Pretty, zan shiga nayi wanka''. Ta gyada kai a tausashe tace ''To''. Yana shiga bandaki ta sulale ta dawo gida. A tsakar gida ta tarar da Inna Salaha tana daka bushsshiyar kubewar data kwana da alwashin dakawa. Tai tsaye ta nufeta zata amshi dakan, Inna Salaha ta kara rike tabaryar ta dubeta cike da tausayawa tace ''Ba ki fa karya ba, maza ki je ki dan sha ruwan kokan naki. Yana nan a dakin girki a rufe''. Ta gyada kai tace ''To''. Sannan ta wuce dakin girkin ta dauki kokonta ta nufi ta zauna tasa kokon a gaba, ta kasa sha sam bata da sha'awar cin komai, har Inna Salaha ta gama dakan kubewarta. Ta shigo falon ta dubeta sosai tace ''Khaleesa ba ki sha kokon ba? Ta ɗan dubeta amma bata yarda sun hada ido ba, tace ''Ba na jin cin komai Inna, kaina ke min ciwo sosai''. Ta zauna tana fadin ''Tsakani da Allah ya za'ayi kanki ba zai ciwo ba? Irin wannan kuka da kike yi tun jiya kike aikin abu daya, ai hakuri za ki yi, kamar yau ne za ki ga Faruq ya dawo. Fatan alheri kawai za ki yi masa da addu'ar samun nasara ba wai ki zauna kina kuka ba, don ni dai ban ga maganin da hakan zai miki ba''. Khaleesa tayi kasa da kanta, ya za'ayi ta gaya ma Inna Salaha cewa ba kukan rabuwa da Faruq kawai take ba, har da kukan fuskantar da tayi ba zai so-ta ba, hasalima shi yana da wanda yake mata sha'awa. Ya za'ayi ta gaya ma Inna cewa tsananin kaunar Faruq ke damunta? Ba yadda za'ayi ta gaya mata. Maimakon haka ma sai ta dubi Inna Salaha tace ''To Inna, na daina''. Daga nan ta mike ta shiga dakinta tana rangaji. Jikin Khaleesa ya dauki zafin zazzaɓi ta dade a akwance akan katifarta, ta rasa ma tunanin da zata yi. Can sama sama take jiyo muryar Faruq yana sallama da Inna Salaha ita kuma albarka take sa masa tare da yi masa kyakkyawar addu'a. Zuwa can ya turo kofar dakin Khaleesa ya shigo, ya zauna daf da kafafunta, cikin mutuwar jiki da tashin hankali wanda a yanzu ya kasa boyewa ya kira sunanta ''Pretty''. Ta dago da jajayen idanunta, ta dube shi amma ta kasa amsawa. Ya lumshe idanunsa, sa'annan ya budesu sosai. Yace ''Zan tafi Pretty, Usman ya iso shi da Momi (Hajiya Juwairiyya). Ga Abba can kuma da Hajiya suna jirana za su yi mana rakiya zuwa filin jirgi''. A sanyaye tace ''To Yaya, Allah ya bada Sa'a. Ya dawo da ku lafiya, ka kuma isar min da sakon sauka lafiya zuwa ga Usman''. Ya jinjina kai yace ''To, batun alkawarinmu fa na jiya? Ta dade tana kallonsa. Sannan tace ''Zan rike alkawarinka har ka dawo, da fatan kuma zabin da zaka yi min shine ma fi alheri''. Ya zuba mata ido ji yake kamar ya matseta a kirjinsa, ya gaya mata matsayinta a zuciyarsa. Da bai sami damar yin hakan ba sai yayi dan murmushi yace ''Bana raba daya biyu Pretty alheri ne, don haka ki rike alkawarina, Allah kuma yayi miki albarka''. A hankali tana kokarin mayar da hawayenta tace ''Ameen''. Inna Salaha ta kwala ma Faruq kira ''Faruq ka fito ka rabu da ita haka nan, ga Alhaji nan ya aiko Malam kiranka''. Jin hakan yasa ya mike da sauri. Lokaci daya gami da shafar gefen fuskarta yace ''Zan yi rashinki, don haka ki kula da kanki''. Ta kasa cewa uffan, illa ido da ta kura masa har ya kai bakin kofa ya tsaya ya juyo ya lumshe mata idanunsa, Sannan ya kara da cewa ''Ki kula da kanki''. Daga nan bai saurari komai ba ya fice, da sauri Khaleesa ta yunkuro ta tashi ta bi kofa da kallo. Hakan ta ji hawaye ya fara malalo mata, ta koma ta kwanta ta kudundune zazzabin ya ci gaba da koda mata jiki. Bayan tafiyar Faruq kwarai ya bar Khaleesa cikin damuwar kewarsa da kuma kaunarsa. Tayi zazzaɓinta na kwana biyu kafin ta warke, sannan tayi kokarin boye damuwarta don dole, don bata son ta tasar ma da Inna Salaha hankali. A cikin haka ne har hutunsu ya kare, ta tattara ta koma makaranta. A makaranta ma ta ci gaba da damuwa musamman idan ranar ziyara ta zo, ta ga Hajiya Zulfa ta kawo ma Bilkisu kaya masu yawa, amma sai ta ga dama za ta ɗan bata kudin da Alhaji Jafar kan aiko mata da shi, suma din ba duka ba. Wanda a da bata damuwa saboda Faruq kan zo ya kawo mata kayan bukatarta, amma yanzu babu Faruq me shagwabata a dalilin hakan rayuwar makarantar ta fara yi mata wahala. Ba don ma ta sami kawar kwarai ba Raleeya, tana matukar taimaka mata ta fannin abinci da sauran al'amuran makarantar, bata kyashin yi mata komai saboda kaunar dake tsakaninsu. A duk kuma lokacin da ta fuskanci tana cikin damuwa Raleeya kan zauna ta yi ta kwantar mata da hankali har sai ta daina damuwa, musamman akan damuwar Faruq. Rana ta farko da Khaleesa ta gaya mata alkawarin da Faruq yasa tayi masa kafin tafiyarsa, Raleeya shiru tayi da alamun jimami da rashin jin dadi a fuskarta tace ''Khaleesa shin me yasa na ji ina raya ma kaina tabbas Yaya Faruq na sonki? Khaleesa ta girgiza kai idanunta jajir tace ''Ki daina raya ma zuciyarki haka domin ni kaina na tabbatar tausayi yasa Yaya Faruq ke min duk abinda yake min, Ni dama na san ban dace da shi ba, don ya fi ni komai, sai dai ki tayani da addu'ar Allah yasa so da kaunarsa kada ya jefani cikin wani hali''. Raleeya ta girgiza kai, ta dafata tace ''Allah shi ya fimu sanin komai, don haka mu bar masa komai''. Haka suka ci gaba da tattaunawa Raleeya na karfafa mata guiwa wanda hakan ya ɗan kwantar mata da hankali, ta kuma sa ma kanta dangana akan rashin Yaya Faruq da kuma tunanin soyayyarsa. Daga bisani dai Khaleesa ta maida hankalinta akan karatu tunda sun shiga ajin karshe, ga shi kuma Yaya Faruq na bukatar ta fito da kyakkyawan sakamako tunda so yake ta zama likita. Yawan tunanin da take yi ko yana iya kassara ma Yaya Faruq bukatarsa. ****************** A kwana a tashi, kwanaki sun shige cikin watanni. Har gashi su Khaleesa suna shirye-shiryen fara zane jarabawar kammala makaranta. Wanda yayi daidai da sauran watanni uku Faruq ya dawo daga kasar waje. A zahiri Khaleesa tayi matukar kokarin rike alkawarin da tayi ma Faruq, domin dai duk da dimbin masoyan dake kawo kansu gareta, a kullum bata saurararansu, bata tsayawa da kowa. Duk nacin mutum haka zai hakura ya kyaleta. Ga ta dai da farin jinin masoyan. Amma bata basu lokacin da zasu zanta da ita har ma su fahimci juna. Tun Inna Salaha na sa mata ido tare da lura da ita har ta gaji tayi mata magan gami da tsawatar mata da cewa babu amfanin kin sauraren masoyanta da take yi. Domin lokacinta ne yayi da zata tsaya ta zabar ma kanta abokin rayuwa na kwarai, domin ita ba yarinya bace karama da ace ma suna ruga ne, ai da tuni ta manta tana dakin mijinta, a nan din ma saboda karatun da Faruq ya sa ta ne yasa har ta kawo war haka. Don haka Inna Salaha ta bata shawarar gara ta tsaya tayi ma kanta zabin kwarai. A wannan ranar da Inna Salaha ta tsawata mata, ta fada cikin matsanancin tunani da damuwa. Tabbas duk duniya babu wanda take so sai Faruq kuma bayan haka tayi masa alkawarin har ya dawo ba zata saurari kowa ba, to ya zata yi? Kwarai ta shiga damuwa, ta kuma rasa mafita, illa addu'a da ta shiga yi akan Allah ya tabbatar mata da abinda ya fi zama alheri a rayuwarta. A cikin haka ne, har Khaleesa suka fara zana jarabawar fita, sun fara lafiya, sun gama lafiya ba tare da shan wahala ba, duk kuma suna sa rai da samun nasara. Taron hukumar makarantar data hada musamman domin su Khaleesa wadanda zasu yi ban-kwana da makarantar. Wato ranar bayanai da kuma raba kyaututtuka. Kowane dalibi na cikin tsafta da kyakkyawar shiga, musamman daliban da suka fita. Khaleesa tayi matukar kyau cikin kayan makaranta, fuskarta fes cike da annashuwa da jin dadi. Kyawun fuskarta da kyawun dirinta sun fito a cikin kayan makarantar. Abu daya ke dakushe mata farin cikinta na ranar shine rashin Faruq a wajen. Duk da kasancewar Alhaji Jafar da Hajiya Zulfa sun zo haka zalika Alhaji Mustapha da Hajiya Juwairiyya duk sun zo, amma rashin Faruq a wajen ba karamin rashin jin dadi ya haddasa ma Khaleesa ba. Taro yayi taro kusan duk iyayen yara sun hallara. Don haka aka fara gabatar da muhimman abubuwa har zuwa lokacin da aka fara gabatar da muhimman abubuwa. Khaleesa Habeeb aka fara kira, a matsayin wacce ta fi kowa iya turanci. Cikin kwarjini da kamala Khaleesa ta fito, ta gaisa da me raba kyautar, sannan ta amsa. Ker idanun Alhaji Mustapha akan kyakkyawar fuskar Khaleesa ya kasa dauke idanunsa a kanta har ta dawo inda Hajiya Zulfa da Hajiya Juwairiyya ke zaune ta mika ma Hajiya Zulfa kyautar, A lalace ta amsa. Khaleesa bata kai ga zama ba aka kara kiran sunanta, ta amshi kyauta a matsayin wacce tafi kowa kokari a (Biology), Nan ma Hajiya Zulfa ta kai ma wacce ta fara daka mata harara ita da Hajiya Juwairiyya Ganin har yanzu ba'a kira 'ya'yansu ba. Shi ko Alhaji jafar sai murna da jin dadi yake, rashin kiran Bilkisu sam bai dame shi ba. Shi ko Alhaji Mustapha sha'awar Khaleesa gaba daya ta kama shi. Tunda yake bai taba jin sha'awar wata 'ya mace ba irin yadda ya sami kansa da sha'awar Khaleesa. A lalace sai da Khaleesa ta amshi kyauta guda takwas har kuma aka tashi taron Bilkisu da aminiyarta Salamatu basu sami kyauta ko daya ba. Hakan ko, ba karamin kona ransu yayi ba, da ran iyayensu mata. Kai tsaye daga makarantar. G.R.A Gidan Alhaji Mustapha suka wuce dukansu. Wannan shine karo na farko da Khaleesa ta taba zuwa gidansu Salamatu wanda hakan ya sa ta dar-dar da nuna bakunta musamman da ta ga gaba daya babu mai bi ta kanta, babu wanda yake sakar mata fuska tunda suka isa gidan. Kowa ya kama gabansa. Ita kadai aka bari a falo tana ware idanu. Gidan cike yake da 'Ya'ya. Wannan ya shigo, wannan ya fito. Bilkisu 'yar gida tuni har tayi wanka ta cire kayan makaranta, ta sa wani (Material) mai kyau na Salamatu. Ita ma Salamatun tayi wankanta ta fito fes cikin shadda (Lemon color). Daga nan kai tsaye (Dining table) suka nufa, suka hau cin abinci ba tare da sun kula da Khaleesa ba, balle fa su ce ta zo su ci abincin. Ita ma bata bi ta kansu ba, kanta na kasa ta kosa kwarai su bar gidan. A daidai lokacin Alhaji Mustapha ya shigo falon yana gyara babban rigarsa a jikinsa, ya dan jima yana kallon Khaleesa cike da sha'awa, kafin ya karaso inda take ''Khaleesa''. Ya kira sunanta cike da fara'a ta dago da sauri tana amsawa cike da ladabi. Ya ci gaba da kallonta, sa'annan yace ''Yaya ke ba ki yi wankan, kin canja kaya ba? Kuma suna ta cin abinci ke kina gefe, ga shi har Alhaji ya fara korafin ku fito ku tafi''. Ta ɗan russuna cike da ladabi tace ''Bana jin yin wankan ne sai naje gida. Abinci kuma cikina a cike yake, na koshi tun a makaranta''. Yayi murmushi yace ''Ko ba ki koshi da abinci ba, ai kya koshi da murna, irin wannan kyaututtuka da kika samu. Ashe kina da kokari haka sosai? Na ji dadin ganin irin kwazonki Allah kuma yayi miki albarka''. Cike da fara'ar data kara kwata kyanta a idanun Alhaji Mustapha, tace ''Na gode Baba'' zai yi magana kenan Hajiya Juwairiyya da Hajiya Zulfa suka fito daga daki, ya dubesu yana murmushi yace ''Dama kamar kun san ya matsu ku zo ku tafi''. Hajiya Zulfa tace ''Ai shi baya son yin dare a hanya'', Hajiya Juwairiyya tace ''Ai ba ma laifi, an dade ai''. Har ya juya zai fita, ya tsaya yana kallon Hajiya Zulfa yace ''Ashe diyarki Khaleesa kokari gareta haka? Gaskiya ta bani sha'awa''. Hajiya Zulfa da Hajiya Juwairiyya suka tabe baki, haka zalika bata ba shi amsa ba har ya fice. Yana fita Khaleesa ta mike ta ɗan rissuna gaban Hajiya Juwairiyya tace ''Momi mun tafi'' tace ''A sauka lafiya', daga nan ta dubi Bilkisu da Salamatu tace ''Salamatu sai wata rana, Bilkisu mu ke'', Bilkisu ta dubeta shekeke tace ''Ai na san hanya''. Jin haka yasa Khaleesa ficewa ba tare da ta kara cewa komai ba. A jikin mota ta iske Alhaji Jafar da Alhaji Mustapha wanda tunda ta fito idanun Alhaji Mustapha ke kanta, yadda take tafiya ma kawai abin ban sha'awa ce ta kasance ga Alhaji Mustapha. Har ta bude kofar mota zata shiga Alhaji Mustapha ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, ta tsaya tana amsawa a ladafce. Ya zura hannu a aljihu ya fito da bandir din Sardauna dubu ashirin ya mika mata, kyautar ta girgiza Khaleesa don haka tayi saurin girgiza kai tana cewa ''A'a Baba ka bar shi kawai''. Alhaji Mustapha yayi murmushi yace ''Me yasa sauran kyaututtukan da aka yi miki a makaranta ba ki ce a bar shi ba? Tayi shiru tana dan murmushi. Ya kara mika mata kudin. Yace ''Amshi, bana bada kyauta a dawo min da ita''. Ta mika hannu ta amsa gami da rissinawa tayi masa godiya. Sannan ta dubi Alhaji Jafar tace ''Abba ka ga kyautar da yayi min? Alhaji Jafar yayi murmushi yace ''To an gode masa''. Ta raste ta bude kofar mota ta shiga wanda yai daidai da fitowar su Hajiya Zulfa. Saboda haka nan da nan su Khaleesa suka bar Zariya. Suka kama hanyar Kano, zuciyar Khaleesa cike da farinciki ganin ta kammala makaranta lafiya. A ranar, bayan isar Khaleesa gida, sai da ta kammala gyaran dakinta tayi wanka, sa'annan ta nufi Malam Habibu da Inna Salaha da makudan kudin da Alhaji Mustapha ya bata. Mallam Habibu na aikin cin gyada suyar ruwa. Khaleesa ta mika masa kudi, a razane ya dubeta gami da karasa hadiye gyadar daya riga ya tauna. Sannan yace ''Khaleesa wannan kudin fa? Khaleesa tayi murmushi tace ''Alhaji Mustapha mahaifin Usman ne ya ba ni''. Malam Habibu ya amshi kudin yana jujjuyasu. A yayin da Inna Salaha tace ''Kin tabbatar shi ya ba ki? Khaleesa tayi murmushi tace ''Haba Inna, ya za'ayi nayi muku karya? Shi ya bani''. Malam Habibu ya dago ya dubi Khaleesa yace ''An gode, Allah ya saka masa da alheri da nayi tunanin dalilin da zai sa ya ba ki wannan kudin da yawa? Sai kuma na tuna da cewa Alhaji Mustapha yana da mutunci kwarai, domin duk wani zuwa da zai yi wajen Alhaji. In dai ina wajen baya tafiya ba tare da ya bani wani abu ba, an gode kwarai da gaske''. Inna Salaha tace ''An gode masa kam! Allah ya biya shi''. Mal Habibu ya mika ma Inna Salaha kudin yana fadin ''Salaha amshi nan, ki aje mana, ki yi musu kyakkyawan boyo''. Inna Salaha ta amsa lokaci daya ta mike. Da ta shige dakinta domin ta adana kudin. Ita ma Khaleesa juyawa tayi ta shige dakinta. ********************* Dare ya tsala, ba ka jin sautin komai. Sai sautin motsin shuke-shuken dake dashe a gidan. Sai kuma jefi-jefin karar motoci. A daidai wannan lokacin Alhaji Mustapha ya gaji da juye-juye akan gado, ya yaye bargon daya rufa ma kansa. Ya mike ya shiga sintiri a tsakiyar dakin. Lokaci-lokaci ya kan tsaya ya dubi Hajiya Juwairiyya da take ta faman sheka barci. A hankali ya kai hannu ya fara shafa farin gemunsa. Yana mamakin kansa na yadda tunanin 'Yar karamar yarinya ya hana masa sakat! Ya hana masa runtsawa. A zahiri ba zai yaudari kansa, ya fada so da kauna da sha'awar Khaleesa. Yarinyar da sai a wannan ranar ya kare mata kallo, ya ga irin baiwar kyau da Allah yayi mata. Khaleesa tana da kyau. Tabbas idan ya sameta a matsayin mata ba karamin dacewa yayi ba, domin ta hada komai da yake kwadayin gani a jikin mace. Hakika yana kaunar Khaleesa, yana kwadayin auranta matukar zai sami haɗin kanta. Alhaji Mustapha dai ya tsunduma cikin bege, domin Bai gushe a haka ba cikin wannan halin har aka fara kiran sallar asubah. Idanunsa sun kekashe da tunanin da begen 'yar karamar yarinya Khaleesa, sa'ar autarsa. Wayewar garin ma haka Alhaji Mustapha yake sukuku gaba daya harkokinsa na ranar a daddafe yayi su. Duk a dalilin tunanin Khaleesa daya tabbatar ma kansa da cewa ba zai iya rabuwa da kaunarta ba da bai san lokacin da yayi masa irin wannan mugun kamun ba. Ya fada tunanin yadda zai bullo ma al'amarin da yadda zai tunkari Khaleesa da wannan maganar ta aure. Domin a ganinsa hakika yayi ma Khaleesa tsufa, mawuyaci ne idan zata yi na'am da shi. Bayan sallar magariba Alhaji Mustapha ya lalubi Alhaji Jafar a waya, bugu uku Alhaji ya dauka, ba su jima suna magana ba Alhaji Mustapha ya gaya ma Alhaji Jafar halin da ya tsinci kansa a game da Khaleesa. Ya kare da cewa ''Na san yadda nake da kai, babu abinda zan nema ta hannunka na kasa samu matukar kana da iko da shi. Kuma a tunanina Malam Habibu da iyalinsa duk a karkashinka suke, zasu so su kuma yarda da duk abinda ka zarta akan 'yarsu, don haka na fara gaya maka''. Alhaji Jafar yayi murmushi sosai gami da gyara zamansa akan kujerar hutawarsa ta harabar gidansa. Yace ''Alhaji Mustapha masu gari! Kwarai na ji dadin maganarka, domin na sanka ciki da baya. Tabbas idan Khaleesa ta sameka a matsayin miji ta ji dadi, domin kai mijin marainiya ne. Na tabbatar zaka riketa da amana, tunda ka san abinda kake yi. Wani manyantarka, duk ba wani abu bane. To amma? Ya dakata gami da hadiye yawu. Alhaji Mustapha bai katse shi ba har ya ci gaba da cewa ''Ka yi hakuri, zan tuntubi mahaifinta. Matukar bai mata miji ba, ko ita bata fitar da miji ba, to zan gabatar da maganarka a gare shi, za kuma ka ji yadda muka yi da shi a wannan daren, tunda na ga alamar a matse kake''. Alhaji Mustapha ya dan muskuta yace ''To Alhaji Jafar, na gode kwarai da gaske''. Alhaji Jafar ya girgiza kai yace ''Ba komai, ai wannan yi ma kai ne, duk daya ne''. Alhaji Mustapha yace ''Sau maganar kayan nan. Dazu Alhaji Sani yayi min wayar cewa ba za a sami iso da kayan gobe ba, sai jibi''. Alhaji Jafar ya gyada kai yace ''Allah ya kaimu, ya kuma iso da su lafiya''. Ameen. Daga nan suka yi sallama da alkawarin Alhaji Jafar zai neme shi a waya don ya ji yadda suka yi da Malam Habibu. Bayan sun yi sallama kwarai Alhaji Jafar ya ji dadin maganar amininsa. Domin ya san Khaleesa yarinya ce mai natsuwa. Yana yi masa sha'awar ta, kamar yadda yake mata sha'awarsa, domin dai ta san amininsa ne na-gari. Alhaji Jafar bai sami damar yin magana da Malam Habibu ba har sai bayan da aka idar da sallar issha'i. Ya fito daga Masallacin gidansa. A yayin da Malam Habibu ke biye da shi a baya cike da natsuwa da girmamawa. Daidai harabar gidan, inda aka girke kujerun zama. Alhaji Jafar ya tsaya ya ɗan waiwayi Malam Habibu yace. ''Yauwa, Malam Habibu ina da maganar da neke son yi da kai mai muhimmanci''. Cike da ladabi Malam Habibu yace ''Lafiya dai ko Alhaji? Alhaji Jafar ya nemi kujera ya zauna, a yayin da yake cewa ''Lafiya lau Malam Habibu, illa maganar Khaleesa ce''. Malam Habibu ya duka kasa, amma sai Alhaji Jafar yace ''Tashi ka yi zamanka kan kujera, ka san na gaya maka bana son ka dinga duka min, yayin da nake magana''. Malam Habibu yayi murmushi, sannan ya mike ya zauna yana mai fuskantar Alhaji Jafar, yace ''Ina sauraronka Alhaji''. Alhaji Jafar yayi gyaran murya yace. ''Dama ina son na ji daga gareka ne, ko ka yi mata miji, ko kuma ita ta fitar da mijin auranta? Malam Habibu ya gyara zama cike da natsuwa yace ''Haba Alhaji, ai kai ne mai yima Khaleesa miji, ba ni ba, tunda ko ba kayi mata ba. To ka ga bata da tsayayye kenan, tunda ita kanta bana tsammanin tana da wani wanda ta tsayar''. Kwarai matuka Alhaji Jafar ya ji dadin furucin Malam Habibu, ransa yayi masa dadi. Yadda ya nuna masa cewa yana da iko akan 'yarsa. Don haka ya gyara zamansa yace ''Da ai na yi zaton ai ko a cikin manemanta ka fitar mata da miji ne''. Malam Habibu ya girgiza kai, yace ''Ko daya ban yi mata miji ba''. Na san dai ka san aminina Alhaji Mustapha na Zariya? Malam Habibu ya gyada kai, yace ''Farin sani kuwa Alhaji''. Yace ''Yauwa, to a zahiri shine ya nuna min yana son auren Khaleesa. Yana son ka ba shi damar da zai gabatar da kansa a gareta, matukar ba ka yi mata miji ba. Tunda ko ba ka yi mata ba. To yana neman damar zuwa gareta, shine nace yayi hakuri zan tuntubeta tukuna, na ji ta bakinka''. Fuskar Malam Habibu cike da fara'a. Ya dago ya dube shi, sannan yace ''Babu komai Alhaji, idan har ka amince da shi, to ban da abin cewa daya wuce nace Allah ya sanya alheri. Komai yana hannunka, babu wata damuwa''. Alhaji Jafar ya muskuta cike da jin dadi yace ''Kwarai na amince da Alhaji Mustapha, ba don wai yana matsayin aminina ba. A'a sai don kyawun halinsa da mutunci. Na yi imani zai rike Khaleesa fiye da yadda saurayi zai riketa. Na kuma gode da wannan karamci naka''. Malam Habibu ya girgiza kai, ''Bakomai Alhaji, Allah yasa a yi damu''. Daga nan suka ci gaba da tattaunawa akan maganar, har zuwa wani tsawon lokaci, sa'annan Malam Habibu yayi masa sai da safe, ya shige bangarensa. Ya bar Alhaji Jafar na laluben wayar Alhaji Mustapha. Bugu daya, ya dauka tamkar yana jira ne. Ba tare da bata lokaci ba ya gaya masa komai, kwarai Alhaji Mustapha yayi murna, ransa yayi masa kal! Ya kuma tabbatar ma da Alhaji Jafar cewa gobe yana bisa hanya. Yayi masa godiya, sa'annan suka yi sallama, zuciyar Alhaji Mustapha cike da farin ciki. Shigar Malam Habibu gida, ya tadda Inna Salaha kwance kan tabarmar tsakar falo, tana sauraron Rediyo. Duk da Rediyon tana shakewa, ba'a faye jin abinda ake cewa ba. Da alama ita ma Rediyon ta dameta. Domin Malam Habibu na shigowa, ta mika hannu ta kashe Rediyon, lokaci daya tana me tashin zaune. Wanda hakan ya ba Malam Habibu rabawa kan tabarmar, ya zauna a gefe yana kallon matarsa. ''Malam ka shigo? ''Eh, ina Khaleesa?'' ''Tana cikin dakinta, ina tsammanin sallah take yi''. Ya gyada kai, Inna Salaha ta yunkura ta mike tana fadin ''Bari na kawo maka tuwonka, dama ina ta maka alhinin kila kafin ka shigo, ya huce''. Malam Habibu ya girgiza kai, yace ''Bar tuwon nan tukuna Salaha, dawo ki zauna mu yi magana''. A sanyaye Inna Salaha ta koma ta zauna, tana dubansa ''Malam wace irin magana ce?" Ya dubeta, sa'annan yace ''Magana ce akan Khaleesa''. Ba Inna Salaha ba, hatta Khaleesa da take kan sallayarta ta idar da sallar issha. Hankalinta ya dawo kan abinda Malam Habibu zai fada a game da ita. Sannu kan hankali cikin natsuwar murya, Malam Habibu ya gama labarta ma Inna Salaha duk yadda suka yi da Alhaji Jafar a game da maganar Khaleesa. Ya kare da cewa ''Salaha idan ki kayi la'akari da irin karamci da mutuncin da Alhaji Jafar yayi mana. Ya rikemu amana, ya zauna damu alhalin bai sanmu ba. Babu abinda ya haɗa damu, bai kyamace mu ba, a matsayinmu na talakawa fitik! Wannan dalilin yasa babu abinda zai nema a gareni, matukar ina da shi na kasa yi masa. Don na san babu abinda zan iya saka masa da shi. Don haka ba Alhaji Mustapha ba, wanda ba shi da makusa, ko wani ne mai masuka ya biyo ta hannun Alhaji, to zan ba shi Khaleesa. Ba zan ba Alhaji kunya ba, balle na tabbatar Khaleesa ta dace da abokin rayuwa a yadda nake ganinsa yana da mutunci. Don haka Salaha, a wannan ranar a kuma wannan daren na tsayar ma da Khaleesa Alhaji Mustapha a matsayin mijinta abokin rayuwarta. Domin Allah, sa'annan domin na faranta ma Alhaji rai''. Gaban Khaleesa yayi mummunan faduwa. Nan da nan jikinta yayi matukar sanyi, numfashinta ya fara yi mata wahalar fita. Nan da nan ta yaye hijabin kanta, ta fara fifita, fuskarta ta sami isasshiyar iska. Shin wane Alhaji Mustapha? Mahaifin Usman da Salamatu? Tambayar da zuciyarta take mata kenan. A gaggauce, lokaci daya kuma tana ci gab da sauraron abinda mahaifinta ke tattaunawa a kanta. Inna Salaha ta gyara zamanta, fuskarta kunshe da fara'a tace ''Wannan hukuncin da ka yanke, daidai ne ni ma kuma na goya maka baya. Ba yarda, domin Alhaji Jafar ya fi karfin komai a garemu. Ita kanta Khaleesar, babu wani wanda na ga alamar ta tsayar. Hasalima ba tsayawa take da samarin ba, balle har ta sami wanda take so. Ban san tunaninta ba, don haka hakan yayi daidai, domin dai Khaleesa ta isa aure. Ta zama uwar mata. Kuma ta kammala karatunta, to me zamu jira da ita? Malam Habibu ya gyada kansa, ya ji dadin hadin kan da Inna Salaha ta ba shi. Dama basu taba samun sabanin ra'ayi ba da matar tasa. Khaleesa na cikin gigitaccen hali na dimauta da damuwa, komai yayi mata dif! Ta ji muryar Malam Habibu na kiranta. Wanda hakan yayi sanadiyyar kara rikicewarta, cikin matsanancin faduwar gaba da sassarafa, ta isa falon ta sami gefe daya ta zauna, ba tare da ta iya yin magana ba. Malam Habibu ya dubeta, a lokacin da Inna Salaha ta mike ta fita, domin dakko masa abincinsa. A hankali ya kira sunanta ''Khaleesa''. Cikin sarkewar murya ta amsa, ya ci gaba da dubanta, yana fadin ''Khaleesa duk wani da ba shi da ranar da zai ma iyayensa, daya wuce yayi musu biyayya akan komai, ban san burinki ko ra'ayinki ba. Tunda kin kammala karatunki yanzu, wanda naso ace akan idon Faruq hakan ta kasance. Domin shine yayi miki sanadin yin karatun. Mai yuwuwa da yana nan, yayi tunanin ki ci gaba. Wanda wannan sabanin ra'ayinmu ne. Don a yanzu ke kanki kin san aure shi ya dace da yanayin rayuwarki''.

Ya dan numfasa, wanda yayi daidai da dawowar Inna Salaha. Ta dire masa abinci da kwanon ruwa a gaba. Sa'annan ta nemi waje ta zauna, ita ma ayi da ita. Malam Habibu ya ci gaba da cewa ''A dalilin hakan, Alhaji Mustapha ya nemi izinin zuwa gunki neman aurenki, na kuma yarje masa, hasalima shine mutumin dana tsayar miki a matsayin miji. A matsayina na mahaifinki, don ya biyo ta hannun wanda ba zan taba iya ce masa a'a ba. Don haka ina fatan za ki yi min biyayya, ki amince da shi. Domin shine zabina a gareki''. Khaleesa ta kasa ko da kwakkwaran motsi, illa jikinta daya dauki rawa. Haka zalika bata sami karfin guiwar yin magana ba, har Inna Salaha ta dubeta tace ''Ai kin ji abinda Malam yace? Bana tunanin kuma za ki bijire ma maganarsa? Ba kuma na son ki dubi tsufan Alhaji Mustapha, illa dai ki yi ma kanki fatan alheri''. Khaleesa ta takura ma kanta gami da daidaita muryarta da kyar, sa'annan tace a hankali cikin murya mai kama data hadiyi wani nannauyan abu. Tace ''Na ji, Allah yasa hakan shi ya fi zama alheri''. Malam Habibu da Inna Salaha sun ji dadin maganar Khaleesa, gaba daya suka hada baki da cewa ''Amin''. Sa'annan suka shiga sa mata albarka. Ba tare da sun kula da matsanancin halin gigitar da Khaleesa ke ciki ba, suka bata damar ta tashi ta koma dakinta. Jikinta a sanyaye tana gauraye hanya tamkar bugaggiya, ta shiga dakinta. Kwance tayi lamau! Akan katifarta, kwakwalwarta ta dau matsanancin caji. Komai na duniyar ya tsaya mata cak! Shin wace irin rayuwa zata fada ma, idan har ta auri Alhaji Mustapha? Wanda ta dauki Dansa Usman a matsayin babban Yayanta, wanda take jin kunya gami da girmamawa, Sa'annan wane irin zama zata yi da Salamatu? Wacce ta tsaneta haka kawai, haka zalika ita kanta Hajiya Juwairiyya data dauketa tamkar mahaifiyarta, ya zata yi ta iya zaman kishi da ita? Shi kansa uban gayyar Alhaji Mustapha, ya zata yi ta iya kallonsa a matsayin mijinta? Alhalin a da a matsayin uba ta dauke shi. Rashin amsoshin tambayoyin da zuciyarta ke raftako mata, yasa ta furta da karfi ''Inna-lillahi-wa'inna-ilaihirraju'un! Nan da nan hawaye ya fara mata ambaliya, tuni ta jike bangaren katifar da fuskarta take. Tasa hannunta na hagu, ta dafe kirjinta da yake dakan uku-uku. ''Wannan wane irin al'amari ne? Ko alama bata yima kanta sha'awar auren Alhaji Mustapha ba. Domin bata taɓa tsammanin zata iya kaunarsa ba. Domin tuni ta sadaukar da so da kaunarta ga Yaya Faruq. Mutumin da ta san har abada ba zata taba samunsa a matsayin miji ba, koda wannan maganar bata bullo ba, balle ta bullo ta inda bata taɓa tsammani ba. Cikin kuka tace ''Me yasa Yaya Faruq ba ka so ni ba? Ta sanya kanta tsakanin kafafunta, ta cigaba da kukan rashin sanin madafa da mafita. Domin dai ganin abin take tamkar mafarki. Kwarai da gaske Khaleesa ta shiga wani mugun hali a wannan daren, ta rasa abinda ke mata dadi. Har gari ya waye, haka komai na harkar gidan ta na yin sa ne cikin rashin kuzari, wanda Inna Salaha tana lura da ita, sai dai ba tayi mata magana ba. Domin dai ta san dalilin bai wuce maganar aurenta da Alhaji Mustapha, wanda ganinta babu fashi, tunda sun riga sun yanke hakan.

********************* Misalin ƙarfe uku saura kwata. Khaleesa na sharan dakin girki, domin lokacin dora miyar dare ya gabato. Malam Habibu ya shigo da dan hanzarinsa, ya shige falo. Bai dade ba, ya fito rike da tabarma a hannunsa. A daidai lokacin Khaleesa ta fito zubar da shara, ya dakata yana kallonta. Sa'annan yace ''Khaleesa ki je ki kimtsa, ki na da bako''. Kafin ta amsa har ya fice. Ta tsaya shiru gabanta na faduwa, tabbas ta san ba wani bakon daya wuce Alhaji Mustapha ''Hala ba ki ji abinda Malam yace da ke bane? Muryar Inna Salaha ta katse mata tunaninta. Ta juya da sauri, suka hada ido da Inna Salaha. Sa'annan ta juya ta aje abin kwashe sharar, ta shige daki cikin tashin hankali, shin ya zata yi ta iya hada ido da Alhaji Mustapha a matsayin wanda zai zama mijinta? Ta kasa yin komai, tana tsaye bata san iya lokacin da ta dauka a tsaye ba, illa dai ta ji muryar Malam Habibu. Yana bata umarnin ta fito ta je Alhaji Mustapha na jiranta. Hijabinta ta janyo da yake yashe saman katifa, ta zura. Sa'annan ta fito, tsaye ta tadda mahaifan nata a tsakar gida, da alamar duk suna jiran ta fito ne. Tana fitowa, bata yarda ta hada ido da daya a cikinsu ba, ta fice. Zaune kan tabarma, a harabar lungun shigowa bangarensu, ta iske Alhaji Mustapha, yana sanye cikin danyar shadda riga da wando, babu babbar riga, sai hular daya murza kalar shaddarsa. Sai tashin kamshi yake na musamman. Haka zalika gilashin dake manne a saman idonsa ya fito masa da kyawun fuskarsa, wanda hakan zai tabbatar maka da cewa zamanin kuruciyarsa anyi tashen kyau da kwalisa. Tunda Khaleesa ta nufo shi, idanunsa ke kanta tamkar zai hadiyeta. Wanda hakan ya tsananta ma Khaleesa jin kunyarsa. Don haka nesa da shi ta tsaya gami da tsugunawa har kasa ta gaishe shi. Cike da kulawa da kauna, ya amsa mata. Ganin bata da alamar mikewa daga tsugunonta, yasa tace ''Khaleesa tashi ki zauna mana, wannan tsugunon, bai yi daidai dake ba''. Khaleesa ta tashi ta koma can gefe jikin bango ta takure, cike da matsananciyar kunya. Alhaji Mustapha yayi dan gyaran murya gami da kiran sunanta a tausashe. Bata iya amsawa ba, har ya ci gaba da cewa ''Ina bukatar ki daina jin kunyata, domin maganar aure ce a tsakaninmu. Khaleesa babu amfanin na tsaya ina gaya miki irin son da nake miki, domin dai na san ina sonki. Haka zalika na ji dadin irin tarbar da mahaifinki yayi min da kuma albishir din da yayi min na cewa ya bani ke''. A gigice Khaleesa ta dago kanta. Alhaji Mustapha ya ci gaba da cewa ''Sai dai kuma duk da haka ina kwadayin jin ra'ayinki, domin idan ba ki yi na'am da ni ba. Ba zan so na tauye miki hakki ba. Don ni ba karamin yaro bane, na san hakki 'ya'ya, don haka ne kika ce Khaleesa? Cikin shakuwar murya da alhini Khaleesa tace ''Ba ni da abin da zance. Sai abinda mahaifana suka ce. Ban da wani zabi, sai zabinsu. Kamar yadda bani da umarni, sai nasu don haka tunda sun amince, Allah yasa hakan shi ya fi zama alheri''. Maganganun Khaleesa sun burge Alhaji Mustapha. Ya kuma sami zuciyarsa da kara kaunarta, ya kuma kara yabawa da natsuwa da hankalinta. Ya zuba mata ido, hakika yayi dace kwarai da gaske. A hankali ya kira sunanta, yace ''Na ji dadin maganarki, na kuma yi miki alkawarin za ki sameni mai kulawa tare da riritaki fiye da saurayi. Dan kimanin shekara ashirin da shida. Da izinin Ubangiji za ki zamo daya daga cikin matan da su kai dacen miji, domin tunda ina sonki babu abinda ba zan iya yi miki ba''. Ita dai kam! Khaleesa ta rasa bakin magana, tana dai jin yadda Alhaji Mustapha ya gwaggwafe yake raftako mata irin son da yake mata, sai ka ce saurayi daya fara zuwa samartaka. Gaba daya abin mamaki yake bata ko a mafarki bata taɓa zaton faruwar wannan al'amarin ba. Alhaji Mustapha ya dade, inda daga bisani yayi mata sallama, bayan ya bata kyautar kudi har Naira dubu ashirin, amma da kyar ta amsa. Tana shiga cikin gida ta mikawa Malam Habibu kudin da Alhaji Mustapha ya bata. Yana karba, bata saurari komai ba, ta shige dakinta kirjinta na harbawa. Kai tsaye bakin katifarta ta zauna gami da rafka tagumi. Yanzu har an ba Alhaji Mustapha ita? Ti-ki-sa! Ko alama zuciyarta bata tunanin zata amshi Alhaji Mustapha a matsayin miji ba. Tana hango ma kanta rashin dacewa. To amma ya zata yi? Tunda mahaifanta sune suka zaba mata shi. Ita kuma a shirye take da tayi biyayya a garesu akan komai, domin sune ginshikinta. Ta kuma tabbatar da cewa ba zata taba yin da-na-sani ba, tunda biyayya tayi. To amma ya zata yi da alkawarin da tayi ma Faruq na cewa ba zata taba tsayawa da kowane namiji ba, har sai ya dawo ya zaba mata miji? Khaleesa ta numfasa a sakamakon tuna alkawarin dake tsakaninta da Faruq. Ta zame tagumi da tayi a hankali. A yayin da daya zuciyarta ke raya mata cewa. Tabbas! Faruq ba zai ki zabin da iyayenta suka yi mata ba. Ba zai so taki yi musu biyayya ba, kamar kuma yadda yake ikirarin zabin da zai mata alheri ne. Haka nan zai yarda da cewa zabin iyayenta suka yi mata, shi ma alheri ne. Da wannan tunanin ta raba, ta kwana lamau akan katifa, tana maida ajiyar zuciya, gami da addu'ar Allah ya tabbatar mata da duk abinda ya fi zama alheri a rayuwarta. Cikin dan kankanin lokaci maganar auren Khaleesa da Alhaji Mustapha tayi karfi. Domin Malam Habibu ya sakar ma Alhaji Jafar ragamar komai. Wanda jin dadin hakan. Alhaji Jafar ya dauki alkawarin yima Khaleesa komai ta bangaren kayan daki da duk abinda iyaye suke ma yaransu a lokacin aurenta. Haka zalika hatta Hajiya Zulfa bata san bidirin da ake yi ba, illa dai Alhaji Jafar ya gaya mata cewa Khaleesa ta sami miji. Amma bai gaya mata ko waye ba, ita ma kuma bata nemi sanin waye din ba. Alhaji Mustapha kuwa sai rawar jiki yake akan Khaleesa, kullum yana hanyar Kano, ga hidimar da yake mata, bai taba zuwa hannu Rabbana ba. Har wayar tafi gidanka. Ya saya mata, wanda shi yake ciyar mata da wayar. Ya damu da ita kwarai da gask, wanda dalilin hakan ya tilasta ma Khaleesa fara dan sakin jiki da shi. Dama abinda yake so kenan, yake kuma jira, don haka ya bukaci a tsayar masa da ranar daurin aure. ********************

Saura kwana biyu ya tura magabatansa. A daren ranar Alhaji Mustapha ya gama komai na al'adar rayuwarsa Kafin ya kwanta, ya kwanta kenan Hajiya Juwairiyya ta shigo dakin rike da kofin sansanyar Madara, ta maida kofa ta rufe. Sa'annan ta iso gefen gadon fuskarta kunshe da fara'a. Ta mika masa kofin madarar. Alhaji Mustapha ya amsa yana kallonta yana fadin ''Ai na dauka yau ba zan sami madarar ba? Don na ga kin saba lokacin da kike bani''. Tayi murmushi, lokaci daya ta fara cire kayanta, tana maida na bacci tace ''Ni na isa na hana maka madarar, dana san idan ba ka sha ba, babu bacci mai dadi, balle zama lafiya. Ban dade da sa ta a firij din bane, sai dana tsaya ta yi sanyi sosai. Don na san ba ka shanta, sai kaji ta yi sanyi ƙarara! Ya fadada murmushinsa yace ''To godiya nake''. Ta gyada kai tace a yayin da ta haye tsakiyar gado ''Aikina ne wannan, don haka ba sai kayi min godiya ba''. Alhaji Mustapha bai kara magana ba. Har sai daya shanye madararsa tas! Sa'annan ya aje kofin, yana hamdala. Ya kai hannu ya kashe wuta. Sa'annan ya juya ga Hajiya Juwairiyya. Kwarai a wannan daren yake son ya gaya na Hajiya Juwairiyya yana da bukatar kara aure. Domin baya kaunar ya munafinceta. A tausashe ya kira sunanta ''Juwairiyyah! Ta ji dadin muryarsa, ta kuma kara kashe mata jiki. A nauyaye ta amsa, ''Na'am Alhaji, ya aka yi ne? Yayi dan murmushi, sannan ya ce ''Ina bukatar ki tattaro min duk hankalinki da fahimtarki, domin ina da maganar da zan yi dake, mai matukar muhimmanci''. Duk da Hajiya Juwairiyya bata san ko wace magana bace. Sai da ta ji gabanta ya fadi. Da sauri tace ''Ina sauraronka Alhaji, wace irin magana ce? Alhaji Mustapha yayi dan gyaran murya. Sa'annan yace ''Juwairiyya, ki na da kirki, kuma ki na yi min komai, domin jin dadina. Ina kuma yabawa, sai dai ina son ki sani, shi komai nufi ne na Allah. Babu wanda ya isa ya kauce ma abinda Allah ya rubuta masa''. Cikin sanyin jiki Hajiya tace ''Don Allah ka fada abinda kake sun ka gaya min, ka daina yi min kumbiya kumbiya. Menene? Alhaji Mustapha ya dan muskuta, sannan yace ''Tsawon shekara goma sha huɗu kenan da rabuwata da Rasheeda. Ban kuma taba tunanin zan kara yin wani auren ba sai yanzu. Domin a yanzu na sami yarinya budurwa, wacce hankalina ya kwanta da ita. Zan aureta jibi za a sa rana, wanda bana tunanin zai wuce wata daya...........?" Firgigit! Hajiya Juwairiyya tayi gami da zillo, tamkar wacce aka tsira ma allura. Wanda hakan yayi sanadiyyar katse Alhaji Mustapha. Ta yunkura da karfinta ta tashi, lokaci daya ta mika hannunta dake rawa, ta kunna wuta. Nan da nan haske ya wadaci dakin. Idanunta da suke cikin bacin rai da gigita fas! Kan fuskar Alhaji Mustapha, wanda shi ma kallon nata yake yi. Cikin nauyin harshe tace ''Alhaji aure za ka kara, ba ma bazawara ba, Budurwa? Shi ma ya yunkura ya tashi ya zauna yana ci gaba da kallonta, yace ''Juwairiyya, Allah ya haramta min auren budurwa ne? Look! Ki na tunanin nayi manyantar da ba zan iya rike budurwa bane? Tayi masa wani sakaran kallo tace ''Ko ba'ayi da kai ba, ai ka yi da kanka. Kamarka, saboda budurwar zuciya ace za ka auri budurwa? Wallahi ka ji kunya, ka kuma ja ma kanka abin magana. Kuma gareni ban yarda ka auro budurwa ba. Don bana son raini ya shiga tsakanina da ita. Don dai na san ba a haife, na haifeta. Ka cutar dani, ka kuma maidani baya. Don haka idan har auren ya zama maka dole, to ka nemi bazawara ne........ Alhaji Mustapha ya yi murmushi, domin jin yadda Hajiya Juwairiyya ke bashi umarni. Ya ci gaba dan murmushi wanda hakan ya kara matukar tunzura Hajiya Juwairiyya. Yace ''Juwairiyya ba ni da ra'ayin auren bazawara, ko can baya da kika ga na auri Rasheeda, to ƙaddara ce. Amma yanzu budurwa nake da sha'awar aure. Nan da kankanin lokaci". Ta banka tsaki gami da sauka daga kan gadon, tana balla masa harara. A fusace tace "Me ake da namiji, wanda bai san me kyautata masa ba. Me na rage maka, amma ka rasa abinda za ka saka min da shi, sai na auro min budurwa. Da can ba ka auro min budurwar ba sai yanzu saboda ka cuceni, ka dagula min lissafi. To don ka ji, ka kuma sani, ba ni cikin maganar aurenka, ba kuma zaka taba samun hadin kaina ba, aure ko? To Bismillah!

Tana gama fadin haka, ta dau zaninta ta fice da sauri, cikin fada da sababi ta bar dakin. A hankali Alhaji Mustapha ya dauke idonsa akan kofar dakin gami da girgiza kai. Yai zaton zuwa wannan lokaci Hajiya Juwairiyya ta rage mugun kishinta na tsiya, domin ya san bai ji da dadi ba a lokacin daya auri Rasheeda, ba shi ya sami zaman lafiya ba sai da ya rabu da ita. Saboda masifar kishi da rashin zaman lafiya a gidan nasa. Hakan ne kuma yasa bayan ya rabu da ita, gaba daya sai auren ya fita a ransa. Tsawon shekaru goma sha hudu kenan. Sai yanzu Allah ya hada shi da Khaleesa yarinyar da yake jin tamkar ya hadiye, saboda so da kaunar da yake mata. A hankali ya koma ya kwanta gami da kashe wuta, ya ja bargo ya rufa ma kansa, ya shiga kwasar baccinsa lakadan! Kamar yadda yake ta kwasar baccinsa, ita ko Hajiya Juwairiyya tana can dakinta ta kasa runtsawa, ta kuma kasa kwanciya. Tana tsakiyar dakinta, sai ta kai gwauro, ta kai mari. Ta rasa abinda ke mata dadi, zuciyarta sai tafasa take kamar yadda ruwan zafi ke tafasa a saman wuta, komai ya tsaya mata cak! Babu wani abu ma fi dasa bakin ciki da bacin rai, irin ta ji Alhaji Mustapha na maganar kara aure. Ta tuna lokacin da zai auri Rasheeda da take matsayin bazawara ma, hauka ne kawai bata yi ba, sai kuma da ta ga bayanta, ta koreta a gidan sa'annan ta sami sukuni. Bata taɓa tsammanin Alhaji Mustapha zai kara yunkurin kara aure ba. Musamman idan tayi la'akari da yawan shekarun da aka diba bayan auren Rasheeda. Shi yasa ta shantake ta mike kafa abin ta, sai kuma yanzu kwatsam! Ba zato, ba tsammani Alhaji Mustapha zai gaya mata zai kara aure. Auren ma budurwa, wacce ta san tabbas yana ganin budurwa, babu yadda za'ayi ya bi ta kanta tsohuwar hannun. Abin kuma da bata kauna kenan. Ta kuma san tana zuwa za ta fara zazzage mata 'ya'ya, ita ko a duniya bata kaunar ta daga ido ta kalli ko wane Da a cikin gidan, wanda ba nata ba. Ta koma kan gado ta zauna gami da rafka tagumi tana ci gaba da tsiyayar zufa gami da jinjina kai. ''Ya zama dole na dau mataki! Ta fada a fili, gami da cije lebba.

******************

Washe gari cikin matsanancin bakin ciki da tashin hankali Hajiya Juwairiyya ta tashi, haka zalika bala'i kawai take neman Alhaji Mustapha da shi, domin duk abinda ta saba yi masa kafin ya fita, a ranar ba tayi ba. Duk shi yayi ma kansa komai. Magana ta fatar baki ma bata hadasu ba, har ya fice harkokinsa. Wato dai ita mace duk manyantarta, bata tsufa da kishi. Tunda halitta ce, ko wace mace ta dinga nazarin irin kishinta, don wani kishin ba shi da kyan gani, ko dadin ji. Irin nasu Hajiya Juwairiyya kenan! Hajiya Zulfa ta fara nema s waya, tun kafin su gama gaisawa Hajiya Zulfa ta fahimci Hajiya Juwairiyya bata cikin kwanciyar hankali, don haka ta katse gaisuwar ta hanyar yi mata tambaya da ''Ya na ji muryarki na rawa ne, Hajiya lafiya kuwa? Hajiya Juwairiyya ta saki wani nannauyan numfashi, sa'annan tace ''Ba lafiya........ Hajiya ba lafiya....... A gaggauce tace ''Ba lafiya, me ya faru? ''Alhaji ne zai kara aure, budurwa inda yake gaya min ma ba za'a wuce wata daya ba''. Da karfi Hajiya Zulfa tace ''Aure? Budurwa? Hajiya Juwairiyya tace ''Kwarai budurwa, kuma ba zan yarda ba, don wannan ba karamin ci baya bane a gareni''. Hajiya Zulfa ta saki ajiyar zuciya tace ''Lallai kam! Idan ma kika yarda, ai kin so ki mutu da ciwon zuciya ne. Ace dai kamar Alhaji Mustapha zai auri budurwa? Tafdijan! Ko alama ban ji ba, koda a wajen Alhaji. Sai dai na ga Alhajinki yana yawan zuwa Kano. Kenan shirye-shiryensu suke yi. Wa ya sani na ko ni ma har da tawa? Hajiya Juwairiyya tace ''Kila ma a Kanon take? Ko wace shegiya ce kuwa, zata gwammace kida da karatu. Don ba zata iya kishi da ni ba. Zan bata mata rayuwa Wallahi''. Hajiya Zulfa ta kwantar da murya tana tausarta. Amma tuni ta aje wayar, ranta a matukar bace, kai tsaye dakinta ta nufa ta dakko gyalenta da jaka gami da key din motar ta. A fusace ta fita, daidai lokacin da Salamatu ta fito daga dakinta, hannunta na rike da madarar Viju, tana tsotsa. ''Momi, ina zuwa? Ta tambayeta garangatse! Hajiya Juwairiyya tace a yayin da take kokarin fita ''Tudun Wada zan je, amma yanzun nan zan dawo, ki kula da gida, idan kuma tabawa ta zo, ki gaya mata abinda kuke son ku ci, ta girka muku''. Salamatu tace ''To, sai kin dawo''. Hajiya Juwairiyya na fita ka tsaye Kusfa ta nufa a cik…