Page 4
Alh Aminu yace yana kokarin kara mikar da kafafunsa sosai, "Muhseen babu abinda yake so face ya zubar mana da kima dav mutunci, domin dai namiji kamar sa ya zauna babu aure, kuma baida wani dalili, maka rasa?, Meye tunaninka?, Domin dai karya kake kace ka rasa matar aure , domin babu matar da ba zata so ka zama mijinta ba , ko da ace baka da ko sisi amma ka tsaya ka dage dole sai kayi ma Allah butulci, Allah ya baka tarin ilimin addini da na boko yadda duk ya'yan mu babu wanda ya kamo ko da kafarka, amma duk ya na neman ya tashi a banza, tunda baka aiki da ilimin naka". Ya karasa magana yana sakar ma muhseena harara. Lokaci ɗaya Haj Sa'a ta buntsuro baki gami da karkace kai gefe. Kaf a cikin ya'yan sheik sadisu Musa babu fitinanniya kuma mafadaciya irin Haj Sa'a , ta kara hade rai, tace ""hmmm gata ne kawai ke dawainiya da shi, kunsan ance gata mugun abu, bakwa ganin har yanzu muhseen bai wuce kwanciya akan jikin kakanninsa ba, shashancin banza kawai da lalatar da kai, ai Bai kamata a zauna ana kalla a shi ba, me kake nema a rayuwa wanda baka samu ba, ka dubi irin kyan da Allah ya wadata ka da shi, ga kuɗi ga ilimi , to me kuma kake nema bayan wannan, ko so kake ka karasa tsufa ba tare da kasan inda rayuwarka ta dosa ba, ko da yake ko yanzu meye marabar dambe da fada , Muhseen ka tasan ma shekara arba'in fa tunda dai ka wuce shekara talatin ", ta dawo da kallonta ga mahsifinsu sheik sadisu Musa tace "Ni Mallam ina da wata shawara gaskiya ". Sheik sadisu Musa ya daga mata hannu yace"ki aje shawararki sai a karshen taro". Ta kauda kai rai bace tace iya kunnanta, "eh ka fadi haka mana tunda an tabo dan lelenka". Haj Basira wacce ke durkushe da kanta kasa ta dago tana cigaba da kallon muhseen tace " Muhseen wannan gaba daya ba mutuncin mu bane. Kayi hakuri ka tseratar da gidan nan da ga maganganun mutane, ka daure ka fitar da yarinya ka yi aurenka domin cikar kamala da darajarka, haka zalika kafi kowa sanin irin darajar da gidan nan yake da shi a garin nan ina ganin gare mu ne za'a yi koyi da kyawawan dabi'u, kuma kaima me yi ma wani wa'azi ne saboda ka karanta ka sani , aure sunnar Annabin Rahama ne da yake farinciki da masu yi, ya kuma ce aure sunna tace duk wanda yaki sunnata kuwa baya tare da ni, ya kuma ce kuyi aure ku hayayyafa domin nayi alfahari da ku a ranar tashin kiyama, shin kai baka son ka zama daya daga cikin wadan da Annabi zaiyi alfahari da su, ka sani ka take sani kiri kiri wanda kasan zunubin wanda ya sani da wanda bai sani ba daban ne, haba muhseen ". Zuwa lokacin gaba daya muhseen ji yake kamar ya dora hannu aka ya fasa ihu, saboda damuwa, wadannan maganganun da ake masa sun fi ruwan zafi kona makoshinsa , gaba daya idanunsa sun Kada sunyi jawur.
Tunatarwan Ko kunsan duk wanda ke karanta Ayatul kursiyyu bayan idar da ko wace Sallah ta farillah, marabar mutum da shiga aljanna bai mutu ba ne, amma tabbas in dai ya mutu to aljanna ce makomarsa. Daga bakin da baya karya Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam .
Ku dakace Ni
Daga taskar ✍️
Yar gidan imam. KALUBLE BOOK 1 2009 TSohuwar ajiya daga Habiba Abubakar Imam ( mrs Aliyu mayare )
Bismillahir rahma nirrahim