KALUBALE BOOK 1

Page 1

by @yargidanimam

Kamar yadda zuri'ar sheik sadisu Musa Jigawa suka saba gabatar da taron yan'uwa, duk karshen watanni biyu.yauma asabar wacce ta kama 30 ga watan Yuni. Tun sassafe hadiman gidan suke ta aikin share share da gogen gidan. Babban gida ne ginin da wanda a yanzu aka maida shi gini na zamani, a dalilin tasowar yara da jikokin gidan da masu gidan rana. An kawata shi kwarai da gaske. Tun karfe goma gidan ya fara daukar baki kowa ya zo katon falon da suka saba gabatar da taron suke wucewa, inda tsoho me ran karfe sheik sadisu yake kishingide a kan lallausar dardumar da ta mamaye falon, ya dora hannunsa akan wani kyakkyawan tuntun shima me taushi ne, idanunsa na manne cikin farin gilashin da ke taimakon sa ganin fuskokin ya'yansa da jikokin sa da ya fi so da komai a rayuwarsa.kafin karfe goma sha biyu falon ya cika ya batse kusan gaba ɗaya kowa ya hallara. Muhseen ne har zuwa wannan lokacin bai iso ba.kamar kullum dama shi kadai ne yake zuwa a makare, sai dai kuma komai makarar da yayi , babu yadda za'a yi a fara taron ba tare da ya iso ba. Kasancewar ya sami kyakkyawan goyon baya daga kakanninsa, sheik sadisu da Haj Gwaggo.

Cikin kankanin lokaci jama'ar falon suka fara korafi gami da kunkuni kamar yadda suka saba. Alh Usman mahaifin Muhseen ya ɗan dubi sheik sadisu fuska babu yabo ba fallasa yace "A gaskiya Mallam ya kamata ace zuwa yanzu ka daina ba muhseen irin wannan fifikon, saboda baifi kowa ba, babu dalilin da za'a ce kullum muna matsayin manyan shi amma ace kullum mune masu zaman jiransa maimakon shi ya jira mu, sannan kuma ace ba za'a fara komai ba sai ya zo, kuma ya fi kowa sanin hakan amma bazai canja ba kullum aikin abu daya". Ya karasa magana ya na aje numfashi. Sheik sadisu ya dago ya yi ɗan murmushi.