page 8
suka mike suka nufi cikin gidan. A tsakar gida su Nura suka tsaya suna magana da Hajiya Halima a yayin da Muhseen ya dage labulen falon Hajiya Goggo, ya shiga cikin sallama, tana daga uwardaki, ta kira shi "Magajin Malam, ga-ni a uwardaka". To matas" ya fada yana kokarin shiga uwar dakin lokaci daya kuma kokarin danne bacin ran da yake ciki, ya shiga war dakan, tana zaune a bakin gado. Hajiya Sa'a na kasa zaune dirshan! Haka nan yana ganinta, ya sami faduwar gaba, yayi niyyar kwanciya kan gadon Hajiya Goggo, kamar yadda ya saba, amma dole ya nemi waje kusa da ita ya zauna, saboda ganin lyayen fada da korafi Hajiya Sa'a da yadda ta tsare shi da Idanunta masu cike da rigima. "Ga-ni Hajiya". Cewar Muhseen. Hajiya Goggo ta zura masa ido tana nazarin irin damuwar da ke kwance a saman fuskarsa, sannan tace "Magana ce Goggonka Sa'a ta zo da ita, kamar yadda tace tayi maganar a gaban kowa, shine ni ma ta zo tayi min, ta kuma bukaci na kiraka domin mu yi maganar, kafin ta tafi gida .wato maganar Haneefa." Nan da nan Muhseen ya ji ransa ya hade, yayi baki miskilallun Idanunsa ya sa ma Hajiya Goggo, wanda ya tilasta mata yin shiru, sannan yace "Hajiya na zo garin nan, ban huta ba, ban sha ruwa, ba ban ci abinci ba, ban yi wanka ba, balle uwa uba kintsa kaina, an sani a gaba da fada. Ban gama gyagijewa ba, kuma kin kirani za ki yi min maganar da take bukatar natsuwa. Haba don Allah, ku bari na natsu mana". Yana gama fadin hakan ya tashi tsam! Ya fice Haliya Sa'a na sababi wanda sababin nata bai sa ya dawo ba. Don haka ta juya kan Hajiya Goggo "Na rantse hajiya ku ne kuke daure ma dan nan gindi, ku ne kuke sa baya ganin kowa da gashi, to shi kenan. Ni dai na gama Magana, na ba shi Haneefa, babu kuma yadda za'ayi yace ba zai karbeta ba. Don ba ido za asa masa ba." Hajiya Goggo ta dubeta tace 'Sa'a ki bi komai a hankali bana son halin nan naki na wutar ciki ai ta bakinsa ne maganar tana bukatar natsuwa". Ta yunkura ta tashi ta yafa gyalenta, tace To shi kenan, na bi a hankali, ni zan tafi gida. Haneefa kuma na nan zuwa, ba za ta dawo gida ba, sai Muhseen ya koma, kuma saboda shi za ta zo gidan." hajiya Goggo ba tace mata komai ba, har ta fice daga dakin, tana kunkuni. ko kun san fadin' bismillahil lazi la yadurru ma asmihi shai'un fil ardi wala fissama'i wa huwal sami'ul aleem. sau uku da safe da sau uku da yamma Allah zai tsare ka ya kuma kare ka babu me iya cutar da kai .
ku dakace ni
daga taskar ✍️
yar gidan imam.
 KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere)
Bismillahir Rahma Nirrahim