KALUBALE BOOK 1

Page 2

by @yargidanimam

Kyakkyawan tsoho ne wanda Allah kadai yasan irin kyan da yayi a lokacin kuruciyarsa. Yace "Haba Usman, ya zaka dinga wannan maganar, ka dai san dalilin da yasa nake masa wannan uzurin , ku duk a gari kuke, shi kuwa fa kada ka manta sai ya kwaso hanya sannan zai zo, Kaduna zuwa Jigawa ba karamar tafiya bace, ba zai yuwu ace yadda kuka zo akan lokaci shima ya iso akan lokacin ba". Ya tashi daga kishingidarsa ya zauna sosai, ya cigaba da cewa ba tare da kowa ya katse shi ba, "Ai yana ma kokari da duk taro yake kokarin yakicewa ya taho, duk da tarin aikin dake gabansa da rashin lokaci, ko ya yi kokarin tahowa ranar juma'a babu dama Saboda kullum ranar aiki ce a wajensa to ya kuke son ya yi?, Meye kuma aibun tsayawa a jira zuwansa, musamman yau da duk taron ma a kansa za'a yi shi, ni bana son wannan korafin da na fuskanci kullum bakwa gajiya da yin sa". Alh Usman shuru ya yi bai kara magana ba masu tunanin kuma suma suyi korafin duk sai suka rufe bakinsu, domin dai komai abinsu dole su yarda su kuma amince da cewa muhseen ɗan lelen Mallam ne, baya son laifinsa ya na kuma yi masa son da ya riga ya zama jinin jikinsa. Ba a dauki wani lokaci ba bayan yin wannan maganar , yaran gidan suka shiga ihu gami da ambatan "oyoyo yaya muhseen, sannu da zuwa yaya muhseen ". Sheikh sadisu ya saki murmushi yace "Dan halak gashi nan ya karaso korafi ya huta". Muhseen Usman Jigawa ya karaso cikin gidan cikin cikar kamala da kayatacciyar shigar da ta kara fitowa da asalin kyawunsa da kwarjininsa.fuskarsa fes cike da annuri, kai amma kamar da Muhseen yake da sheik sadisu kusan har tayi yawa, sunyi matukar kama kamar shine ya haife shi, hatta digon tawadar Allah da sheik sadisu yake da ita akasan habarsa shima Muhseen ya na da ita. Kaf tun daga kan ya'yan sheik sadisu zuwa jikokin sa babu wanda yake kama da shi kamar Muhseen. Haj Gwaggo tana jin Muryar muhseen a tsakar gida tayi saurin ta tashi daga kan kujerar falonta ta fita fuska cike da farinciki da jindadi, ta dogare jikin kofa tana murmushi tana fadin "Magajin Mallam ka iso? Ina nan zaune ina addu'ar Allah yasa ka iso lafiya", ya juyo gaba ɗaya cikin fara'a yasa hannu ya rungumo yar tsohuwar matar sheik sadisu jikinsa, yana fadin "zo nan matata na ji kamshin jikinki, na gaya Miki yadda nayi rashin ki, ke kuma wane irin rashina ki kayi?". Cike da so da kauna tace "Magajin Mallam ba ni iya gaya maka irin rashinka da nayi, ka iso lafiya ko? Ya hanya? ". Ya sake ta yace "Hanya Alhamdulillah Haj Gwaggo, mun same ku lafiya?". Ta gyara tsaiwarta tace " lafiya kalau," ta kara kallonsa tace "maza jeka wajen taron kai kadai ake jira, ina jiyo babanka yana korafin rashin zuwanka akan lokaci, don haka idan ka shiga kada kayi musu wannan miskilancin naka ka ba su hakuri , kaji ko?".