KALUBALE BOOK 1

page 7

by @yargidanimam

Kan kujerun da aka girke a tsakiyar lambun gidan Shelk Sadisu Muhseen ya zabi daya ya zauna, ya dora kafafunsa biyu saman tebur din dake gabansa. Zuciyarsa sai tukuki take, ransa na kara baci, hakika daya san irin tijarar da zai samu kenan, da bai zo wannan taron ba, al'amarin ya dame shi kwarai. Menene laifinsa? Shi komai ai lokaci ne.shi ma ai yana son yayi auren.Amma shi kada i yasan halin da yake ciki. Abba da Nura ne, su ma suka shigo cikin lambun. Nura yasa hannu ya dafa kafadar Muhseen cike da fara'a yace "Babban Yaya, sai hakuri fa idan kace zaka dinga sa damuwa akan irin wadannan abubuwan sai kazo kana samun damuwa ba gaira ba dalili" Muhseen ya dago kansa yana kallonsu, har suka zauna suna fuskantarsa. Nura ya kara cewa "Babban Yaya ni kaina raina bai yi min dadi ba, yadda aka sa ka gaba da tsangwama, shi komai ai lokaci ne, mu da muka yi auran, ai Kannenka ne. Amma da yake lokacinmu yayi, ai mun yi auran. Don haka kada maganganunsu, su dameka, don Allah har kazo kaje kana zaben tumun dare"

Muhseen ya mumfasa, yana kallonsu da lumsassum kyawawan idanunsa yace 'Haba Nura, dole na damu, kada ka manta fa gaba daya idanun dangina na kaina, suna ganin kamar son raina ne, ni ma abin yana damuna kwarai da gaske. Amma ya zan yi? Ya zan yi na nuna masu ni ma ina cikin damuwar hakan." Abba ya dan yi tsaki yace "Dan Allah Babban Yaya, ka sharesu, idan ka yi auran, sune za su zauna maka da matar? Ka rabu da su, ka bi a hankali, ka samo wacce kake so, wacce za ka ji dadin zama da ita." Nura ya dan dube shi yace 'Abba ka manta abinda Goggo Sa'a tace ne? Muhseen ya dago ya dubesu, fuska tamke yace 'Ku bar wannan maganar Nura, ai, duk cikin kannena babu wacce ma ba na jinta a raina irin Hanefa, yarinyar da ko magana ba hadani take da Ita ba, bayan gaisuwa. Ina zan kai Haneefa? Yarinyar da idanunta a bude suke karr! Nura yace "Ka san halin Goggo Sa'a da kafiya, tunda ta furta, to sai dai Allah ya kyauta kawai." Muhseen yayi shiru yana tunanin maganar Nura, wacce ya san gaskiya ce. Tsawon lokaci su Muhseen suna tattauna damuwarsa, kafin Hajiya Goggo ta turo Balarabe kiran Muhseen, gaba dayansu