KALUBALE BOOK 1

Page 9

by @yargidanimam

Muhseen na fita, dakinsa ya nufa cikin sassarfa, yana zuwa kofar dakin ya sa hannu a aljihunsa ya fito da makulli ya bude,ya shiga . katon falo ne da dakin barci guda daya, babu hoton kowa a falon, sal hoton Sheik Sadisu da matarsa Hajiya Goggo. Dukkan su cikin fara’a suke a hoton. kujerun falon sun y matukar hadurwa. Dakin tsaf yake yasha gyara kasancewar duk lokacin da zai dawo ,Haj Gwaggo takan sa a share ko’ina a kuma gyara .Yana shiga firij ya nufa, ya bude ya dauko robar ruwan Eva, ya bincine murfin, yasa bakin robar a bakinsa, bai cireta ba sal da ya shanye ruwan ciki tass! Sannan yay wurgi da robar ruwan tsaklyar falon, idanunsa sun kada sun yi jajir. Yana huci gami da dafe gyefen kansa da ya ke sarawa yana fadin .

"Ba su san damuwata ba, basu san hakun da nake ciki ba mutuncinsu kawal suke son na kare." Ya fada kan kujera, ya lumshe Idanunsa, haka nan ya Ji wasu irin zafafan hawaye na malala masa , a fili yake fadin "Ni ma ai ina son na yi auran." Ya fada yana cije lebba daga bisani ya yunkura ya tashi, ya shiga dakinsa ya cire kayansa, ya maida doguwar riga fara sol Me santsl, sannan ya fito falo ya kwanta a doginwar kujera. Ya rufe idonsa rufl Bai dade da kwanclya ba. Hajlya Goggo ta shigo da katon tire a hannunta har ta zauna, ta bude Cooler na abincin, ta zuba masa a faranti, ta tsiyaya masa fura a kofi, ta bude masa lemon (Five alive), amma har zuwa lokacin Muhseen bai bude idanunsa ba, a hankall ta kira sunansa "Magajin Malam". Ko motsi bai yi ba, balle ya bude Idanunsa. Ta matso kusa da shi, ta dora hannunta a saman kyakkyawar sumar kansa tace 'Na san idonka blyu, ba na son ka yi fushi da ni, bude idanunka ka tashi ka ci abincl, mu yi magana kasan dai idan akwai abinda na tsana bai wuce damuwarka ba, ka tashi ka ci abinci ka natsu muyi magana kaji ko”.

A hankali ya bude idonsa, yana kallonta, sosai ta kara jin komai ya dagule mata ta ji babu dadi a ranta , da ta ga idanunsa cike da kwalla tace "Kuka kake yi? Me yasa haka? Ka na neman tashin hankalina ne? Ya girgiza kal "A'a Hajiya". Tace "To kada ka sake, na ga hawayenka a kasa, tashi ka Ci abinci ka mallaki natsuwarka don Allah ." "Ya yunkura ya tashi, ta mika masa farantin abincin. Ya yamutsa fuska gami da girgiza kal yace "Furar kawal zan sha". Ba tare da musu ba, ta maida farantin ta'aje, ta dauko kofin furar ta mika masa. Yasa hannu ya amsa, haka yake sha kamar yana shan magani saboda dacin da bakinsa yake masa bayan ya gama sha, Hajiya Gwaggo ta kwashe kofunan ta maida saman farantin, sannan ta turesu gefe, ta juyo ta zubama dan likan nata idanu, bakinta yana dauke da maganganu amma tasan dole ta bishi a hankali domin dai yau tasha alwashin sai ta ji damuwa da matsalarsa a game da aure wanda da anyi masa magana yake fadawa wani irin hali.