KALUBALE BOOK 1

page 5

by @yargidanimam

Alh Nasiru daya sarkin zafin irin Haj sa'a ya saki tsaki yace "Babu abinda zai dauka duk maganganun nan da ku kayi masa ba zaisa ya canja da komai ba tunda haka ya zaba Muhseen yakamata ka san abinda kake yl,domin nayi imani miskilancinka na tsiya ke hanaka lalubo yarinyar da kake so. To ba-ka Isa ba, mun gaji, ka yi gaggawar bayyanar mana da yarinyar da kake so." AlhajI Usman mahalfinsa da zantuttukan suka fara tuke masa zuclya, ya dubl Muhseen yace "Abinda kake so kenan, kuma ka samu, kuma duk abinda kaga yafi maka shi zaka yi bana kara bata baki na Aure kada ka yi, ka yi ta zama, tun ana kiranka gwauro, yanzu an fara kiranka da Tuzuru, gaba kuma ba'a san me za'a kiraka ba, ka Je ka yi ,Idan bata mana da kake yi shine burgewarka, to ka cl gaba, babu abinda zance da kal." Kalaman mahalfinsa sun fi kowace kalma tsaya masa a rai tare da kara dasa masa tsananin tashin hankall da bacin ral. Gaba daya gumi ne ke feso masa, duk bayan rigar jikinsa ta jike da ruwan gumi. Hajiya Hallma ta dubi Muhseen, cikin so da kulawa. tana matukar son sa tana ji da shi a ranta sosai. , haka nan jininsu ya hadu tace "Magaljn Malam ka yi hakuri, idan ka na cikin wata matsala ne, ka gaya mana, mune dolenka, mu ne damuwarka ta shafa. Da-na, kada ka manta dul ilimimka, duk kudinka, ba ka da wata daraja. Darajarka daya ce, ita ce aure. Meye abin kyamatar ka a aure? lye! To ina son idan ra'ayinka ne, ka yi hakuri ka'aje shi, idan kuma ba ka sami yarinyar bane, ka zo ka duba a cikin yarana, ki sansu, ka sami daya a cikinsu, idan kuma lokaci ne bai yi ba, to zamu ci-gaba da yi maka addu' ar Allah ya kawo lokacin." Hajiya Sa'a ta dalla mata harara tace "Hajlya Halima kin ji ki da wata irin magana wane irin lokaci ne bal yi ba? Dan Allah ki bar wannan maganai wannan katon mutumin ne, za ki kira masa lokacin auransa bai yi ba , kuma maganar ya je ya duba yayan gidan ki wannan ma duk ba ta taso ba , saboda akwai shirin da na riga na gama yi akan wannan" ya karasa magana tana kara mimmike kafafu cike da isa.

Shi kansa Sheik Sadisu daya taso da maganar, duk sai abln ya dame shi, yadda kowa ke fadin magana akan Magajin nasa tamkar dama suna jiran sa, koda yake babu tamkar, dama jiransa din suke. kowa ya dade da zuwa wuya da shi amma babu wanda ya samu irin wannan damar sai yau domin kowa ya kasa yi masa magana domin shakkar Malam. Amma yau daya gaji, ya fada da bakinsa, shine suka sami hanya.