Page 3
Yayi murmushi yace "Zanyi yadda kikace Hajiya ta", ya mika mata ledar tufa da duk zuwan duniya sai ya tsaya ya sayo mata saboda sanin tana matukar son tufa ( apple ). Tana karba ya wuce da sauri cikin sassarfa zuwa falon sheik sadisu. Yana shiga falon cikin sallama, idanu suka yo masa caa, sheik sadisu ya mika masa hannunsa yace "zo nan magajin Mallam ka zauna kusa da ni", cikin murmushi ya nufi wajen sheik sadisu duk ya kosa ya rabu da jikinsa, daf da shi ya zauna gami da kama hannunsa. Sheik sadisu Musa yace "Ya hanya?", Cikin kasa da murya yace "hanya lafiya kalau Mallam, ayi min afuwar rashin zuwa akan lokaci, don Allah a cigaba da yi min uzuri". Sheik sadisu Musa ya girgiza kai yace "Babu komai tunda ka iso lafiya komai ya yi dai dai", ya yi murmushi lokaci ɗaya ya juya wajen iyayensa duk ya gaishesu duk sun amsa cikin fara'a Alh Usman ne kawai ya amsa fuska tamke. Babu wani bata lokaci bayan buɗe taro da addu'a daga nan suka fara abinda ya tarasu. Farko anyi maganar bikin ya'yan Alh sani wanda shi ke bi ma mahaifin Muhseen Alh Usman, daganan anyi maganar taimako da za'a haɗa ma babban dan Alh sanin domin ya tsaya da kafafunsa ya kama sana'a, sai maganar ƙara haɗa kai da kuma kaunar juná. Sai magana ta karshe wadda itace karfin haduwar. Sheik sadisu ne ya fara magana yana kokarin kara gyara gilashin idonsa. "Sai maganar magajin Mallam, wacce take damuna , nasan kuma tana damun kowa anan'" ya dan numfasa yana kallon muhseen wanda ya yi kasa da kansa da alama yasan maganar da sheik sadisu Musa zaiyi. Sheik sadisu ya cigaba da cewa " ina da buri ace kafin Allah ya dauki raina naga auren muhseen, idan so samu ne ma har ya'yansa na gani, amma na rasa abinda ke damun muhseen rasa tunaninsa da kullum ake magana ɗaya ya ki maida hankali ya yi abinda ya dace, yaƙi ya gabatar mana da wacce yake so, a zahiri a matsayinsa na babban jikana ya isa ace zuwa yanzu ya'yan sa sunyi girma, ku dubi kannansa Kabir da sadisu duk yaya garesu, amma shi yaƙi na rasa meye damuwarsa, duk abinda ake nema a wajen da namiji kana da shi, haka zalika kana da rufin asirin da har mata hudu zaka iya rikewa ba mace daya ba". Ya kara numfasa fuskarsa tana nuna yadda zuciyarsa take ji agame da abinda bakinsa ke gittawa, " Tun ina yi masa magana ni da shi, yau gashi harta kai nayi magana a gaban kowa, ga ya'yan yan'uwansa nan ko a ciki ai ka samu matar aure, amma babu wannan agabansa, aiki kawai kasa a gaba, to ni dai na kai makura". Ya na yin shuru Alh sani ya amshe maganar yace "Ni kaina ina cikin damuwa akan hakan, domin ba mutuncin mu bane ace ɗan da ya fito daga wannan gida ace ya dauki rayuwar yahudu yasa a ransa , mu zauna da yaro kamar Muhseen babu aure bashi kuma da niyyar yi ( ya waiwaya ya na duban Mallam ), yanzu Mallam ko a gidana yara mata nawa ne marasa aure wanda ko wacce zan iya aura masa yara uku ne kuma duk sun isa aure, me zai hana ya je ya sasanta da ɗaya daga cikinsu su fahimci juna, amma al'amarin nasa ya tasar ma tuke kowa gaskiya". Shima Alh Aminu ya gyara zamansa yana duban muhseen wanda ya sadda kansa kasa yana zaune tamkar ruwa ya ci shi , ko kwakkwaran motsi baiyi domin dai yasan yau tunda sheik sadisu ya fadi damuwarsa a cikin wannan taron to yasan ya kai shi karshe ne, yadda bai son laifinsa baya iya fadan lefinsa a wajen kowa, zuciyarsa ta kara narkewa da rashin jindadi domin ko kadan baya kaunar duk wani abu da zai sosa ran kakan nasa, duk sai yaji ya na neman ya tsani kansa.