page 6
Shelk Sadisu ya waiwayi Muhseen, Idanunsa sun yi Jajir! Ya san cikin kowane lokaci, Idanun Muhseen na lya fitar da kwalla, nan da nan ya jI komal ya tsaya masa, a dallin hakan ya dakatar da maganar ya dubi kowa yace "To ya Isa haka nan. Gaba dayanku Ina bukatarku da ku sa Muhseen a cikin addu'arku Allah ya bashi mata ya gari Allah yasa jinkirin alheri ne" Sannan ya dubi Hajiya Sa'a yace 'Sa'a wace irin shawara gareki? Ta gyara kafaffen daurin dan-kwalinta, sannan tace "Malam dama shawara ce kuma umarni ne?" "Wa ki ke ba umarni Sa'a? sheik sadisu ya tambayeta yana kokarin dora idanunsa akan nata , Haj sa'a tayi dan murmushi. Tace "Malam Ina son nace na ba Muhseen umarnin ya je ya daidaita, da 'yar wajena Haneefa ne, tunda Ba zai lya zabowa ba, to ni na ba shi Haneefa Malam, ba na kuma fatan za ku ki goya min baya, domin sanin kanku ne, matukar ba haka muka yi masa ba, ba zai taba yin auren ba, don haka ga Haneefa nan na bashi ita ,kuma ko bai karbeta ba sai dai ya san yadda zaiyi da ita domin ni dai na riga na ba shi ( ta waiga tana kallon mutanen cikin falon ) ko ya kuka gani Yan-uwana."? Kaf! cukin yan'uwan nata babu wanda zai lya ce ma bukatarta a'a, domin suna gudun fadanta, korafi da mitar da kowa ya san halinta ne, hakan ne yasa kowa ya daga kansa, alamar yayi! masu son bashi nasu yayan duk haka suka hakura ba don ransu ya so ba, sai don a zaua lafiya kawai idan ba haka ba sai Haj sa'a ta dauki gaba har karshen rayuwa. Muhseen ko ji yayi gaba daya tashin hankalinsa ya kara karuwa. So yake kawai yaji abinda Sheik zai ce, shi ma kuma gyara kishingidarsa yayi. Yace "Na Ji maganarki Sa'a zan tattauna da Magajin Mallam din domin jin abinda ya yanke domin rayuwar sa ce bamu da ikon karbe masa damarsa" Muhseen ya ji wani sanyi a kirjinsa, gami da lumshe idanunsa a yayin da Hajiya Sa'a ta turbune fuska sam! Ba haka taso ba, ta so kawai Sheik ya karfafa maganar ya kuma tursasa muhseen amincewa tunda shine ke zartar da komai. Babu wanda ya ji ta bakin Muhseen, har Alhajl Aminu ya rufe taron da addu'a.
Muhseen ne ya fara fita da hanzari, duk da Sheik yaso ya dawo da shi. Amma sai ya kyale shi, domin tabbas ya san yanzu Muhseen na cikin bacin rai, yana bukatar ya sami kebewa domin ya lallashi kansa da kansa.